Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
daman suna ta yanda za’ayi a qara musu duk wanda suka siya ba wasu na arziqi
bane yanzu gashi an samu sun gode sosai.
Haka kawai kuma se naji nauyin qin bayar da komai din da nayi, dan haka washe gari
naje Awo da yake da mota na fita dan Asabar ce Bashir yana gida sena Biya na siyi
wasu kulolij masu kyau guda uku da zannuwan gado manya masu abun rufa suka uku na
wuce gidan Dadan na kai mata.
Taringa zubamun godiya amma qiriqiri Addah dana tarar ta nuna sunyi kadan, har tana
cewa “Yanzu a matsayin ki guda a nuna wadannan kayan ace ke kika kawo ai se a raina
ki ni dana ga wadanda akace an kawo daga gidan ku inji su hudun duka se naji wani
iri nida na dauka mota za’a sauke mana” da wasa da dariya tayi maganar amma duk me
hankali ai yasan me take nufi. Dan haka nima cikin wasan na mayar mata da martani
nace
“Yo Addah kin manta ance taqamar mace gidan mijinta kudin uba ai ado ne kawai, kuma
a iya qarfin mijina nayi wannan ai kuwa na kai a yabamun su kuwa da suka bayar fa
kara suka mun bawai dole ya zamar musu fa se sunyi ba”
Washe garin ranar muka tashi da Alhinin Rasuwar Aliyu Abokin su Bashir, mutuwar ta
dake ni kwarai dan A jiya bayan na dawo a gidan na tarar dasu shi da Bashir harda
Bala suna hira, yana ta tsokana ta wai bana jin nauyin jikina nake iya tuqi nace
masa ai Laifin abokinsa ne da be kai ni ba, na wuce ciki na barsu yana ta faman yi
mun Addu’ar sauka lafiya ashe rabuwar kenan da safe se kiran Bashir akayi wai ya
rasu da Asuba anji shi shiru be fita Masallaci ba Qaninsa ya duba shi aka tarar
babu rai.
Mutuwar Matashi akwai firgitarwa musamman ta mutun irin Aliyu me mutunchi da
mutunta Jama’a ya samu shaida ta kwarai sosai, haka muka tafi Jana’iza Allah sarki
Mamansa se Kuka takeyi su biyu ne Yayanta daga shi se qaninsa haka budurwar da ze
aura da suka zo Abin tausayi gaba daya se jikina ya sake yin sanyi da lamarin
duniya.
Tunda akayi rasuwar Bashir ya zama wani iri, ranar kwana uku, ranar kwana uku da
daddare muna zaune shiru yake cewa
“Allah sarki Aliyu, ranar kafin ki shigo yake cewa mun Wallahi Bashir kayi dacen
mata Allah yasa mu a danshin ka dan Allah ka riqe yarinyar nan da kyau dan Alkahiri
ce a rayuwarka kuma matar rufin Asiri ce.
Kaga dai a yana yin da kukayi aure gashi a hankali abubuwa suna ta warwarewa bata
nuna gazawarta ba ni kuwa kana kallo yarinyar nan Momy ba yar kowa ba amma ta dauki
buri ta dorawa kanta wai fa dana kaita taga gida na rainawa tayi wai ban dora bene
ba, ta shiga kawo mun wasu tsare tsaren banzanta, Ni fa in ba’ayi wasa ba auran ma
fasawa zanyi.
Idan da rabo nayi a Aljanna, ashe bamu sani ba tafiyar ma tazo gangara” se ga
hawaye ya zubo ta gefen idonsa.
Jikina ya qara macewa dakyar na iya cewa “ Allah ya sa muyi kyakykyawan qarshe,
waya sani ko nika mutuwar zanyi”
“Karki sake fadan haka In sha Allahu lafiya lau zaki haihu” ya fada yana kama
hannuna.
Wannan rasuwar ta rage kaifin shagalin bikin su Fainusa dan duk wani makusancin
Bashir yasan Su su hudun nan tare suka tashi, Ranar Asabar data kama kwana shida da
rasuwar Aliyi aka daura auran a ranar kuma kowa aka kaita gidanta. Daman Banje kai
Amare ba dan gidan mu ma na tafi da hayaniyar yan biki ta fara yawa se dare Bashir
yaje muka tafi gida.
Kamar ciwo na jira kuwa yana yin parking nayi wani ciwon baya da mara lokaci daya
sunyi mun sallama, se Bashir ya shiga ya dakko mun Akwatina muka kama hanyar
Asibiti. Tsabar takaici ina cikin azabar ciwon da nakehi kamar haihuwar ta taho gab
ne wai Bashir tambayata yakeyi yanzu ya za’ayi idan haihuwa ce bamu siyi kayan Baby
ba bansan sanda na qunduma masa zagi shiga kayan babyn ba nace ya mun shiru ko ya
sauka a motar,
Haka muka qarasa aka shiga filin daga, zo kuga idon Ma’u a labor room ashe aka ce
wasa Farin girki wannan ciwo sallama ne, haka dai akayi ta gumurzu har Asuba, cikin
ikon Allah Ana kwada kiran Assalatu na santalo qaton Baby na me kama da Bashir sak
kamar an tsaga kara hasken Fata ta kawai ya dakko.
Murna a gurin Bashir kamar ya taka rawa, kafin Gari ya gama haske Asibiti ya fara
cika da dangi na harda nasa, Hajia Babba da Hajia Umma ne suka zo, a kunne na
radawa Hajia Umman akan tace gida zasu wuce dani dan tun farko farko danayiwa
Bashir maganar wankan gida yace ba wannan maganar ban sake ba.
zuwa rana kuwa da likita ya tabbatar babu wata matsala aka bamu sallama Hajia Umma
tace gida aka yi dani, ze musa Addah ta tace muje babu komai daman sunyi niyyar
kawo nin, saboda haushi ko sallama Bashir beyi mana ba ya kama hanya ya tafi.
Oho nidai muma mukayi tafiyar mu gida, daman na dade da hada kayan tafiya wankan
muna zuwa aka tura su Khadija gidan suka dakko mun ina ta Addu’ar Allah yasa kar a
tambayi ina kayan wanka da sauran abubuwan da ake siya ilai kuwa kafin ma mu qaraso
Hajia Anjin saka su Baba Jummai sun shirya mun dakin da zan zauna duk wani abun
buqata na zaman jego an tana da.
Seda muka kwana muka wuni sannan Bashir yazo shi ala dole fushi yake yi, ko a
jikina jegona kawai nakeyi ingantacce haka yarona Aliyu da tun a Asibiti yayi masa
Huduba shima yana samun kula sosai.
Kwanan mu biyar aka kawo kayan barka daga gidan su Bashir tareda ragon suna. Yan
rigunan su ba laifi da turamen Atamfa uku nawa, haka aka taresu cikin karamci suka
tafi yan barkar da suka tarar yan uwan mu nata yan qananan maganganu dan kowa yayi
zaton yanda yanzu ya samu budi babu laifi zeyi abinda yafi haka ni kuwa ko a jikina
dan dama ba jiran abinda zasu kawo nake ba, ko sanda na masa magana kawai dan
haqqinsa ne ya kamata yayi.
Ranar suna munsha shagalin mu, na ringa shiga ina fita ta Alfarma. Amirah da tun
kwana biyar da suka zo tana gurina da yake anyi hutun makaranta daman nayi mata
dinku na duk inda na shiga tana nan yan gidan mu suyita tsokanarta ana yar Anty
tayi dariya.
Zaryar da Bashir ya ringayi ta saka aka tattara ni satin mu uku muka koma se na
tafi tareda Baba Jummai da zata qarasa mun Arba’in.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 36
Shekarar Aliyu daya na samu cikin Jafar, nasha kuka sosai saboda ba qaramar wuyar
raino nake ci da karatu ba sannan yanzu kuma ga wani sabon cikin har rigima se da
mukayi da Bashir ya kuma tabbatar mun se ya bata mun rai in har wani abu ya samu
cikin nan bisa gangancina.
Haka na hada ciki da raino ga karatu da lokacin ina Level 3 ga hidimar gida idan na
fita makaranta duk yammar da zanyi haka zan dawo nayi girki da abubuwan dana fita
banyi ba kuma Bashir babu ruwansa ko yaya na kuskure ya ringa mita kenan.
Ganin Aliyun yana cin abinci sosai yasa na tambayi Bashir ko zan ringa barinsa a
gurin Addah idan zanje makaranta, da farko qi yayi seda na tasa shi da kuka sannan
ya yarda washe gari kuwa da zan fita na hada masa duk abinda nasan ze buqata na
kaishi gidan.
Faran faran ta karbe shi musamman daman na hada dan ihisani na kaimata, na tafi
makaranta ta hankali kwance tunda nasan za’a kulamun dashi.
Ranar qarfe biyu na taso, tun daga Get din gidan nake jiyo kukan Aliyu gabana ya
yanke ya fadi na qara sauri ina shiga na tarar dasu a tsatstsaye akan Aliyu da yayi
faca faca da ruwan kwata yana ta tsanyara kuka abin tausayi.
Da sauri na qarasa na daga shi, a bakin Mama Binta Kishiyar Addah nake ji wai
Amirah ce ta dauke shi suka fita waje wasa shine wai ta ajiye shi ya tsallaka kwata
ya fada ciki, ita Addah bama ta gidan tuni ta fice, haka na dauke shi muka tafi
gida raina duk a bace.
Idan ba wulaqanci ba taya za’a barta ta fita dashi har ya fada kwata. Seda ina masa
wanka naga inda ya kuje a jikinsa, haka na lallabashi yayi shiru bayan na bashi
abinci da paracetamol na ruwa dan jikinsa yayi duki kafin na goya shi na shiga aiki
ina tunano irin tijarar da Bashir zeyi mun idan ya samu labari.
Ilai kuwa yana dawowa ya fara dudduba yaron kamar yasan me ya faru se ji nayi yana
kwala mun kira, haka muka kwana yana masifa ya kuma ce karna sake kai masa yaro ko
ina nima din daman ba sake kai shi zanyi ba.
Haka na ci gaba da karatu da raino cikina wanda yana wata takwas Bashir ya sake
rasa aikinsa sakamakon korar ma’aikata da Banki sukayi haka suddan kuma ta rutsa
har dashi.
Sosai muka shiga tashin hankali musamman yanda korar tazo musu ba tareda tsammani
ba gashi a lokacin shekara ta qare lokacin biyan kudin Hayar mu yayi ga shirin
haihuwa ta shi kansa Bashir din a sannan ya koma Mesters kuma kowa yasan yanda
Masters yake da cin kudi.
Haka nayi ta qoqarin kwantar masa da hankali da nuna masa In Allah ya yarda komai
ze zo da sauqi mu ci gaba da Addu’a kawai Allah ze kawo mafita.
Hidimar yanzu data farkon Auran mu ba daya ba, a wancan lokacin muna da ajiyayyun
kayan abinci wanda sune jigo sannan sauran buqatun mu ba wasu masu yawa bane yanzu
kuwa shi yake siyan kayan abinci ga qaruwar Yaro da shima akwai nasa buqatun na yau
da kullum da dole suna buqatar kudi chanjin rayuwar da muka samu se nan da nan ta
nuna a jikina musamman saboda yanayin da nake ciki ga tsohon ciki ga karatu da yazo
mana gangara.
Haka muka ci gaba da malejin rayuwa kullum cikin saka ran samun budi daga qofofin
ubangiji, da dan abinda nake samu daga kasuwancin da nakeyi nake riqe damu dan sam
Bashir beyi wani tanadi ba ba kuma zan dorawa yan uwana nauyin da Allah ya sauke
musu ba dan iya zumunchi sunyi mun ya kamata ace yanzu kuma shima ya jajirce ya
riqe gidan sa.
A sanda yana aikin Babu yanda banyi da Bashir ba akan ya ringa cire wani abu a
Albashin sa duk wata yana saving amma yaqi. Shi irin mutanen nan ne da a rayuwarsa
idan ya samu kudi kawai a biya buqatar da take a lokacin baya ajiyewa saboda
buqatar kota kwana.
Nayi nacin har na gaji akan bayan aikin yaje ya samu Baffa suyi maganar kasuwar ya
ringa gwada wata sana’ar ko babu komai ya zama mutum yana da wata madafar bayan
albashi saboda gudun bacin rana akwai sanda har magana ya gaya mun wai ko fata nake
masa ya rasa aiki ya ringa fushi yana jin haushi na daga nan nace bazan sake masa
magana akan yin wata sana’a ba.
Abinda na lura dashi wannan a halin mazan Bauchi da Gombe yake sunbada amanna da
aikin Gomnati, kadan daga ciki ne suka yarda da kasuwa, Nidai dana tashi gidan mu
naga ba’a zaman banza zan ci gaba da saida saidena dan bazan dogara da se abinda
miji ya dakko ya bani ba.
A wannan yanayin na haifi Jafar, wannan karon a gida na na zauna daman kuma ban
saka rai da samun komai a gurin Bashir ba kodan halin da muke ciki ma da yaya ya
biya kudin haya haka dai akayi suna na kuma samu Alkahiri sosai daga yan uwana.
Bayan haihuwar Jafar abubuwan da suka faru ba masu dadi bane dan sosai muka shiga
matsin rayuwa, tun muna iya siyan kayan abincin wata a ajiye har seda takai mun
koma awo a kullum na abinda za’a dafa kuma duk nice qarfin riqon gidan a abinda
nake samu zan bashi yayi a haka har seda muka cinye jarin nawa duk ma abinda zan
samu a haka yake qarewa tunda komai da shi mukeyi babu wani abu da yake shigowa
Bashir daidai da ci gaban karatunsa da tallafi na yake yi seda takai har mota ta na
siyar na bashi kudin akan ya kama wata sana’ar sedai wane tudu wani gangare kudin
suka narke, Bala ya bawa akan ze saro masa kaya daga Lagos wai yan Fashi suka tare
su suka karbe sukayi masa dukan tsiya dan seda yayi kusan wata a kwance yana jinya.
Haka muka ci gaba kullum ina hanyar zuwa gida karbar kudi seda ta kai ni da kaina
na fara jin kunyar hakan na dena zuwa, aiki kuwa kullum ina tafe, ina Teaching ga
wasu training centers dana ke koyarwa suma duk dan dai mu rufawa kan mu asiri seda
ya zama wata rana idan mun samu abinda zamu ci da rana sedai ni dashi mu haqura da
na dare yara suci nakan kwana ina kuka wani lokacin idan na tuna yanzu fa akwai
wadanda tunda suka somi rayuwa cikin irin wannan qunci da matsin suka tashi ko?
Idan kaga yanda na koma sena baka tausayi yanda kasan nice Mijin ba Bashir ba dan
shi yana zaune a gida zan fita aiki na dawo kuma na dafa abinda ya samu muci wannan
abun yana bala’in baqanta ran yan uwana kuma yana daga dalilin daya sa duk suka
zuba mun ido suga gudun ruwana ni kuwa ko a jikina, Ina son Bashir bana jin duk
abinda zanyi masa na fadi kuma ko banyi dan shi ba zanyi dan yayana dan haka ban
taba jin haushin kaina akan abinda nake yi ba.
Abin takaici daya lokacin qannen sa da sukayi aure Allah ya taimake su gaba daya
sun samu gidan hutu dan haka yanzu gidan su basu da wata matsala ko wacce na iya
qoqarin ta se kuma ya zamana sun ware Bashir domin ko gidana yanzu babu wadda take
zuwa tunda bani da abinda zan basu.
Ita kanta Dadan yanzu wani gani gani takeyi mun idan munje gidan babu wannan sakin
Fuskar irin nada wanda duk cikin zugar Addah ne, a cewarta baqin ciki da kyashi ne
ya hana nasa a bawa Bashir kudi a gidan mu na gwammace mu zauna cikin talauchi ni
da shi din saboda wai ina baqin cikin yana wahaltawa yan uwansa sama dani, a raina
nace ashe sun san da yana da shi din ma su ya ringa wahaltawa bani ba dan kafin ya
mun abu daya ya musu goma sannan wane baqin ciki zanyi da har zan zabi zama cikin
Daidai da Addah se in manta rabonda na sakata a ido ko su Aliyu na kai gidan ba’a
minti Ashirin se a dawo mun dasu tace fita zatayi, Amirah kanta yanzu ta rage zuwa
idan nace mata me yasa se tace Addah ce take hana ta rayuwa kenan se kana dashi
mutane suke yi da kai a duniya.
Ana cikin haka wata rana Bashir ya shigo gida cikin tsananin murna yake nuna mun
saqon gayyatar da wani wani kamfani suka aiko masa daga Lagos, a cikin ayyukan da
Alhaji Qarami ya ke ta fafutukar nema masa se yanzu Allah yasa daya suka gayyace
shi, a yanda yake gaya mun mutum biyu za’a dauka kuma su biyar aka gayyata
Jarabawar gwajin nan da kwana uku ze tafi.
Tun daga ranar na fara Azumi ina Yiwa Bashir Addu’ar nema sa’a. Gogan kuwa se shiri
yake ya binciko tsofaffin littattafan sa yana ta karatu. Ana gobe ze tafi da
daddare har wurin daya yaha zaune yana fama da takaddu na kalleshi nace
“Baban Ali da ka ajiye karatun nan haka ka huta Addu’a ya kamata muyi tayi dan a
irij wannan abun fa sa’a ake nema ba wai karatu ba”.
“Ma’u kenan, a irin karatun da nayi na tabbatar da duk tambayar da sukayi mun sena
amsata sannan duk wata kwarewar aiki da zasu nema ina da ita, kedai kawai ki fara
shiri dan har na hango mu a Lagos” ya fada yana ci gaba da bude littafinsa, se na
ja numfashi na gyara kwanciyata nace
“Toh Allah ya tabbatar da Alkahiri”.
Washe gari ya hau mota se Lagos, kwanan sa biyu ya juyo bayan sunyi Jarabawar ya
dawo da tabbacin kamar ma ya samu aikin dan har yana ce mun “ko mutum daya zasu
dauka nasan nine, bakiga yanda su kansu masu Jarabawar suka ringa jinjina qoqari na
ba”
Ni kuwa nace masa
“Kadai ce In sha Allahu, kuma muci gaba da Addu’a idan rabo ne za’a samu”.
Sati daya sakamakon ya fito amma babu sunan Bashir wasu mutum biyu daban ne dan
daya ma babu shi a wadanda sukayi Jarabawar tare, ina jin abokin da yayi yana gaya
masa wai dan wani Minister ne aka aiko da sunan sa dole aka cire mutum daya aka
saka shi.
Haka Bashir ya ringa qunci da bacin rai akan rashin samuwar aikin, duk yanda naso
na nuna masa komai na rayuwa rabo ne idan Allah be tsaga da naka ba duk wuya haka
zaka haqura bazaka samu ba amma yaqi fahimta qarshe ma abin ya zamar mana rigima
har yana gaya mun magana akan niyyar samar masa aiki ne kawai ba’a yi ba aka
wahalar dashi idan ba haka ba duk hanyar da muke da ita ace an rasa ta inda za’a
samar masa aiki me yasa su yan gidan mu mata da maza da sun gama makaranta suke
samun aiki ga Abubakar tuni ya samu chanjin aiki daga inda yake a Kano zuwa NNPC.
Ganin fa yana neman ya raina mun hankali yasa nima na horance masa, nayi masa tatas
na gaya masa ai ba haqqi na bane na samar masa aiki dan haka idan ze tashi ya nema
tun wuri ya nema kuma na cire hannuna daga duk abinda ya shafi sabgarsa, idan har
ya aureni ne saboda ya samu kudi toh ya sawwaqe mun kawai.
Wannan abun ya bala’in dagawa Bashir hankali se gashi har yana bina yana bani
haquri akan sharrin shaidan ne shi ba abinda yake nufi kenan ba, haka muka ci gaba
da jalan ta rayuwa yau fari gobe baqi a haka na kammala karatuna na fara hidimar
qasa.
Ranar wata Talata da bazan manta da ita ba, muna zaune da yamma nida Jafar dan a
lokacin Aliyu ya fara zuwa Islamiyyar da take cikin layin mu. Shekarun sa uku a
sannan tuni bakinsa ya bude sosai dan haka nake hadashi da Amirah suna tafiya kuma
sosai yake karatun dan in aka dawo ya ringa tilawa Bacci kadai yake saka shi yayi
shiru.
Lokacin zafine kuma babu wuta dan haka na shimfida mana tabarma a tsakar gidan muka
zauna Jafar nata wasa da Yar motarsa me Batiri ni kuma ina duba takaddun Test da
nayiwa dalibai na a makaranta Aka bugo Get, Hijab na na saka na leqa, Alhaji Buba
ne me gidan da muke haya shida wani mutum da wani saurayi