Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   25 / 80

72K to 75K   out of 238.5K words

ina bacci kamar
wata kafura bayan tasan ko baccin bana iyayi, kuma ni maganin mura nasha shine
bacci me nauyi ya kwashe ni” ta fara qoqarin miqewa, tana sane ta ture kwalbar
maganin dan sauran na ciki ya zube ita kuma ta koma dabas ta zauna a dole jiri take
gani.

Sake yunqurawa tayi ta miqe se ta tafi kamar zata kife Bashir yai saurin tarota
yana cewa “yi a hankali mana” nan idonsa ya saka akan kwalbar maganin, seda ya
zaunar da ita kafin ya daga kwalbar yana kallonta yace “Amirah kina hauka ne, syrup
kika sha saboda kin kasa bacci?”

Kuka haiqan ta saka masa tana cewa “to ni yaya ake so nayi? Bana iya bacci ni kadai
nasan damuwar da nake ciki babu wanda ya damu da ni har kai din ai baka zo ba bate
kasan halin da nake ciki”.

Seda ya yi qoqari ya hadiye bacin ransa, kafin ya sassauta murya yana cewa
“shikenan, yanzu ki daure kiyo alwala kiyi sallah, lokaci yana qara ja” ya juya ya
fita jin ana kiran wayar sa.

Seta miqe tabi bango, dab da zata shiga bayin ta waiga tareda ballawa Fainusa
harara ganin babu wanda yake kallonta ta shige ciki.

Daga Dada ko har Fainu bude baki sukayi suna kallon wannan Drama, ita Dada mamakin
yanda zata ce bata bacci kuma kowa babu me kula da ita, to wanne baccin ne batayi
yarinyar da duk dare seta leqo su kuma ta ganta tana baccin ta qalau kai har na
rana yi take, gaba daya fa jimamin na kwana biyu tayi ta ware se idan taga idon
mutane ne zata wani koma kalar tausayi duk fa tana ankare da ita.

Ita kuwa Fainu Murmushin takaici tayi ta nemi gefen gado ta zauna tana cewa “Allah
ya kyauta” lallai Amirah ba qaramar makira bace, kullum tana jin yanda take
kalallame shi a waya tana raina masa hankali to Yayan shima ba kirki ne dashi ba
bare ka gaya masa gaskiya amma dai jiki magayi.

Sanda ta fito Fainusa kawai ta tarar a dakin, bata so ba dan har wani kwararrabe
fuska tayi a zatonta Bashir yana nan ganin Fainusan yasa ta saki tsaki ta dauki
Hijabinta tana cewa “aikin banza mutum bashi da aiki se sa ido”.
“Wai Amirah ni sa’ar kice? Ni kike gayawa wannan dan uwarki” Fainusa ta fada tana
miqewa tsaye

“Karki sake zagar mun uwa nidai” Amirah ta fada tana murguda baki,

“Idan na zaga me zakiyi?” Cewar Fainusa tana qara matso Amiran,

“Nidai karki sake zagina dai tam” Amiran ta fada kafin ta juya ta tada sallah, idan
badan tsoron kar ko Bashir yana kusa ba da ramawa zatayi ai uwa bata fi uwa ba.

Kwafa Fainusa tayi, taso ta fadi wani abun da be mata ba wallahi seta tsinkawa
shegiya mari idan yaso duk abinda Yayan ze yi yayi. Ai daman saboda taga tana
auranshi ne yasa ta raina uban kowa ko amma zatayi maganin ta wallahi.

“Haka kawai dan mutum yana baqin cikin ana auran dan uwansa baze iya dauke kai yaga
ana abin arziqi ba shine ze takurawa mutane, idan anji haushi mutum ya koma gidan
mijinsa mana” Amirah ta fada daidai sanda Fainusa ta fito daga wanka.

“Idan gidan uban ki nake zaune se kice an takura miki, sannan aure da kike magana
kibi a sannu qaddarar zawarci bata wuce kan uban kowa ba” tana fadar haka ta qarasa
gaban mirrow ta hau shiryawa, amma tabbas yau se yar iskar yarinyar nan ta bar mata
daki.

Ita Amirah zatayiwa gorin zawarci yarinyar da a shekaru ta girme mata da har
shekara shida shine zata tsaya tana gaya mata wadannan maganganun dan kawai
taqamarta tana auran yayanta? Tabbas dole tayi maganinta wallahi.

Ita kuwa Amirah sum sum ta fice daga dakin ganin yanda fuskar Fainusan ta chanza
tasan tsaf zata iya rufeta a daki ta nada mata mugun duka. Tayi tunanin zata
taradda Bashir a Palour seta ga babu kowa, zama ta tayi tana jiyo motsin Dada a
Kitchen din amma hankalin ta be bata ya kamata ta shiga ta taya ta aiki ba.

Bayan Bashir ya gama amsa wayar, harya danno Number Asma’u ze kira se ya dakata.
Wani nauyinta yake ji besan me ze ce mata ba idan ya kira. Seya karkata kiran zuwa
Number Aliyu amma a kashe.

Dadi ma yaji da ya sameta a kashe dan qilan ya zama yana tare da Ma’un hakan kuma
ze zama qari akan laifinsa.

Dakin Alhajinsu ya shiga ya same shi a zaune kan sallaya yana lazumi. Bayan sun
gaisa da mamaki Baban yake tambayarsa yaushe yazo.

Seya shiga shafa qeya yana cewa “jiya da dare Baba, Engineer Sha’aban na biyo zasu
taho tareda His excellency bayan mun dawo daga Delta.

“Kace ko gida ma baka je ba kayi yo nan” Baban Ya fada yana kallon fuskarsa, rasa
abin cewa Bashir yayi dan haka yayi shiru kawai.

“Ka kyauta, tashi kaje” Baban ya fada ya maida hankali ya ci gaba da jan carbinsa.

Yana fitowa ya tare Naziru da ya fito daga Palour Dada da Kofin shayi a hannunsa.

“Ji mana” ya dakatar da Nazirun kafin ya fara masa magana wayar sa tayi qara. Team
leader sune yake gaya masa ranar Monday suna da presentation, dan haka yau idan sun
huta gobe Friday zasu hadu a office dan su tattara reports din hannun kowa” bayan
sun yi sallama Bashir ya kalli Naziru yace

“Kayi mun booking morning flight gobe”.
“Ai Yaya babu jirgi fa, an samu yar matsala sun dakatar da jirgin Gombe zuwa lagos
till further notice. Sedai ka hau mota kaje Kano tukunna ka tafi ta can”.

Kallon sa Bashir yayi kamar me son ganin gaskiyar maganar a fuskar sa, da hannu
yayi masa alama da ya tafi, kafin ya lalubo Number Wani Agent da yake siya masa
ticket ya kira.
Irin bayanin da Nazirun yayi masa dai ya maimaita se ma qari daya masa akan Yau
jirgin qarfe bakwai da rabi ne se na sha biyun rana, gobe kuma babu jirgin Safe se
Shidan yamma.

Godiya ya masa ya kashe wayar kafin ya shiga lissafin yanda zeyi, qarfe 10 na safe
ake buqatarsa a office goben, dama babu zancen yau dan jirgin safe ya tafi yanzu
kuwa qarfe takwas na safe ta gota, indai ba fiffike zeyi ba baya tunanin akwai ta
yanda ze isa Kano kafin sha biyu na rana. Goben da yayi tunanin samu ance sena
Magriba shida yake da Meeting qarfe goman safe to yanzu yaya zeyi??

Wai wane tsautsin ma ya saka shi tahowa yanzu gashi ya saka kansa a cakwakiya da
hargitsin da yake jiransa a can gida, Mafita daya ce kawai Ya tafi a Mota in sha
Allahu dai daga nan zuwa cikin dare ai ya isa. Da wannan shawara yayi Na’am dan
haka ya juya ya shiga palour Dada.

Amirah na kwance akan kujera ya shiga seta miqe ta zauna tana gaishe shi, kujerar
dake kallonta ya zauna ya amsa dai dai sanda Dada ta fito daga Kitchen din ta try a
hannunta. Fainusa ta kwalawa kira ta fito cikin shirin fita, Try din ta bata tace
ta kaiwa Alhajin su sannan ta kalli Bashir tace

“Yanzu zaka karya ne ko se an jima?”
“Eh yanzu Dada, dana gama zan kama hanya ne ma”.

Daga ita har Amirah kallonsa sukayi,
“Da wuri haka?” Dadan ta tambayeshi, se ya miqe yana cewa “Wallahi Emergency ne ya
taso mun a office, kinsan jiya muka dawo toh kuma ana buqatar wasu bayanai gobe
gashi na taho dasu nan kuma babu jirgi dole mota zan bi”.

“Tab amma kaima da ganganci kake, me yasa ka taho kasan kana da ayyuka a gabanka.
Yanzu a yanda hanya take zaka bi mota har Lagos, to kana da tabbacin ma zaka isa
kafin goben nan ina se dare motocin suke tafiya koh?” Dada ta fada tana riqe baki.

“Addu’a za’a mana Dada In sha Allah zamu je lafiya, yanzu dana shirya zanje Tashar,
Idan babu masu tafiya yanzu inaga Zan dauki Shatar mota ne kawai na tafi dan kinsan
su office babu ruwan su dole na kai musu takaddun nan gobe qarfe goma”

“Toh Allah ya rufa asiri, se kije ki hada masa abin karyawar ki kai masa tunda
sauri yake” Dadan ta fada tana kallon Amirah data daskare a gurin. Dakyar ta
yunqura ta tashi, lallai ma. Daga zuwansa jiya da daddare zece yau ze juya, wallahi
qarya yake ta tabbata babu wani kiran office kawai Matarsa ce tace ya dawo shine ze
fake da wani aiki ai kuwa bazata sabu ba wallahi.

Kayanta hada ta kai masa Dakin Nazirun, sanda ta shiga yana wanka, seta nemi guri
ta zauna tana jiran ya fito dan babu yanda za’ayi ta barshi ya tafi wallahi.

Da gudun bala’i ta fada jikinsa tareda fashewa da kuka lokacin daya fito daga
wankan, gaba daya yayi baya kamar zasu fadi Allah ya taimaka ya dafe bango dan a
bazata ta fado masa se ya tureta daga jikinsa yana cewa “ke mahaukaciyar ina ce
zaki fadowa mutum haka idan da na fadi naji ciwo kuma fa, mtsw” yaja tsaki yana
hararar ta.

“Yanzu dan Allah ko tausayina bazaka ji ba, daga zuwanka jiya ko zama bamuyi ba
kaji damuwata ba yau zaka ce zaka tafi saboda wadda ka baro acan tafi ni, shi kenan
kaje, amma sedai ka zaba ko ni ko ita wallahi dan na gaji da yanda kake nuna
banbanci a tsakanin mu. Gara ka rabu dani kaje can ka zauna da matar so”.

Kallonta ya ringayi har ta kai aya. Wai ya zaba ko ita ko Ma’u shi abun ma dariya
ya bashi a ransa yace “idan zabi za’a bani dole sedai na zauna da daya yarinya aike
zan saitawa hanya, na rabu da Ma’u nabi ina naga haske??

A fili kuma se ya saki murmushi ya janyo ta jikinsa yace “Allah ya huci zuciyarki
haba Amaryata, yanzu kina kallo ko gida banje ba jiya na taho garin nan ko iya
wannan be isa ya nuna miki yanda na damu dake ba.

maganar na zaba a tsakaninku kuma ai bata taso ba kinfi kowa sanin Yanda Nake Son
Ma’u, ban kuma ga abinda ze raba ni da ita ba se mutuwa sannan kema saboda ina
sonki na aure ki dan haka ki dena kawo maganar rabuwata da daya daga cikin ku.

And official call na samu dole na bar garin nan a yau, idan kuma so kike a kore ni
daga aikin na rasa kudin siya muku abinci shikenan”.

Qara lafewa tayi a jikinsa, taji haushin yanda ya wani fadi yana son ma’u amma ai
ba qarya bane ita ma ta sani, ganin yana cikin yana yi me dadi yasa ta ce bari ta
gwada sa’arta.

Tana jikinsa suka qarasa kan gadon ya zaunar da ita ya dakko mai ya fara shafawa,
taya shi ta shiga yi kafin cikin muryar shagwaba tace “Yayahh”

Kallon ta yayi ba tareda ya amsa ba, ganin hankalin sa yana kanta taci gaba da cewa
“Toh naji Yaya ka tafi amma da ka gama abinda zaka yi ina jiranka ka dai san
alqawarin da kayi mun ni uku nake so ma ba biyu ba” ta fada tan rufe fuskarta da
hannayenta.

Murmushi yayi yace “karki damu, just be ready for me”.
Murmushin ita ma tayi kafin ta ci gaba da cewa

“Se kuma Yaya gaba daya kayan dakina an lalata su kuma...” ganin kallon da yake
mata lokaci daya fuskar sa ta chanza ya sakata yin shiru,

“Uhm ina jinki kuma me” ya tambaye ta yana saka rigar sa, seta girgiza kai tace “
babu komai”

“Gara da ya zama babu komai din” ya fada yana zama ya jawo kayan abincin ya fara
ci. Seda ya gama tsaf ya zuge jakarsa sannan ya kalleta yace

“Karki sake kawo mun maganar kayan dakin ki ko wani abu, saboda banyi lissafin nawa
damage din nace a biya ni ba ko?
Zan tafi yanzu, zuwa gobe ki koma gida”.

Seta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace “Dan Allah yaya gidan yayi mun girma
da yawa tsoro nake ji, ka barni na koma gidan Addah kaga in nace zanzauna anan ma
kullum fada muke da Anty Fainusa”.

Seda ya kalleta na dan wani lokaci kafin yace “ok ki koma din, shikenan ni zan
tafi”.

Ganin bata motsa daga gurin ba sema yan hawaye da take gogewa yasa yace mata

“Come on babu ko goodbye” ya fada yana dagata tsaye, light kiss ya mata kafin ya
saketa yayi gaba ta bishi a baya. A qofar dakin Alhajin su taci burki, harya saka
qafa jij ta tsaya yasa ya waiwayo ya kalleta
“Shigo mana” ya fada yana qarasawa ciki. Se Alhajin ya dago ya kalleshi yana
murmushi yace “Amirah ce ko, ka barta kawai ban san menayi mata da bata iya zuwa mu
gaisa ba”.

“Hmmm” kawai ya iya cewa sukayi Sallama da Baban yayi masa fatan sauka lafiya ya
fito. Shareta yayi ya shiga dakin Dada itama sukayi sallama kafin ya fito har
Naziru ya saka masa jakar sa a mota.

Tana bayansa kamar Jela suka fita, tunda yaji bata zuwa tana gaida Baban ransa ya
sake baci, gaba daya dana sanin zuwa ma yake yi dan dai babu biyan buqata se kayan
takaici daya kwasa kawai haka ya shige motar Naziru yaja tana tsaye kamar ta kurma
ihu, yanda suka faro a dadin rai taso su qarashe haka ko ba komai ta samu kudin
kashewa yanzu gashi ya tafi da sabon fushi.

Sanda suka isa ya taki sa’ar samun qaramar mota sharon saura mutum biyu dan haka ya
biya kudin mutum biyun kawai ya shiga suka dau hanya. Seda tafiya ta fara miqawa
sannan ido ya raina fata.

Rabon daya je Lagos a mota kusan Shekara Goma sha biyu kenan sanda ya taba samun
wani aiki har aka kirashi interview daga qarshe aka ce wai ba’a dauke shi ba.

Wannan aikin ko lokacin daya same shi da aka kirashi documentation harda ticket din
jirgi Alhaji Qarami ya hada masa na zuwa da dawowa tundaga nan kuwa da Al’amura
suka bude masa shida tafiyar mota sedai inda jirgi baya zuwa.

Akace tafiya yankin Azaba tabbas Bashir ya kwashi Azabar tata. Wata irin tafiya
yayi da a rayuwarsa ze iya cewa be tabayin me wahalarta ba. Haka suka kwana suna
tafiya sau uku kacal suka tsaya shima sallah kawai sukeyi wasu su nemi abinda zasu
ci sannan a qara wuta.

Bashir dai Azumin dole yayi in banda ruwa babu abinda ya shiga cikinsa har suka Isa
Lagos da Asubar Ranar Juma’a.

Firkai firkai dashi kamar wanda ya qwato daga hannun Yan Kidmashin ya shiga
kwankwasa gidan bayan da Shatar Taxi din daya dauko ta sauke shi.

Lokacin Asma’u na kitchen sauran yaran kuma suna zaune a palour suna qarasa saka
sport wear dinsu dan yau Juma’a. Da farko duk basu zaci gidan ake kwanwasawa ba
tunda waye ze zo musu da sassafen nan shida ma yanzu tayi.

Jin Basu bude ba yasa Bashir neman dutse ya hau buga qofar kamar an aiko shi dan a
yanda yake ba shida qarfin da ze fara binciko keys a jakarsa, daga ciki Asma’u ta
fito daga Kitchen din tana kallon yaran da sukayi cirko cirko tace

“Waye wannan yake mana bugu kamar mara hankali” seta nufi gurin qofar. Seda ta leqa
ta yar bular da ake ganin mutum, da mugun mamaki taja baya. Fuskar Bashir ce, tasan
a kowanne yanayi bazata kasa gabe shi ba amma da seta ce wannan me kama da shi ne.

Qofar ta bude da sauri tayi gefe ganin yana neman fado mata ya wuce ciki bayan ya
watsar da kayan sa a bakin qofar, seta kwalawa Aliyu kira ya tafi da sauri ta nuna
masa kayan tana cewa “shigar masa dasu dakinsa” ta juya ciki tana mamakin daga ina
yake.

Bashir kuwa Yana shiga ya zube akan kujera, yunwa, gajiya da bacci sun hadar masa
gaba daya. Kallonsa yaran suka shigayi kamar sunga baqo kafin suka gaishe shi ya
daga musu kai dan baze iya bude baki ba.

Yanda Asma’u tayi kamar bata san da wanzuwarsa a gurin ba yayi bala’in bashi
mamaki, shirinta ta ci gaba daya yi. Yana kallo suka qarasa cinye abin karin su
yaran sukayi masa sallama suka fice gurin mota ita kuma ta shiga daki ta dakko
jakar ta.

Ina sane nayi tamkar na manta dashi a gurin, yana ganin nayi hanyar qofa yai saurin
dakatar da ni da muryarsa a har dashewa tayi saboda yunwa yace “Ma’u baki ganni ba
zaki tafi kuma”.

Seta na dakata na kalle shi, da dan guntun murmushi a fuska ta nace “Na ganka Baban
Ali ai nayi maka sannu da zuwa tunda ka shigo ko baka ji ba?”

“Hmmm” ya fada kafin ya yunqura yana cewa “Nagaji wallahi a mota na taho, gashi
qarfe goma ya kamata inje office ki taimaka mun da abinda zanci bari nayi wanka”.

Se da na saki wata dariyar takaici, ina kada key din hannuna nace “wato ka rantse
dai se ka biyo mota toh ai gashi dai kaji abinda ake ji. Abinci kuma akwai komai na
buqata a Kitchen se ka nemawa kanka kaga mun makara ma se mun dawo” na juya nayi
tafiyata ina jin yanda ya raka ni da kallo har na kulle qofar.

Wato daga dan rainin hankali se Bashir, Allah ya qara. Abinci kuwa babu komai a
Freezer mun cinye kwana biyun nan kuwa ban zauna ba bare nayi ko miya ce na ajiye.

Malam Bashir kuwa dakyar ya iya miqewa ya shiga Kitchen din, ya zata ze samu ko
ragowar abinda sukaci ne ya tarar da wayam, ya bude Freezer nan ma danyun nama ya
tarar babu ko guntun abinci.

Cike da takaici ya bude Fridge din shima babu komai se tarkacen ruwa da lemo se
wani guntun nama ya samu a foil paper ya dauka da sanyin sa da komai ya cinye.

Ganin fa babu mafita ga yunwa ga lokaci na sake qure masa yasa ya kunna Fanfon
Kitchen din ya tari ruwan zafi, Madara da Milo ya zuba sosai ya dagawa daya ya
kwankwade ya sake hada wani yasha rabi ya hango bread ya dauka ya hada, seda yaji
cikin sa ya dan farfado sannan ya haqura yaja kafafuwansa ya tafi daki.

Wayar s ya fara sakawa a chaji dan tun a hanya da dare ta mutu, Yau daya se be ji
haushin abinda Ma’u ta masa ba, idan da haka kawai ne tayi masa wannan wulaqancin
yasan me raba su se Allah amma yau daya tuna girman nasa laifin se yaga ai ba komai
tayi masa ba.

Kamar me maye haka yana layi yayi wo wanka ya fito, badan ba kwanciya zeyi ya dan
rage bacci amma yasan tabbas ya kuskura ya kwanta a yanda yake jin baccin nan qila
sedai ya farka yaga magriba tayi.

Bayan ya saka kayan sa ya tattara abinda ze buqata kafin ya kunna wayarsa yayi
order Bolt, se ya fito qofar gidan ya zauna kamar wani Almajiri, yunwa yake ji dan
ba wai ya qoshi bene kawai haqura yayi idan ya fita se yaci abincin sannnan ga
bacci har ji yake kamar zazzabi ze rufe shi, haka ya hau motar suka kama hanya.

A cafeteria office din su yaci abinci, Patrick abokin aikin sa da suka shiga tare
ya ringa kallonsa da mamaki ganin yanda yake lodar abinci kamar wanda ya shekara be
ci ba, kasa daurewa yayi yace masa

“Bash lafiya

25 / 80