Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
masa wani abu a wayar da mukayi qarshe, iya hasashena ban
gano komai ba dan lafiya mukayi hira kamar ma be tafi muna fushi da juna ba. Haka
na ringa juyi a gado ina tunane tunane to wane sabon shafin ne kuma ze bude mun,
koma dai menene Allah ya bamu wuce wa lafiya da haka bacci yayi awon gaba dani.
Daga mamaki mani abun na Bashir tsoro ya koma bani, dan fa washe gari be biyo
kirana ba, da yake na koma aiki nima ranar na shiga busy ban wani nutsu ba se da
daddare na duba wayar na tabbatar da be kira ba kuma qarin abun mamaki da magriba
ma seda ya kira Aliyu ya bawa dukka yaran sukayi waya harda tambayar me ze taho
musu dashi.
Nidai ido na kawo na zubawa sarautar Allah, duk tsiya dai ze dawo gidan se inji me
ya faru kuma.
Na zata ranar Larabar ze dawo tunda itace cikar sati da tafiyar su daman kwana
biyar yace ko sati to gashi har yau Talata dan haka na saddaqar se gobe ze dawo.
Bayan na tashi aiki na biya na dakko yara, dukda magriba ta kawo kai haka na biya
wata yar kasuwa da ake siyar da Dangin su Kaji masu rai, Bashir yana son Danderun
Zabi dan haka na siyi manya guda biyu aka yanka su aka fige kamun muka kamo hanyar
gida Ba mu muka isa ba se ana shirin shiga sallar Isha saboda holdup.
Jakata kawai na ajiye muka shiga Kitchen tareda Amna, seda na wanke Zabon tsaf
yanda nake so kafin na saka a kwando su tsane na bar Amna ta hada kayan hadi dan
tana fashin sallah ni kuma na tafi nayi magriba da Isha .
Sanda na dawo ta hada komai na marinate dan tasan yanda nake so, seda na saka wuqa
na huda jikinsu sosai yanda kayan hadin zasu shiga na shafe lungu da saqo na ko ina
ya juqu sannan na nade a Foil paper ya nadu da kyau, Already ta kunna oven yayi
zafi dan haka na dora su akan Baking try da aka zuba ruwa na kunna wuta sama da
qasa na rufe.
Ban san sanda ze dawo ba da safe ne koda daddare dan haka A daren nan seda na hada
masa zobo irin wanda yake so na saka a fridge, na gyara zogale na yanka Albasar da
zanyi masa Dambun shinkafa nice harda dakan gyada kamar aljana na turara tsakin
shinkar na saka komai a fridge yanda gobe kawai sedai na hada.
Na gaji tiqis, haka na koma palour na kwanta ina yi ina duba naman dana saka ina
qara ruwan dan karya qone nice har qarfe biyu, jin bacci na neman fin qarfina na
kashe kawai tunda nasan zuwa yanzu yafi rabin dahuwa in Allah ya kaimu gobe na ci
gaba.
Dakyar na iya tashi sallar asuba dan ji nayi kamar ma ina kwanciya aka tashe ni.
Haka ina yin sallah na koma kan aikin, ga shirin yan makaranta da ni kaina. Qarfe
bakwai muna breakfast Bashir ya kirani.
Rai a sake na amsa wayar duk da qasan zuciyata akwai haushin qin kirana da yayi
amma na daure dan babu qarya nayi kewarsa sosai, rabon da mu kebe tun muna Gombe.
A dake ya amsa gaisuwar da nayi masa, mukayi shiru gaba daya kafin ya nisa yace
"Yau zamu dawo In sha Allah zuwa dare zan shigo gida".
"Masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya nayi kewarka da yawa". Na fada cikin
shauqin da na kasa dakatar da kaina.
Wani miskilin murmushi yayi kafin yace "Na sani ai"
"Oh ka ma sani kenan" na fada adan shagwabe.
"Zan kiraki anjima" ya fada, ko kafin na bashi amsa ya katsewa wayar, sena ajiye na
ci gaba da kurbar Tea na rai fes.
Seda nayi yar murya sannan aka bar yaran suka shiga makaranta saboda mun makara,
School Bus nace su biyo idan an tashi kawai dan inaga idan Bashir ya dawo kawai zan
masa magana su ringa bin school bus din kamar zefi sauqi.
A office ma ban wani maida hankali ba, qarfe biyu na dauki excuse na tafi gida.
Seda na gyare gidan qal na chanza Bedsheet din dakin Bashir na saka turaren wuta.
Kayan harkar dana hada na shanye kafin na dakko wani hadin dilka da Anty ta bani na
na mutstsike jikina tsaf na turara sannan na dauraye jikina na koma Kitchen.
Na riga naci qarfin aikin tun jiya, Danderun na duba yayi luguf dan tun shigowata
na ci gaba da bashi wuta gaba daya gidan ya dume da qamshinsa ga na turaren da nayi
se suka hadu suka bada wani kalar qamshin yan gayu, nan da nan na hada Dambuna
sannan na dora tuwon semo da miyar Danyar kubewa taji naman rago dan Bashir yana
sonsa.
Kafin Magriba munyi wanka nida yaran munyi kwalliya yanda kasan ranar sallah. Wata
Atamfa na saka Batik Maroon da akayiwa dinkin A line me dogon hannu babu ado a jiki
se aikin stones da aka mata se walwali takeyi na kashe daurina na baza qamshi duk
inda na juya yara se sun ce "kai Mami kinyi kyau wallahi" ni kuwa se jin dadi
nakeyi.
Ina tahiyar qarshe a sallah naji waya ta tana qara kafin nayi sallama ta katse.
Bayan na idar na janyota dan nasan Bashir ne, ilai kuwa wani kiran nasa ya sake
shigowa.
"Ranka ya dade Mijin Ma'u, ka iso nazo na bude maka qofa ne" na fada da yar dariya.
Dariyar shima yayi cikin jin dadin sunan dana kira shi yace
"Mun dawo amma ban qara so gida ba"
"Masha Allah, sannunku da dawowa, muna jiranka nida yara mun shirya maka babbar
tarba".
"Dagaske, me kika tanadar mun?" Ya tambaye ni, seda na gyara zama kafin nace
"Duk abinda kake so" na bashi Amsa.
"Ke kadai nake So Ma'una" yayi maganar cikin wani salo da yayi mun dirar mikiya dan
har seda naji kamar numfashina ya tsaya na dan lokaci, jikina ya karbi saqon sa
dagaske, se na yi qasa da murya kamar me gudun wani yaji abinda zan fada nace
"Na tana dar maka kaina, kai kadai nake jira Farin cikin Ma'u". Na fada sannan muka
kashe waya. Cike da zumudi na tashi na mayar da dankali na na sake gyara fuskata
sosai na qara turare. Palour na dawo muka zauna motsi kadan mu kalli qofa kowa ya
qagara Abbi ya dawo har dai aka kira Isha Malam Bashir shiru.
Tafi tafi fa har qarfe tara babu Bashir gashi yara har sun fara qorafin yunwa suke
ji, se na tashi a sanyaye na dibar musu abincin bayan sun shimfida Table mat a qasa
dan kar a bata gurin suka zauna suka ci.
Muna zaune goma ta buga zuwa sannan hankalina ya fara tashi anya lafiya kuwa gashi
na kira wayar sa har sau biyu bata shiga daga qarshe ma aka ce a kashe take.
Muna tsaye tsuru nida Amna da Aliyu dan ragowar sun kwanta, Aliyu ya kalle ni yace
"Mami ko naje na tambayi Baba Audu naga yana gida".
Se a sannan ma tunanin yazo mun da mu gayawa Baban, na dago kai da niyyar bashi
amsa wayata dake hannuna tayi qara alamar shigowar message. Number Bashir ce, sena
bude da sauri na fara karantawa
"I'm sorry Ma'una, na wuce Gombe" Abinda ya rubuta kenan.
Wani duhu ne ya gifta idona na saki wayar a qasa nayi baya kamar zan fadi Amna da
Aliyu suka riqe ni,
"Mami meya faru? Wani abu ya samu Abbin?" Aliyu ya shiga tambayata a rikice, dakyar
na iya cewa
"Dauko mun Inhaler" se ya sake ni ya tafi da gudu dakina. Wayata Amna ta dauka ta
bude, ina kallon ta bayan ta karanta message din ta goge daidai sanda Aliyu ya dawo
yana bani Inhaler ya karbe wayar aga hannunta yana cewa
"Na gani me aka turo" se ya bude ya kalle ta yace "Ni banga komai ba, Mami wai
menene?".
Seda naji numfashi na ya daidaita, Ina da Asthma kuma yawan ci baqin cikin Bashir
ne yake motsamun ita dan ni da na shiga damuwa ko tashin hankali zanji numfashi
shina yana sama sama.
"Ku tashi kuje ku kwanta babu komai, ashe ma basu taho ba" na fada ina qoqarin
miqewa. Se Aliyu ya zuba mun ido kamar be yadda da abinda na fada ba, seda na sake
maimaitawa sannan suka miqe.
Hannuna ya kama yace "Mami muje ki kwanta toh"
"Aa Aliyu sena kwashe abincin nan karsu lalace" na fada cike da qarfin hali dan na
matsu subar gurin ko zan samu damar fashewa da kukan daya tokare mun maqoshi.
Qarfin hali kawai nayi muka kwashe kayan, ina shiga dakina na jingina da qofar na
fashe da wani irin kuka na zallar baqin ciki da takaici, wannan wane irin wulaqanci
ne, meyasa kwata kwata Bashir baya darajani?
Meyasa ze yaudareni yace yana hanya sannan ya zagaye ya tafi gurin Kishiyata? Idan
ya ce mun Gombe ze wuce ai bazan hana shi ba tunda itama matarsa ce amma wannan ai
zalunci ne yasa na bata lokaci na na shirya tarar sa sannan ya zagaye ya tafi gurin
wata.
Haka na kwana ina kukan baqin ciki idona sunyi luhu luhu ga wani azababben ciwon
kai daya kamani, sauqi daya dana samu Amna ba zataje makaranta ba saboda wani satin
zasu fara WAEC ita ta shirya yaran ta basu abinci sannan tayi musu order Uber suka
tafi.
Ina zaune a gaban mudubi ina shafa mai bayan na samu nayi wanka dakyar ta shigo da
Try ta dora Mug din shayi da plate din dankalinda kwai. Akan Coffee table ta ajiye
kafin ta zauna akan daya daga cikin kujerun.
"Mami" ta kira suna na, sena waiwayo nayi mata kallo daya na mayar da kaina.
"Mami kiyi haquri dan Allah, wallahi ba laifin Abbi bane kin san su Anty Amirah har
gidan bokaye suna zuwa qilan Asiri sukayi masa" ta fada muryarta na rawa alamar
kuka zatayi.
Sena juyo na kalleta ina murmushi nace
"Kinsan menene Amna?" Seta girgiza kai alamar Aa, numfashi naja kafin naci gaba da
cewa
"Abbin ku be kyauta mun ba, inda ya fadamun ba yau ze dawo ba kinga da ban sha
wahalar hada masa abinci ba. Kina kallo fa jiya ko baccin kirki banyi ba ina gasa
masa zabo amma duk wannan wahalar ta tashi a banza kuma fa da magriba ma fa seda
mukayi waya yace sun dawo yanzu ze taho gida".
Na qarasa ina share hawayen daya zubo ta gefen ido na, gaya matan da nayi se yasa
naji wani sanyi sanyi a zuciyata.
"Haka ne Mami, nidai kiyi haquri ki dena damuwa daman abinda suke so kenan"
"Na haqura Amna, kije ki kwanta ki huta toh nima idan na karya bacci zanyi" na fada
ina miqewa na bude wardrobe na dakko Doguwar rigar Yadi me laushi na saka. Tura
abincin kawai na ringayi dan bakina sam babu dadi. Bayan na gama na sha Paracetamol
na kwanta.
Dakyar ya yakice tunanin abinda Bashir yayi mun na samu bacci me nauyi ya dauke ni,
gana jiya da banyi ba ga bashin na shekaran jiya.
BASHIR
Tun washe garin da ya sauka a Delta da daddare suna waya da Amirah tana ci gaba da
yi masa kukan data ara ta dorawa kanta.
Cikin kukan take cewa "Kowa ya kira ni yayi mun gaisuwa dangi na kusa da na nesa
amma banda Anty, ai ko ba komai tsakanina da ita ya kamata ace tayi mun gaisuwa ko
su Aliyu ma ai duk ya kamata su kirani ko banza qanwarsu ce" .
"Ma'u bata kira ki ba?" Ya tambayeta da mamaki,
"Bata kirani ba mana inda ta kira ai Zan gaya maka indai kuma ba murna take da
mutuwar Iman ba". Amiran ta bashi amsa. Wannan fushin cewa bata kira Amirah ta mata
gaisuwa ba shi ya hana shi kiranta har tsahon kwanakin da yayin.
Ko ranar data kirashi da Amiran suke waya, sanda kiran ya shiga harga Allah yaso ya
daga dan yayi missing dinta amma daya gayawa Amirah nan da nan ta rikice ta fara
masa kuka, basu kuma gama wayar ba se gurin sha biyu dan haka suna gamawa bacci ya
kwashe shi.
Gaba daya yanzu shi tausayin Amirah yake ji. Koshi me ΕΈaΓΏa Shida rasuwar yarinyar
nan ta tabashi sosai bare ita me guda daya sannan ga irin wahalar da tasha shiyasa
yake biye mata ko zata samu sassaucin abinda take ji.
Rabar laraban kuma da zumudin son ganin Asma'u ya taho, yasan be kyauta mata ba ya
kuma bari ne se ya dawo sannan ya goge laifinsa, sanda ya kirata dagaske yana Lagos
saukar su kenan amma suna ajiye waya Amirah ta kirashi tana kuka tamkar ranta ze
fita.
Akan gashi har anyi sati da rasuwar Iman amma beje ya ganta ba.
"Ni daman nasan baka sona Yaya, baka qaunata farin cikin Anty da ΕΈaΓΏan ta ne kawai
matsalar ka baka damu da ni na rayu ko na mutu ba. Karinga tunawa nima matarka ce
kamar ita, kuma ina da haqqi akan ka. kuma idan har ban yafe ba kasan Allah babu
ruwan sa seya kama ka da haqqina". Tana gama fadar haka ta kashe wayar ta, bugun
duniya kuma taqi dagawa.
Gaba daya ji yayi hankalinsa ya tashi, shifa duk abinda za'ayi kar a saka batun
Allah ya isa. Ya fito kenan ze taho gida suka hadu da daya daga cikin Directors
dinsu shima dan Gombe ne suka gaisa se yake gaya masa Gombe ze tafi yanzu.
"Sir Daman akwai jirgi yau ko a mota zaka tafi" Bashir din ya tambaye shi, se yayi
murmushi yace
"Haba Engineer mota kuma a daren nan ai kayi mun fada, a jirgine His excellency
yazo wani taro, kasan Abokina ne, toh na samu alfarma za'a rabani Private Jet mu
tafi.
"Ai Sir ku manayan mutane ne da zan samu a rabani nima ai dana biku na dana" ya
fada yana shafa kai, se Director yace "dagaske kake ko wasa se na kira Protocol
naji idan ze samu".
Beyi zaton za'a samu din ba kawai ya amsa, yana kiran protocol din kuwa yace su
taho yanzu su akw jira. Babu damar yayi wa Director wasa da hankali dole ya bishi
suka tafi dukda shi kansa yasan be aikata daidai ba, amma yasan Asma'u tana da
Fahimta, gara ya fara gyarota da Amirah sannan ya dawo kan Ma'un sa dan yasan ita
bazata taba yi masa Allah ya isa ba kome zeyi mata.
A Flight mode ya saka wayarsa dan karma ta kirashi besan me zece mata ba, seda ya
sauka a Gombe, yana kan hanyar zuwa gidan su ya tura mata da wannan Text din.
Sanda ya isa har sun rufe gida seda ya kira Naziru ya bude masa tukkana. Da mamaki
Nazirun yake kallonsa, ya karbar masa Jakar suka shiga ciki kai tsaye ya wuce
dakinsu da Jakar shi kuma Bashir ya wuce Dakin Dada dan burinsa yanzu yaga Amirah
yaga halin da take ciki.
Palour babu kowa dan har sun kashe fitulu alamar sun kwanta, kai tsaye dakin
Fainusa ya nufa inda yasba ze samu Amiran. Har ze tura qofar ya daka saboda tuna ba
ita kadai bace a dakin baisan a yana yin da ze tarar dasu ba seya dakata.
A hankali yayi knocking, seda ya buga sau uku sannan Fainusa ta taso ta bude qofar
tana hamma a zaton ta ma Dada ce, seta yi saurin saita kanta ta shiga gaishe shi, a
ranta tana mamakin daga ina da tsohon daren nan kuma.
Fita tayi daga dakin ta koma palour shi kuma ya shiga. Abin mamaki matar da Tace
bata iya bacci da ta kwanta mafarkin Iman takeyi se gata tana shaqar baccinta
kashirban se a iya sace ta ma bata sani ba.
Tashinta ya shiga yi amma ko motsi se wasu surutaj banza data ringa masa qarshe ya
haqura ya koma dakin Naziru ya kwanta dan already Nazirun ya gyara masa Gadon sa
shi kuma ya koma Dakin Sa'ad ya kwanta.
Juyi ya ringa yi kawai ya kasa baccin, tunanin halin da Ma'u take ciki kawai yake.
"Allah sarki Ma'una yar Aljanna nasan ke me haquri kuma zaki fahimce ni" ya fada a
fili kamar yana gabanta. Dakyar ya samu yayi bacci ya qudurce a ransa dai In sha
Allah gobe ko a mota ne seya tafi Lagos.
ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 27
Amirah
Da Asuba duk tashin da Fainusa ta ringa yiwa Amirah tayi sallah ko motsi batayi ba.
Ba wai dan bata jin ta ba, Aβa kawai ita ta tsani wannan tashin Asubar da sukeyi
tun kafin ayi assalatu.
Tana lafe akan gado ta jiyo Fainusa tana gayawa Dada zuwan Bashir din jiya da
daddare, seta miqe zaune. βKardai ya shigo ya ganni ina sharar bacciβ ta fada tana
zaro ido.
βWayyo ya zanyi yanzuβ ta sake fada a fili tana tunanin mafita. Tunda akayi rasuwar
take masa qaryar bata iya bacci da daddare shi yasa kullum suke raba dare suna waya
se yayi dagaske take barinsa ta kwanta.
Jiyan ma abinda yasa bata kirashi ba baccin taji da wuri, seta shirya a ranta da
safe in sunyi waya se tace masa ai tasan ya koma gida ne bata so ta kirashi Anty
taji haushi toh yanzu gashi qilan ya ganta wai ya ma akayi be gaya mata ze zo a
jiyan ba. Yanzu ita wace qaryar zata zabga masa?
Ganin ba mafita ya sakata tashi da niyyar ta yiwo alwala idonta ya sauka akan
Maganin tari akan Mudubi. Nan take ta tuno ranar sadakar uku aka siyowa Yaron Anty
Amina Babbar Yayar su Bashir da take aure a Bauchi, se akayi rashin saβa aka karbo
na manya dan haka bata bashi ba ta ajiye a dakin.
Da sauri ta dauke shi, seda ta leqa ta jikin qofa ta hango Dada da Fainusa suna
Nafila kafin ta bude kofar Toilet a hankali ta shiga ta tuttar da fin rabin maganin
a rariya kafin ta koma ta kwanta bayan ta ajiye shi saitin kanta ta bar kwalbar a
bude.
Har qarfe shida tana kwance a gurin, Fainusa data gama Azkar dinta ta shiga dakin
yin wanka dan zata fita gurin aiki tana koyarwa a makarantar secondary dake kusa
dasu ta tarar da Amirah a bararraje tana bacci babu Alamar ta tashi tayi sallah.
βLallai yarinyar nan, daman baki tashi bama kikayi sallar nidai naga randa zakiyi
hankaliβ ta fada bayan da ta danawa Amirah duka a cinya ta bude ido da sauri dan
dukan ya shigeta.
βAkan me zaki zo ki dakeni, Allah ya isana wallahiβ ta fada tana sosa inda ta dake
tan.
βNi kike yiwa Allah ya isa mara kunyar banza kawaiβ Fainusa ta hayayyaqo mata, Dada
da tajiyo hayaniyar tasu ta shiga da sauri tana cewa
βBismillahi safiyar taku tayi zaku fara ba, kamar masu ganin hanjin juna yanzu kuma
me akayi?β
βDada wai fa wannan mara kunyar tunda na tashe ta da Asuba ashe bata tashi tayi
sallar ba, shine yanzu fa dana shigo na sake tashinta ta fara zagina tana mun Allah
ya isaβ.
Bude baki Amirah tayi da niyyar magana ta hango Bashir ya turo qofa, se kawai ta
fashe da kukan qarya harda sheshsheqa tana cewa
βWallahi Dada ba haka akayi ba, ni ban ji sanda ta tashi ni ba ban ma san safiya
tayi ba kawai yanzu tana shigowa ta hau dana mun duka wai na kwanta