Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   41 / 80

120K to 123K   out of 238.5K words

mun magiya da nayi haquri na saurare shi amma nayi masa banza haka ya
qaraci nacinsa ya fita ya bar mun dakin.

Haka muka ci gaba da rayuwa a gidan tsakanina da Bashir daga kallo se harara shi
kuma kullum yana nan a lalace gurin roqona da bani haquri amma nayi kunnen uwar
shegu dashi dukda qasan raina na fara hucewa bafa wai dan na manta da abinda yayi
mun ba Aa sedai kawai na yarda cewa komai muqaddari ne a rayuwa daman tun a lauhul
mahfuz an rubuta faruwar wannan al’amari a rayuwar mu.

Kusan sati biyu ranar ya same ni da batun komawa Lagos saboda hutun daya dauka ya
qare, a lokacin bani da zabi kodan aikina da makarantar yara da suke zaune a gida
ya kamata na koma sannan hakan ze dada nisan tani da Amirah dukda ko a yanzun ma
tun ranar farkon suka shigo bamu sake haduwa ba. Haka muka fara shirye shiryen
tafiya, ana i gobe zamu tafi ban san meya shigar da Ahmad bangaren ta ba se kukan
sa muka jiyo a waje Amna ta tafi da gudu ta dakko shi ina duba fuskar yaro naga
shatin yatsu da alamar marinsa akayi.

Cikin tsananin bacin rai na tambayeshi waya mare shi, yana kuka da maganar sa da
bata gama fita ba yace “Anty Amirah ce, da safe Abbi ya nuna masa gurin yace tana
ciki shine yaje suyi wasa (Sun saba tana wasa dasu) saboda na zubar da Tea ban sani
ba ta mare ni”.

Zan dauki komai amma banda taba mun yara musamman ma ya zamana da cin zali amma
tayi kadan dana taka gurinta nayi mata kashe di dan haka zan jira wanda ya ajiyeta
yazo shine daidai yina. Da yamma Bashir ya dawo, yana shigowa Ahmad din ya tafi
gurinsa da gudu ya fashe da sabon kuka yana gaya masa abinda ya faru.

“Ka ja mata kunne karta kuskura ta sake taba mun yara idan ba haka ba zan dauki
mataki” na fada ba tareda na kalle shi ba. Se ya juya da Ahmad din a hannunsa suka
fita ban san me yace mata ba dab da magriba dan har nayi alwala naji ana buga qofa.

Farida nacewa taje ta bude, tana budewa kuwa ta turo qofar da qarfi dan qiris ya
tage ta buge Faridan, seda ta qaraso tsakiyar Palour ta wani tsaya ta kama qugu
tace “Saboda munafunci shine za’a hadani da Mijina dan na daki yaro, ai barna yayi
mun kuma ko yanzu wani ya sake zuwa yayi mun wani abu se na daka yaro sedai duk
abinda za’ayi ayi, mtsw aikin banza kawai...” ban bari ta kai qarshen rashin kunyar
tata ba na kai mata wani bahagon mari cikin sa’a na sameta dakyau na doke bakin
fitsarar take kuwa leben ta ya fashe kafin ta gama gane abinda ya faru na sake kai
mata wani ta dama ta fasa qara ta dafe kunci dama da hagu tana ihu daidai lokacin
Bashir ya shigo.

Ban damu da shigowarsa ba ko ihun da takeyi na nunata nace “wannan gargadi nayi
miki duk ranar da kika sake tako qafar ki gurin nan ki qaddara ma gaisuwa ce ta
kawoki ba wai kinzo yimun fitsara da rashin kunya ba wallahi se nayi miki dukan da
zaki kasa tashi, wawiya mata hankali kawai” na juya na haye sama Bashit yabi bayana
muka barta a gurin tana zunduma ihu.

“Ma’u meya faru” ya fada bayan daya tarar dani”
“Kaja mata kunne tafi kowa sanin ni ha sa’arta bace idan tana ji da rashin kunya da
fitsararta ni daidai nake da ita zan koya mata hankalin da bata dashi” na juya na
tayar da sallah ta na barshi a tsaye.

Washe garin ranar muka koma Lagos, Sanda muka je na tarar Bashir ya sake gyara mana
palour an chanza komai na ciki, sannan ga sabuwar mota me kyau model din shekarar a
ajiye a inda nake saka mota ta, lambar jikin tsohuwar tawa dana gani a jiki ya
tabbatar mun da tawa ce.

Haka ya ringa yi mun abubuwa har makaranta ya chanzawa yara ya mayar da su wata da
tun farko naso a saka su yace tayi tsada abubuwa dai kala kala wanda duk na neman
shiri ne, daga qarshe dai bayan dogon jan rai da ban haquri dana sha kala kala daga
gurin Bashir na haqura na sakko muka dawo zaman mu lafiya badan na manta abinda
yayi mun ba sedan ban isa na jada hukuncin Allah ba.

Iya horon da zan yi masa nayi ya kuma sauke kai ya bani haquri da tarin
alqawarurruka kala kala Albarkacin son da nake masa da dattijantakar mahaifinsa ga
kuma Alfarmar Mahaifiyata daya shiga na cire komai daga zuciyata ta na nemi muqulli
na kulle wancan baqin littafin na rayuwar mu muka bude sabon babin rayuwa me cike
da qauna da Aminci, haka rayuwa taci gaba da gara mana yau fari gobe baqi har kawo
wannan lokacin da me afkuwa ta afku, Bashir ya yanke igiyoyin auran mu a lokacin
dana gama ammana da bashi rayuwata.

CiGaBaN LaBaRi

Afuwan Uzuri ya riqeni kuyi manaji da wannan 🙏🙏


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 40

CiGaBaN LaBaRi
Sosai kaina ya dauki ciwo har ina jin kamar jiri ne yake dibana daga zaunen se
kawai na sulale akan abin sallar na kwanta tareda duqunqune jikina cikin hijabi,
Hawaye ne ya silalo daga idona nasa gefen hijabin na share tareda jan majina.

Ina sha Allahu na gama kuka akan Bashir, tun a baya ya kamata na fuskanci cewar ba
nice a gabansa ba ya aureni ne saboda wata buqata ta qashin kansa amma na ringa
yaudarar kaina da cewa Bashir yana sona.

“Bashir na sonki Ma’u akwai dai wani Al’amari daya tilasta faruwar hakan amma
Bashir baze sake ki yana cikin hayyacinsa ba” bangaren zuciyata wanda ya bawa
Bashir Amanna dari bisa dari ya raya mun, se naji kamar sauran bangaren na zuciyar
tawa sun karbi wannan batu, girgiza kaina nayi a fili nace

“Ina baze yuwu ba, ban kai wannan lalacewar ba, Bashir ko kaine Autan maza in Allah
ya yarda na gama aure da kai, ko son ka ze kashe ni sedai na mutu da na sake zama
dakai” se kuma na Fashe da kukan dan kasa dakatar da kaina.

“Mami kiyi haquri ki dena kuka” Amna da bansan lokacin data farka ba ta fada tana
dafani, sena tashi zaune na janyota jikina na rungumeta na sake fashewa da wani
kukan na gaske dan daman ina da buqatar wanda ze rungumeni nayi kukan. Seda nayi me
isata kafin na rarrashi kaina zuwa sannan itama kukan takeyi.

Na tashi dakyar ta kamani na shiga bandaki nayi fitsari tareda sake aabuwar Alwala
kafin na fito ta shimfida mun bargo akan inda na tashi dan nace bazan hau gado ba.

Ni kadai na ringa juyi a qasan dan ko kusa bacci beyi alamar daukata a daren ba ga
wani ciwon mara dayake taso mun idan ya murda se ya lafa nasan baze rasa nasaba da
halinda nake ciki ba shima dan cikina yana tayani baqin ciki.

Da safe qarfe shida Anty ta kirani akan Aliyu da Jafar suje su karbo musu abin
karyawa, qarfe bakwai da yan mintina sun gama shirin su tsaf na tafiya makaranta na
dakko muqullin mota na bawa Aliyu kenan dan Antyn ce zata kaisu muka ji ana dannan
Door bell,

“Kuje maza inaga ga Antyn can karku makara” na fada da kyar dan dauriya kawai
nakeyi ni kadan nasan abinda nake ji a jikina dama zuciyata gaba daya. Suna fita
Amna data tafi rakasu ta dawo da sauri tace mun
“Mami Abbine” dukda yana yin danake ciki haka na miqe a fusace nabi bayanta in ga
dalilin daya kawo shi, kafin na fita har yaran sun gama shiga mota banda Aliyu daya
kafe daga qofar gida na tarar uban yana cewa “bazaka zo ka shiga mu tafi ba kana
bata mana lokaci”

“Ni ku tafi kawai bazan je tareda kai ba” Aliyun ya fada kai tsaye ba tareda ya
kalle shi ba, Bashir ze sake magana nayi saurin katse shi da cewa “sauke mun yara
malam waya nemi taimakonka bare kace zaka kai min su makaranta, ke Farida ku fito
ga Anty nan zata kaiku” daidai sannan Anty ta qaraso gurin.

Ko kallon inda nake Bashir beyi ba sema fada daya balbale Aliyu dashi akan yazo su
tafi amma yaron nan ko gezau yana tsaye, a fusace ya nufo shi da niyyar ya jashi
nayi saurin shiga tsakiyar su, zanyi magana Anty tace mun
“Ya isa Asma’u ku dena haka a gaban yara, kai Aliyu wuce ku tafi ke kuma muje
ciki”.

Kallona Aliyu yayi, cikeda takaicin abinda Antyn tayi mun na daga masa kai alamar
yaje Bashir yayi kwafa ya shiga motar shima yaja suka tafi kafin Anty ta kama
hannuna muka shiga gidan.

“Haba Anty me yasa zakiyi mun haka akan wanne dalili zan bashi yarana ya kaimun su
makaranta”

“Asma’u kenan, ke Bashir ya saka amma na fiki jin takaicin abinda ya faru. Yara
kuma karki manta fa yayansa ne babu yanda za’ayi ki rabashi dasu baya ga haka yanzu
nema zaki sakar masa nauyin su dan wallahi daidai da gishirin da zaki zuba musu a
abinci daga yau se Bashir ya siya. Duk wani abu da Uba zeyiwa Yayansa dole ki bar
masa yayi musu yanzu taimakon da kikayi masa a da saboda kina matarsa ne yanzu kuwa
bazaki ci gaba da kular masa da Yara ba tunda ya sake ki.

Yanzu ki tashi kije kiyi wanka bari na koma na dakko miki naki abincin toh kici se
muje Asibiti bakiga yanda kika zabge a dare daya ba dan Allah ki saki zuciyarki
Asma’u abinda ya faru ya rigada ya faru sedai mu kiyaye faruwar na gaba kuma”.

Haka ta fita ta barni, na miqe nima duk zuciyata babu dadi na shiga wankan, sanda
na cire pant din jikina naga kamar jini jini a jiki daman tun dazu naji kamar zubar
abu daga jikina amma ban mayar da hankali ba, haka nayi wankan na fito a sanyaye.

Doguwar riga na saka na zumbula hijabi kamar me takaba, ko turare ban iya sawa
jikina ba na dawo palour na zauna shiru ina jin marata na mintsinina na hada kai da
guiwa kai baka ce nice Ma’un nan yar kwalliya da kyale kyale ba.

Tare suka dawo gidan da Baba, be zauna ba daga tsaye yayi mun sannu ya sake yi mun
gajeriyar nasiha ya wuce gurin aiki bayan ta raka shi ta dawo ina nan na rafka uban
tagumi.

Se da Anty ta takuramun kafin na iya shan shayi ina kurbarsa kamar madaci haka nake
jin sa a bakina, duk sona da dankali gashi yana tururi har wata hanta ta gasa mun
se qamshi suke yi amma yau banji sun burge ni ba bare naci se faman bani baki
takeyi nidai jin ta kawai nake amma hankali na yayi nisa da inda muke.

Sallamar Yaya Abubakar ce ta dawo dani hayyacina. Cikin mutuntaka suka gaisa da
Anty Halima yana ta yi mata godiyar yanda take kulawa dani tace babu komai ai ani
qanwarta ce.

“Ma’u yaya babu dai wata matsala ko” ya fada bayan dana gaishe shi, sena ajiye
kofin hannuna nace

“Babu komai Yaya amma fa shi ya tafi da yaran makaranta, nifa Yaya ka gaya masa
babu ruwansa da yarana kawai ya fita a sabgar su”.

“To in banda abinki Asma’u an taba raba yara da ubansu ne Bashir fa kin rigada kun
hadu dashi babu ta yanda za’ayi ki raba. Maganar kuma ya dena shiga sabgarsu ai
bata taso ba dan yanzu nema ze shiga lamarinsu sosai, and ki sani in har kika nuna
masa qulafucinki akan yaran nan da wannan damar zeyi amfani ya ci gaba da quntata
miki idan kuma ba kin shirya komawa masa kici gaba da karbar wulaqanci ba shine
seki dage kuyita rigima akan yaran dan haka tun wuri ki cire maganar yara a ranki,
ko dauka dake ko babu ke zasu rayu kuma babu abinda ze same su se wanda Allah ya
qaddara

“Abunda nake gaya mata kenan nima ta cire wani zacen yara a ranta tunda ma gaki
gasu ko ya karbe su fa kamar kuna gida daya ne dan be isa yace ze kullesu ya hanasu
zuwa gurinki ba haka kema idan a hannunki suke bazaki hanasu zuwa gurinsa ba.

Ni nan da kika ganni ai kin sani tawa uwar tun ina shekara uku ta fita daga gidan
mu ta barni ina watangaririya a tsakar gida tsakanin matan uba babu takamaiman
mariqiya sannan Babanmu ma bame jan yara a jiki bane bare na samu gatansa uwa ta
kuma tayi mun nisa a lokacin Maradi ta tafi tayi aure seda na girma na mallaki
hankalina sannan na je inda take amma ba gani ba ban mutu ba babu kuma abinda ya
same ni, dan haka ki share komai Ma’u ki bi yaranki da Addu’a ko a hannunki ko a
hannun ubansu Allah ya kula miki dasu”.

Haka suka hadu sukayi ta yi nidai jin su nakeyi amma bana zaton akwai abinda za’a
fadamun da zesa na barwa Bashir yarana, saki dai na saku amma fa dole abarmin riqon
yarana koda kuwa ze sakar mun nauyin su gaba daya zan dauka zanci gaba da kulawa
dasu.

Wayata dana bari a daki Amna ta kawo mun ana kira, Yaya Bilki ce na daga wayar na
saka a kunnena.

“Asma’u abinda ya faru kenan? Yanzu Anty Suhaima ta kirani take gayamun amma
wallahi Bashir ya cika butulu wanda besan halacci ba” ta fada cikin sanyinta, se
nayi murmushi kawai nace “hmm” dan ban san abinda zan ce mata ba.

“Amma Goggo bata sani ba, Alhaji Qarami yace kar a gaya mata ze kirata da kansa
saboda kin san yanayin jikinta yanzu be kamata a gaya mata abin tashin hankali ba”
ta sake fada, daga nan mukayi sallama tana sake jaddada mun da nayi haquri.

“Ki tashi yanzu ki samu ki kwanta dan da ganin fuskarki bakiyi bacci ba, nima zanje
yanzu yau zan qarasa aikin da nazoyi zuwa dare zan dawo In sha Allah” Yaya Abubakar
ya fada yana miqewa yayi mana sallama ya tafi.

Mintina kadan Anty tace itama bari taje gida ta dan kintsa guri kafin masu daura
gadon su dawo a gyara dayan dakin, sena miqe ina cewa “Bari na kwanta a nan toh,
Amanah zoki kwashe kayan nan ki saka su a Kitchen” na nufi kujera da niyyar
kwanciya Antyn tayi saurin dakatar dani tana cewa

“Tsaya Asma’u karki zauna kinyi staining”.

Da sauri na juyo da hijabin jikina na duba, se kuwa ga Jini nan sosai a jiki da
yake ruwan qasa ne me haske gabana ya yanke ya fadi dan ba period bane sedai idan
cikin jikinane yake zuba, yanda taga rikice ne ya sakata cewa

“Lafiya Koda matsala ne?”

“Akwai matsala Anty muje Asibiti dan Allah kafin cikin ya samu matsala”.

“Ciki kuma daman ciki ne dake” Anty ta fada cikin mamaki, ban Amsa taba na wuce
daki na canza riga da hijabin jikina muka fita.

Clinic din da yake cikin estate din mu mukaje dan gani nakeyi kafin mu kai
Asibitinda nake zuwa ai cikin ma ya gama zirarewa. Muna zuwa suka dauki jinina
kafin Likita yace na kwanta yayi mun scanning, “incomplete abortion” yace, ina ji
ina gani suka sakamun wata kwaya, ban wani ji ciwo sosai ba saboda cikin qaramine
sosai cikin dan lokaci abinda yayi saura ya fita akayi mun allurai suka bani
magunguna muka wuce gida.

Banji dadi ba dan dagaske na kwallafa rai akan cikin nan, Amma na fawwalawa Allah
dan shi kadai yasan dalilin yankewar igiyar aurena da Bashir a jiya sannan ya
taqaitamun iddarsa a kwana daya kacal, Allah yasa hakan ya zama Alkahiri a rayuwar
mu gaba daya.

Haka na wuni ranar jikin quncin zuciya musamman da abin ya zamar mun duka biyu,
Qarfe hudu motar makaranta ta kawo yara kafin sannan har An dakko gadajen su Aliyu
Anty ta gyara musu dakin, kayan su da ba’a gama jerawa ba jiya suna qarasa komai
ita da Amna nidai ina kwance a daki ina ta faman tunane tunanen makomata tunda dai
yanzu na tabbatar da aure tsakanina da bashir ya qare ko a gobe ina iya daura sabon
aure.

BASHIR
Bacci ya kwasa sosai tamkar babu wani abu daya faru, qarfe biyar na asuba ya farka,
ganin babu Ma’u a gefe yasa ya zauna yana jiran ta fito daga bandaki shima ya shiga
yayi Alwala dan an kusan shiga sallah, seda ya shafe kusan minti goma a zaune jin
shirun yayi yawa yasa ya miqe ya kwankwasa qofar yana cewa

“Wai me kike tayi ne har yanzu baki fito ba so kike sena makara ko..” yai shiru
ganin qofar ta bude amma babu kowa a ciki, tsaki yayi ya shiga ya dauro Alwala ya
fito, se daya kunna fitila yaga yanayin da dakin yake ciki sannan kwakwalwarsa ta
tariyo masa abinda ya faru jiya.

Idan yace beji komai ba yayi qarya, haka ya zura jallabiyya ya kama hanyar
masallaci shi kadai duk se yaji wani iri dan ya saba tareda Aliyu Jafar da Abdallah
suke zuwa.
Haka ya dawo gida ya zauna a palour ya dafe kansa, yana so ya ga rashin kyautawar
abinda yayi amma zuciyar data ingizashi tayi qoqari ta kare komai ta yanda laifin
Ma’u yake ci gaba da gani har yanzu.

“Wai ma me tayi mun ne?” Ya tambayi kansa, bashi da me bashi amsa ga guilty
consciousness (na manta fassarar da hausa 😂) yana neman kama shi se kawai ya miqe
ya shiga wanka dan baya so ya bawa zuciyarsa wata dama da zata sa ya zargi kansa da
laifi(Yawwa na tuna 😂), haka yayi wanka ya shirya yana ta tsaki, ga kayan duk a
watse haka ya tsinto wadanda ze saka ya shirya ya sake fitowa palour, babu abinci
haka ze riqe yunwarsa idan yaje office yaci gashi daren jiyan ma ba wani abin kirki
yaci ba.

Bayan ya dauki yaran suna tafe a zuciyarsa yana ayyana da sun dawo dole su koma
gidansu, kwana daya kenan ta fara saka musu wani abu a zuciyar su a kansa inga ya
barcmata su qilan wata rana suce ma ba shine ubansu ba, haka ya sauke su a
makaranta ya wuce office, seda ya fara tsayawa Cafeteria ya siyi abinciya zauna ze
fara ci kenan Amirah ta kirashi dan yanzu kira sau ukun nan rana safe dare setayi
masa sun gaisa.

“Ina cin abinci idan na gama zan kiraki” ya fada bayan da suka gaisa.

“Kai amma yau ka makara har yanzu baka fita ba takwas ta wuce fa ko hutun naku be
qare ba?”ta fada da mamkin jin wai abinci ma yake ci yanzu,

“No ina office, acan nake karyawa yau” ya fada kafin ya kashe wayar, yasan yanzu ci
gaba zatayi dayi masa tambayoyi. Ilai kuwa yana hanyar shiga office dinsa bayan ya
gama cin abincin ta sake kira, kamar ma baze daga ba amma daya tuna yana so ya gaya
mata ta shirya idan so samu zuwa jibi zata taho seya daga wayar bayan daya zauna
akan kujerar sa.

“Ya akayi Yau Anty ta barka kaje cin abinci a office kuma ko bata nan?” Ta fada da
son jin gulma. Ba amsa mata ba yace

“Ki fara shiri zuwa jibi zaki taho nan”.

A bazata abin yazo

41 / 80