Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   3 / 80

6K to 9K   out of 238.5K words

abinci”

Kallon rashin fahimta na bita dashi fahimtar haka ya sakata Dafani tace “I’m sorry
kin samu miscarriage saboda faduwan da kikayi”

“Miscarriage kuma? Cikine dani daman?”
“Eh almost 3 months ma baki sani ba?” Ta jefin tata tambayan, se lokacin na gane a
fili nayi magana. Sena qaqalo murmushin dole to ban ma san me zance ba dadi zanji
ko rashin dadi ma oho nan ta barni ta shiga toilet din, mintina kadan ta fito bayan
ta tara mun ruwan. Ita ta rakani har toilet din kafin ta baroni na fara wankan.

Sosai naji dadin ruwan bayan na gama nayi brush da sabon tooth brush din data ajiye
mun na saka pant da pad da duk a nan na gansu sannan na daura sabon towel babba na
rufo kaina da qarami na fito ina jina wata sakayau a raina ina yaba tsarin Asibitin
komai nasu tsaf kamar A Turai.

Turus na tsaya kofar toilet din ganin Mutum a zaune bakin gadon dana tashi wanda da
alama an kuma chanza bedsheet din kai, haka kawai na tsinci kaina da daure fuska
abinda yai ma yara da safe yana dawomun se kawai na juya da niyyar komawa cikin
toilet din yai zuruf ya miqe tare da biyo ni kafin na samu damar rufe qofar ya turo
ta ya shigo ciki bani da zabi kawai na durqushe a qasa na fashe masa da kukan da
ban san nima na menene ba.
https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Page 4

Zama yayi shima a qasan tareda janyoni jikinsa ya rungume yana bubbuga bayana a
hankali, cikin qaramar murya yake cewa “I’m sorry Ma’una I’m sorry” ni kuwa kaman
yana cemun ki qara volume ne. Kuka nake dagaske kukan takaicin daya dade yana
shaqamun, qara tuno wasu abubuwan nake ina qarawa kukan nawa Armashi nasan Bashir
baze hanani ba zebarni nayi iya yina ne a cewarsa kuka rahma ne idan yayi yawa ne
yake zama matsala.

A duk sanda irin haka ta faru ko yayi mun wani abu da har takaini da zubda hawaye
dama shi ba Namiji bane me bada haquri duk kuwa girman laifin da yayi zedai saurare
ki da kunne duk irin mita da qorafin da zakiyi se kinci babbar Sa’a ne zece miki
“Uhmm” in ta kai maqura daya san shi yake da laifi shine ze rungume ni a jikinsa
nayi kukan iya yina yana bubbuga baya na har nayi shiru dan kaina to yau an Auna
arziqi har na samu arziqin sorry, Miskili kenan aka ce kafi mahaukaci ban haushi.
Se ya tunamun da lokacin rasuwar mahaifin mu kamar haka ya riqeni nai kuka a
jikinsa har seda naji wani kaso na radadin zuciyata ya ragu sannan ya rabu dani ya
koma gurin karbar gaisuwa.

Nurse ce ta dawo dakin, sheshshekar kukana da ta jiyo daga toilet ya sakata bude
kofar da sauri a zatonta ko wani abun ne ya same ni amma se ta tarar damu

“Haba Alhaji ya zaka barta tana kuka bayan kasan condition dinta please patient
taso ki zo ki saka kaya a jikinki kar sanyi ya kamaki”. Fincikewa nayi daga jikinsa
na fito ina ci gaba da sheqa kukana, kamar qaramar yarinya haka ina saka kayan
baccin data ajiyemun ina kuka har na gama na dauki Mug din tea data hadamun na
hausha ina kurba ina kuka kai abun ma abun dariya. Tsayawa tayi kawai tana kallon
ikon Allah dan Bashir dai ba sabon abu bane a gurinsa indai Rigimar Ma’u ce, ganin
dai dagaske nake ya saka Nurse fita ta kirawo Dr Bolaji.

Tare suka shigo, kallona yayi ya nufi inda Bashir ya tsaya wanda kallo daya zaka
masa ka hango tashin hankali da damuwar da fuskar sa ta kasa boyewa, ban san me
yace masa ba naga sun fita waje se Nurse din ta juyo wurinata miqa mun magunguna
data ballo tana cewa “kiyi shiru kishanye tunda ya tafi se ki kwanta na mayar miki
da drip din”

Shirun nayi ina jan majina da ajiyar zuciya hancina kuwa yayi jajir kamar me mura
na hadiye kwayoyin tare da gyara kwanciyata raina Fes, a zuciyata nace “Wallahi
kadan ka gani yanda zanyi kwanan Asibiti dalilinka kaima bazaka runtsa da dadi ba,
ko minti goma ban qara ba bacci ya sure ni ga gajiyar kuka ga allurar baccin data
qara a ruwan ko na samu na huta.
Daga ita har Dr Bolaji daya dawo kallona kawai suke Dr yai murmushi ya nufi qofa
yana cewa “This Madam na correct trouble maker”
Nurse ta saka dariya kawai tabi bayansa dan dakko abubuwan da zata buqata ita zata
kwana dani.

BASHIR
Tuqi kawai yake gaba daya baa nutse ba kansa in banda sarawa babu abinda yakeyi, a
duniya babu abinda yake rudashi da hargitsashi irin Asma’u. Matar nan Tasan duk
wani lungu da saqo da zata shiga ta tado masa da hankali (kuji fa) in banda fitina
irin tata shi yanzu ai ta lafiyarta yake yi amma yaga alama ita neman tada zaune
tsayene kawai a gabanta yanzu. Yana tafiya yana jin yadda wayarsa take ta faman
vibrating Daidai ya faka motar kira ya sake shigo masa, a mugun fusace ya daga dan
yasan Amira ce.

Tun dazun ya gaya mata yana da uzuri idan ya gama ze kirata amma shine take zabga
masa kira kamar ta na binsa bashi a qalla ta masa missed calls sunfi 100. Yana daga
wayar ta fara magana cikin Son kwaikwayon salon da Asma’u take magana dashi tace

“Yayana ina ta kiranka tun dazun baka answer ba kafasan duk yau banji muryar ka ba
ga baby ma yana ta misss.....” tsabar takaici be bari ta qarasa ba ya daka mata
tsawar da seda cikinta ya juya sannan ya cigaba

“Ke wacce irin wawuya daqiqiyar yarinya ce, kin kirani nace in na gama abinda nake
zan kira ki amma shi ne kika ci gaba da kira kamar kina bina bashi ko? Shiyasa Ma’u
ta fiki dan ita bata da shishshigi da wannan mugun takurar, Stupid ki sake kiran
wayata wallahi in bani na kiraki ba zakiga hukuncin da zan dauka akanki” qit ya
kashe wayar.

Wani huci yake fitarwa kaman kumurci, gaba daya yaji bala’in haushinta yake ji dan
itace ummul aba’insin ta komai dayake faruwa. Dukda bata shigo rayuwarsa ba da bata
juya masa daddadar rayuwar da suka gino me cike da so, qauna da sadaukarwa ba shida
Ma’un sa.

Yafi minti 30 a cikin motar yama rasa tunanin me zeyi se sannan yaran suka fado
masa a rai ba shiri ya fito daga motar ya shiga gidan. Gaba daya suna zaune a
palour sunyi zuru zuru alamun sun sha kuka sun qoshi har yan biyu basuyi bacci ba,
suna ganinsa suka nufe shi gaba daya tareda sake fashe masa da sabon kuka daya sa
gaba daya yaji dama shima yayi kukan ko zeji sauqin abinda yake ji a ransa.

Dakyar ya samu sukayi shiru, Amna ya tambaya sunci abinci tace Aa, dare ya rigada
yayi dan 12 harta gota dan haka yace ta hada musu cornflake kawai su sha. A qaton
bowl ta hado shi suka hadu kowa da spoon suna sha yana kallonsu dan bayajin ko ruwa
ze iya bita maqoshinsa. “Kai anya ze iya rayuwa babu Asma’u kuwa?” Ya tambayi kansa
“Idan ta mutu fa” wata zuciyar ta qara tambayarsa
“Kai ina insha Allahu ma sena rigata mutuwa” ya fada a fili ba tareda yasan a fili
yake maganar ba da Alama Ma’u na dab da zarar dashi 😂😂

Bayan sun gama yace suje su kwanta amma qememe Suka qi yana tashi suka bishi Amna
Farida da Aliyu ne kawai suka zauna a palour, ba yadda ya iya haka ya jera su akan
gadon ya shiga toilet ya dauro alwala ya fara sallah dan yasan bama ze iya bacci ba
yau, haka yai ta jera salloli in ya gaji ya huta har bacci barawo yai nasarar sace
shi.

HAJIA AMIRAH
Sororo tabi wayar da kallo hawaye na kwace mata ta kalli Mamanta Adda Fatu da har
tafi Amirah kidima dan a hands free ta saka wayar, ita dama bata so ta sake kiransa
ba tunda yace ze kirata amma Adda Fatu ta sata a gaba dan a yau take so ya aikowa
da Amirah kudaden da sukayi qaryar zatayi siyayya saboda tafiyarta Lagos amma wani
uzurin daban take so tayi dasu.

“Adda kin gani ko bamu samu biyan buqata ba yanzu mun ballo matsala Allah kadai
yasan yanzu hukuncin da zeyi mun” ta fada tana share hawaye.

“Ke dalla can ba abinda zeyi miki qarshe ma kiga ya kira ki yanzu ya baki haquri ta
yuwu wani ya bata masa rai kika taka sahun barawo” bata qarasa rufe baki ba sukaji
alamar shigowar message wayarta, baki washe Adda tace “kingani ko duba muga ko
kudin ya sako”

Ita dai Amirah jikinta be bata ba dan tasan waye Bashir a tsorace ta bude message
din ashe MTN ne suke gaya mata zata iya aron kati dan nata ya kusa qarewa. Wata
muguwar dariya Ummi qanwar ta ta sheqe da ita tana tashi zaune daga kwanciyar da
tayi tace

“Wai ke kin yarda Yaya Bashir ne ze kiraki ya baki haquri to sannu uwarsa, ai
wallahi ki shirya ma Allah kadai yasan abunda ze biyo baya dan kinsan sarai fadansa
kamar na kurma yake baya mutuwa”

“To se kijie ki saka shi ya dauki matakin ai dan uwarki shegiya me baqar fuska”
Amirah ta fada tana hayayyaqo mata

“Gata nan a zaune ai uwar tawa baqar fuska kuma na gode keme farar ai gaki nan kin
zama Bora a gurin miji, Allah dai ya rabamu da auran cin Amana” Ummin ta mayar mata
dan itama ba baya bace gurin fitsara. Nanda nan fada ya kaure a tsakaninsu seda
Adda Fatu ta zuzzunduma musu Ashar sannan suka yi shiru kowa tana harar yar uwarta.

“Shegu kuda baku gudun abun magana a daren nan kunsan an kasa kunne a jiyo zancen
mu a yada shine zaku min tijara kishiyoyi naji ni kubarni nayi tunanin mafita ma
kun hanani” ta fada tana hararar su duka. Yunqurawa Amira tayi dan cikinta yayi
girma sosai ta shiga daki har tana takewa Ummi qafa da gangan

“Salon na taba ki wani abu ya same ki ko to bazan kula kiba aniyarki ta biki” Ummi
ta fada.
“Tashi ki shige kafin na rade ki yar kwal uba” Adda Fatu ta fada tana neman madoki,
setayi saurin barin wurin dan tasan tsaf zata sha dukan kuwa.

Tunani ta shiga yi ta yanda zata samu kudi kafin wayewar gari, bashi ne tun na
lokacin Auran Amirah har yau bata gama biyaba kusan shekara biyu dan a zatonta zasu
samu a hannun Bashir din ganin yanda Ma’u take wadaqa sedai tunda akayi auran ita
dai bata ga kyautar dunkulalliyar dubu dari yayiwa Amiran ba, ze dai aje mata komai
na buqata amma baze bata kudi ba.

Ganin ba mafita kuma ta tabbatar kaman yanda matar tace da safe zata biyo kadin
kudinta ko kudi ko kayan kudi tofa rashin mutunchi zata mata dole ta nemi mafita
qarshe ta yanke shaqarar zuwa gidan su Bashir din gurin Nafi ai ita Uwarsa ce idan
ta kira shi baze qi dagawa ba, da wannan shawara ta kwanta akan asubanci zatayi
kafin matar tazo insha Allahu ta dawo.

LAGOS
Malam Bashir kuwa dakyar ya iya farkawa da Asuba kansa kaman an dora masa Dala
tsabar ciwon da yake masa, basu iya fita masallaci ba a gida sukayi sallah suka hau
shirin makaranta dan zasu fara biyawa Asibiti su duba Mami.
Tea suka dafa suka soya kwai suka karya, basu daukar mata komai ba se kaya kala
daya wanda zata saka idan An sallameta tunda Asibitin nada uniform na marasa lafiya
baa buqatar kaya haka abinci ma a can ake basu..

A hankali ya tura qofar hadi da sallama, a nutse ta dago ta kalleshi tareda amsa
sallmar, fuskarta dauke da wani kyakykyawan murmushi. Magana take yi da yaranta
kowa na gaya mata yanda yayi missing nata.

Qara shigowa yayi idanunsa akanta yana qarewa kyakykyawar fuskarta me cike da
kalama kallo ganin yanda Omo blue din Uniform din Asibitin ya amshi fatar ta matuqa
kamar wasu kayan kwalliya. Aliyu ne ya bashi kujerar da yake zaune akai still
idanunsa akan ta yaja ya zauna dukda daqi sake dagowa ballantana ma su hada idanu
da ita.

Shigowar Nurse da taje kawo mata breakfast yasa ta daga kanta Yaran suka shiga
gaida Nurse din tana amsa musu da kulawa, Dan gyaran murya yayi tareda kallon yaran
yace “kuje mota ku jirani kar mu makara idan mun taso se mu sake biyowa aga Mami
ko? Basu musa ba da daddaya suka fice bayan sun mata Addu’ar samun sauqi itama
Nurse aje kayan tayi ta gaishe shi kafin tayi waje abunta.

Cikin sanyi jiki ya miqe zuwa gefenta da tun kafin ya qaraso ta dauke fuskarta zuwa
dayan side din, be haqura ba ya bita, can qasan maqoshinya furta “How are you
feeling now? Ina ne yake miki ciwo?”

“Oh really ka damu ne daman da lafiyata toh Alhamdulillah Yanda kaso be samu ba
jinina ya sauka ya dawo dadai”. Be kula maganar taba ya sake matsarta yana cewa
“Why? Me yasa baki gayamun that you are pregnant ba??”

Ita se a yanzu ma ta gane dalilin wannan fake concern din wato saboda cikin da ya
zube, murmushi tayi me kama da yaqe tana tashi zaune sosai tace
“Baban Ai kenan, to ina ruwanka da ina da ciki ko bani da shi naga yanzu ai baka
damu dani da yaya nane bako? Ko da yake dama ai bazaka damu ba tunda qaddarace
tasaka kuka hada Zuri’a dani
Yanzu ai gashi za’a haifar maka jininka yayan dangi na meye zaka damu akan wanda
Allah ya taqaita samuwarsa bare yazo shima a barshi a titi a bula masa qura ko yaje
makaranta ko kar yaje duk ba matsalar ka bace.

Wallahi Baban Ali kayi nasarar doramun Hawan jini amma ina tabbatar maka bazan bari
ka nakastamun rayuwa ba idan kuwa haka ta faru sedai muyi mutuwar Kasko”.
Kaman wanda aka dasa haka ya bude ido da baki yana Kallon ta, kai wannan Mata wai
ita bata yafiya ne a ko yaushe burinta ta ringa hukuntaka da kuskuren da ka aikata?
To in ba haka ba meye na dawo da wadannan maganganun marasa dadi? Yana shirin maida
mata da martani wayarsa ta dauki qara, hadiye bisashshan yawu yayi kafij ya zaro
wayar yana tattara kalaman da ze bata amsa dasuba zuciyarsa.

Sunan “DADA da ya gani ya saka shi saurin daga wayar ya kai kunnensa. Cikin harshen
fulatanci ya shiga gaisheta ta Amsa tana tambayarsa Asma’u da yara.

“Bashir Meya sami wayarka Amirah tace tun jiya tana kira baka dagawa” ta fada bayan
sun gama gaisuwar.

“Qarata ta kai kenan, ai kuwa seta gane bata da wayo” ya ayyana a ransa a fili kuwa
se yace
“Dada Ma’una ce bata da lafiya tayi Bari muna Asibiti tun jiyan”
“Subhanallahi a garin yaya” ta tambaya muryarta na nuna Alhini se ya sake narkewa
abin tausayi yace

“Nima ban sani ba ina office aka kirani wai ta yanke jiki ta fadi ina zuwa muka
hato Asibiti” ya yanko maganar da shi besan gaskiya ya fada ba ko qarya. Asma’u dai
kallonsa kawai takeyi tana qara mamakin Bashir a ranta, miqo mata wayar yayi seta
tsaya kamar bazata karba ba kome ta tuna kuma ta karba.

Sama sama ta gaida Dadan tareda amsa ya jikin da take mata dan itakam ai sun shata
ta warke abinda mutanen nan suka mata ta yaya zata manta dashi?

Kallonta Bashir yake a ransa baya jin dadin yanda alaqar Dada da Ma’u ta lalace be
kuma san ta yanda ze gyarata ba, yasan sun mata laifi amma Ma’u ma akwai ruqo da
kafiya ai.
Miqo masa wayar tayi ya karba sukayi sallama da Dadan sannan ya kashe. Hannu yaki
ze riqe nata tayi saurin janyewa se ya girgiza kai kawai yace “Ki kwanta ki huta
bari naje mun makara ma idan mun taso zan ga Dr ance be shigo ba yanzu naji yaushe
zeyi discharging naki”

Bata amsa ba shima be saka rai ba dan haka yaja qafafunsa ya fice yana sake kallon
Wayarsa dan ganin da gaskw sun makara din.
Asma’u kuwa da harara ta raka shi kafin ta zumburi baki tana qunquni tace “wato in
dawo kaci gaba da Gallazamin ko toh ba inda zani se na tatike Aljihun ka qat na
huta wallahi”
Ita kadai tayi ta sababi har bacci ya dauketa sannan tayi shiru.

Bashir kuwa sauri sauri ya kai yaran har an rufe get dakyar suka karbe su suna ta
masa qorafin in suka sake makara bazasu karbe su ba shida ya ajiye su ya wuce nasa
aikin da baya zaton ze amfani komai yau. Gaba daya shima ji yake kamar bashi da
lafiya ga wani mugun bacci dayake jin idon sa yayi fici fici har wani yaji suke
masa,haka ya lallaba ya qara sa office din.

GOMBE
Bayan da Dada ta ajiye wayar se ta maida hankalinta kan yayartata Adda fatu datayi
kamar bata gane me Dada da Bashir din suka tattauna ba.
“Ashe Ma’u ce bata da lafiya tayi bari suna Asibiti” Dadan ta fada.
“Allah sarki Allah ya bada na aike” Adda Fatu ta amsata a ranta kuwa murna tayi
gara ma da cikin ya zube ita duk wadannan yayan data zuba bazata haqura ta barwa
Amirah itama ta samu rabonta ba ita dai fatan ta Allah yasa ba ita Amiran ta gado
ba dan ta fara ganin sare sarin hakan, seta gyara zamanta tana cewa

“Kinga daman maganar shirye shiryen tafiyarta lagos din nan ce lokaci nata tafiya
yace ze turo mata kudi tayi siyya anan kafin ta tafi yanda kinga in lokacin haihuwa
yayi ta howa kawai zatayi komai na jiranta a nan to kuma naga yana nema ya shiriran
tar da maganar ga yarinya kuma ko baccin kirki wallahi bata iya yi to Allah ya hada
ta da jarababben ciki gara dai yazo ya tattarata su tafi dan nikam na fara gajia
gaskiya”.

Kallonta kawai Dada tayi ita kam Adda Na bata mamaki da kunya wallahi in ba haka ba
ina ita ina irin wannan magana ai tsakaninsu ne can ko amma ita babu ruwanta tana
manta cewa Matsayin Suruka take a gurin Amira ba kowacce magana ya kamata ta ringa
yi da ita b, dakyar ta bude baki tace

“To Adda nake ga siyayya ai bawata matsala tunda in kayane ai can Lagos sun fimu in
taje din se su siya acan su turo kuma ni da zaki ji ta tawa ma da tayi haquri ta yi
zamanta a nan tunda yana zuwa sati biyu dan gaskiya abinda ake shirin yi ba Adalci
bane. Yarinyar nan Asma’u mun mata abubuwa da yawa ni wallahi har kunyarta nake ji
to yanzu kuma akace wannan gaskiya ya zama da daukar Alhaki kuma.

https://chat.whatsapp.com/GBC9U1ddKHO94q4CSL2jZ8


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar Qaddarah)

Page 5

“Ban gane ba Nafi me kike nufi da ta haqura da binsa ko baki gane halin da yarinyar
nan take ciki bane, yarinya na buqatar mijinta a kusa idan kuma ba halaka ake so ta
fada ba se naji, nifa dama na gane take takenki kina so ki fifita bare akan yar
uwarki ko Nafi. Kuma da kike zancen za’a shiga haqqin Asma’u ita Amirar daba uwace
ta haifeta ba ai ba’a shiga nata haqqin

3 / 80