Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   54 / 80

159K to 162K   out of 238.5K words

yayi murmushi yace
"Da wurwuri haka"

"Alhaji barka da hutawa" Dada ta fada tana qasa da kanta kamar wadda taje wani
baqon guri, seya rage radio yana kallonta yace

"Barka dai Nafi, halan batan hanya kikayi yau kika shigo dakina ko?"

"Batan hanya kuma Alhaji, zuwa nayi naji ko laifi nayi naga kwana biyu gaba daya ka
shareni a cikin gidan nan kamar baka san da zamana ba ko wani abun kake so sedai ka
saka su Naziru suyi maka ban sani ba ko wani laifi na aikata maka a cikin kuskure"

"Nidin kuma Nafi? Aa baki mun komai ba gani nayi dai ai daman ba se na kiraki ko na
saka ki aiki kikeyi mun ba to bansan ko gajiya kikayi ba kika janye shiyasa nake
saka yayana gudun karna takura miki da hidimomina tunda har kin qosa da kanki"
Alhaji Amadu ya fada yana murmushi qasan ransa kuwa mamakin Dada kawai yakeyi, ya
sani buqatarta ce ta kawota danya jiyo wasu daga maganganunsu ita da Fainusan daya
leqa da niyyar kiran Fainusan shiyasaya dawo ya kunna radio a zuwan besan wainar da
suke toyawa bama.
bama.

"Kayi haquri Alhaji wallahi ba haka bane, gani nayo kamar kayi fushi dani akan
abinda yaron nan ya aikata ne shiyasa ni kuma bansan ta yanda zan wanke kaina a
gurinka ba nasan laifina kake gani" Dada ta fada tana qara sunkuyar dakai.

"Duk wanda yayi na gari ai kansa Nafi, bari nadan kwanta na huta tunda naga Azahar
da saura, idan Sa'adu ya shigo kice masa da yamma ze kaini Gidan Malam Isah na sake
dubo jikinsa tunda Naziru yace wuni zeyi a makaranta yau" ya fada yana tura keken
sa zuwa bakin gado, Dada ta miqe da niyyar taimaka masa ya dakatar da ita.

Dakansa ya hau gadon ya gyara kwanciyarsa dab daman matsalar baya ce ta saka yake
qagara miqewa amma tunda Yan biyun gidan su Ma'u suka kawo masa wani ganyaye na
gargajiya daga Chana wancan dawowar da sukayi ake dafa masa shayi dashi duk wani
ciwon daya shafi qashi yaji sauqin sa cikin ikon Allah, bama shi kadai ba duk
tsofaffin da suka bawa a unguwar tasu kowa se dai sambarka dan yanzu yana kama abu
ya miqe akan qafafunsa tafiya cedai wannan ya fawwalawa Allah shi ya bashi qafafun
kuma yanzu ya karbe abunsa ransa ma wata rana karbar abinsa zeyi balle wata qafa da
da ita da babu duk yana iya gabatar da uzurirrikan rayuwarsa.

Kwanciya yayi ya juya baya jin har sannan Dada na dakin se ya juyo yana cewa

"Nafi akwai wani abun ne kuma naga kin zauna kinyi shiru?"
Seda ta hadiyi yawu kafin ta iya cewa

"Alhaji daman akan maganar yaron nan me neman auran Fainusa ne,dazu ya kirata yace
wai ya fasa shine nake so naji ko zaka tuntubi waliyyan nasa muji menene matsalar
idan da yanda za'a gyarata"

"To ikon Allah ya fasa kuma yace? To Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri" ya fada ba
tareda wata damuwa a fuskarsa ba.

"Alhaji tana can fa tana ta kuka har tana cewa mutuwa zatayi ko ta gudu ta bar gari
dan Allah ka kirasu muji ko da akwai abinda za'a iyayi" Dada ta sake fada kamar
zatayi kukan itama.

Seya yunqura ya tashi zaune yana cewa
"Me auran shekara Goma sha bakwai ma an saketa babu wanda ya biyo ba'asi ko yace a
mayar da ita se ita da ko tsayayyar magana ba'ayi ba?

Idan ta mutu ai shikenan kinga ta huta guduwa daga gida kuma in shi ymta zaba to ta
jira zuwa Juma'a zan bada sanarwa a masallaci cewar na yanke alaqa da ita ko an
ganta a wani guri kar wanda ya alaqantata dani ba yata bace dan karma taje ta kwaso
mun damuwa irin wadda kuka jefa Alhaji Murtala a ciki" ya qarasa maganar yana danna
wayar sa.

Da sauri Dada ta daga kai ta kalleshi, ya akayi yasan da maganar cikin Ummi bayan
Addah ta tabbatar mata babu wanda ya sani shiyasa suke neman hanyar da Asirinsu ze
rufu kafin abu ya fashe kowa ya sani in har kuwa Alhaji yasan zancen to babu shakka
labari ya rigada ya gana gari sune suke shirmen su da tunanin babu wanda ya sani
kenan.
Muryar mutumin daya kira a waya ce ta katse mata tunani, tana ji suka gaisa kafin
Alhajin ya ke ce masa

"Yanzu Me dakina take samuna da maganar cewa Unaru ya janye maganar aure ko? Shine
nace bari na kiraka na tabbatar daga bakinka tukunna"

"Wallahi Alhaji nima da safiyar yau dinnan ya same ni yake gaya mun na kuma yi masa
fada na gaya masa be isa ya mayar damu qananan mutane ba, yanzu haka ka ganni shiri
nake zanje na samu uwarsa na gaya mata halin da ake ciki shiyasa ma ban kiraka ba
na bari se mun gama yanke sa rana tukunna sedai kawai ka gammu" mutumin ya fada
daga daya bagaren

"Aa Alhaji baza'ayi haka ba, babu wanda fa yayi masa dole akanta shi ya gani yace
yana so dan haka yanzu ma bamu san dalilinsa na cew aya janye ba. Ka barshi kawai
Allah yasa hakan ne yafi Alkahiri amma batun a tilasta yaro ma be taso ba shine
ma'auri ba kuma auran fari ba bare ace za'a bashi shawara rajin kansa yasaka shi
tunanin qarawa tunda kuma ya janye a qyale shi kawai" Alhaji Amadu ya fada kai
bazakace yar sa ake cewa an fasa aure
Haka sukayi sallama wancan yana ta faman bada haquri da alqawarin idan komai ya
daidaita zasu zo, yana kashe wayar ya kalli Dada data saki baki tana kallonsa yace
"To kinji dai abinda ya fada. Idan aure take so anjima zan bada sanarwa a masallaci
duk wanda yake sonta yazo zan bashi sadaka har sadakin ma ni zan biya masa idan
kuma taqi ai kinji abinda na fada a farko seta zabi abinda ya mata a ciki.

Ni yanzu kin cinye mun ma lokacin baccina bari na tashi nayi ta hailala da
istigfari maganin masifa kafin a kira sallar" ya qarasa yana janyo carbinsa.

Haka Dada ta kwashi qaqafunta ta fice, a bakin qofa taci karo da Fainusa da ashe
tana labe tana jin komai bata kulata ba ta wuce dakinta can qurya ta shiga kiran
Addah a waya.

GIDAN ADDAH

Addah na tsaye akan Ummi dake kwarara amai a bandaki tana zazzage mata ruwan masifa
da bala'i kiran wayar Dada ya shiga. Bata daga ba ta ci gaba da sababinta, magani
ne ta karbowa Ummin na zubar da ciki tana shi shine ta amayoshi tas kuma wannan
shine karo na uku data kashe kudi aka karbo mata magani amma ciki na nan daram ko
girgiza beyi ba.

Kiran wayarta da ake tayi babu qaqqautawa ya saka ta fito cikin bala'i ta daga tana
cewa
"Wai Nafi wannan wace kalar lukutar masifa ce da zaki ringa kirana kamar naci miki
bashi ki barni naji da abu daya mana haba"

"Addah dole na kiraki ai, kika cemun babu wanda yasan da zancen cikin Ummi amma ya
akayi har Alhaji ya samu labari anya kuwa magana bata fasu ba Addah?"

"To idan ma magana ta fasu Nafi se akayi wace kutumar uba eye nace se akayi me? Da
zaki ce mun Amadu yasan zancen waya sani ko a munafuncinki kika gaya masa tunda
kema ai ba sanin zuciyarki nayi ba waya sani ko kina cikin masu farin ciki da
abinda ya same ni in ba haka ba shi mijin naki yana kanannade a kujera ta ina ze
jiyo wani labari?

Ni karki sake kirana indai ba mafita kika samo mun ba, kuma abin kunya ai ba kanta
farau ba kumaba ita zata rufe ba wasu da yawa Allah kadai yasan shegu nawa suka
haifa aikin banza kawai" ta kashe wayarta kafin ma Dadan ta sake magana.

Kan Ummi data fito daga bandakin da kyar ta koma tana cewa
"Dan uwar ubanki ba kwanciya zakiyi ba tashi zakiyi mu tafi gidan Balaraba yanzu ai
Qanwarta sarai ta taba yin ciki sukaje aka cire muje ta raka ni gurin dan dole se
abin nan ya fita ko bangon duniya zancen yaje qarewarta se an cire idan yaso senaga
shedar da za'a bayar idanan tashi gulmar".

Kuka Ummi ta saka tana cewa ki qyale ni Addah in dai ba so kike na mutu ba dan
Allah ki rabu dani. Qaddarata ce tazo a haka kuma kece sila dan haka ki barni na
haife abinda yake cikina ban sani ba ko shine silar kaffarata a gurin ubangiji"

"Wallahi sedai ki mutu dan ubanki dama amfanin me zakiyi mun idan kin rayu bayan
abin kunyar da kika janyo mana, ki tashi tun wuri mu tafi kafin nazo na haye kanki
na murqusheki daga ke har shegen dan cikin naki ku mutu kowa ya huta".

Haka Ummi tana ji tana gani Addah ta tasata a gaba tana kuka suka tafi. Matan gidan
da sukayi cirko cirko suna
suna kallonsu dan duk abinda ta ke fada sunji saboda ba a hankali take magana ba.

Daman sun san da qishin qishin din maganar yanzu gashi sun tabbatar suna fita kuwa
Binta da tafi kowa tsugudidi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira Alhaji Murtala.

Yana zaune a kasuwa a daidai lokacin wani Amininsa Alhaji Yero ya same shi da
maganar cikin Ummi daya ji a bakin Matansa.

Hankalin Alhaji Murtala yayi qololuwar tashi da jij maganar wata irin tsanar Addah
yaji tana saukar masa shidai tunda ya auri Fatu bazece ga wani abun Alkahiri daya
same shi ta dalilin ta ba a kullum cikin jefa shi a masifu kala kala take.

Kiran wayar Binta na shiga ya daga, ba maganar gaisuwa ta shiga rattaba masa cewa
"Alhaji ka kira Addah duk inda take ta dauki Ummi tana kuka da komai sun tafi
tackaita a zubar da ciki kar yarinyar nan ta mutu mu shiga uku ka kirata ka dakatar
da ita".

Wata zufa yaji tana sakko masa, kiran wayar Addah ya shigayi tana ringing amma bata
dagawa seda ya kirata sau goma a na sha daya ta kashe wayar. Babbar rigarsa ya cire
saboda yanda yaji tana neman shaqeshi ya ringa safa da marwa a cikin shagonsa yana
ayya na irin wulaqancin da zeyiwa Fattu a wannan karon, tabbas yakai bango kuma
dole ya dauki matakin da ze shigar da ita hankalinta.

Wayar Amirah ya shiga kira ringing biyu ta daga tana gaishe shi, be amsa mata ba
cikin kakkausar murya yace mata

"Ki kira uwarku ki gaya mata wallahi idan wani abu ya samu Ummi a sanadiyyar zubar
da cikin data tafi kaita se na daureta dauri har qarshen rayuwarta sannan ki gaya
mata daga inda ta tafi karta dawo mun gidana na saketa saki biyu" yana gama fada
matan ya kashe wayar sa.

Sosai zuciyarsa take tafarfasa, Addu'arsa Allah yasa kar wani abu ya samu Ummin dan
wallahi bega wanda ze hana shi shari'a da Fattu ba.

Hajia Addah kuwa Napep suka haye se gidan Hajia Balaraba suna tafe a hanya tana
surfawa Ummi zagi har suka isa.

Ta tarar da Hajia Balaraba tana wanka dan haka suka zauna a palour suna jiranta ba
adauki lokaci ba kuwa se gata ta fito daga dakinta a kallo daya Addah ta hango irin
yanda tayi sanyi laqwas kamar ba Balaraban data sani ba mace me izza da taqama.

"Aa Fattu kece yau a gidan namu yaushe rabo" Balaraba ta fada tana zama akan
kujera, se Addah ta tabe baki kafin tace

"Zaki fadi haka mana tunda kin samu yanda kike so kij watsar dani bayan da kika
kaini gidan dan damfara ya cinye mun kudi ai dole kice yaushe rabo, ni ba wannan ta
kawo ni ba ma.

Likitan da ya cirewa Sarai qanwar ki ciki zaki hadani dashi wannan tsinanniyar
yarinyar taje ta kwaso mun abun kunya dama yana qare da maqiya ballantana yanzu ta
janyo mun abun magana a ringa nunani a gari"

"Kai kai Fattu ki bari dan Allah, irin wadannan mugayen kalaman da muke jifan yaran
mu dasu su suke tasiri akan su suke lalatasu.
Ummi a garin yaya me ya kaiki irin wannan abu ke da nake yiwa kallon nutsatstsiya
ko yar uwarki da take da rawar kai ta gama yammatancinta lafiya Me ya sa Ummi"
Hajia Balaraba ta fada cikin Jimami.

Ummi ta qarawa kukan ta volume tana
cewa "Wallai Hajia sharrin shaidan ne kuma da laifi Addah, seda na gaya mata ga
wanda nake so tace ko zan mutu bazan aure shi ba"

Duka Addah ta kai mata tana cewa "Na fada din yanzu ma na maimaita ko zaki mutu
bazaki aure shi ba shegiya da bata san ciwon kanta ba.
Ke kuma ni ba mayar da zance ne ya kawo ni ba ki bani lambar waya ko Adireshi na
tafi dan a yau nake so ayita ta qare kafin maganar taje kunnen ubanta".

"Cikin wata nawa ne?" Balaraba ta fada tana janye tagumin da tayi, se Addah tayi
caraf ta ce

"Ko wata tara ne se an cire shi babu ruwanki kawai nidai ki hadani da me aiki badai
maganar kudi bace zan bayar ba matsala"

"Dan Allah Hajia karki barta ta kaini cikin fa wata hudu ne wallahi mutuwa zanyi
Nasan gara ta barni ko a gurin haihuwarsa na mutu nasan nayi shahada Allah yasa
haka ya zamar mun kaffara" Ummi ta fada tana sake rushewa da kuka, se Addah tayi
kanta da duka Hajia Balaraba ta shiga tsakani tana bata haquri

"Fattu Yarinyar nan tafiki gaskiya, ko sarai da kikaga a lokacin munje an cire wata
biyu ba'a ko busa masa raiba magani kawai ya bata tasha cikin ya fita amma wannan
wata hudu fa, kisan rai zakiyi qarshe idan ba'a dace ba itama a rasata gaskiya kiyi
haquri ki dauki qaddarar data zo miki a haka tunda ke kika jawowa kanki. Yarinya ta
kawo mijin aure kinqi ai dole ki karbi duk sakamakoj daya biyo baya kuwa".

"Tashi mu tafi dan Uwarki ai ba ita kadai tasan likitan zubar da ciki ba ke ni da
kaina nan ma sena zubar da shege idan na naushe ki yanzu" Addah ta fada tana
finciko Ummin, se Balaraba tayi saurin tareta da cewa

"Ba a nan ba wallahi ku fita can idan ma kin kasheta a daure ki ke kadai baza'a ce
a gidana a kayi ba" haka ta taso qeyar Addah har Get Addah na zazzaga rashin
mutunchi tuni yan unguwa suka fara taruwa ana kallonta haka dai ta angiza qeyar
Ummi har tati tana kuka kafin suka samu Napep kai tsaye tace a kaita wani Sha ka
tafin Private Asibiti data taba zuwa duba wata qawarta a can qasan gurin GSU, a
yanda taga kalar likitan ta tabbatar ze iyayin komai in dai ze samu kudi.

Ita se yanzu ma ta tuno dashi da meze kaita gurin wata balaraba harta bata lokacin
ta a banza.

AMIRAH

A tayani bawa yan whatsapp haquri, na sake experiencing irin matsalar kwanaki tun
jiya message dina sunqi tafiya sedai su shigo abinda ya hanani posting a nan kenan
saboda suma basu samu ba

Inata qoqarin yanda zan shawo kan matsalar yan WHATSAPP A QARA HAQURI πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™

And you wattpad readers ban ga kuna following account din ba


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 50


AMIRAH

Wuntsulawa tayi daga kan gadonta zuwa qasa tayi zaman yan bori. Number wayar Addah
ta shiga nema cikin tashin hankali ta ringa kira amma a kashe seta mayar da akalar
kiran zuwa Ummi itama dai amsa daya aka bata wato a kashen.

Bata san sanda kuka ya kwace mata ba, ita ba sakin da Babansu yayiwa Addan ne ya
dameta ba illah zancen zubar da ciki dataji. Bazata taba manta qawarta wata Harira
Sani ba lokacin suna Sakandire tayi ciki a gurin zubarwa ta mutu tun daga sannan
take bala’in tsoron abinda ze hado ace za’a zubar da ciki. Yanzu idan Ummi ta mutu
yaya zatayi bayan duk duniya bata da wata shaqiqiyar yar uwa sama da ita.

Ganin ta kasa samun wayoyinau yasa ta yanke shawarar kiran Sa’adah maqociyarsu,
tasan bazata rasa sanin wani abu da yake faruwa ba nan da nan ta danna lambar tayi
sa’a tana shiga kuka ta daga.

β€œAnty Sa’adah ki taimaka mana ki kaiwa Addah waya nayi ta kiran layin ta dana Ummi
baya shiga” Amirah ta fada bayan da tayi qoqari sosai gurin danne kukan ta.

Sa’adah dake kwance akan gadon ta tayi daidai dan tashinta daga bacci kenan ma ita
ta yatsina fuska tareda hararar wayar kafin tace
β€œAyyah ai kuwa anyi rashin sa’a kin ganni ina gidan mu a can na kwana jiya.

Idan ba sauri kike ba anjima kadan zan tafi idan yaso sena kiraki kuyi maganar”

β€œShikenan toh idan ban same ta ba na sake kiranki” Amirah ta fada tana kashe wayar.

Daga can bangaren kuwa Sa’adah tsaki taja kafin a fili tace β€œgayyar tsiya kawai, ni
blocking number ki ma zanyi bazaki sake samuna ba tunda ku baku san mutunchi ba
haka kawai da na saki baki sedai inji ana in matsa za’a shigo da Amarya ko toh
Allah ya toni asirin ku gashi nan kuma yayi mun sakayya ya hada ku da dan shege” ta
sake tabe baki tana gyara kwanciya.

(Abinda ya faru mijinta ne ya ringa soyayya da Ummi a boye ba tareda ta sani ba se
daga baya shine ta janye alaqa dasu gaba daya)

Amirah kuwa rasa wa zata kira tayi, fuskarta shabe shabe da hawaye, daga ita se yar
bingikar rigar baccin ta net data kwana da ita wanda hatta da pant din jikinta ana
gani ta fito daga dakinta da tun jiya data shige bata sake fitowa ba kai tsaye ta
wuce su Aliyu dake zaune a palour suna karyawa ta nufi kan Dining inda Bashir yake.

Wata muguwar tsawa ya daka mata daidai sanda ta isa kansa ta tsaya. Kallonta yakeyi
da idanunsa da suka chanza kala nan take saboda bacin rai dakyar ya bude baki yace
mata

β€œKe wace irin dabba mara tunani ce zaki fito a haka ki wuce ta gaban Yara samari?
Saboda baki da tarbiyya ko baki kuma san mutunchin kanki ba bace mun daga nan kafin
na kifar dake”.

Duk yanda ta tsorata da irin tsawa da hargagin da yake mata bata ko motsa taku daya
daga inda take ba, cikin kuka tace masa

β€œTo nima ai dole ce ta fito dani, Baba ya kirani yace ya saki Addah kuma ta tafi ta
kai Ummi a cire mata ciki tsoro nake ji karta mutu ban san ina zan saka kaina”
β€œZaki matsamun daga nan ko se nayi ball dake mahaukaciyar banza kawai, ta mutu mana
ina ruwan wani ko ni na aike? Wallahi kika bari na miqe sena karya miki qafa idan
yaso naga da yanda zaki sake fitowa nan gurin” ya fada yana qoqarin miqewa amma
ciwon kan daya samu dakyar ya barshi ya sake dawo masa yanzu sanadiyyar bacin ran
da zuciyar sa ta shiga.

Waiwayawa yayi inda su Aliyu suke zaune yaga babu kowa seya sauke ajiyar zuciya a
hankali ya kalli Amirah data juya dakinta tana rusa ihu hannaye biyu akai. Ture
abincin gabansa yayi wanda shima Aliyu ne ya hada musu dan ita gwanar se yanzu ma
yaga idonta tun jiya da yamma.

Gaba daya kansa ya masa zafi, ya fahimce wannan yarinyar kwata kwata batasan me
takeyi ba. Idan ma yace ze cigaba da zama a gidan qara masa ciwo zatayi se kawai ya
dauki muqullin motarsa ya

54 / 80