Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
gefe na na dago da sauri jin
kamar nasan muryar, Ambassador Mutallab Ali ne shida wani a teburin da yake gefen
namu se wannan PA din nasa yana tsaye yana zare ido.
"Ranka ya dade barka da rana" na fada ina sunkuyar da kai da tuno yanda na dannawa
lambar sa block tun a kiran farko qila yayi ta kira harya haqura tunda bata shiga.
"Daga kiran waya malama Asma'u se kikayi blocking dina kuma laifin me nayi?" Ya
fada kamar ya shiga zuciyata. Kaina na qas ina dan murmushin yaqe ya sake cewa
"Tunda na kira naji line busy nace to gimbiyar bata son damuwa bari a barta ta
huta, kwanabiyu abubuwa sun sha kaina shiyasa ma ban sake gwadawa naji ko an bude
ni ba se gashi yanzu Allah ya hadamu dan haka a gabana zaki bude na gani".
Wato yanda ya dage yana magana ni gaba daya ma kunya ya bani ko ganin girman kansa
beyi ba yake wani lankwashe harshe gashi kuma Abokin nasa se wata dariya yake kamar
wanda akewa cakulkuli ni duk ya bani Haushi nama rasa me zance musu.
"Kinyi shiru Asma'u, koda yake fara dakko wayar kiyi unblocking dina mayi magana
daga baya dan yanzu sauri nakeyi, Alhaji Sani ka ganta nan ita ce yarinyar danake
baka labari"
"Ah ai na ganta tayi sosai kuwa bazamu bari wannan ta wuce mu ba" wanda ya kira da
Alhaji Sani ya fada cikin hausarsa da bata fita sosai daga ji ba cikakken Bahaishe
bane se na fara laluben wayata akan Tebur din da nake, Ajiyar zuciya na sauke dana
tuna na manta ta a mota da zamu fito na juya na kalle shi da dan murmushi nace
"Ai kuwa na manta ta a gida ina sauri zamu fito" daidai sannan Aliyu ya qaraso da
Waiter na binsa da ledojin abinci. Tsabar wulaqanci kallo daya ya musu ya dauke kai
kamar wanda yaga kashi ya zauna a kujera yana muzurai.
"Wannan Qaninki ne?" Ambassador ya fada yana kallon Aliyun, sena qaqalo murmushi
nace
"Aa, first born dina ne, Aliyu baka ga mutane bane?"
"Nagansu mana" ya fada kansa tsaye kamar be gane yaran ya gaishe su nake masa ba.
Tsabar takaici na bude baki kawai ina kallon yanda ya hade fuska yaja Ice cream din
daya taho dashi a hannunsa ya hau sha, zanyi magana Alhaji Sani ya tare ni da cewa
"Aa barshi yaro ya gida? Ina qannenka kana taya Babanku kishi ko banga laifin ka
ba".
Murmushi Ambassador yayi kafin ya miqawa PA hannu se yayi saurin bashi wata
briefcase dake hannunsa, budeta yayi ya ciro rafar Dala dari dari guda biyu ya
ajiye mun daya yace
"Gashi idan kun gama seki biyu kudin muna sauri ne bari mu wuce, Yaro ka saka katin
waya ko" ya ajiye ragowar dayar a gaban Aliyu.
"Haba Ranka ya dade ai da ka barshi mun rigada mun biya ai" na fada ina tura masa
kudin, gaba yayi abinsa yana cewa
"Zan sake gwada wayar naji idan kin koma gida" ya wuce suka take masa baya bayan da
Alhaji Sani ma ya sake ajiyewa Aliyun wata Dalar harda dafa kansa yace yana yar
dariya yace
"Yaron kirki me taya Babansa kishi" suka fice gaba daya.
"Wallahi sekaci ubanka Aliyu ni ka kunyata a idon mutane ka nuna musu baka da
tarbiyya ko?" Na fada kamar zan kwada masa mari Saboda haushin abinda yayi din. Ice
cream din ya ture kamar zeyi kuka yace
"Toh ni Mami ina ruwana da su dazan gaishe ni ai ban san tare kuke ba tunda bada su
muka zo ba"
"Zaka rufe mun baki ko sena kwade ka anan, idan ba tare muke ba daman haka kukeyi
idan kunga na gaba da ku? Ko darajar shekarunsu beci ka gaishe su ba tunda ai ba
kai ba ko ubanka sun girme shi" na fada cikin masifa.
Seya miqe tsaye ya kwashe kudin gabansa yana cewa
"Nidai kiyi haquri"
"Ajiye su dan ubanka, ka wulaqanta su saboda baka da kunya ka dauki kudin da suka
baka" na fada ina fizege kudin, saboda wulaqanci se ya saka dariya ma yana cewa
"Toh Mami ai ba roqar su nayi ba, ki bani kinga se na kaiwa Abbi ya auro wadda zata
ringa dafa masa abincin da kika ce".
Tsabar mamaki kawai bude baki nayi ina kallonsa, lallai Aliyu ko da yake ba
laifinsa bane wannan yafi kama da Tunanin Bashir qila shi yake karanta masa duk
abinda zeyi to kuwa duk zasu ci ubansu shida Bashir din.
Haka muka wuce gida dani dashi babu wanda ya sake cewa komai. Tare muka ci
abincingaba aya aka gama aka tattare gurin, Seda akayi Isha ina daki Aliyu ya leqo
yana cemun ze tafi seda safe
"Ba anan zaka kwana ba?" Na tambaye shi,
"Eh zanje can gidan da safe na dawo" ya fada yana sosa kai.
"Allah ya kaimu, kuja mana qofar idan kun fita" na fada ina ci gaba da lazumi na.
Washe gari da wuri na shirya fita aiki saboda babu makaranta duk yaran ma suna
bacci abinsu. Naci gayuna, Shayi kawai nasha na dauki jakata ina cikin kulle qofa
Bashir ya qaraso qofar gidan shima cikin shirin fita aiki.
"Barka da Safiya Ma'u" ya fada yana kallona.
"Ina kwana Baban Ali?" Na mayar masa da amsa ina ciro muqullin mota daga jakata.
"Ashe kun dawo, se ganin Aliyu nayi yace jiya da yamma kuka dawo"
"Uhm wallahi saboda aiki kasani, da se satin sama idan hutu ya qare zamu dawo" na
bashi amsa cikin sauri sauri ina danna mabudin motata.
"Nace in ba damuwa inaso zamuyi magana ne dan Allah ko zuwa anjima idan na dawo se
nazo gida" ya fada yana shafa kai kamar wani yaro,
"Toh magana kuma dani? Allah ya kaimu" na bashi amsa ina shigewa motata, shiya rufo
mun murfin yana mun adawo lafiya wai sabon salo kiran sallah da usur, seda na kai
qofar gidansa na hangi Amirah tsaye cikin shiri kamar a tsikara mata tsinke ta
fashe tsabar kumburi da alama fita zasuyi ya tsayar da ita.
Da yamma kuwa gurin qarfe shida sega Bashir, na fito wanka kenan dan nima ban dade
da dawowa ba sannan Farida ta shiga take gayamun ga Abbi.
"Ma'u wata magana naji da hankali na ya kasa nutsuwa da ita wai aure zakiyi" ya
fada bayan da muka gaisa. Sena kalle shi yanda gaba daya yabi ya rikita kansa duk
ya sukurkuce gayun nan da yakeyi da yanzu babu da alama ko hutawa ma beyi ba yana
dawowa ya taho nan dan rigar saman kayan sa kadai ya cire.
"Toh ashe labari ya iso maka a ina kaji?" Na tambaye shi da dan murmushi a fuskata
seya zaburo kamar ze sauko daga kujerar da yake yace
"Bangane ba kina so kice mun da gaske ne Ma'u aure zakiyi? Wane irin Aure? ki zauna
da wani namiji bani ba ko hada soyayyata da ta wani a zuciyarki?"
Seda na gyara zama dakyau na dora qafa daya kan daya ina girgiza su kafin nace
"Aure kala nawa ne Bashir? Shi din dai wanda ka sani na mata da miji da zasu zauna
a qarqashin inuwa daya.
Batun na zauna wani namiji kuma da Mace yar uwata kake so na aura ko yaya? Ita kuma
soyayya ai yanzu tashi ce kadai a cikin zuciyata tuni anyi waje road da taka tsohon
labari kenan".
Miqe wa tsaye yayi har yana tunkude kayan Lemon da aka kawo masa suka zube a qasa
ya nunani da hannu yana cewa
"Qarya kike Asma'u bazaki taba son wani Namiji a duniya ba bayan ni idan ma zakiyi
aure da gaske sedai kiyi kawai amma badan so ko jin dadi ba ina kuma tabbatar miki
da cewa duk ma inda kike tunanin zakije sekij dawo dan zuciyarki bazata taba aminta
da wani bayan ni ba wannan alqawari nayi miki"
Ko a jikina na miqe tsaye nima ina kallonsa cikin ido nace
"A lokacin dana nuna maka kaine rayuwata Bashir ka dauka shirme nake ban san kaina
ba a sannan, a yanzu kuwa ka bude mun ido ka kuma bani damar da nayi karatun sanin
matsayina da abinda ya cancanta dani.
Oh wai fata kake mun nayi aure na sake dawo maka? Toh ai tunda na iya zama da kai
da halinka Bashir ni kuwa wane kalar miji ne zan gagara yin haquri dashi zance ma
kawai kake yi wannan" ina gama fada nayi gaba zan bar gurin yayi saurin shan gabana
tareda riqo hannuna, kallon dana jefa masa na kayi hauka ne yasa shi saurin sakina
yaja baya yana cewa
"Kiyi haquri naji koma menene ki gaya mun duk abinda bakya so zan dena wallahi
nidai kiyi haquri ki dawo dakinki muci gaba da zama kinji wallahi bazan iya rayuwa
babu ke ba".
Ni kuwa kaga yanzu ma na daura danbar rayuwa ba tareda kai ba, kai ni ai yanzu bama
zan iya maimaita zaman da nayi a baya dakai ba Bashir kaje kawai ka zauna da matar
da Allah ya zaba maka ka barni nima na gwada wata rayuwar haba karka zama me son
kanka mana"
"Ma'u dan Allah..."
"Dan girman Allah Bashir ka fita, da nasan wannan maganar ce zata kawo ka ma da tun
da safen munyita wallahi base kazo ka tasani gaba da magiya ba ko da dole ne nace
bana so bazan koma ba ka qyale ni mana idan kuma kana da qarfi seka dauke ni aka ka
maida ni gidanna ka haba" na fada a hasale dan ya ishe ni kuma.
"Shikenan seki shirya ganin gawata dan duk ranar da kika auri wani bani ba nasan
daga lokacin rayuwa ta zata zo qarshe".
"Allah ya jiqanka, karka damu su Aliyu bazasuyi maraici ba" na fada ina wuce shi.
Ina ji a jikina yanda ya bini da kallo harna shige daki.
BASHIR
Jiki a sanyaye ya kama hanyar gidansa yana tunanin wai shi mezeyi Ma'u ta dawo
masa?
Ya gwada duk yanda akace masa yayi nasa dabarun amma duk a banza kullum ma sake
botsarewa takeyi a maimakon ta sakko. Yanzu mutum biyu suka rage masa da yake ganin
zasu iya shawo kanta daga Babansu se Alhaji Qarami.
Kai shi yana kunyar Alhaji Qarami wallahi abinda ya masa a rayuwa ko darajar wannan
yaci ace ya dagawa Ma'u qafa koda ita ta takaleshi yaci ya dauke kai. Baban dai ze
kira tunda dai ai duk tsiya ubansa ne bakuma ze zabi Ma'u akansa ba kuma ai shima
yana son zamansa da ita dan haka ze saka baki ta dawo masa.
Wayar Baban ya kira amma Dada ta daga take gaya masa yana bacci saboda jikinsa ya
matsa kwana biyu. Shi se sannan ya tuna da zancen kudin maganin da ze tura musu
gashi account dinsa yayi qasa sosai saboda hidimar sallah da yayi kuma wata ya raba
balle ya saka rai da zuwan Albashi.
"Kai komai ma ya rikicewa mutum kudin kansu sun dena Albarka kamar wanda ake kwashe
su" ya fada a fili bayan da yayi wa Sa'ad transfer abinda ya samu na siyan maganin,
dan abinda ya masa saura baya zaton ze rufa masa watan gashi za'a koma makaranta
biyan school fees kadai ya ishe shi yana ganin dole seya karfi wani abu a kudin
super market saboda biyan kudin makarantar dan da wuya ya taba kudin idan an hada
lissafi ribar sake mayar da ita ake se idan ta qure masa ne yake taba wani abun a
ciki.
Yana shiga gida ya tarar da Amirah na murqususun ciwon ciki kuma, kai Jama'a haka
suka kwasa se Asibiti likita ya ringa fada akan wai wani abun tasha irin magungunan
Hausa, daya matsata qarshe take gaya masa wai magani Addah tasa aka aiko mata daga
Gombe a qaryar su na zaqi ne tunda cikinta ya shiga kusan wata Bakwai yanzun shine
ta karbo mata zancen gaskiya kuwa sabon malami ta samu ta hannun Anty Talatu ita
tayo musu aiken saboda sun gaya mata sun rasa kan Bashir din zaman dai se a
hankali.
Ya kuwa ringa bala'i kuwa yana cewa Idan wani abu ya samu cikin ita ta sani babu
ruwansa tunda ita bata tausayin kanta haka suka dawo bayan da aka bata magunguna su
kansu seda ya kashe kusan dubu Hamsin a daren.
Kwana biyu a tsakani aka kirasu a waya cewar Ummi ta haihu ta samu ya Mace amma ta
koma murna Addah ta ringayi tana hamdala da akace yar ta mutu sedai murna ta koma
ciki jin wai an daurawa Ummin aure da dai shi mijin da bata so ta aura din dan
daman seda sukayi yarjejeniya da iyayensa akan tana haihuwa za'a daura aure suka
yarda dan haka ana kiran Alhaji Murtala daga can Katsina inda ya kaita gurin wani
Amininsa cewar ta haihu ya tashi ya tafi gidan su saurayin ya gaya musu. Ana sallar
Azahar kuwa a masallaci aka daura musu aure se saka ranar da zata dawo ta tare.
Kusan Sati guda gaba daya Bashir ya zama gashi nan ne, abubuwa sun rikice masa duk
yanda ya dauki shawo kan Ma'u da sauqi abinya shallake haka nacin yake roqon yake
amma kamar wanda yake shika dusa dukda shima dai da tasa irin wautar.
Wani irin biko yakeyi me kamada fin qarfi saboda a duk sanda ya tashi yi mata
magana nuna mata yake kamar ya zamar mata dole bazata oya rayuwa babu shi ba dan
haka ta haqura ta dawo masa wanda sam shi be dauki hakan da wani laifi ba gani yake
kamar yana tuna mata da girman soyayyar da take tsakanin su ne wanda ita kuma
wannan abun shi yake wara qona mata rai take jin dole ta barshi ko dan ta nuna masa
cewar ba tare aka dauro rayukansu aka aiko duniya ba.
Ana saura sati daya a koma makaranta kamar yanda aka saba suka tura mata da
Takardar biyan kudi saboda daman lambar wayarta ce akai in an turo mata seta turawa
Bashir din ya bada kudin.
A yanda aka saba an samu qarin kudin makaranta ga kudin littattafai saboda sabuwar
shekara aka shiga za'ayi canjin aji ga kudin jarabawar WAEC da NECO da JAMB na
Aliyu da ze shiga aji shida dan haka da aka hada lissafin sega kudi sun tasarma
kusan Miliyan biyu.
Ita kanta seda ta jimanta wannan al'amari ta rasa abinda yasa makarantar suke haka
basa bada notice na qarin kudi sedai kawai idan an kawo maka teller ka gani kamar
wadanda suka bawa iyayen yaran ajiya koda yake makaranta ce ta yayan masu dashi
suma karanbani ya saka suka kai yayansu ai.
Ta Whatsapp ta tura masa da takaddun lokacin yana zaune a Office be dade da gama
waya da Amirah ba da take masa zancen kudin siyayyar haihuwa gashi jikin Alhajin su
ya qara zafi dan shirin kaishi Kano akeyi ma Asibitin Malam nan ma dai duk wani
lissafin kudin ne dai yanzu ga wannan ubannin kudi na makaranta kuma sun taso masa
duk a ina ze qwaqulosu?
Wai to ta yaya da duk yake hidimomin sa har ya samu rara a asusun sa ba taredaya
girgiza ba? Albashinsa Miliyan daya ne duk wata saboda babu Fansho babu garatuti
idan ka gama banda sauran alawan da suke samu kala kala musamman yanzu daya samu
qarin matsayi packages harda na banza basu ake dan haka yake facakarsa baya ma
lissafi bare ya ajiye na buqatar kota kwana tunda kudinna shigo masa koda yaushe
daman Super markets dinsa Gombe sune tanadin Bayan Ritaya wanda se a yanzu yake
hango tarin gatan da Ma'u tayi masa data saka shi a harkar kasuwanci nan dan yanzu
ba qaramin habaka jarinyayi ba tunda ba'a tabasu duk ribar da aka samu ciki a ke
maidata.
Text ya tura mata akan ayi masa haquri kafin a koma ze bayar nan ya shiga hado ta
inda zasu fito, dole dai ya karbi kudi a gurin Sa'ad din idanyaso daga baya ya
mayar dan su makaranta babu ruwansu ba jira zasuyi ya samu ba shawarar daya yanke
kenan a take kuwa ya kirashi akan yana san ya karbi miliyan uku se Sa'ad din yake
gaya masa sunyi sarin kaya, kudin da suke dasu a qasa ko Miliyan daya bazasu kai ba
na banki kuma ze dauki lokaci dan yamamta account din ya samu matsala ta yanda
sedai kudi su shiga amma bazasu fita ba dan haka dole sedai idan zeje Gomben da
kansa ya gyara tunda shine signatory din.
A daren ranar yana zaune a qofar kujera ya dasa kujera yana aikin tunani, daga inda
yake yana iya jiyo hayaniyar yara daga gidan Ma'u saboda yanda Estate din yayi
shiru.
Hira suke cikin raha anata qyaqyata dariya kamar yanda sukeyi a ko wanne dare
lokacin da tana gidansa wani lokacin idan yaga dama ya zauna ayi dashi wani lokacin
kuma yana daga gefe yana sauraronsu yana murmushi dan ita irin mutanen nan ce masu
biyewa shirmeb yara ta haka take sanin duk abinda suke ciki basa boye mata tunda ta
mayar dasu kamar qawayenta.
Ya ilahi me yasa duk beyi tunanin komai ba ya rusa Wannan kyakykyawar rayuwar ta
gidansa? Yanzu da ace bata kusada yaran a ina zasu ringa samun wannan walwalar da
farincinin saboda yanzu sam babu wata damuwa a tattare dasu, kamar daman a haka
suka tashi tsakanin gidaje biyun musamman da baya takura musu da zancen kwana duk
inda suka so yanzu zamansu suke shiyasa Aliyu ne kadai yake rayuwar qunci da damuwa
a cikinsu kodan shine babba yafi su tunani da gane abinda yake faruwa.
"Abbi tunanin me kakeyi tun dazu ina tayi maka magana baka ji ba" maganar da Aliyu
yayai tareda girgizashi ta dawo dashi hayyacinsa. Se ya sauke ajiyar zuciya yana
kallonsa yace
"Tunanin da yawa Aliyu, gaba daya kaina ya qulle ga Maminku sam ta kasa fahimta ta
tayi haquri akan abinda ya faru ban san yaya zanyi ba Aliyu".
"Abbi duk abinda ya faru ai laifinka ne, haka kawai kaje ka qara aure kuma Abbi ka
rasa wa zaka aura se Anty Amirah bayan kasan Mami cefa ta riqeta, kazo ka ringa yi
mata abubuwa duk akanta kawai saboda kaga tana da haquri sannan fa Abbi saboda ita
ka sake ta sannan yanzu saboda kaga baka jin dadi bata nan kazo kana cewa ta dawo
ai kasan bazata yarda ba" Aliyun ya fada bayan daya zauna.
"Na sani kuma duk na karbi laifina, auran Amirah da rabuwata da Maminku duk
qaddarace Aliyu gaba daya ba a san raina komai ya faru ba amma babu yanda muka iya
da abinda Allah ya qaddar. Ni dai yanzu ku taimaka nasan ai ku zata saurare ku ku
bata haquri ta dawo gidan nan nayi Nadama bazan sake maimaita duk abinda ya faru a
baya ba.
Idan ma so take Amirah ta koma Gombe zata tafi nidai tayi haquri a mayar da auran
mu kawai zanyi mata duk abinda take so kaji kuje dukkan ku ku sameta dan Allah
Aliyu nasan ai kai bazaka so kaga rayuwata ta shiga garari ba saboda rashin Ma'u"
Bashir ya fada yana kama hannun Aliyu daya tsura masa ido.
"Zanje na sameta dukda tace karmu sakeyi mata maganar ka amma ina so kayi mun
alqawari.."
"Koma menene na yarda in har zaka shawo mun kan Ma'u duk abinda kake so zan baka"
Bashir yayi saurin tare shi. Seda ya sauke ajiyar zuciya kafin yace
"Kayi alqawarin idan Mami ta yarda zata dawo zaka saki Anty Amirah saboda nasan
indai kana tare da