Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   61 / 80

180K to 183K   out of 238.5K words

kuwa ni din an gaya masa sakarya ce da zezo yana wani kirana a
waya kuma na kulashi.

"Ko dan darajar so ai zaki iya saurar sa Ma'u" wata zuciya ta raya mun se gashi yau
nida kaina na qundumawa wannan zuciya tawa me qoqarin tsayawa Bashir zagi, ban
haqura ba na janyo wayata na goge lambarsa daga ciki sannan na dora layin akan
tsarin da kiran baquwar lamba baze shiga ba sedai naga missed call ni na kira dan
idan ma nayi blocking nasa ze iya chanza lamba ya kira amma yanzu kuwa koda ace ze
sake lamba dari bazata taba shigowa ba.

Ina shirin tashi Yusuf ya kirani. Duk wunin ranar bamuyi waya ba saboda ya gaya mun
tun daran jiya daman yana da Meeting se sanda ya samu sarari ze kira shine se
yanzu.

"Nayi fushi" ya fada bayan da muka gaisa.
"Me kuma ya faru? Kai da waye zakayi fushi?" Na tambaye shi dai dai sanda na shiga
motata.

"Badai se yanzu kike tashi daga aiki ba?" Yusuf ya tambayeni sanda yaji na kunna
motar, seda na mayar da wayar jikin sipikar motar kafin na amsa shi da cewa

"Wallahi se yanzu, kwana biyun nan ayyuka ne suke yi mun yawa shiyasa nake dadewa a
office"

"Gaskiya aikin nan yana wahalamun da mata ya kamata na dauki mataki akan sa fa, ko
dai a rage yawansa ko kuma suyi asarar haziqar ma'aikaciya wadda mayar da kamarta
se an duba".

Murmushi nayi ina ci gaba da tuqina nace

"Naji kace kayi fushi, me akayi maka ne?"

"Oh tambaya ma kikeyi? Kece mana. Gaba daya yau ko kirana bakiyi kinji ya nake ba
ko da yake daman ai baki damu dani ba, ni kadai nake damuwa dake idan banji
lafiyarki ba amma ke nasan ma mantawa kikeyi dani idan ban kira ba".

Yanda yayi maganar ne ya bani dariya har seda na dara kafin bace

"Haba dai waya gaya maka ban damu dakai ba?"
"Ni na ga haka da kaina amma ki fada naji idan kin damu dani din"

"Na damu da kai mana ko ban fada maka ba kaina ai ka sani" na sake fada. Seda yaja
wani murmushi kafin yace

"Na dai jiki kawai amma ni banga haka ba. Kinga ni ina sonki amma nasan ke duk
duniya ma baki da maqiyin daya kaini yanzu".

"Haba wacce irin magana ce wannan Yusuf? Taya zaka ce bani da maqiyi kamar ka
yaushe na gaya maka haka?"

"To idan ba gaskiya bane ki fada da bakinki cewar kina sona mana sena yarda" ya
sake fada yana yin qasa da murya kamar me rada. Ba tare da tunanin komai ba nace

"Ina sonka mana Yusuf kaifa dan uwa....."

"Karki qara komai kin rigada kin gama magana ai tunda har kika furta kina sona da
bakin ki yanzu zan kira Alhaji Qarami na gaya masa. Daman yace na nemi soyayyarki
shi kuma ze tsaya mun da izinin Allah a wannan karon sena sameki Asmyta" Yusuf ya
katse ni ciki tsananin murnar da muryarsa ta kasa boyewa.

Be barni nayi magana ba ya kashe wayar, mamaki da dariya suka kamani duka lokaci
daya. Wai da girmana da komai Yusuf yayi mun wayo dukda ni bada wata manufa na fadi
Ina son sa ba kawai dai na fada hakan ne jin yanda yayi magana bawai dan har cikin
zuciyata abin da yake raina kenan ba.

Tuqina naci gaba dayi hankali kwance harna isa gida. A bakin qofa na tarar da
Bashir a tsaye ya harde hannaye da alama ni yake jira, na gama daidaita fakin kafin
na fito fuskata a sake na shiga gaishe shi ina qare masa kallo yanda naga gaba daya
ya zabge yayi baqi kamar wnada yayi jinyar shekara daya.
"Bari na shiga sena turo maka yaran seda fa na gaya musu su ringa zama a gidan
ubansu amma saboda rashin ji irin nasu shine suka taho Yi haquri yanzu dana shiga
zan tattaro maka su kuwa" na fada ina qoqarin wuce shi na shiga gida seya dakatar
dani da cewa

"Ba gurinsu nazo ba Ma'u gurinki nazo ina so muyi magana".

"Toh gurina kuma?" Na fada ina kallonsa da mamaki, be amsani ba na ci gaba da
magana ina cewa

"Kaga yanzu na dawo ko sallar magriba banyi ba ga gajiya na kwaso, idan ba abin
sauri bane ka bari ko zuwa gobe Juma'a da wuri zan taso ko kuma Weekend ma kawai
kaga ina gida se muyi maganar"

"Maganar sauri ce Ma'u, na kiraki a waya ma bata shiga na tura miki da saqo duk
babu amsa" ya fada yana tsatstsareni da ido. Ko a jikina, gaba na sakeyi ina cewa

"Koh? Qilan saboda idan banyi saving lambar ba kira baya shigowa ne, to tunda kace
abin sauri ne bari idan na dan huta zan aiko yara se su gaya maka" na fada ina tura
qofa na barshi a tsaye.

Har qarfe tara na gama cin abinci kenan sega Abdallah wai Abbi yace yana jirana. Da
mamaki na kalle shi nace ina Abbin yake dan nifa shaf na manta da mun hadu da wani
Bashir ma har munyi magana ban qarasa cika da mamaki ba seda Abdallan yace mun wai
ai yana qofar gida tun dazu ya saka kujera ya zauna.


Haka na saka dogon hijabi ba na fita saboda dai wulaqanci babu kyau. Yana nan zaune
kamar wani sabon Almajiri na zauna a Empty kujera dana tarar ina cewa

"Kasan shaf na manta ma da munyi magana, koda yake ban zata zama kayi ba tunda nace
idan na gama zan aiko yara su kiraka ai".

Zamowa qasa naga Bashir yayi kamar wanda yaje neman gafara a gaban Dada ya kama
qafata na janye ya riqe qasan hijabina yana cewa

"Ma'u haquri nazo baki akan abinda ya faru tsakanin mu. Wallahi nayi nadama,
sharrin shaidan ne ya angizani kuma na gane kurena na yarda idan babu ke a tare
dani rayuwa ta bazata taba cika ba. Dan Allah ki yafe mun ki Yi haquri mu koma wa
auran mu nayi miki alqawari baza kiyi nadamar komawa zama dani da dan nasan kina
sona nima ina sonki zamu ci gaba da zaman mu cikin aminci kamar yanda muka faro
shi".

Ido kawai na saka masa ina kallon wannan wasan kwaikwayo har ya kai qarshe kafin na
miqe ina cewa

"Ka tashi dan Allah ko da yake kai naga baka tsoron kaga hotonka a Ticktock yanzu
idan ba haka ba meye na durqusa mun. Asma'u ce fa Bashir daka danqara mun har saki
biyu saboda matar so ka kuma bani rana daya tak dana tattara inawa inawa na bar
maka gida har ka manta wannan shine zaka zo kana durqusa mun wai nayi haquri na
komawa auranka?

To bari kaji, shi son da kake iqirarin a koma Saboda darajar sa daga sanda ka
tsinke igiyoyin auran nan suka tattaro Son gaba daya sukayi awon gaba dashi, dama
ai saboda auran ne ko tunda babu shi kaga babu sauran wani so tsakani na dakai, ko
da kaga ina gaisuwar mutunci dakai darajar zuri'ar da take tsakanina dakai ne amma
badan haka ba kai Bashir baka isheni ni Asma'u kallo ba ka sani.

Ada tabbas na So ka amma a lokacin da bansan menene So ba ba ayanzu da na hadu da
limamin So ya fayyace mun shi na gane ma'anarsa ba. Dan haka idan kana mafarkin ni
zan komawa auranka to ka tashi dan kuwa tamkar a baka tsinke a ce ka zunguro sama
ne kaga kuwa wannan abu ne da baze taba yuwu ba kayi sake Bashir nayi maka nisan da
har abada bazaka tarar dani ba"

ina gama fadar haka nayi shigewata gida na barshi a tsaye zuciyata kuwa yanda take
bugawa ina tsammanin wanda yake tsaye kusa da ni ma ze iyajin bugunta.

A karanta da haquri, wani qundumemen uzuri ne ya taso mun beyond my control 🙏🙏🙏🙏


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 55

BASHIR

Kamar wani dolo haka ya rakata da idanu harta bacewa ganinsa kafin ya sauke ajiyar
zuciya me qarfi ya miqe daga durqushen da yayi yana jin kamar an sare masa qafafu
tsabar yanda jikinsa yayi sanyi.

Tabbas Wannan ba Asma'u daya sani bace data jiqu cikin so da qaunar sa, ba Asma'un
da take shiga damuwa saboda damuwarsa ba bace wadda take hana kanta bacci a duk
sanda yake cikin damuwa ko bacin rai wannan wata Asma'u ce ta daban a gabansa.

"Idan ma kana mafarkin zan koma gidan ka to ka farka dan nayi maka nisa na har
abada Bashir kayi sake" kalamanta suka ringa dawo masa a sanda yake jefa qafafunsa
inda shikansa be sani ba dan burinsa a sannan ya ganshi a cikin gida kawai ya samu
makwanci.

Shirim ya fada kan kujera ya dafe kansa da hannaye biyu yana juya shi. Wai menene
SO?Yaya SO yake? Menene tattali da kulawar da mace take da buqata wanda Asma'u ta
rasa a gurinsa da har take iqirarin ta samu wanda ya fayyace mata su?

Allah shine shaidar sa yana son Asma'u son da duk duniya be taba yiwa wata mace
irinsa ba. Yana sonta tana kuma da wani matsayi na daban a zuciyarsa ta yanda
tayiwa sauran mata zarra amma kowa ya gaza fahimtarsa mutane suna yi masa gukunci
da zahirinsa ne kawai ba tareda sanin ainihin abinda yake cikin zuciyarsa ba wai me
yasa kowa ya gaza fahimtarsa?

Dole ya san abinyi ba ze zuba ido yana gani ya rasa Asma'u ba faruwar haka daidai
yake da yankewar duk wani farin ciki da walwala daga cikin rayuwarsa ya shaida
hakan dan kuwa gashi a iya lokacin da suka rabu tun sannan be sake kwanan farin
ciki ba. A kullum sabuwar damuwa da tashin hankali ne suke dirar masa.

Gidansa ya rushe, nutsuwar sa ta gushe lafiyarsa kanta ta tabu a cikin qasa da
watanni shida besan yaya ze tsinci rayuwarsa ba ace ze qareta ba tareda Asma'u a
cikin ta ba.

Wai ma wane ibtila'i ne ya haushi da har ya kaishi ga sakin Ma'u?
"Qaddarah" zuciyarsa ta raya masa se ya dafe kansa da hannu biyu yana fadin

"Hasbunallahu wani'imal wakeel" a fili yana jin yanda qirjinsa yake masa quna wanda
ya zame masa jiki yanzu a duk sanda ya zauna yana tunanin makomarsa da Ma'u to se
yaji wannan ciwon kamar numfashinsa ze dauke wani lokacin.

Wayar sa ya janyo daqyar idanunsa sunyi jajir sun kawo ruwa, lambobinsa yake bi
yana karantawa ya rasa waze kira a yanzu. Duk wadanda ya kamata ya fadawa damuwarsa
a yanzu ya dade da datse alaqa me kyau a tsakaninsu saboda a da yana ganin kamar
suna masa katsalandan a rayuwarsa da qoqarin nuna masa yanda zeyi gashi yau ranar
su tazo amma bashi da kwarin guiwar kiransu.

Lambar Bala ya kalla, wani tuquqin baqin ciki ya taso masa nan take ya danna mata
block tareda goge ta gaba daya. Ba tun yanzu ya kamata ya ankare da ingiza me kantu
da Bashir yake masa ba amma se yanzu da komai ya lalace sannan ya fito masa da
ainihin kalar sa gaskiya.

"Allah sarki Aliyu, Amini na kwarai Rahmar Allah ta kai maka" ya fada yana dauke
kwallar data ziraro masa ta gefen ido, yana kewar Aliyu da gasken gaske Aboki ne
irin wanda ya zamar masa dan uwa wanda samun irinsa se an tona.

Aliyu ne kadai yake iyawa da halinsa, koda ace ya nuna masa gaskiya yaqi binta baya
haqura ze yi ta naci da nusar dashi har se dan karan kansa ya fahimci hakan ya kuma
ya aikata abin hirar su ta qarshe ta sake fado masa snada yake jaddada masa daya
kula da Asma'u domin matar rufin asiri ce Allah sarki ashe shi ya hango masa abinda
shi be gani ba gashi yanzu a daidai sanda Asirinsa ke neman ya bankade Aliyu baya
nan ballan tana ya tayashi maido da mayafin ya lullube rayuwarsa.

Abubakar ne ya fado masa a rai, shi kuwa be yi wannan riqar da ze iya tunkarar
Abubakar a yanzu ba bayan duk abubuwan dasuka faru tundaga auransa da Amirah zuwa
yanzu daya sakar masa qanwa ya tabbatar ma baze saurare shi ba idan kuwa ya saurare
shi to tabbas maganganu ze yayyaba masa da se yayi dana sanin kiransa.

Haka ya ringa saqa da warwara, shi da kansa ya tsinewa hali irin nasa yafi sau dubu
ganin cikin lambobin sama da dari biyar da suke cikin wayarsa ya rasa shaqiqi daya
da ze kira ya gaya masa damuwarsa ya bashi shawara akai.

Duk wadanda zasu bashi shawarar arziqi yayi fada dasu a lokuta mabanbanta lokuta
amfabin zama da mutane lafiya kenan a rayuwa yanzu gashi yana cikin damuwa amma ko
cikin yan uwansa da suke ciki daya ya rasa wanda ze tunkara dan ba saurarar sa
zasuyi ba.

Wayar sa ce tayi qara, da sauri ya daga ganin Naziru ne me kiran a ransa yana
Addu'ar Allah yasa ya sakko ne ya neme shi suyi magana dan yana da yaqinin ko iya
Naziru idan ya shiga maganar ze iya shawo masa kan Ma'u saboda dab dakinta ne akwai
kyakykyawar alaqa sosai a tsakaninsu.

A cunkushe kamar an wa Naziru dole ya gaida Bashir, ya amsa masa kafin yayi shiru
yana jiran yaji abinyze fada

"Jirgin qarfe bakwai da rabi zata biyo idan sun sauka zata kirawoka" Naziru ya fada
a taqaice.

Be damu da sanin wacece me zuwan ba yace masa
"Zan tura maka da Lambar samuel yanzu idan sun sauka kawai ta neme shi ze kawota
gida, yawwa Naziru dan Allah...." qarar da wayar tayi alamar an kashe ce ta katse
masa magana Wato Naziru ya gama jin abinda yake da buqata ya kashe masa waya.

Tagumi ya buga a gurin, ga damuwa, ga Yunwa ga ga kai abubuwan ma sun masa yawa.
Tunawa yayi da ko sallar Isha beyi ba yasa ya miqe dakyar ya wuce dakinsa.

Gaba daya ko ina a hargitse yake komai yana nan zaune da kafafunsa daidai da
takalman sa duk inda ya cire ya ajiye anan suke basu matsa ba yo daman waye ze
gyara masa?

Badan ya tsawatar bama da har dakin nasa zata ringa sauke kwandon hauka da rashin
hankalinta a ciki ai.
Haka ya dauro Alwala ya fara jera salloli yana ta kaiwa Allah kukansa har seda
gabbansa suka gaji kafin ya zauna yana jin yanda cikinsa yake karta.

Dole ya tafi Kitchen ya hada shayi ya sha da burodi dan babu komai idan basu din ba
sannan ya sake dawowa ya zauna a palour se sannan ma ya tuna da beji motsin yaran
ba se ya miqe ya leqa dakinsu Aliyu.

Gaba dayansu suna ciki sun kwanta bacci, dakin Amirah ya koma bega Farida A ciki ba
seya sake komawa kai tsaye ya kunna filita ya qarasa kusada kan Aliyu ya tsaya yana
kiran sunansa.

"Ina Faridah?"
"Tana gidan Mami" Aliyun ya fada a cuskule kamar ma daman ba bacci yake yi ba se ya
juya yana ce masa

"Kayi muku Addua seda safe" ya kashe fitilar yaja musu qofa.

Ranar dai kwanan zaune yayi idan yayi sallah ya gaji se ya zauan ya hau jan charbi
har aka kira Sallar Asuba suka fita masallaci suna dawowa ya kwanta saboda wani
bacci daya ji yana neman fin qarfin sa.

Can kamar a mafarki ya ringa jiyo karadi da hauragiya kamar ta Addah, qofar dakinsa
dayaji ana duka tasa yayi juyi yana jan tsaki saboda katse masa daddadan mafarkin
da yakeyi ya bude ido dakyar yana tambayar waye

"Nice nan Bashir gamu mun iso" ta fada daga waje. Dakyar ya iya tashi ya bude qofar
a ransa yana mamakin wanene ya turo masa wannan matar? Kaf dangi a rasa wa za'a
turo musu se Addah ai ba taimaka musu zatayi ba sedai ta qara masa yawan damuwar
dayake ciki.

"Fisabilillah saboda wulaqanci irin naka Bashir seka turamun wani qedari da ko zo
na kashe ka be sani ba duk ka gama kadamun hanta kasan da yanda na iya gano inda ma
yake a cikin iyafot din ina zuwa kuma naganshi wani basamusen Arne. Nidai badan
sunyi turanci da Naziru ba kuma Nazirun ya gaya mun na bishi babu komai Alqur'an da
sedai nayi ta yawo a iyafot din idan suka gaji da ganina na nuna musu hotonka ai
nasan dai baza'a rasa wanda yasan inda kake ba" Addah ta shiga jera masa bayani
tana riqe da wata qatuwar Akwati kamar wadda tayo hijira.

"Ya akayi suka barki kika taho da wannan jakar" ya fada yana kallon Akwatin tata.

Seta gyara tsayuwa tace
"Kaidai bari ai Allah ya tsinewa mutanen nan seda sukawa jakata tsirara kamar
wadanda na sako uwarsu a ciki, dakyar fa seda Yaron nan Naziru ya biya wani kudi
wai nayi lodi da yawa kafin suka barni na wuto da ita dukda haka seda suka kwashe
mun wasu abubuwan wallahi nidai nayi Allah ya isa".

Juyawa yayi ze koma ciki dan kansa harya fara masa ciwo da wannan surun nata se
kuwa ta tareshi tana cewa

"Ina kuma zaka? Ita Amirar tana ina ko bata ji shogowata bane? Sannan ina zan ajiye
kayan nan ga Yunwa ni ina jin ai se a bani abin kari".

"Ina zuwa" ya fada yana shigewa ciki tareda murzawa qofar key. Wayar Dada ya shiga
kira yana shafa goshinta ko tsayawa gaisuwa beyi ba yace mata

"Dada me yasa zaki turo mana Addah kin manta matsala ce matar nan nida nake neman
sauqi ya zaki qara mun damuwa?"

"Toh Bashir idan ba ita ba wa kake so tazo karka manta fa ita ta haifi Amirah kuma
ko ba haka ba yar uwata ce kaga tana iya zuwa gidan ka ta zauna ai. Nidai Koma mene
ne dai se kayi haquri ka dauke kai kwana nawane da Amirah ta warware ai zata dawo
ne ta barku ko" Dadan ta fada.

Sallama sukayi dan bashida abinda ze kuma fada toh mema zece bayan aikin gama ya
gama ai tun kamin ta taho ya kamata a gaya masa da se ya dauki mataki yanzu kuwa ya
zeyi ma da ita.

Wanka ya shiga yana jiyo yanda take ta mita tana buga masa qofa harya shirya tsaf
kafin ya bude qofar ya fito.

"Wannan wane kalar wulaqanci ne haka, ka barni a gantale ko masauki baka bani ba
idan Nafi ce tazo haka zaka barta a tsaye ka shige daki ka rufo qofa koda yake
mantawa nayi ai ba mutunchi ne dakai ba daman to ina ita Amirah tunda uwarta ce ni
ai bazata wulaqantani ba".

"Nifa bance a turo ki bama kawai ki jira yanzu za'a zo a mayar dake Airpoki wuce
gida" Bashir ya fada cikin hade rai.

"Ai wallahi ko ubanka Amadu be isa ba dan naga guri nan zama me nawuda ta samu
katifa duk baqin cikinka se naci arziqin da kuka tare a nan bakwa tunawa da mu se
abinda kuka ga dama kuka yafa mana ina ita daya shegiyar nace maka tunda ita na
haifa ai bazata koreni ba" Ta fada tana riqe qugu kamar wata qaramar yarinya.

"Tana Asibiti se gobe za'a sallamota" ya fada a cuskule yana qoqarin wuceta.

"Yau naga abinda ya ishe ni, to ka kaini Asibitin mana kana jan qafafu kamar na
zalbe zaka wuceni zamane daram ba inda zani sedai baqar zuciyarka ta kashe ka shege
me baqin halin tsiya@ ta fada tana gyara mayafinta. Ba tareda ya kalleta ba kuwa
yace mata

"Ba'a zaman jinya ki jira da Yamma wanda

61 / 80