Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   74 / 80

219K to 222K   out of 238.5K words

ya dauro dan an kira sallar Magriba, seda ya saka jallabiyya a
jikinsa kafin ya dauki wayar har ze zura a Aljihu yaga saqo akai daga lambar Balan,
tsaki yaja ya fita daga dakin yana qoqarin goge saqon dan idan ma haquri yake bashi
yayi ta banza dan shi dashi dai har Abada, har ya iya kallon fuskarsa yace idan da
matar daya rabu da ita zata yarda daya aureta a matsayinsa na Amininsa ai wallahi
in ba muqullin Aljanna bane a hannun Bala baya sake kula shi ba shima sedai idan
shi kadai yake rabawa sannan.

Iqamar da yaji an tayar ta saka shi jefa wayar a Aljihu ba tareda ya goge saqon ba
ya qara saurin tafiyarsa, a masallacin suka hadu dasu Aliyu, kallo daya yayi masa
ya sunkuyar da kai shima be tsawwalla ba yana kallo suka fice daga masallacin dukda
yana son magana da Aliyun, dole su chanza wani plan din tunda wannan ya rushe dan
baze fa zuba ido yana ji yana gani ya rasa Ma'u ba.

Seda yayi sallar Isha kafin ya kamo hanyar gida, kiran sa akayi daga gidan
abincinda yayo musu order ya daga ya qara yi musu kwantance yana kashewa saqon
Bala daya bude dazu be kai ga gogewa ba ya dawo kan wayar.

"Ina tayaka baqin cikin yin wuf da tsohuwar matarka da akayi, gaskiya Bashir ka
cika mara sa'a tunda har ka rasa mace Irin Asma'u"
Abinda aka rubuta a saqon kenan.

Wani tsaki yaja kamar ze tsinka harshensa ya goge saqon, ransa a bala'in ya shiga
magana kamar wani sabon kamu yana cewa
"Wallahi Bala gamo na da kai baze yi kyau ba, saboda bala'i bazaka fita daga sabga
ta ba ko shikenan Allah ya hadamu zaka maimaita abinda ka rubuta yanzu, nida Ma'u
kuwa mutu ka raba sedai baqin ciki ya kashe duk me yinsa"

Ko gani dakyau baya yi ya haye kan step din qofar gidan sam be lura da Anty dake
tsaye kamar wadda aka bawa aiki ba seda ta kira sunansa.

A dan firgice ya juya ya kalleta, fuskar ta a washe tana Murmushi me kama da dariya
babu wannan hararar da take masa duk sanda suka hadu kamar zata rufe shi da duka
tace

"Ai daga ciki nake ai aka ce baka nan ka tafi masallaci shiyasa nace bari na jira a
nan karka dawo banga wucewarka ba".

Tsayuwarsa ya gyara ba tareda yayi magana ba yana jiran jin dame tazo kuma dan
wannan murmushin nata toh Allah yasa dai ya zama Alkahiri

"Se mukaji Abin Arziqi a bazata, koda yake be zama lallai ya iso maka ba tunda muma
duk yanzu saqon ya same mu kaga abin Allah daga zuwa tambayar auran Ma'u se kawai
iyaye sukace a daura ayi duk wasu shiri daga baya, To me za'a jira abu ba auran
budurwa ba Allah na tuba an daura aure dai akan sadaki me daraja bana tunanin ko
auranta na fari ma tayi tsadar haka, kai gaskiya Ma'u tayi Goshi".

Yanda take maganar seka rantse da Allah wata qawarsu take bawa labari ko irin
shaqiqin Ma'u da ze yi matuqar farin ciki da jin labarin, ta gama tsaf ta juya tana
cewa

"Bari naje nima nayi sallar, kaini farin ciki yau ban ma san inda zan nufa ba
wallahi Allah kenan wani ya qika da wuni wani da shekaru ze soka, gashi ta fito
daga inda ba'a san darajarta ba ta shiga inda suke mararin samunta sema kaga yanda
akace yan uwansa nata murna wallahi".

"Hasbunallahu wani'imal wakeel, La'ilaha'iah anta subhanaka inni kuntu
minazzalimin" Bashir ya fada yana kaiwa qasa saboda yanda yaji qafafunsa sun gaza
daukar sa gaba daya, kamar me ciwon Asthma haka numfashinsa ya shiga sarqe wa,
qoqari yake ya bude baki ya dakatar da ita amma ya kasa harta bude gidan ta ta
shige tana ci gaba da dariyarta.
"Ina tayaka baqin cikin Wuf da akayi da tsohuwar matar ka" saqon Bala ya dawo masa
a qwaqwalwa. Dagaske Ma'u ta daura aure da wani ko kuwa da Bala da Anty wasa suke
so suyi masa da hankali amma ai babu wanda yasan wani a cikin su ballantana su
shirya yi masa yawo da tunani ai.

Hannunsa daya masa nauyi ya daga yana so ya zaro wayarsa amma ya kasa. To wama ze
kira ya tabbatar da gaskiya ko qaryar maganar a yanzu?
Amma ai yafi kusa da Ma'un, a gurinta ya kamata ya samu tabbaci na koma menene.

Cikin azama ya yunqura ya miqe kamar bashi ne ya fadi qasa yanzu ya gaza tashi ba
se gashi a kan qafafunsa cikin sassarfa ya isa qofar gidan Ma'u ya shiga bugawa
kamar wanda yazo karbar Bashi.

Abdallah ne yazo ya bude masa, kafin yayi magana ya shige ciki ya fara kwada kiran
Ma'u yana wulga ido cikin gidan yaga ta inda zata bullo.

ASMA'U

Suman wucin gadi nayi a zaune har Anty ta fice ta barni bana tsammanin ko numfashi
ina shaqa a lokacin. Qarar wayata ce tasa na gane a raye nake amma sam bani da
qarfin da zan dauketa dan kwayar idona kadai na iya juyawa na kalli wayar na sake
maida ita na zurawa qofa ina jiran naga wani yazo ya tasheni daga baccin da nakeyi.

"Mami ga Abbi nan yazo, kizo ki ganshi kamar wani abun ne ya faru gaba daya a
hargitse yake" Farida data shigo da gudu ta fada amma na gaza buda baki nayi mata
magana se ido kawai dana zuba mata ido kamar wadda ta hadu da cutar mantau.

"Mami, Mami ki taso kinyi shiru ko kema baki da lafiya" ta fada bayan data maso
kusa dani ta hau girgizani, ajiyar zuciya me qarfi na sauke nace

"Bacci nake kika tashe ni ko Farida?"
"Bacci a zaune kuma, idonki ma a bude yake fa Mami" ta fada da mamaki tana kallona.
Zan sake magana kiran da Bashir yake kwalamun ya shiga kunnena kamar ma a qofar
dakin yake seta miqe da sauri tana cewa

"Dan Allah ki taso ki gani Mami gaba daya ba'a hayyacin sa yake ba bamu san meyake
damun sa ba daman jiya be kwana a gida ba se yanzu ya dawo" ta juya da sauri ta
fice ina qoqarin tsayar da ita.

Yanda yake kwala kiran kamar wanda yake gayyar yaqin duniya na uku yasa na tattara
dan qarfin daya rage mun a jikina na miqe, ina kaiwa qofar na jiyo shi cikin qaraji
yana cewa

"Zaku gaya mun ko kuwa, dagaske ne Ma'u ta daura aure da wani daban bani ba? Da
gaskene wani banza ze rabi gonar da take mallakina?"

Saurin bude qofar nayi na fita jin yanda ya qarasa maganar cikin tsawa dan ni kaina
seda na razana, a dari naja da baya na riqe qofa ganin yanda ya juyo ya kalleni da
idanunsa da suka rine kamar zeyi aman wuta gaba daya kamannin fuskarsa sun chanza
zuwa wani daban da ban taba ganin sa a irin yanayin ba.

"Yawwa Ma'u ki gaya mun waccen matar qarya takeyi ba gaskiya ta fada ba, ki fada
mub da bakinki babu wani Namiji daya isa ya mallake ki a duniya bayan ni" ya fada
yana nufo ni, da saurin gaske na koma dakin na turo qofa dan Na tabbatar idan har
ya riqe ni to qila ni kuma a haka nawa ajalin zezo, gaga labarin daya sakani
gajeran suma se Bashir ya qarasa aikin ya murqushe ni na mutu.

Yanda yake buga qofar dakin yana kiran na bude idan ya balla ta ya shigo bazan ji
dadin abinda zeyi mun ba. Na fito na gaya masa qaryane kawai shi abinda yake so
yaji kenan to ni me zance masa bayan ni kaina ban gama tantance sahihancin labarin
baki nima a cikin rudanin nake kamar sa ai an gara shi ba abinda ya shafe shi bane
ni kuwa fa, taya ma za'a ce wai an daura mun aure daga zuwa tambaya sekace wata yar
tsana.

Wayata da aka kira na janyo da sauri ban ko tsaya duba waye ba dan neman wanda ze
kawo mana dauki daga buyagin Bashir kawai nake

"Hello Asmy inata buga qofa ba'a bude ba ko baku nan ne?" Aka fada da muryar da
rudun da nake ciki be barni na gane waye ba.

"Ka shigo a bude take dan Allah kayi sauri Bashir ze illata mu dani da yara" na
fada ina tsalle kamar wata yarinya tunda dau naji ance ana waje ai magana ta qare
dauki yazo kawai.

YUSUF
Duka daya yayiwa qofar da qafa ta bude idan ma a kulle take oho shidai ya bude ya
fada gidan cikin azama jin abinda ta fada. Ido hudu sukayi da Bashir dake aikin
biga qofar dakinta yayi biji biji kamar wani sabon hauka ya waiwayo a fusace jin an
shigo gidan karaf suka hada ido da Yusuf suka shiga muzurai kamar wasu sababin
zakaru.

"Me ya kawo ka gidan nan? Bana gaya maka ka fita daga harkarta ba karna sake ganika
a kudada mata ta shine ka dawo to kuwa yau senayi maganinka, idan ma dakai ake hada
baki saboda a baqantamun rai duk senayi maganin ku zan nuna muku Ma'u tawace ni
kadai" Bashir ya fada a zabure yana nufar inda Yusuf yake a tsaye ya harde hannaye
a qirji seda yakai dab dashi ya tsaya yana huci kamar ze kai masa duka.

Murmushi Yusuf yayi yana kallonsa yace
"Yaka tsaya? Ka qaraso mana kayi maganin nawa ko ko ba haka kace ba?"

Muzurai kawai Bashir yake yana sake kallon Majiya qarfin da suke tsaye a bakin
qofar daga bayan Yusuf jikinau kamar wadanda aka gina da Bulo ko karan hauka ya
cije shi baze yarda fada ya hadashi da daya daga cikin su bama balle harsu biyu
yanda suka zubo masa ido jira kawai suke a basu umarni su far masa yasan.

"Ya ka tsaya ne Malam Bashir kai nake jira fa" Yusuf ya sake fada, ganin Bashir na
kallon bayansa yasa ya waiwaya shima seya saki murmushi me kama da dariya yayi musu
alamar daua fita, suka rusuna masa a tare suka juya waje se ya maida kallonsa kan
Bashir cikin qasa da murya yanda yaraj da suka zura musu ido bazasujiyo abinda yake
fada ba yace

"Ashe ma duk kurarin banza kakeyi yan wadannan qananun kwarin sun tsorata ka duk
fiffiqar da kakeyi ta tashi a banza. Bari kaji abu daya ze hana na wulaqanta ka
saboda wadannan yaran, bana so mutunchi na ya zube a gaban su dan bazasu taba
girmamani ba idan har na wulaqanta ka a gabansu amma hakan bashi yake nufin idan
muka hadu a inda babu ido zan saka karnukana su yagalgala ka ba.

Karka dauki shirun da nake maka a baya a matsayin tsoro ko bazan iya mayar maka da
martani bane Aa saboda a lokacin daga ni har kai laluben allura muke a duhu ba'a
san hannun da ze dauka ba, amma yanzu da na tabbatar da Allura tazo hannuna ta zama
halalina mallakina yanzu zan baka amsa daidai da duk abubuwan daka fada a baya.

Kace ina shiga gidan matan aure zaka bata mun suna ka gayawa duniya ni manemin
matan aure ne ko? To bari kaji daga yanzu idan na sake jin labarin anga koda sahun
tayar motar ka ne a qofar gidan nan sena batar dakai"

Yanda ya fadi batarwar seda Bashir ya bude ido dakayu ya kalle shi, gani yayi ya
juye masa kai bazakace wannan mutumin me yawan murmushi da fara'a bane.

"Kwarai ni ba suna zan bata maka ba dan baka da sunan da zan bata ba kuma kashe ka
zanyi ba amma zan batar dakai, babu wanda ze sake ganinka gaba daya za'a shafe
labarinka Bashir.

Babu kai babu MATATA, duk abinda ya shafi Yayanka nine wakili tsakanin ku idan
bazaka iya tunkarata kai tsaye ba ka nemi wani cikin yan uwanta ka ringa magan
dashi amma banyarda ba koda wasa magana ta sake hadaka da MATATA, ina da kishin
abinda nake so na kuma san qima da darajar sa idan kana musu ka gwadani Bashir
indai shirya mayar da yayanka marayun qarfi da yaji matarka tayi takabar dole
Bashir ka sake Shigowa gidan nan ko ka tare MATATA a hanya"

A nutse yayi maganar amma tamkar saukar aradu haka Bashir ya ringa jinsu a tsakiyar
kansa. Kalmar MATATA da yake fada tafi komai juya masa kwakwalwa dagaske kenan Ma'u
tayi aure kuma wannan mutumin ta aura?

Qarar bude qofar dakin Ma'u da sukaji ta saka su waiwayawa gaba dayan su a tare
kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.

ASMA'U

Sadaf sadaf na bude qofar dakina na fito yanda kasan barawo ya shigo sata tunda na
dena jiyo hargagin Bashir na tabbatar da mun samu an kawo mana dauki kenan.

Gaba daya suka waiwayo suna kallona cikin wata irin Azama Yusuf ya iso gabana ba
zato se jina nayi gaba daya a jikinsa ya rufe ni ruf seka rantse Farida ya rungume
ko Amnah saboda yanda na zama wata yar firit a jikinsa.

Wani irin shokin naji ya taho mun tun daga tsakiyar kaina ya dire kan qafafuna, ban
farfado ba naji sautin muryarsa tareda dumin numfashinsa da yake fitar da qamshin
Na'ana'a daidai kunnena yana cewa

"Karki bari linzamin kishina ya kwace Asmy, meyasa zaki fito gaban wani namiji a
haka ya kallo abinda yake mallakina".

Innalillahi, yanda kasan wadda wuta taja haka naji jikina ya dauki rawa nan da nan
na shiga qoqarin janyewa daga jikinsa amma yaqi bani damar hakan sema qara qarfin
ruqon da yayi mun yayi ta hanyar dora hannayensa biyu ya sake damqe quguna ya dora
habarsa akan gashin kaina da se a sannan na lura ashe daga ni se wata doguwar rigar
shifom me hannun Bes na fito kaina ko arziqin dankwali be samu ba.

"Yusuf ka bari meye haka dan Allah? Yara fa suna kallonka" na fada a rikice jikina
yana rawa jin yanda yake qara danqe quguna yana qoqarin daidaita fuskarmu.

"Wadanne yaran? Tun kafin ki fito suka shige daki, ai kinyi qoqari sosai Asmy gurin
basu tarbiyyar barin guri idan manya suna magana" ya qarasa tareda hade bakinmu
guri daya ba tareda ya bani damar cewa komai ba, sumbatata yakeyi seka rantse da
Allah babu wani abu daya iya a duniya sama da wannan ni kuwa ina tsaye kamar
Bishiya yar shekara Dari bidirinsa kawai yake cikin wani irin sauqi yanda kasan
dagani se shi muka rage a cikin duniya".

Qarar fashewar abu ta saka shi sakina dakyar yana mayar da numfashi muka daga kai a
tare muka kalli inda Bashir yake tsaye, yawun dake barazanar sarqeni na hadiye ina
raba ido kamar an jijjiga bera a jarka se na bude baki taread dora hannu akai ganin
yanda hannun Bashir yake digar da jini gefe guda kuma mudubin Console dina ne a
rugurguje da alama shi ya nausa da hannunsa.

"Kash ya zaka huce akan mudubi beji ba be gani ba, wai daman kana tsaye baka yarda
da abinda na fada maka ba kenan? Ka tabbata wannan shine karo na qarshe da zaka
sake ganin abinda yake haramiyarka ka kuma fita idan ba haka ba inada tsageru
daidai da kai biyu kawai ka gani anan idan kuma kana musu ka jira minti biyar tayi
yawa sena saka sun zagaye gidan ka.

Wani irin kallon da na gagara fassarawa Bashir ya bimu dashi dagani har Yusuf din
kafin ya tsayar da idonsa akaina se kuma ya juya cikin rangaji ya fice daga gidan
har sannan hannunsa yana zubar da Jini.

Ya bata mun farin cikina, gaba daya ya rusamun tsarin dana zo dashi na tarbar
Amaryata" Yusuf ya fada yana kallona har sannan hannayensa na saqale da quguna wani
irin abu nake yana shiga jikina duk yanda naso na bude baki nayi masa magana kona
fizge jikina na kasa yanda kasan wadda ya saka waya ya daddaure haka nake jina.

BASHIR

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 63

BASHIR

Ikon Allah ne ya shigar dashi gidan sa, yana shiga falon ya zube a qasa kamar
qaramin yaro hawaye suka fara masa sintiri a fuska, be damu da ciwon hannunsa da
har sannan jini na diqa ba ya ringa buga kansa yana cewa
β€œNa rasata Na rasata, na rasa farin cikina”.

Addah data fito daga Kitchen hannunta dauke da Flask data damawa Amirah kunu tayi
saurin ajiye shi ta nufi Bashir cikin tashin hankali tace

β€œWaka rasa Bashir? Nafi ce ta mutu ko Amadu?” Addah ta fada tana tafa hannaye.
Amirah da fitowarta kenan daga wanka ta jiyo maganar su itama se gata, da sauri ta
qarasa kusa dashi ta tsugunna,

β€œYaya Jini hannunka, dame kaji ciwo?” Ta fada tana qoqarin kama hannun. Seya riqo
kafadunta yana cewa

β€œNa rasa Ma’una dagaske Ma’u ta auri wani ta zama matar wani daban bani ba rayuwata
tazo qarshe” ya qarasa yana sakin wani kuka me tafe da sheshsheqa.

A tare Amirah da Addah suka saki wani dogon tsaki Addah na dire nata ta dora da
cewa
β€œAmma Bashir ka isa asararrare, yanzu dan ubanka saboda mace kazo zaka saka zuciya
ta ta buga na zata yar uwata ce ta mutu ashe kai tsabar lalacewa akan matar daka
saka kake Kuka? To kaida Allah faduwar gaban da ka sakani ban yafe ba kuma nayi
matuqar farin ciki da wannan al’amari Mun yada kwallon magwaro mun huta da quda.
Yo in banda ma lalacewa da kana sonta ka saketa ko kuwa wani sabon salon dinar
Albarka ne da zaka zo kana mana dirama a nan? Wai da uwar mema ka yanke hannunka ko
dambe kaje kukayi da Sabon Mijin ya yanke ka haka? Se ka tashi kasan nayi kafin
jinin ka kuma ya tsiyaye ka shiga uku Aikin banza kawai” ta juya ta dauki Flask din
kununta tayi dakin Amirah tana ce mata

β€œDallah taso ki saka kaya duk ya wani gigita mutane da danyan jego kin fito kai a
bude ke ai wannan abin ki hada walima ne ma wallahi yanzu ai se hankalin sa ya dawo
kanki tunda mayyar tayi aure”.

A sanyaye Amirah ta miqe itama tabi bayan Addah tana waigensa. har ga Allah tayi
bala’in jin dadin labarin ko banza yanzu dole duk wani tunanin dawo da Ma’u da yake
ya janye gida ya tabbata nata ita kadai taci karanta babu babbaka.

Har suka rufo qofa Bashir na kallonsu kalaman Addah kuwa ji yai kamar ya shaqota ya
huce duk haushin sa a kanta. Hannu yasa ya share hawayen fuskarsa kafin ya yunqura
be sani ba ya dafa hannun daya yanke da sauri ya daga saboda zagin dayaji har
tsakiyar kansa ya riqe hannun yana dubawa.

Sosai Mudubin ya yanke shi dan gashi nan naman gurin ya fito,
β€œAbbi ka tashi muje clinic a duba maka hannun kaga fa jini yana ci gaba da zuba”
Aliyu daya shiga gidanya fada yana kallon Bashir.

β€œMe yasa bakagaya munba Aliyu? Me yasa baka sanar dani da wuri ba na dakatar da ita
yanzu ya kake so nayi? Shikenan na rasa Ma’u, Mamin ku fa ta auri wani bazata sake
dawowa gidannan ba”.

Kasa hada ido dashi Aliyu yayi, kamar shim hawayen yake kansa a qasa yace
β€œAbbi nima ban sani ba. Ita kanta Mamin nasan bata sani ba seda Anty taje ta gaya
mata daka tsaya kunyi magana zata fada maka”
β€œQaryane ta sani ita ta shirya komai saboda ta

74 / 80