Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
mugunta ta gano shine dalilin wannan Dariyar.
Be gama tunanin kuwa ba na fara voice note still ina dariyata nace "Alhamdulillahi
layi ya fara ja ashe? To Allah ya qarawa mazajenmu budi suyi ta auran mana qannemu"
na tura ina sake sheqewa da wata dariyar ganin yanda Safiya Sani Labor keta kumfar
baki da daukan Alwashi kala da kala ita ma yayar Amarya Zulaiha Balarabe tana aiko
da nata.
Masifar da Safiya takeyi seta tunamun da lokacin da za'ayimun tawa kishiyar mun
hadu gurin gate together dabanyi niyyar zuwa ba saboda a lokacin bana cikin
nutsuwata. A kallo daya zaa gane damuwar da nake ciki duk na hargitse, na tuna
yanda ta sakani a loko tana mun wa'azi.
"Wallahi Asma'u kin bani mamaki kin kuma bata wayonki kamar wadda bata san Allah
ba, duk ina karatun islamiyyar da kikayi? Kin karanta Alqur'ani tsaf kin haddace
da fassara amma kina nema ki kasa aiki dashi. Karin auran nan kinsan umarnine na
Ubangiji in har Namiji nada hali da biyu akace ya fara sedai ko in baze iya adalci
ba ko kina so kice Bashir ba Adali bane?? Sannan ma ke ai kiji dadi koba komai
kinsan wadda za'a auro miki ciki da bai baki da fargabar azo a tarwatsa miki gida
tunda Ai Amirah kusan tarbiyyarki ce ma. Haka matar nan ta dage tanamun wa'azi har
na sauketa kan layin gidanta mukayi sallama na wuce a raina ina Addu'ar insha
Allahu itama se an mata taji in da dadi (Ni fa alokacin duk wanda ya bani haquri se
na masa Addu'a Allah yasa shima a masa kuma Alhamdulillah gashi tana karbuwa kuwa
🤣🤣).
Wani mulmulen ashar ta dannomun bayan taji voice dina nan kuwa na samu nayi na ci
gaba da kunnata kafin kace me fada yabar kan Yayar Amarya ya dawo kaina harta na
jcewa qila dani aka hada baki nace oho dai aikin gama ya gama biki saura 2 weeks ,
wannan nishadi ya mantar dani wanzuwar Baban Ali a gurin har wurin 12 sannan yara
suka fito muka ci gaba da sabgogin mu. Gaba daya dai haka muka cinye weekend din ba
dadi tsakanin mu Monday muka koma aiki. Office dinsa yafi kusa da makarantar yara
dan haka kullum shi yake fita dasu ni kuma tunda ina rigashi tashi sena biya na
debo su amma yau bayan mun fito gaba daya har Ahmad ya kama handle ze bude gaban
mota ya dakatar dashu da cewa "kuje Maminku ce zata kaiku"
Sororo nayi ina kallonsa araina nace meye haka toh sukuwa yara suka dauki Murna dan
dama mitarsu kullum yawanci Friends dinsu Momys dinsu ke kawo su school dalilin ma
daya sa na dawo ina dakkosu ke nan dan da duk shiyake hadawa. Tafiya ta qaru haka
nayita sauri gudun makara na samu na ajiyesu amma dukda haka ni seda nayi latti dan
school din tana gaba da office dina innaje sena dawo baya while shi kuma yana gaba
da school din dole seya wuceta zeje nasa office din.
Wuni nayi ina mamaki wato duk sati da sabon salon da ze bullo dashi? Allah dai ya
kyauta.
A daddafe muka cinye satin kullum kuwa sena makara dan kafin na kaisu na juyo
traffic ya fara haduwa, abun takaicin wani sa'in zamu hadu a hanya har Horn ze mun
in na tsaya ajiyesu ya wuce ni abin na qona mun rai ni kuma nayi alqawarin bazan
masa magana ko na tambayi dalilin dayasa yake hakan ba nasan dai duk sare sarin
neman fitina ne in tanka su samu nayi dani a dangi to an dena (Dangin fulani dangin
magana 😎).
Muna haka Weekend ya zagayo wannan karon ma yaransa ya diba suka fita yawonsu,
abunda ya ragemun haushi ranar Saturday wuni nayi rama baccin gajiyar sati daban
samu nayi ba danayi sannan Sunday fita mukayi nima da Matan layin mu dama muna haka
once in a month zamu hada picnic muje beach a dan warware takaicin Namiji 😂😂 mu
shaqi iskar duniya to wannan Lahadin ma can muka wuni dan a gida na fita na barsu
ma muka dawo kusan lokaci daya.
Yanda Bashir ya tsume haka nima na tsume na fita a sabgarsa sam tunda haka yake da
buqata ina jinsa ze raba dare yana waya da Amaryarsa har inji yana ce mata tayi
haquri ta kusa dawowa kusada shi ai, wani lokacin naji haushi wani sa'in nayi
mamaki kai Namiji dai a barshi kawai.
A da idan aka cemun Bashir ze sake kallon wata mace da sunan soyayya zance qarya ne
amma daga sanda ya koyamun hankali ko ji nayi mace na shan Alwashi akan Namiji zan
dakatar da ita dan tabbas Akan Bashir na sake yarda da akace Namiji Badan goyo bane
(Inji Asma'u fa 😁).
Ranar Laraba na tashi da ciwon kai da ya saukar mun da zazzabi, ina nade akan gado
har Bashir ya fita masallaci, a zaune na iyayin sallah ina idarwa na koma kan gado
na nade har ya dawo ya fara shirye shiryen fita office. Dukda ya ganni akwance
which is unusual hakan be saka ya tambaye ni dalili ba abinda yai matuqar qona mun
rai ace har mun kai matsayin haka kamar wasu maqiya to wai duk me yayi zafi ne?
Seda ya gama shirinsa tsaf sannan ya kalleni
"Yau bazaki je aiki ba kenan? Se ki tashi ki miqasu karsu makara" yasa kai ya fice
daga dakin. Wasu hawayen baqin ciki ne suka fara tsere a fuskata, idan Bashir ya
gaji da zama dani gara ya fito ya fada mun yafi wannan Kisan mummuqen da yakeyimun
ai, shigowar Jafar ta sakani share hawayena, ya matso kusa da ni yana cewa
"Mami mun shirya fa ko Abbi ne ze kaimu yau?" Cikin muryata da kuka ya fara dishewa
nace mace
"Kuje maza ku bishi Jafar bani da lafiya"
Nan da nan fuskar yaron ta chanza zuwa tausayi yace "sorry Mami kinsha magani toh?
Bari na hado miki breakfast to Abbi baze kaiki Asibiti ba?"
Dole na qirqiro murmushin dole nace "it is not that serious Jafar Kaina ne yake
ciwo nasan stress ne dana qara hutawa ze dena, maza kuje ku tafi and don't tell
your brothers ku wuce Makaranta kawai Allah yai muku Albarka ya bada Ilimi me
amfani" na qarasa ina dafa kansa se ya amsa da "Amin Mami Allah ya baki lafiya, Bye
love you" ya mun peck a goshi ya fita da sauri dan su kansu kwana biyu ba wani gane
kan Abbin suke ba.
Yana fita na miqe dakyar na tsaya bakin window ina hangensu,
Shiya gaya musu Abbi ne ze kaisu dan haka suka fita da sauri dan har ya gama Shan
Tea ya fita yama kunna mota. Da ido ya bisu ganin sun jere masa a gaba, cike da
baqin miskilancinsa yace " yadai kunzo kun mun layi a gaba?"
"Abbi Mami ce tace kai zaka kaimu bata da lafiya" cewar Jafar.
Seda gabansa ya fadi jin bata da lafiya dan ciwon Asma'u ba abune me sauqi ba, irin
mutanen nan ce da suke dadewa basuyi ciwo ba amma in ya kwanatar dasu kamar
bazasuyi ba. Harya niyyata daya koma yaji me yake damunta se wata zuciyar tace masa
qila dan taja attention dinsa ne ya sakata kwanciya tace musu bata da lafiya dan
Asma'u can pretend yasanta sarai dan haka ya qara gintse fuska tareda bude qofar sa
ya shiga yana cewa "kuje ku ce mata tazo ta kaiku you are getting late"
"Abbi kana jifa yace bata da lafiya base ka kaimu ba tunda hanyar zaka bi" Farida
ta fada dan ita yar gaba gaba ce daman, be amsata ba yai wa motarsa key ya qara
gaba se suka rakashi da idanu gaba daya kamar yanda nima Mamakin sa ya nemi kashe
ni a tsaye BASHIR dai shine haka? BASHIR dana sani me jarabar son yaya da
tattalinsu kamar kwai, to kodai shiga tsakanin mu akayi da BASHIR ne?????
https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
Page 3
A salube suka shigo gidan gaba daya suka zauna A palour banda Abdallah daya zarto
dakin da nake, yana ganina ya wullar da school bag dinsa ya taho da gudu jikina se
ya sa kuka, nasan kukan me yake Abdallah akwai son karatu indai ba ciwon gaske ba
baya Missing school.
Bubbuga bayansa nake da sigar rarrashi ina qoqarin hana nawa hawayen fitowa.
“Mami kinga Abbi ya tafi ya barmu kuma Yah Jafar ya gaya masa bakida lafiya amma ya
tafi” ya fada in between tears, se na jashi zuwa gefen gadon dan jin kaina yana
dada sarawa ga zazzabin na sake ruruwa.
“Ka dena kuka, sauri yakeyi yana da meeting ne shiyasa”
“Mami bafa yanzu bane se 10 naji yana waya da Uncle Samuel ai”
“Abdallah bana hana ka ba, idan babba ya fada maka magana ka dena jayayya”
“Amma Mami...”
“Shiii ya isa kirawo mun Amna se na kira muku Uber ya kaiku” na katse shi dan bana
son aja maganar, fita yayi ba jimawa Amna ta shigo itama fuskarta da damuwa.
“Ki dauko wayata kiyi muku order Uber bazan iya driving ba bana jin dadi” na fada
mata ina kaiwa Kwance jin jiri na dibana.
“Mami ko mun tafi ma kafin muje mun makara bazaa bude mana get ba sedai kiyi waya
ki fada bazamu zo ba”.
Agogo na kalla tabbas kafin a samu uber su tafi lokaci ya qure dan haka na miqa
mata hannu ta bani wayar, Number da suka tanada dan wani uzuri nayi dialing dakyar
ina ringing kadan suka amsa, cikin muryata dake nuna halin da nake ciki nayiwa
receptionist din bayanin Bazasau samu zuwa ba bani da lafiya Abbinsu kuma yayi
tafiya, fatan samun sauqi tayimun tareda cewa idan gobe ma babu me kawo ayi musu
Registration na school bus tunda tana zuwa har nan estate din namu, shaf na manta
da zancen ma school bus se yanzu dan haka ba bata lokaci nace tayi kawai.
Har na gama Amna na tsaye bayan na aje wayar tace “Mami in kawo miki ko tea kisha
se kisha Paracetamol kafin Abbi ya dawo kuje Asibiti?”
Kai na daga mata ta fita ba dadewa se gata da try ta doro tea se toast bread da
kuma paracetamol da ruwan roba. Da daddaya suka shigo suka mun sannu har sannan
Amna na tsaye seda na shanye ta ballomun maganin nasha nakwanta sannan ta fita.
Koda na farka bayan Azahar na danji dadin jikina dan zazzabin ya sauka sefa ciwon
kan da sauran jiri da nake ji, wanka na lallaba nayi na dauro Alwala a raina ina
qara mamakin Baban Ali da haryanzu ko waya beyo yaji sun tafi ko basu tafi ba.
Agunda nai sallah na zauna naji anyi knocking, izinin shigowa na bada Aliyu ya
shigo da Sallama hannunsa dauke da Babban try da suka dora abinci.
“Mami kin tashi tun dazu muke leqowa kina bacci”
“Na tashi Yaya (haka nake kiransa saboda qannensa su saba) ina su Ahmad naji
shiru?” Na tambaye shi
“Bacci suka kwanta bayan mun dawo daga masallaci, Maman Ruth ta shigo muka ce mata
kina bacci(Maman Ruth maqociyarmu ce)”
“Lallai an samu yanda ake so bacci yanzu, me kuka dafa ne” na fada ina jawo try din
gabana.
“Irish porridge Yah Amna ta miki mu kuma Rice and Beans muka ci da fish”.
Kwanon na bude faten se tururi yake da qamshi kai kace Wata babbar chef ce tayi
girkin. A plate na zuba wanda zanci muna dan hira da Aliyu har na gama ya kwashe
kayan ya fita se nima na fito palour dukda dauriya kawai nakeyi amma kaina yana
ciwo sosai, ban idasa zama akan kujera ba wani irin jiri ya kwashe ni daga nan ban
sake gane komai ba nidai na farka kawai Na ganni kwance a gadon dana tabbata na
Asibiti.
BASHIR
Tunda ya bar gidan hankalinsa ya kasa kwanciya, har ya kai get din estate din ya
juyo da niyar daukansu se kuma Shedaniyar zuciyar da take ingizashi ta sake yi masa
fanfo. Har ya kai office yana tunanin sun taho ko basu taho ba lokaci lokaci yana
duba Mirrow koda ze hango su a bayansa amma shiru harya wuce makarantar tasu. Yana
shiga Office be zauna ba ya kira layin makarantar ya tambaya ko sunzo nan matar ta
sanar dashi Madam ta kira ta bada excuse ai haka ya aje wayar jiki a sanyaye jin
dagaske dai ashe bata da lafiyar ba lambo tayi ba kaman yanda yayi tunani, duk haka
ya shiga aiki sukuku babu kuzari har sanda ya shiga Meeting kafin su shigama yana
Kallon kiran Amira amma yaqi dagawa dan se yaji yana jin haushin ta ita ce ummul
Aba’isin ta komai da yake faruwa ai.
Tun yana sallar Azahar da be samu yi ba se qarfe uku bayan sun fito daga dogon
meeting din da suka share awoyi sunayi wayar sa take ta qara dan ya manta be sakata
a silent ba, yana sallamewa wani kiran ya sake shigo wa ya zarota a fusace dan ya
ayyana Amira ce kadai zata iya masa irin wannan kiran mahaukatan sedai ya cika da
mamaki ganin Number Asma’u da yayi saving da MA’UNA akan screen. Be kai ga dagawa
ba ta yanke kafin ya yi wani abu aka sake kira se yai saurin dannawa dan tabbas
yasan ba lafiya ba.
Muryar Aliyu ce cikin kuka yake ce masa “Abbi kazo Mami ta yanke jiki ta fadi tun
dazu bata motsi” ai se yaji tamkar a saka guduma an bugi kwakwalwarsa Asma’u ta
fadi meya sameta? Innalillahi.
Ikon Allah ne ya kawo shi gidan kawai yana shiga ya tarar dasu a zagaye da ita suna
kuka kamar wadanda aka cewa ta mutu se ya matsa da sauri ya dagota yana jijjigata
“Asma’u Asma’u ya shiga kiran sunanta. Danshin da yaji a hannunsa daya tallafo
qasan ta ya saka shi duba wurin Jini ya gani wanda duk basu lura ba se yanzu ai
kuwa yaran suka sake rudewa da Kuka kamar me shikansa dauriya yayi ya dagata tareda
cewa Amna da Aliyu su fito suje Asibitin sauran Yaran kuma yace su Shiga gidan
Maman Ruth kafin su dawo dan Anty(Amaryar Ogan sa ta take flat din dake kallon
nasu) ta tafi Zamfara garinsu bikin qanwarta.
Bashi da Nutsuwar da ze ja mota dan haka yau Amna da kullum yaga Asma’u ta bata
driving se yayi bala’i to gashi yau ta masa rana, ita kanta jikinta rawa yake cikin
ikon Allah dai suka qarasa asibitin dan basu da nisa sosai.
Emergency a ka karbe ta, bayan kusan Hour daya Dr Bolaji ya fito daga dakin da suka
shiga da Asma’un. Alama yayi wa Bashir daya biyo shi office
Se ya kalli Amna da Aliyu da fuskokinsu suka kode saboda kukan da suka sha,
“Ku jirani a nan ina zuwa” ya fada tareda bin bayan Dr Bolaji.
Bayan ya nutsu a office din Dr Bolaji ya kalle shi tareda turo masa takardar daya
gama rubutu.
“Strees da damuwa suka hadar mata har ya jawo jininta ya hau sosai shine kuma yai
sanadiyyar fitar cikin jikinta, ga wannan kaje ka kai Pharmacy zasu baka bill na
kayan da akayi amfani dasu se ka karbo wadannan magungunan kuma, Allah ya taqaita
abun amma ku kiyaye faduwa irin wannan ko a gaba ze iya jawo mata Paralyze bama dai
fatan hakan” Dr Bolaji ya fada cikin harsheb turanci yana maida kai ga takaddun
dake gabansa, kamar kazar data sha ruwan zafi haka Bashir ya miqe ya nufi Pharmacy
din dan karbo magunguna.
Sanda ya dawo ya tarar da Nurse ta fito daga dakin da Bedsheet a hannunta daya baci
da jini da kuma kayan jikin Asma’u da suka kawota dasu. Tambayan ta yanda zaayi da
maganin yayi tace ya shiga dasu ya ajiye zata dawo yanzu seya tura qofar dakin a
hankali ya shiga.
A ciki ya tarar da Aliyu da Amna kowannensu na share hawaye nan da nan yaji shima
hawaye da be zata ba sun sakko masa, shikenan ya rasa Babyn da be masan dashi ba.
Allah ya dorawa Bashir jarabar son Yara a rayuwarsa, ya kance shi beqi ya haifi
yara Ashirin bama in ya fadi haka Asma’u se tayi dariya tace
“Haba se kace Akuya in dai ba kuma mata hudu zakayi ba”. A lokacin ya kan ce mata
ke zaki zama Akuyar kuwa kiyi ta zubo su dan kinsan nidai babu gurbin wata mace
bayan ke a cikin rayuwata. ko bayan data haifi Yan biyu Asma’un taso tayi planing
acewarta yaran sun isa haka amma ya fitittike yace idan tayi koda be sani ba be
yafe ba dan shi yana son yaga ya tara zuri’a masu yawa kuma Alhamdulillah yanzu
Allah ya hore masa yana da yanda zeyi ya kula dasu, yasan bazatayi ba shi yasa
dadewar da tayi bayan Yan biyu be dame shi ba yasan daga Allah ne bayan haka dama
ance in shekaru suka fara ja haihuwar na ja baya ita ma kuma Asma’un na kusan
shekaru 33 ne yanzu.
A hankali ya ajiye ledar kan drawer dan Nurse tace karsuyi motsi me girma daze
farkar da ita ya qarasa gefen gadon yana kallonta tayi wani fresh tana bacci kaman
bame ciwo ba se ya rankwafa kanta tareda kissing goshinta, under his breath yace
“get well soon my Ma’u, I’m sorry for hurting you”.
Zaman kurame sukayi shida yaran kowa na tunanin abinda ya dame shi basu Ankara ba
se jin kiran sallar Magriba sukayi se a sannan ya tuna ai ko La’asar beyi ba. Shida
Aliyu suka tafi masallaci har suka dawo kuma bata farka ba dan haka cikin damuwa ya
koma gurin likita yana gaya masa.
“Babu damuwa mun mata Alluran bacci ne dan ta samu ta huta sosai jinin ya sauka
zata farka amma se zuwa cikin dare, kaje kawai kayi settling bills babu buqatan me
jinya Nurses din mu zasu kula da ita”.
Jiki a sabule ya koma dakin, Gurin da Su Aliyu suke ya kalla yace su tashi su tafi
gida
“Abbi ni zan kwana a nan” cewar Amna
“Aa baa barin me jinya mu tafi da safe kafin ku tafi school se mu biyo ku dubata”.
Dakyar suka tafi har shi kansa ji yake kaman ya sake zama sedai tuna sun bar sauran
yaran yasa dole suka tafi bayan ya biya kudin duk abinda ya kamata ace ya biya din.
ASMA’U
Basufi awa uku da tafiya ba na bude ido lokacin qarfe tara na dare harta dan gota,
jinina yana da qarfi sosai ba kasafai Allurar bacci take daukata na dade ba.
Sakayau na tashi kaman an zare mun qaya dukda bansan ainihin abinda ya same ni ba
amma babu ciwon kan babu jiri se kawai kasala da nake ji da kuma bakina da sam ba
dadi. Ina qoqarin miqewa Nurse ta shigo tana ganina ido biyu ta fada da fara’a tana
cewa “Sannu patient har kin farka lallai kina da qarfin jini muda muke tunanin se
kin kai gobe ma”
“Murmushin na mayar mata cikin muryar marasa lafiya nace “gashi har na tashi kam
amma naji dadin jikin ma sosai ai”
“Karki tashi Bari na sake duba Bp na gani” ta fada ganin ina qoqarin miqewa daga
gadon, zama na koma nayi ita kuma ta dauko Abun auna BP, seda ta gama ta kalleni
still tana murmushin tace “kinga kuwa yayi normal bari na hada miki ruwa to ki
wanke jikinki dukda naga bakiyi staining bama se kici