Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   67 / 80

198K to 201K   out of 238.5K words

an yafe
mana laifi"

"Allah ya shiryaka Baba Naziru, ka gaida su Baba zuwa gobe zan shigo nima mu gaisa"
munayi sallama ya wuce.

Seda aka kwana uku da sallah kafin ranar da yamma na shirya zuwa gaida Alhajin su
Bashir. Ko babu komai darajar qaunar da yake nunamun ya cancanci naje, da La’asar
na kwashi Khadija da Alawiyya muka tafi dan ranar gidan mu a cike yake maqil da
Jama’a ranar ake zuwa wunin sallah wasu ma sunzo kenan tunda saura kwana uku a fara
bikin su Bilal.

Da qafa muka tafi muna zuwa kan kwana daidai gidan su Ibbah na kalli gidan ina cewa
“Oh Allah sarki rayuwa ko ina Ibbah yake oho dan nafi shekara goma sha rabona dana
ganshi”

“Wato yanzu har tuno da tsofaffin samarinki kikeyi saboda kin samu yanci, yana nan
kamar ma acikin gidan yake zama da yayi aure kin san Mamansu ta rasu da dadewa da
ya koma Ingila daga baya ya sake dawowa nan” Alawiyya ta bani amsa.

Seda na harareta ina gyara zaman Gyalen kaina daya zame nace “ke se ana zancen
arziqi se ki sako na tsiya meye kuma wasu tsofaffin samari mtsw” haka muka qarasa
gidan su Bashir tun daga waje muke jiyo hayaniyar Jama’ar gidan da alama suma yau
suka zo ga yaransu nan nata wasa a Gareji muna shiga suka hau gaishe mu.

A tare muka rangada sallama kafin muka cire takalman mu muka shiga Palour Dada inda
suke zaune gaba daya suna hirar tun daga kan Anty Amina har zuwa Sadiya autarsu a
mata suna ganin mu sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su.

Afiya ce tayi qarfin halin farayi mana maraba se Samirah da Sadiya da suke kan
Three sitter suka miqe suna ce mana ga guri mu zauna muka samu kujera kuwa muka
harde aka shiga gaisawa ina lura da yanda suke qaremun kallo kamar masu neman wani
abu a jikina sena sake gyara zamana ta yanda zasuga dinkin doguwar rigar Lashin
dana saka ga qafata tasha qunshi haka hannaye na zobuna harda na aro duk na hada na
saka.

“Yanzu fa muke cewa zamu shigo gidan ai mu gaisa se gaku kunzo” Anty Amina ta fada
tana dariyar yaqe, ban tanka ta ba nayi murmushi ina duba wayata da saqo ya shigo,
Yusuf ne yana gayamun sun sauka a Abuja yanzu nayi masa sannu da zuwa da bangajiya.

“Su Asma’u ne lale maraba sannunku da zuwa” Muryar Dada ta katseni se na dago na
kalleta yanda take bude mana haqora haka kawai na saki murmushi wanda na zallar
takaici ne. Daga inda nake na dan zamo kadan na gaisheta, yanda kasan zata goyani
haka ta ringa amsawa ta juya ta koma Kitchen ta kwalawa Fainusa kira se gata ta
fito da qaron Try an shaqe shi da kayan lemo ga Kwanon Dambun nama dana Alkaki duka
aka hado mana.

“Baba yana ciki ne naga bamu ganshi a qofar gida ba” na fada ina kallon Sadiyah, se
Dada daketa faman musha ruwa tayi saurin Amsawa da cewa

“Yana nan, yau din beji dadi bane shiyasa ya zauna a ciki kinsan iskar maraice
yanzu seta tado masa da zazzabi. Kusha ruwa bari nayi masa magana” ta juya ta fita.

Juyawa nayi na kalli Alawa da Khadija da suketa muzurai karma Khadija taji labari
nace
“Kusha ruwa mana Khadija”
“Alhamdulillahi seda muka qoshi kafin muka fito daga gida” Alawiyyan ta fada tana
miqewa, se Khadija ta tashi itama tana cewa

“Muje Anty ku gaisa tunda gurinsa muka zo lokaci yana tafiya”

“Au gurinsa kukazo to ai shikenan, ina namu yayan suke se a turo mana su suzo gurin
iyayansu” Samirah da tun asali daman suna yar tsama tsakaninta da Khadija saboda
sun taba hada saurayi qarshe kuma ba wadda ta aure shi a cikinsu ta fada, se kuwa
ta waiwaya ta galla mata harara kafin tayi magana nayi saurin moqewa ina cewa

“Muje, Anty Amina se anjiman ku Allah bamu Alkahiri”

“Toh Ma’u ku gaida gida se mun shigo daman wallahi bari mukayi mu hadu tare gaba
dayan mu se muzo miki jaje kiyi haquri” Anty Amina ta fada tana taka mana.

Alawiyya da har takai qofa ta juyo tace
“Ku mata jaje kuma meya sameki Ma’u da za’azo miki jaje? Indai zancen rabuwarta da
Bashir ce kuyi zamanku wallahi ba se kunzo ba abu wata da watanni ai tuni muka gama
karbar yan taya murnar base kunzo bama mu yafe muku wallahi”

Gaba daya suka raka mu da ido ina jiyo Fainusa tana cewa
“Kema Anty meye haka dan Allah kina kallon yanda suka shigo suna kallon mutane
kamar wasu kashi ai gashi nan kinja sun gayawa mutane magana mtsw”

“Dallah gafara can an jawo din seki dakeni ai nasan kinji haushi” Amina ta fada
tana harararta.

“Gaskiya dai Yaya Bashir ya luza ji yanda mata tayi luwai abinta zawarci ya karbeta
ba irin wasu ba” Suwaiba data fi kowa iskanci ta fada nan da nan suka fara rigima
da Fainusa dan dai ita kadai ce Bazawara a gurin kuma kowa yasan da ita take tunda
daman sun ba mudai muka shige Palour Alhajin Su Bashir inda Dada harda qara
shimfida mana qatuwar Dadduma akan Carpet din dayake gurin.

Cikin girmamawa muka gaishe shi gaba daya.
“Ki gafarce ni Asma’u wallahi nauyi da kunya ta saka na kasa kiran ki, Bashir be
kyautawa kansa ba amma babu komai Allah yasa hakan shiya fiye muku Alkahiri” Baban
ya fada daga kwance da alama jikin ya takura masa da gaske.

“Babu komai Baba, nima ai nayi laifi da ban kiraka na gaishe ka ba kayi haquri”

“Aa karki kuma ai ke kika cancanci ban haquri,ki ci gaba da haqurin dai in sha
Allahu zaki dauke shi a gaba. Ina Alhaji Abdu? Dazu da safe yazo ai ya kawo mun
magani kin gansu can wai shi likita ne saboda jiya na gaya masa ina ciwon kai da
daddare da zasu tafi” ya fada yana nuna mun paracetamol din da yake gefensa.

“Au wai daman kai ze kawo wa? Yazo yana ta tambayata wai maganin ciwon kai na
zatama shi ze sha na bashi a she nan yayiwo”

“Nan yazo ai ya jima ma, amma fa nayi nayi yaci abinci yaqi wai Mami ta hana su
kwadayi banda abin Abdullahi nan ai gidan su ubansa ne ko yana inda yafi nan ne ko
da yake qila ba’a fayyace masa ba” Dada ta fada da yar dariyarta, sena daga kai na
kalleta kawai nayi murmushi

“Yaushe zaku wuce saboda aiki? Koda yake akwai bikin Su Bilalu na manta se an qare
zaku koma kenan” Baba ya sake fada ba tareda yabi takan zancen Dadan ba.

“Eh se an gama biki Baba, daman sati biyu zamuyi gaba daya”
“Toh Allah ya taimaka yasa ayi a sa’a. Kema Allah ubangiji ya fito miki da Miji na
gari kiyi auranki kinji”
“Amin Baba, Ai Allah ma ya kawo mata sedai ayi Addu’ar fatan Alkahiri kuma”
Alawiyya tayi caraf ta amsa.

“Kai madallah amma naji dadi ubangiji ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu gani kai
nayi murna sosai, Nafi kinji abin Allah ko Baba ya fada har yana miqewa zaune.Dada
da tun fara maganar Alawiyya tayi kasaqe tana kallon ta tace

“Uhm” tareda yaqen dole,har muka gama hirar da zamuyi Baba nata sa mana Albarka
muka miqe. Jakata na zuge na ciro bandir din yan dari biyu sababbi dana tanada na
ajiye a gabansa ina cewa

“Gashi Baba babu yawa a siyi Goro, an jima na turo su su duba jikin naka”
“Kai kai Haba Asma’u dauke kudinki kinji ai gaisuwar da kika zo mukayi ma tafi
komai Nagode Allah yayi miki albarka” ya fada yana turomun kudin se na nufi qofa
ina cewa

“Dada se anjiman ku toh”. Seda Alawiyya da Khadija ko wacce ta qara aje masa dubu
biyar biyar kafin muka kama hanyar gida. Har Get Dada da duk jikinta yayi sanyi ta
rakamu kafin ta juya, har mun fita Samurah ta kwaso da gudu tana tambayata wai
“Anty zan samu chanjin sabon kudi?”

“Sabon kudi ai yana banki Samirah, ki nemi Sa’ad mana sune ma’aikatan banki” na
bata amsa muka qara gaba.

Oh ikon Allah, ada fa idan zanje gidan irin haka sena shaqe uwayen kuloli da Abinci
kala kala, Dubu Goma nan sena aje mata ta goron sallah banda wadda zan rabawa kaf
jikokin gidan idan sunzo sannan su kansu qannen nasa wasu su fake da chanjin sabon
kudi wasu kuma kai tsaye ma zasu ne na basu barka da sallah idan kuma zamu tafi
nawa Yayan ko yar biyar babu me basu idan ba Amiru ba shi daman har gida yake zuwa
ranar idi tareda Sa’ad da Naziru suci tuwon sallah ya raba musu kudi amma matan
babu me karar ko dan kunne ta kawowa Farida seni jaka na hidimta musu nayiwa
Yayansu kai kar Allah ya kawo abinda baze wuce bama.

A daren ranar Alhaji Qarami yaki rani bangarensa yana tuntubata wai ya muke ciki da
Yusuf?
“Mutumin nan na qaunar ko Ma’u, dukda baka shaidar Dan Adam amma ina kyautata masa
zato akanki wallahi ga danginsa suna sonki”

“Uhm toh Yaya nidai ina ta Addu’a Allah ya zabamun mafi Alkahiri dai, kuma fa shi
Yusuf din nan ma ni ban gama gane masa ba. Wai ita matarsa wane irin aure nema suke
tana wata duniya yana wata nifa sau daya naji yace yaje can inda take” na fada ina
gyara zama.

“Wayaga Ballan sori, ke har lissafin wannan kikeyi ma ai in kinji ana da ita da
babu duk daya to wannan mata ta Yusuf kenan. Ita fa tsabar Gayunta ne ta girmi
zaman Najeria, daman yar uban gidansa ce Ambassador Musa Manzo ya aureta uwarta
Baturiya ce.

Shikansa Baban nata irin wannan gantalallen auran sukeyi da uwar tana can America
shi da sauran Matansa suna Nigeria se sanda yai ra’ayi yaje ko ita tazo to itama
Inteesar din da akwai yayarta itama me aure ce duk haka dai suke wannan gantali da
Yusuf din.

Dan haka ma ki saka ranki a inuwa kamar ma ke kadaice bakida wata kishiya dan yanda
kika San ba Mata ba wallahi. Su yawon shaqatawa da zaga duniya da kwalliya suka
saka a gaba. yo tikita ta yanka masa fa yaje ya nemi duk wadda yake so akan dai
tazo Nigeria tayi zaman aure wai kuma a haka sonsa take kamar me badan ma Allah
yasaka nutsatstse neba aida yayi tambari yanzu a neman matan banza tunda auren fa
kusan shekara biyar kenan ana wannan gantalin kawai ki amsa mana musha biki se mu
daura Addu’a qanwar mu ta zama Firs Lady ai mukam ras damu” Anty Ladi da muke cewa
Momi uwargidan Alhaji qarami ta koromun wannan jawabin.

Tagumi na rafka ina jinta, ikon Allah kunji wata sabuwa kuma su haka suke kenan
daga uwar har yayan?

“Toh kinji ai se kuma me kike buqatar sani ki tambayeta” Yaya ya fada yana yar
dariya.

“Kai ni fa Yallabai randa mukaje ganin ginin nan nasa kwana nayi da takaicin da
yanzu mu zamuje muyita iyayi muna zuba kaya gidan qanwar mu, na ringa raya da ina
da Yar data isa aure ko qanwa to fa duk ma yanda za’ayi se an hada auran su da dai
a dakko bare taci arziqin dan nasan aure ze qara.

Harfa na fara tunanin na qyasawa Suwaiba se kuma nace kar kayiwa kishiya hanyar
arziqi se abu ya samu a manta dakai kwatsam se gashi wannan abu ya wakana kai nifa
harda sujudushshukur nayi kana fita randa ka gaya mun maganar nan, yo ko zuwa nayi
na dauki hoto a gidan ai an biyani wallahi”

Sosai muka ringa dariya nida Yaya musamman wai kar ta gayawa Anty Suwaiba
kishiyarya ae arziqi ya samu su manta da ita.

“Ku zauna kuna dariya shi ai yasan me muka gani wallahi keni ko bakyason sa dan
Allah ki aure shi kowa ya san gaba kika ci ba baya ba”

“Aa dai gara tana son nasa dai, ni na zata ma sun gama komai ai yanda yake addabata
da waya duk lissafina kawai mu hada danasu Bilal a daura daga baya se suyi tariya
ko” Alhaji Qarami ya fada

“Ai da ka gama mun komai wallahi yallabi kawai ayi haka, kai infa aka biye ta Ma’u
ba wanda zata so wannan mijin nata me fuskar shanu ya rigada ya rubuce sunanta a
Allon qarfe se ta Allah kawai gara in ma dole za’a mata ayi a wuce Gurin”

Dariya sosia Momy ta ringa bani daman ita haka take akwai abin dariya, tana da
matuqar kirki ta kuma kama girmanta a matsayinta na matar babban wan mu babu raini
haka babu wulaqanci kowa natane sefa wanda yazo mata da abin da be mata ba bazata
dauka ba.

A gaba da sakani da hudubobi dan Alhaji tashi yayi ya barmu bayan daya jaddadamun
na san matsaya dan Goggo fa dagaske tace tana dawowa dole na fitar da miji nayi
aure kona tattaro na dawo Gombe na bar aikinsa yayi sanadin gurgudewar aurena.

Ranar raba dare nayi ina saqa da warwara, daga qarshe na tashi na raya daren
addu’ata dai a kullum zabin Alkahiri daga Allah (To Hajia Ma’u kwankwasa qofa
za’ayi ace fito ga zabin da Allah ya miki ko yaya? Ke zaki saki ranki ki bude
zuciyar ki sannan ne zaki fahimci abinda Allah ya zabar mikin).

BASHIR
Haka ya sallace cikin quncin zuciya da takaici da dana sanin me yasa ma be tafi
Gombe ba shima. Sallah guda haka ya zauna a gida yana zare ido dama dama ran idi
yaci abinci dan Fried rice Amirah ta daure tayi musu ranar harda Salad ga Zobo me
sanyi da dabgen kaji.

Haka yaci ta a babu yanda ya iya to yaushe rabon ma daya samu kamarta din? Babu
tuwon sallar nan dasu Sinasir da waina kai gaba daya Eatate din qiyau miyau kodan
qamshin abincin sallar nan da zakaji gari ya dauka babu toh duk musulman sun wuce
garuruwanau sallah shima tsautsayi ya zaunar dashi dan be tabayi ba se wannan
karon.
Yana daki yana aikin kallon status din Jama’a na sallah kowa da Yayansa sunje Ido
seya tuna yanda Ma’u take tasa shi su kashe hotuna ran sallah da duk wnada ya kalla
seya yaba wannan karon ko Babbar rigar ma ajuye ya sakata seda yaje masallaci aka
gaya masa ya gyara dan sanda ya shirya ya tafi Matar gidan bata ma fito daga daki
ba bare ta taya shi shiri, daya dawo dai ya tarar ta cancada kwalliya da kayan daya
mata ta kuwa yi kyau sosai masha Allah haka gidan an gyara abinda ya sauqaqa bacin
rabsa kenan sannan ko ba komai ya dan samun abin kaiwa bakin salati.

A status din Amnah yaga hotunan su na Idi, shaddar gurin Yusuf me babar riga yaran
suka saka sunyi kyau kamar ka sace su ka gudu haka ya ringa zooming yana murmushi
da jin kansa na fasuwa wai fa yayansa ne da Ma’u, yo ko dan su ai dole ma ta haqura
ta dawo su zauna.

Hoton da sukayi ita da yaran ta cakare kamar wasu qannenta sun sakata a tsakiya ya
tsaya yana kallo nan da nan ya kwafa ya dora a status dinsa kuwa. Haka ya wuni
kallon hotuna Daya gaji da zaman gida ya fita zaga gari, su Addah dai ana palour
ana warkajami da Kajin da sukayi Dabgensu.

Ranar kwana uku da salllah da yamma sakakiya Dada ta kirashi tana gaya masa abin
tashin hankali zancen wai Asma’u ta samu miji sun daidaita lokaci kadan ya rage ta
daura aure.

Yana zaune a gurin da yake zuwa cin abinci lokacin ta kirashin, tsabar rikicewa
besan sanda ya watsar da lemon hannunsa ba ya miqe jiki na rawa ya shiga neman
layin Ma’u sam ya manta ma da cewar ta toshe shi seda yaqi shiga sannan ya koma
kiran Amnah, akayi rashin Sa’a bata gida sun tafi yawon sallah gidan qawayenta.

Seda ya je mota aka bishi da bill dan be biya ba da ze tafi, Yarinyar nan ce ta
kwanaki.
“Me yasa a koda yaushe kake cikin yanayin damuwa da tashin hankali ne Bawan Allah?”
Ta fada bayan daya bata kudin ya shiga mota.

Harara ya zabga mata yace
“Gafara daga nan kona take miki qafafu” ya figi mota yayi gaba, seta kama baki tace
“Toh daga magana? a sauka lafiya to nima maganina kenan ta juya ciki abinta.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 59

An daura auran su Bilal munsha shagali sosai dan mun dade rabon mu da biki a gidan
mu.
Washe garin ranar daurin auran ba tareda na sanar da Bashir ba muka kwashe kayana
na sedai yaji a gari mukayiwa gidan qaf tsinke bamu bari ba dan wannan dibar kayan
harya fi na Lagos tunda da yan gidan mu mukaje daidai da gadon dakinsa daya siya da
kudinsa seda suka cire wai Yaya sun bani kayansa kuwa haka suka zube masa akan
Katifar dayaci arziqi aka bar masa.

Seda suka ga gida ya zama kango kafin suka haqura, na kwashi abubuwan da nake so
akayi packaging ragowar kuwa Wani shago da suke siyan kayan hannu muka kaisu, sun
siya da daraja sosai dan kayan masu qarko ne da kyau kuma basuyi komai ba tun kafin
mu bar gurin aka fara wawason su suka cake mun uwayen kudadena a akawun muka tafi
zan juya su zuwa sanda Allah ze yanke mun na sake siyan wasu. Kwana uku muka qara
muka tafi dukda naso na bar su qarasa hutunsu se kuma dai muka koma gaba daya.

Tare muka gyara gidan dukda ba wani datti yayi ba dan mun kulle ko ina sanda zamu
tafi. Seda muka gama komai nace wa Aliyu yayi wanka ya rakani mu siyo abinci saboda
saukar Yamma mukayi base munyi girki ba.

Muna tafe a hanya Yusuf da bamu samu mun hadu a Gombe ba ya kirani mukayi magana.

"Mami dan Allah ina so muyi magana" Aliyun ya fada bayan dana gama amsa wayar, sena
waiwaya na kalleshi. Tuntuni na lura da rashin walwalarsa ko biyonin da yayi nasan
da dalili gaba daya ya canza dukda daman bashi da sakin fuska sosai amma yanzu abin
ya qaru ko yaushe yana cikin qunci da damuwa.

"Ina jin ka nima daman inaso nayi magana dakai me yake damunka duk kabi ka takura
rayuwarka Aliyu?" Na fada ina kallonsa.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan daya faka motar dan shi yake janmu saboda gurin da
mukaje babu nisa daga gida.
"Mami bana jin dadin yanda kukeyi keda Abbi, nasan yayi miki laifi amma Mami tunda
ya baki haquri to ki haqura mana ki yafe masa"

"Aliyu ni laifin me Abbin yayi mun? Kuma koma menene ba kana kallo ba ai shiyake
zuwa kullum har inda nake yana takala ta da fada dan haka shi ya kamata kaje ka
yiwa magana ya dena abinda yakeyi tunda har kayi hankalin gane badaidai bane" na
fada fuska a daure dan karma ya kawo mun wani shirme,

"Toh amma Mami.."
"Kaga ni yunwa nake ji zaka shiga ko a mota zaka zauna" na katse shi ina balle
murfin qofar. Seya gyada kai kawai ya kashe motar muka fita yanda muka jera seka
zata irin qanina ne haka muka shiga gurin na samu guri na zauna tareda gaya masa
abinda zeyi mana order.

"Assalamu Alaikum ranki ya dade" naji an fada daga

67 / 80