Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   55 / 80

162K to 165K   out of 238.5K words

fice daga gidan.

Yana fitowa yayi mugun gani, Asma’u ce tsaye da wannan mutumin daya tsana sama da
kowa a duniya yanzu suna magana se dariya sukeyi kamar wasu masoya.

A fusace ya nufi inda suke sedai kuma meya tuna yaci burki ya koma da baya
zuciyarsa na masa zafi kamar wanda ake watsawa tafasashshen ruwa.

Motar sa ya bude ya shiga ya kifa kansa akan sitiyarin yana sauke numfashi a jere a
jere, ya tabbatar idan har yaci gaba da ganin Ma’u da wani namiji zuciyarsa tana
iya bugawa ya mutu lokacin sa beyi ba.

A zatonsa tunda har ya bata haquri yace su komawa auransu zata saurareshi ko dan
darajar so da kuma yaran da suke tsakanin su amma se yake gani kamar ma ta goge
shine ma daga babin rayuwarta.

Al’amuranta kawai take yi kamar babu wani abu me suna so daya taba shiga tsakaninsa
da ita, to wai yanzu wa ze kaiwa kukansa ya samr masa mafita ne??

Bala ne ya fado masa arai, se ya janyo wayarsa ya kira lambar Balan a ransa yana
lissafa tsahon lokaci rabonda suyi waya tun ranar daya gaya masa ya saki Ma’u.

Seda ya kirashi sau biyu amma ta qaraci qararta ba’a daga ba be haqura ba ya sake
kira dan dai yau Sunday yasan Balan yana gida ko baya da haka yana da buqatar wanda
ze tattauna dashi ko zeji sanyi a ransa.

Sake kira yayi yana ringin daya aka kashe, ya kalli wayar dan ya sake tabbatar da
rejecting kiran akayi seya sake dannanwa tana shiga kuwa aka sake kashewa abin yayi
bala’in bashi mamaki dan tunda yake da Bala be taba qin daga masa waya ba kai ko
lokacin aiki ne balle har ya kira ya katse se yau amma dai ya kyautata masa zato
qila yana wani uzuri ne a lokacin.

Motar ya kunna kawai ya hau titi yayi ta tafiya idan ya gaji da tuqin ya samu guri
ya tsaya gaba daya zuciyarsa ta hargitse da tunanin Ma’u, ya kasa hasasowa kansa
rayuwa babu ita.

Sati biyun nan kadai yaji jiki dauriya yakeyi dan karya nuna gazawarsa amma yaga
alamar a wannan karon Ma’u ta daura aniyar kaishi qasa so takeyi se taga raunin sa.

ASMA’U
Da safe Yusuf ya kirani akan ze zo anjima ya dauki Ma’u, dakaina na tashi na hada
mata kayanta da yan abubuwan da ba’a rasa ba a nake dasu duk na hada mata kafin na
koma daki na kwanta amma sena kasa komawa bacci.

Tunanin makomata na shigayi a yanzu. Har yanzu na kasa yarda da cewa dagaske Bashir
ya cire ni daga rayuwarsa ba kuma ya buqatar sake zaman aure dani tunda tun waccen
ranar be sake tarata akan makomar auran mu ba kai ni bamu sake haduwa ba ma se jiya
a gurin taron su Amnah.

Wasu hawaye ne suka zubomun na saka hannu na share, tabbas dole na yarda da gaskiya
komai dacinta cewar Bashir baya sona, alfarma yayi mun ya aureni ya zauna dani
saboda tarin soyayyar dana nuna masa.

Haka nan se kuma banji haushin sa ba, so ba qarya bane dan ni zan bada shaidar
hakan kuma ba’a tilastawa zuciya taso abu na yarda duk hasasheb da nakeyi akansa a
baya kawai dan ni ina cikin mayen sonsa ne shiyasa ban taba ganin laifinsa ba amma
yanzu na gane Bashir baya sona idan ma ya soni to be kai ko kwatan irin son da nayi
masa ba, qaddara da rabon haihuwa ta tsawaita zaman mu yanzu kuma da Allah ya kawo
qarshen gashi ya raba mu.

Dole na haqura da Bashir na koyawa zuciyata yanda zata rayu ba tareda shi ba duk da
nasan ba abu bane me sauqi dan da soyayyarsa na raini zuciyata idan har nace zan
cire shi gaba daya daga raina na tabbatar daidai yake da zare duk wata walwala da
jin dadi da sukayi saura a rayuwata ko da yake meya tage mun nema?

Tunda Bashir ya sake ni nayi ban kwana da farin ciki, duk wata walwala da nake
nunawa a iyakan fuskata take amma qasan zuciyata Allah kadai yasan irin wutar da
take ruruwa a ciki amma dole na na koyi rayuwa ba tare da shi ba.

Dole na daraja kaina na haqura dashi tunda har ya fito ya nuna mun alfarma yayi mun
daya zauna dani tsahon lokaci yanzu daya samu zabin ransa ya gwammace rabuwa da ni
uwar yayansa saboda farin cikinta.

A yanzu babu lissafin aure a gabana dan na rufe, bana tunanin akwai sauran gurin da
zan iya saka soyayyar wani kuma bayan Bashir a cikin zuciyata.

Zan riqe kaina na tsaya da kafata na nemi na kaina na zamarwa mata irina da muka
dauki soyayya da zafi madubi na kuma haska musu cewar rabuwa da Mijin da kike so ba
shine qarshen rayuwa ba, sannan duk son da kake yi wa mutum idan har ya nuna baya
buqatarka a rayuwarsa ka barshi koda kuwa hakan yana nufin rasa komai naka in dai
zaka tsira da mutunchinka.

Ina cikin wannan tunanin bansan lokaci yaja ba seda naji wayata tana qara ina
dubawa naga Yusuf ne ashe har qarfe goma da rabi na safe tayi.

Bandaki na shiga na wanko fuskata kafin na dora dogon Hijabi har qasa akan riga da
wandon baccin da suke jiki na, ina shirin Fita Farida ta shigo tana cemun ga Dadyn
Little yazo muka fito tare har qofar gida inda yake tsaye jikin wata shegiyar mota
ya saka qananan kaya a raina na ringa mamakin yanda sam Yusuf baya tsufa, duk sanda
na ganshi gani nakeyi kamar qara zama yaro yakeyi.

“A kwana a hantse se kyakykyawa, Allah yasa dai ban tashe ki daga bacci ba” ya fada
fuskarsa dauke da murmushi yana kama hannun Farida, nima murmushin na mayar masa
ina cewa

“Aa, ai tun sanda mukayi magana dazu ban ma koma ba ina zaune, ban ma zata da wuri
zaka zo ba ai”.

“Ta matsa na mayar mata da yarta inaga gobe zasu wuce” ya fada yana bina da wani
kallo da gaba daya ya saka ni diriri cewa. Sakin hannun Farida yayi yace mata taje
ta hadawa Ma’u kaya tana wucewa ya matso inda nake tsaye yana cewa

“Kinga yanda kike wani kyalli kuwa daman ashe kin fi kyau babu kwalliya ban taba
sani ba”
Saurin ja da baya nayi nace “Yusuff..” be bari nayi magana ba yayi saurin tareni da
cewa

“Yi haquri, ni kaina idan ina tare dake kasa riqe bakina nakeyi amma dagaske kin yi
kyau Ma’u, ina so naga Mace da Hijab ga wannan qamshin naki ya ilahi Allah kadai
yasan yanayin da yake jefani”

Juyawa nayi, seda na kai bakij qofa nace masa
“Bari ta fito, na gode kwarai Allah ya qara zumunchi”

Se kawai ya tuntsure da dariya harda sunkuyawa yana kallona yace
“Matsoraciya, naga ma rowar gidan naki kike yi mun ko bayan nasan miskilin mijinki
baya ciki. Wai ma ya akayi kika bari ya ajiye ku maqotaka da kishiyarki? Kinga idan
nine ko qasa bazan hada muku ba bare unguwa daya saboda bazan yaba bari wani abu ya
sosa miki rai ba indai ina da ikon hanawa”.

Cikin gida nayi shigewata ina jin yanda zuciyata take bugawa da qarfi kamar wadda
tayi tsere, na rasa dalilin da yasa indai Yusuf yayi mun magana nake shiga irin
wannan yanayin, yanzu da ace ina da aure muka hadu dashi haka zamu ringa dibar
wannan dakon zunubin??

Seda nasha ruwa me sanyi dukda banci komai ba kafin na wuce dakin Amnah na tarar
suna drama da Ma’u ta riqe akwatinta qam baza’a fita dashi ba.

Duk yanda naso na lallabata na nuna mata Dadynta ne yazo amma fafur tace itafa
bazata tafi ba taga gurin zama, haka ta ringa birgima tana buge buge a qasa mamaki
yasa kawai na tsaya ina kallonta ni ba abin na mammaketa ba ubanta na waje dan da
ace yan biyu ke yi mun tabarar da tuni naci ubansu dan ni ba’a haka dani wannan
yarinyar kuwa naga alamar an gama sangartata se a hankali kawai.

Dole na fita na gaya masa, badan naso ba ya shigo gidan, yayi lallashin duniya taqi
ji qarshe a wuya ya dauketa tana kwala ihu kamar wadda aka sace ya sakata a mota
yaja suka tafi muna daga mata hannu, haka muka wuni yara sukuku abu kadan ace
Little kaza ni kaina nayi kewarta dan tana da shiga rai barta da yar banzar barna
kamar beran turawa.

GOMBE
ADDAH
Tiryan tiryan me Napep ya kaita har qofar Asibitin data kwatanta masa saboda saurin
da take ko musu batayi ba ta dakko kudin daya ambata mata ta bashi ta shiga jan
Ummi da dauk ta galabaita suka shiga ciki.

Kai tsaye gurij Nurse din dake bada kati taje ta ce mata likita suka zo gani aka
yanka mata kati dari biyar ta zaro ta bayar, babu mutane da yawa a gurin, mace biyu
suka tarar su na uku ganin yanda Ummi take kuka ma Nurse din ta dauka ko ciwo ne
dan haka ta roqar musu alfarma Gurin wadan da suka tarar ta ciki na fitowa suka
shiga.

Likitan na zaune kai idan ka ganshi me hankali dai baze yarda ya dubashi ba saboda
yanda yake a hargitse sam be mayi kala da likitoci ba, ba bata lokaci Addah ta
zayya na masa abinda yake tafe dasu da kuma buqatarta.

Shiru likita yayi yana kallonta, Addah da taga yayi shiru ta har ziqo tana cewa
“Ko bazaka iya bane ka fada ka zuba mana ido kamar maye yaga nama, ni karka bata
mun lokaci idan baka yi mu qara gaba ai likitocin kuna da yawa”.

Seda yaja numfashi kafin yace “cikin wata nawane Hajiya?”

“Wai wata hudu tace, kana ji ko karka damu da wani watannin sa ka markade mun dan
banza ko nawa ne zan biyaka”

“Yawwa daman maganar ta kudi ce Hajiya tunda kinga cikin ya girma dole cireshi zeyi
wahala dan haka se kun biya kudi da yawa amma tunda kince babu matsala to za’ayi
aiki zaki biya dubu dari biyu da hamsin ne kudin aiki se kuma dubu hamsin na
magunguna da jini da zamu siya saboda tsaro gaba daya kinga dari uku kenan” Likita
ya fada yana wani murmushi da gani banza ta fadi

Dafe qirji Addah tayi ta zaro idanu waje tace “Likita dari uku fa kace cire cikin?
Ina laifin in baka dubu hamsin shima saboda naji kace da wahala amma da ni dubu
talatin ce kaga na ruqo ta” ta qarasa tana bude yar jakar ta ta zaro kudi, seda
likita ya ha tareta kafin yace

“Bata mun lokaci daman kawai zakiyi Hajiya ba aiki kuka zo ayi muku ba. Kinsan
hatsarin da yake cikin abinda kika zo yi kuwa idan fa aka samu matsala aka kamani
daurin shekaru zansha a banza ki gudu abinki kinga ku tashi tunda naga wasa nema ya
kawo ku na samu na duba sauran da suka zo da gaske”

Ganin da Addah tayi ga samu ga rashi yasa ta marairaice tana cewa
“Dan nan ba wasa bake ba kudin ne daka fada sunyi yawa amma yanzu shikenan, kayi
mana ragi naji abinda zan bayar In sha Allahu baze gagara ba”

“Ki bada dubu dari biyu shine qarshen magana idan beyi miki ba ga hanya nan” ya
fada yana hade rai, Addah tayi shiru, a jakarta gaba daya dubu hamsin ne ribar
kasuwarsu da Alhaji ya bata jiya, tama tabasu basufi Arba’in ba yanzu ina zata
kwakwulo dubu dari da sittin ta hada dan bazata taba bari wannan damar ta wuce ta
ba.

Ajiyar zuciya tayi ta kalli likita tace
“Shikenan na yarda, yanzu ga dubu Arba’in zan baka idan yaso ta zauna zanje gida na
karbo ragowar sena kawo maka”

“Aa ai ba anan za’ayi aikin ba Hajiya, inada guri daban da nakeyi kuma se da
daddare zaku zo zan baki lambar waya da Adireshin gurin se ku same ni acan” Likita
ya fada nan da nan Ummi ta qara wa kukan da takeyi qasa qasa qara, mayar da
hankalin sa kanta yayi yana cewa

“Ki rarrasheta Hajiya ta dena kukan nan dan idan jininta ya hau za’a iya samun
matsala a gurin aikin. Yanzu zan rubuta muku magani ku siya a waje daya zata shanye
shi yanzu dayan kuma idan kunje gida kamar saura awa hudu ku taho yin aikin ta saka
kwaya daya a qasan harshen ta zasu nuna muku ko wanne da yanda zaku yi dashi din”.

Godiya sosai Addah ta ringa zuba masa kamar wanda ya bata kyauta, ta kawo dubu
talatin da biyar ta bashi biyar din zata siyi maganin sannan suyi kudin mota.

Tana fita kuwa a dan gurin siyar da maganin Asibitin nasa suka tsaya ta siya a take
ta saka Ummi seda tasha na shan suka kama hanyar gida tana ta lissafin inda zata
samo kudi.

Amirah ce ta fado mata a rai, daman shegiyar yarinyar tunda ta tafi bata tuna da
ita ba balle ko biyar bata aiko mata da ita nan da nan ta kunna wayarta ta shiga
kiran Amiran.

AMIRAH
Tana zaune a daki tana kuka, san baqaqen maganganun da Bashir ya gaya mata basu
dameta ba ita yanzu ta yanda zata samu Addah ta hanata abinda tayi niyya take, tana
tsakanda aikin kukan kiran ya shiga.

Da sauri ta faga wayar tana cewa
“Addah kina ina ne tun safe nake neman wayar ku bana samu ke da Ummi?”

“To uwata, an baki ajiyata ne da kike tambayar ina naje ko yaya ina ruwanki? Ni
yanzu kirani nayi ki tura mun kudi zan samu POS na tsaya yanzu na basu lambarki ki
sako kudin na cire”

“Addah me zakiyi da kudi? Ina Ummi? Kun koma gida ne Baba ya kirani dazu yana
cewa...”
“Wai dan uwar ubanki Amirah zakiyi abinda nace ne ko tambayoyi zaki tsaya yimun
kamar alqaliya?

Baba ya kira yace miki ubanki ina ruwanada wani Baba babo mata ni wutar gaba na ta
isheni yanzu, na samu wanda ze cirewa yar uwarki abin kunyar data kwaso mana kudin
nake hadawa yanzu anjima zamu koma ayi aiki” Addah ta katse Amirah.

Se Amirah ta zaro ido kamar tana gabanta tace
“Addah mutuwa akeyi wallahi kin manta Harira lokacin tayita zubar da jini har seda
ta mutu dan Allah Addah karki sa na rasa Ummi kinga ita kadai ce yar uwata.

Ki qyaleta ta haihu wallahi ko ni zan dauki abinda zata haifa na riqe nasan Yaya
baze hana ba”

“Idan kika sake cewa wani abu se kinci ubanki Amirah, bazaku kasheni ba yanzun nan
zan turo miki da akawun na fasa zuwa POS din ma zan shiga gidan Talatu kawai mu
zauna a can zuwa lokacin da zamu koma idan yaso se na turo miki da ko na Dan ta ne
ki saka kudin nasan in muka koma gida wannan Uban naku ba lallai ya sake barina na
fita ba” tana gama fadar haka ta kashe wayarta tana aunawa Amirah Ashar shidai me
Napep se leqenta yake ta mudubi Allah Allah yake ya sauke su ya samu wanda ze bawa
labari.

Amirah kuwa tana jin Addah ta kashe waya ta shiga neman layin Babansu, yana dagawa
kai tsaye ta gaya masa Addah na gidan Anty Talatu ta kashe wayar tana Addu’ar Allah
yasa Babansu yaje kafin su Addah su koma inda tace.

Addah kuwa a gidan Anty Talatu suka yada zango, yar uwarta ce yayan mata suke yar
bala’i ce ta gaske itama dan har tafi Addah rigima.

A tsakar gida suka tarar da ita tana wa wata jikarta masifa, ko sallamar Addah bata
amsa ba seda taji yarinyar na gaida Addan sannan ta waiwaya inda suke tana huci.

“Aa Fattu kune a tafe? Ku shigo mana ita kuma wannan me aka mata ta dora hannu aka
tana kuka? Nifa bana son fitina shiyasa kikaga bana qaunar baqar yar nan taki
saboda mugun halinta gara Amirah tafi mun ita sau dubu”

Cikin dakinta suka shiga tana gaba suna binta a baya. Seda ta kawo musu ruwa me
sanyi da Fura, ta futa ta bawa jikar tata kudi tace taje qaro taliya leda daya dan
gama miyar ta kenan sun maida ruwan taliyar yarinyar ta juye tayi wanka dalilin
masifar tata kenan.

“Daga ina haka Fattu da uwar ranar nan fatse fatse keda bakya gajiya da yawo”
Talatu ta fada bayan data zauna.

Se Addah ta janye tagumin data buga tace “ki bari kawai Talatu wannan yarinyar ce
ta kwaso mun tashin hankali” nan ta zayya na mata abinda yake faruwa.

Anty Takatu ta hau salallami tana tafa hannu tace “yanzu Ummin? Ke da nakeyiwa
kallon ta kirki kai yaran yanzu se abarku abinda se dai muji daga nesa shine kika
kawo mana a cikin zuri’ar mu Allah ya wadaranki dai Ummi”
Nan suka hadu suna ta nanata zancen, seda ta dafa musu taliyar suka ci kafin Anty
Talatu ta kalli Addah tace

“Ni Fattu maganar zubar da cikin nan ki barta kina gani dai ance mutuwa akeyi
wallahi, yanzu abinda duk ya kamata ayi shine tunda tasan uban ciki a nemo shi a
taru a rufawa juna asiri ko yaya ne ayi musu aure shikenan”

Hayayyaqo mata Addah tayi tana cewa
“Ban gane abar ciki ba in barta ta haihu kenan a ringa nunani a gari ace nayi jika
shege to bazata sabu ba wallahi, kuma zancen aure da kije badai da wannan
matsiyacin ba sedai idan mutuwa nayi”

“Ai kuwa idan baki mutu na zakiyi ta goya shegu tunda ke zuciyarki irin ta kafiran
farko ce. Yanzu tashi zakiyi mu zagaya nan baya gidan me sittin tara a kwantar da
cikin daga nan a nemo yaro idan sukayi aure wata kadan se a tayar dashi dukma uban
da za’a fada dai daga baya ne tunda sun rigada sun yi aure”.

Shiru Addah tayi qasan zuciyarta ta yarda da shawarar Anty Talatu, miqewa sukayi
Anty Talatu tace Ummi ta shiga ciki ta hau gado ta huta kafin su dawo suna zuwa
qofar gida sukaci karo da yan sanda a tsatstsaye.

“Lallai Asabe, ba nace ta bani sati daya zan biyata kudin ta ba shine zata hadani
da hukuma ai kuwa wallahi tayi ta kudinta muje duk uwar da za’ayi ayi amma bazan
biyata ba kuwa” Anty Talatu ta fada dan a zatonta wata mata da rigimar Adashi ta
hada su tace zata dakko mata yan sanda ce ta turo su.

Fitowar a Alhaji Murtala daga mota ce ta dakar dasu Addah ta shiga zare ido tana
komawa bayan Anty Talatu.

“Gata nan yallabai” ya fada yana nuna musu Addah nan da nan yan sanda mata biyu
sukayi kanta se ta sake riqe Talatu tana cewa

“Me kuma nayi Alhaji? Wane munafunchin aka qullamun da zaka dakko mun yan sanda
saboda ka tozarta ni”

“Ai kin rigada kij gama tozarta kanki Fattu, ina Yata take? Se na tabbatar da
lafiyar ta idan wani abu ya sameta daga nan kotu zamu wuce dan se nayi shari’a dake
Fattu” ya fada cikin tsananin dacin rai.

Anty Talatu ce ta tare yan sandan da suke neman jan Addah tana cewa
“Ummi tana ciki Alhaji lafiyarta qalau, bari na kirawo maka ita ka ganta wannan
kuma ai abu ne na cikin gida be kamata ace ka saka hukuma a ciki ba”

Daga bakin soron gidan ta tinga kwalawa Ummin kira, Ummi da har bacci yadan fara
fizgarta ta fito jin muryar Talatun tana fita tayi arba da Baban su seta fada
jikinsa ta fashe da kuka tana

55 / 80