Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
da uwarta taja masa ma bata
dameta balle taji ya qafarsa kawai kudi ze bata a mugun fusace ya nuna mata qofa ba
tareda yayi magana ba.
Amirah dake ta Addu’a a ranta Allah yasa ya bata goman ta ajiye dan tunda tazo sile
biyar bata hadasu ba kai ko katin waya bashi ne kusan dubu biyar taci na Mtn saboda
ya dena saka mata, da tana Gombe kuwa duk satin Allah yar dubu dayar nan dai seya
saka mata wani lokacin ma biyu ga yar cuwa cuwar da takeyi ta karbi kudi a hannun
Naziru na cefane anan kuwa shi yake siyo komai kuma se abinda ta gani kawai dan
waca wacar nan data san anayi a gidan bata san me yasa yanzu kusan komai a
qididdige yake ba ba yanda ta saba ganin sanda Anty tana nan komai na danqare a
Freezer ba sedai su bude su diba.
Ita da yake ya raina mata hankali se abinda yaga dama yake siya ya ajiye kuma idan
ya qare abinda yake ci ze siyo da wuri, daman nama ne yafi damuwa dashi, tana son
kifi amma tunda tayi masa wani farfesun kifi ita kanta dai ranar data ci haka
qarnin yayi ta taso mata be sake siyowa ba tayi nacin harta gaji to tunda ta samu
ciki ma ya dena cin abincinta, daman yaran ba ci suke ba sedai su dafa abinda suke
so ko su shigo dashi daga can gidan sedai tayi ta qara qararta ita kadai ga cikin
me dan banzan kwadayi haka zata yita hadiyar yawu idan ta jiyo qamshin abincin
makwafta.
Tsawat daya daka mata ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi dan ashe yana ta
mata magana ma bata ji ba, da sauri ta tattari qafarta tayi waje tana fita suka
kusa karo da Addah dake labe a bakin qofa cikin matuqar takaici Amirah ta kalleta
kafin ta wuce dakinta wata kwalla na sakko mata.
Bashir kuwa sallah kawai ya tayar dan idan ya tsaya takaicin Amirah yana iya shaqe
shi kawai aga ya fadi, so kuma yake yayi isha ya zauna ya tsarawa Ma’u Saqo ya tura
mata dan ya qudurce indai soyayya ce matsalar to kuwa ko Sharukan se dai yazo ya
kwashi kos a gurinsa a wanna karon.
ASMA’U
Bayan dana dawo daga rabon abinci sallah kawai nayi na kwanta dan na gaji sosai
bani na farka ba se dab da magriba. Kiran Yaya Abubakar na gani guda biyu na shiga
bandaki na wanko fuskata da bakina kafin na dawo na zauna na danna kiran lambar sa.
Bayan mun gaisa yake cemun
“Dazu Bashir ya kirani a waya wai yana bani haquri, ban san rashin kunyarsa harta
kai haka ba se yau tukunna nadai ja masa kunne akan karya kuskura ya sake kirana in
ba haka ba yasan sauran”
“Lallai Baban Ali shi har yana da qarfin guiwar kiran ka kenan, haka fa jiya yazo
qofar gidan nan wai yana bani haquri harda durqusawarsa” na cikin mamakin tsaurin
idon Bashir.
“Asma’u” ya kira sunana da sautin da yake nuna muhimmancin abinda ze gaya mun sena
gyara zama dakyau na amsa ina sauraronsa yaci gaba da cewa
“Kafin ki auri Bashir kin taba tambayata abinda yasa bana farin ciki da auran ku ko
to yau zan baki amsa. Bashir Abokina ne kin sani tun na yarinta dan haka nasan
halinsa ciki da bai, halayyata da tashi sunyi kamanceveniya ta wani bangaren saboda
dani dashi murdaddun mutane ne da ake shan wahalar gane gaban mu.
A bangaren auratayya muna da buqatar samun tsayayyar mace me taurin zuciya da
ra’ayin riqau ta yanda dole sedai ko mu zubda makaman mu mu bita ko kuma ya zamana
anyi 50 50 ma’ana kowa ya riqe bangare daya bawai wadda zamu taka yanda muka ga
dama ba kuma ta biyu.
Baki dace da Bashir ba saboda ke mace ce me sanyin hali da saurin yarda tareda
sadaukarwa inda ace Aliyu marigayi ne ya nemi auranki dukda yaso hakan amma Bashir
yayi masa shigar sauri, a lokacin da na zamo kan gaba a komai saboda nasan bazaki
taba nadamar zabarsa ba saboda halayyat ku kusan daya ce, dake dashi zaku ringa
rige rigen kyautatawa junan ku amma Allah be hukunta faruwar Al’amarin a haka ba ya
qaddara cewar Bashir din dai shine Mijinki harda rabon zuri’a a tsakanin ku.
Banaqin Bashir saboda shima mutumin kirki ne kuskurensa kuma ajizanci ne irin na ko
wanne dan Adam kuma na tabbatar da nima da ace irin ki nake aure da ko ba dukka ba
se an samu kwatankwacin halayyar Bashir a cikin gidana saboda nasan duk abinda na
dakko zata yarda kuma ya zauna.
Bance Bashir baya son ki ba amma ki sani son da kike masa ko nace kina bayyana
soyayyarki sama da tasa shi kansa wannan babban dalili ne da Namiji ze riqe ya kuka
juyaki duk ta yanda yaso saboda yasan kina sonsa zakuma ki zauna dashi a duk yanda
yake.
Abinda nake so na gaya miki Ma’u, Bazan hanaki ba idan har zuciyarki ta aminta da
ki koma gidan Bashir amma ki riqe abu guda daya shine ke din dai kece ba wata
sabuwa ta daban ba haka Bashir yana nan a Bashir din da kika sani babu abinda ze
chanza daga halayyarsa ta ainihi duk wani chanji da ze zo miki dashi na dan
lokacine dole wata rana se an koma gidan jiya.
Karki duba kowa ko wani abu ki duba makomar rayuwar ki, Kin cancanci samun rayuwa
me cike da Farin ciki Ma’u kiyiwa kanki gata, idan har farin cikin ki yana tareda
Bashir ki koma gidansa ku zauna zamu ci gaba da binki da fatan Alkhairi kamar yanda
muke miki a koda Yaushe idan kuma kina da zabin daya fishi Allah ya tabbatar miki
da Alkahiri yasa kiyi farin ciki dashi na har abada”.
Shiru nayi kamar wadda aka zarewa laka har Yaya Abubakar ya gama mun magana dakyar
na iya cewa
“Nagode Yaya, nima a yanzu banida wani zabi se abinda Allah ya zaba mun, in sha
Allahu yau zan fara istikara ina kuma fatan Allah ya saka mun duk abinda yafi
Alkahiri a zuciyata Nagode kwarai Yaya Allah ya saka da Alkahiri”
“Babu komai Allah ya jishshemu Alkhairi, Ina Yaran ina fatan dai babu wata matsala
ko?”
“Babu komai Yaya, ai yanzu ma kusan anan suke dan bacci ne kawai yake mayar dasu
can gidan shima wani lokacin anan suke kwana kuma baya magana dan Farida daman ta
dawo nan gaba daya”
“Toh haka ake so, kin gani ko tashin hankalin daman bashi da amfani yanzu gashi a
ruwan sanyi ai kusan sun dawo hannunki, Allah ya wuce mana gaba”
“Amin yah rabb Nagode yaya a gaida su Anty Nasiba” daga haka mukayi sallama ina ta
juya maganganunsa a raina, matsaya daya dai na zauna akai itace ta neman zabin
Allah tunda shine dahir
Bayan sallar Isha ina zaune ina lazumi sega Amnah da leda niqi niqi tun kafin ta
ajiye qamshin abinda yake ciki ya doki hancina nan take kuma na gano na ina ne.
Kallonta nayi da alamun tambaya ta ajiye su kusada ni tana cewa
“Abbi ne ya kirani a waya yace na kawo miki”
“Zaki tattara ki wuce mun dasu daga nan ko yaya, me yasa daya kiraki baki zo kin
gaya mun kafin ki fita ba” na fada ina rufeta da fada. Setayi rau rau kamar zatayi
kuka tace
“Mami Abbi ne fa ba wani ba, kuma ai...”
“Amnah ni kike gayawa Abbi ne ba wani ba Abbin ubanki ne ko yaya? Ki shiga
hankalinki Amnah kuma ki kwashe kayan nan ki fita dasu kafin na bata miki rai”.
Kayan ta diba seda ta kai bakin qofa kafin ta waiwayo ta kalleni tace
“To mu zamu ci Mami idan ke ba zaki ci ba”
“Amnah se naci ubanki idan na taso wallahi ki tattara ki mayar masa idan ba haka ba
zamu gamu”
Da sauri ta fice ta barni ina mita ni kadai, qamshin naman kuma seya tado mun da
tsohon kwadayi dan ina bala’in son Gashin gurin. Seda nayi Shafa’i da wutri na nayi
Addu’oi kafin na fito palour ina jin badan dare yayi ba da tabbas sena fita na siyo
naman nan dan dai bazanci na hannun Bashir ba.
Turus nayi daga bakin qofa ina kallonsu yanda sukayi face face da naman sunaci wasu
nacin shawarma.
“Yanzu Amnah me na gaya miki?” Na fada ina kallonta, se tayi saurin ajiye Naman
hannunta tana zare ido tace
“Wallahi Mami shiya ce mu cinye kuma ma seda Addah da Anty Amirah suka diba da gaba
daya ma suka qwace seda Abbi yayi ta masifa kafin suka bamu kuma Addah ta sake biyo
mu ta dibar musu”
“Shikenan ai kun kyauta, idan kin gama ki dafa mun Indomie ki kawo mun” na fada ina
komawa ciki.
Wayata na dauka, Ina so na kira Yusuf wata zuciyar kuma tana hanani. Saqo ne ya
shigo wayata, Bashir ne na bude na fara karantawa bansan sanda na bushe da dariya
ba saboda ganin irin abubuwan da ya rubuto wato kalaman soyayyane kala da kala a
ciki gaba daya se naga abin wani banbarakwai.
Ina gama karantawa na goge shi ina tuno da wani saqo da Yusuf ya turo mun dazu da
yamma se kawai na danna kiran lambar sa.
“Allah yasa muga Annabi” ya fada yana daga wayar, senayi murmushi me sauti nace
“Amin”.
“Amma Asmy batan lamba kikayi ko?”
“Me ka gani?”
“Babu komai, kawai dai nasan kina sane bazaki kirani a waya ba sedai tuntuben lamba
kikayi”
“To shikenan bari na kashe tunda haka kace” na fada kamar zan kashe din se yayi
saurin tare ni da cewa
“Aa bafa haka nake nufi ba, Allah ya taimaki Amaryar Yusufa barka da dare toh ya
kike?”
“Barka dai Excellency ya aiki ya Jama’a?”
“Aiki Alhamdulillah kinsan kuwa yau wunin Site nayi na dawo duk na gaji wallahi
Asmy, ya gida ya yara ya kuma kewata?”
“Ni na rasa irin son kudinka dai Yusuf, idan ba haka ba dan Allah ina kai ina Wani
supervision na aiki? Dan Allah ka barwa sauran Jama’a suma su samu mana”
Dariya yayi yace
“Asmy kenan, nifa ko Inyamuri baze nunamun neman kudi ba, dazu naje wani qauye zamu
siyo gyada muna zuwa suka lullube motata nace kai ku matsamun ni ba wannan ya kawo
ni ba neman Halal na fito yau”.
Dariya sosai nayi, daga nan muka shiga hira har Amnah ta kawo mun Indomin, Allah
Alah nake mu gama magana ba tareda ya taso mun da zancen dazu ba, seda zamuyi
sallama kuwa yace
“Saura kwana shida, ina Addu’a Allah yasa naji Alkhairi”
“Amin Allah ya sa muga Alkahiri” nima na fada daga nan mukayi sallama.
Ban kwanta bacci ba se gurin uku da rabi na dare, sosai nayi sallolina da Addu’oi
na rufe da sallar Istikara tareda kyakykyawan yaqinin samun haske a cikin
al’amarina na kuma bude zuciyata ko Bashir, ko Yusuf ko ma wani ne daban Allah ya
zaba mun zan karbe shi nayi fatan ya zame min siradin zuwa Aljannah.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 57
BASHIR
Iya bakin qoqarinsa yakeyi gurin aiwatar da abinda Musa ya gaya masa, duk yanda
yasan ze shawo kan Ma’u yi yake amma kamar wadda yake qarawa wuta fetur daman baya
samun ta a waya duk ubannin saqonnin da yake tura mata kuwa bata taba maido masa da
ko guda daya ba.
Ya rasata ina ze sameta suyi maganata fahimta, baya son zuwa gidan ta tunda tace
masa bata so amma dole ya zama me gadin qarfi da yaji, da wuri yanzu yake baro
office yazo kanlayi ya kasa ya tsare amma ko sun hadu ma wani shashasha take mayar
dashi dan daga gaisuwa bata ma bashi damar magana zata wuce abinta.
Abun na bala’in ci masa tuwo a qwarya, ga azumi yana gaba towa baya so suyi azumi a
wannan yanayin. Gidansa daman tuni yafi qarfin sa in har yana son nutsuwa to fa
sedaiya fita waje dan karadi da surutun Addah kadai ya ishe shi. Shi bata barshi ba
ita Amiran da take fama da kanta itama bata tsira ba ga jaye jayen magana da take
dakko masa haka kawai seta wanke qafa ta shiga gidan maqota kuma in dai taje seta
takalo wani abun haka za’ayi ta tararsa ana kawo qararta sedai yai ta aikin bada
haquri.
Kusan sati ana wannan yanayi ranar yana zaune da daddare a dakinsa haka kawai
zuciyarsa ta ayyana masa kiran Goggon su Ma’u.
“Nasan tana sona da Ma’u kuma ita kadai ce zata fahimceni a yanzu in Allah ya
taimaka seta shawo mun kanta a sanyi komai ya daidaita” ya fada a fili yana janyo
waya cike da kwarin guiwa ya shiga kiran Goggo.
Seda ta dan jima tana ringin kafin ta daga da sallamarta suka gaisa yanda suka saba
yana tambayarta jikin Baffa tace da sauqi kafin itama ta tambayeshi su Amirah da
yara yace duk suna lafiya se sukayi shiru gaba daya.
“Lafiya dai ko Bashir naji kayi shiru” Goggon ta katse masa shiru, seda ya hadiyi
wani yawu kafin ya gyara zaman sa ya sunkuyar da kai kamar yana gabanta yace
“Daman Goggo kira nayi in bada haquri, wallahi nauyi da kunyarki ta saka tun
lokacin da abin ya faru na kasa kiranki se yanzu dai na daure nace bari na kira”.
“In banda abinka Bashir meye abin bada haquri kuma kamar wanda ya aikata wani
laifi, shi zaman aure ai raine dashi idan lokacin mutuwar sa yayi kuma ba yanda aka
iya ko da dalili ko babu haka ana so ba’a so za’a rabu, karka ji komai wallahi
Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri a gare mu baki daya” Goggo ta fada a sake babu
damuwar komai tattare da ita.
Cike da qarfin guiwa Bashir ya shafa kai yace
“Hakane wallahi duk abinda ma ya faru Goggo laifi na ne kuma dai sharrin shaidan ne
amma yanzu na gane kuskurena kuma in Allah ya yarda haka bazata sake faruwa ba”
“Ai ita rayuwa daman haquri akeyi amma babu komai ai koma dai laifin waye a cikin
ku Ai abubya wuce Allah yayi wa kowa zabin Alkahiri a gaba”
“Ai Goggo Alkahiri dai yana nan tare damu dan in sha Allah zamu koma kuma babu
abinda ze sake faruwa a gaba se Alkahiri, badan ma wancan tsautsayin daya faru ba
ai da yanzu ma ta dawo dakinta qila tana shirin haihuwa koma ta haihu amma yanzun
ma muna saka rai in Allah ya yarda kafin Azumi komai ze daidaita.” Bashir ya sake
fada da qarfin guiwa.
“Toh haka da sauri har kun daidaita kenan?” Goggo ta tambaya cikin mamaki, se ya
shafa kai kamar yana gabanta yace
“Aa dai tukunna, kinsan mutuniyar ne akwai rikici itama wani lokacin to har yanzu
dai inata ban baki ne amma taqi ta bani dama amma nasan dai in aka ci gaba zata
haqura shi yasa ma na kira yanzu ko za’a dan taimaka a saka baki tunda tana jin
maganar ku qila tafi saurin sakkowa”.
Seda Goggo taja ajiyar zuciya tana jinjina qarfin halin Bashir kafin ta iya ce masa
“Eh to ai duk da na gari da yake so yaga daidai dole yaji maganar iyayensa. Zancen
mu saka baki kuma ai bata taso ba Bashir dan a yanzu Addini da kansa ya bata damar
zabar abinda take so dan ta wuce Budurwa bare ace za’a fada mata yanda zatayi.
Idan taga tana da sha’awar zama dakai mu masu yi muku Addu’ane idan kuma tace Aa
shikenan se muce Allah zabawa kowa rabon Alkahiri”
Yanda kasanta saka guduma ta kwade masa guiwoyi haka yaji duk ya rikice har wata
zufa ce ta tashin hankalo ta shiga zubo masa. Cikintawar murya yace
“Goggo a haqura kuma dan Allah a dai duba ko dan darajar yaran nan Goggo be kamata
mu rabu ba”
“Yo Bashir mantawa kayi dasu sanda ka saketa ne? Kuma ina duk cikinsu babu me shan
Nono. Daidai da Biyu sun isa su riqe kansu su zauna ba tareda uwarsu ba shekara
Bakwai ai da yawa idan ma kuma kana ganin bazaka iya riqe su bane seka kawo mana
daman kai ka damu da abaka yayanka amma mu muna so zamu riqe su Allah ya raya har
zuwa sanda zasu mallaki hankulan kansu.
Sannan daman ina so na kiraka akan zancen Farida, kaga ita mace ce to na nemi
alfarma ka barwa uwarta ta riqeta samarin kuma su zauna dakai shikenan. A gaida
matar gidan Da yaran se anjima” tana gama fadar haka ta kashe wayar bata ma bashi
damar sake wata magana ba.
Kamar wanda akawa mutuwa haka ya zabga tagumi tunda Goggo bata goyon bayansa toh
ina ze kama??
ASMA’U
Sosaina dage da kai kukana da neman zabi zuwa ga sarkin sarakai. A wannan taqin
tsakanin Yusuf din da Bashir har na rasa wanda yafi uzzurawa rayuwata dan yanzu
Bashir ya dage saqon ban haquri da kalaman soyayya karo da karo seya turo mun
Ashirin a rana haka kiran waya sedai nayi ta ganin missed calls dinsa tunda nayi
blocking layin se kawai nayi murmushi na share.
Sauqin dana samu da Yusuf tafiyar gaggawa data same shi zuwa qasar Turkiyya zeyi
wata daya dan se cikin azumi sannan ze dawo.
Yanzun kam Wasai nake jin zuciyata duk wannan qunci da takura da nake ji da wata
makauniyar soyayya yanzu ya yaye, ina matsayin da zan iya karbar ko wanne irin
al’amari hannu biyu bani da wata matsala tartibiya, rayuwata kawai nake a kullum
kuma ina nanata Addu’ar neman zabin Allah a dukkan lamurana ba tare da na gajiya
ba.
Shirye shiryen shigowar watan ramadan muka fara, ana saura kwanaki uku a dauki
azumi ranar da wuri na taso daga aiki saboda ina so muje muyi siyayyar abubuwan da
bamu dasu.
Seda mukayi sallar magriba kafin muka fita, na saka simple doguwar riga da hula se
na yafa siririn mayafi a kaina muna tafe muna hira da Jafar dana dauka yamun
rakiya. Ina ajiye mota ya juyo yana cemun
“Lah Mami ga motar Abbi, shima yazo siyayya daman dazu da safe naji yana cewa Anty
Amirah tayi list tace wai sedai su taho tare..”
“Jafar na hanaka wannan shegen surutun amma baka ji tambayarka nayi ko yaya” na
katse shi ina qoqarin fita daga motar. Biyo bayana yayi muka shiga supermarket din,
kai tsaye Gurin buhun huna muka fara biyawa dan akwai Kunu da qosan sadaka da ake
mana duk azumi sanda muna tareda Bashir, wannan karon ma bazan fasa ba. Dan har a
Gombe ina so ayi dan sosai na samu rarar kudin hayata bana, an fitar da lissafin
zakka da komai amma dukda haka na samu kudi har mamaki nake to wai da duk ina suke
shigewa da bana gane lissafin ne.
Wake da Gero se pastar mai muka siya na bar musu tunda motata bazata dauka ba sa
kawo mana gida se muka wuce cikin kantin muyi abinda ya kaimu, ina tafe ina amsa
wayar da Goggo ta kirani. Saka Albarka ne da addu’ar fatan nasara da dacewa a
duniya da lahira taketa zubamun dan se yau aka gaya mata batun Umarar dana biya
mata.
“Idan naje zan dage da yi miki Addua Ma’u, Alah yasa da an sallace ki fitar da miji
kiyi aure dan zama haka ba qimar mace bace sam” ta fada. Sena marairaice ina cewa
“Kai Goggo gaba daya wata nawa ba auran biyar fa shine har zaki fara maganar na
sake wani, nidai ba yanzu ba danni makaranta ma zan koma na