Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   28 / 80

81K to 84K   out of 238.5K words

lura tunda yazo bata ga sunyi waya ba.

Seda Bashir yasha ruwa kafin yace “Ina ganin zata ajiye aikin ne kawai idan yaso ta
cigaba da kasuwancinta kema ya kamata ki samu wani abinyi zaman haka ya isa”.

Tamkar Amirah ta taka rawa haka taji amma ta dake, cikin kisisina tace “Toh yaran
kuma fa su acan za’a barsu ko suma nan zasu dawo?”

“No su zasu zauna can saboda School”

“Amma Yaya indai makaranta ce anan ma fa akwai ko wacce iri kake so, ni ba wannan
ba ma abinda yafi damuna Tarbiyyar su kasan fa yaran da suka tashi a Kudun nan duk
zaka gansu se a hankali ko a gida ana musu tarbiyya tunda kullum suna fita su
cakudu da yara kala kala se kaga anayi tana warwarewa. Ni da zakaji shawarata ka
dawo dasu nan ga makarantu nan na kudi masu kyau a saka su”.

Shiru Bashir yayi yana tunani, baza’a hadama karantun boko nacan da na nan ba amma
maganar tarbiyya tabbas tayi gaskiya abinda yasa ya hana Amna yin Jamb wannan
shekarar kenan yace ta bari se next year saboda kafin nan ta dan qara girma da wayo
yana tsoron turata Jami’a cikin Yayan Arnan nan.

Su kansu su Aliyun yasan badan Ma’un ma Jajirtacciya bace irin yaran da suke cakude
dasu a makaranta da sun debi dabi’un da ba nasu ba.

“Haka ne kuma, shikenan zanyi magana da Ma’un se muga yanda za’ayi”.


Litinin ya koma Lagos da wannan qudurin a ransa. A daren ranar suna cin abinci
bayan ya gama ya kalli Asma’u da tunda suka zauna ta kasa cin komai yace “Inason
magana dake idan kun gama” ya wuce dakin sa.

ASMA’U

Yana tashi nima nabi bayansa gaba daya jikina baya mun dadi dan haka ina shiga na
kwanta akan gado ina jiransa ya fito daga yin Brush.

“Daga Next month Amirah zata fara zuwa nan”.

“Wata sabuwa” na fada a raina, sena miqe zaune ina kallonsa nace “toh ni mene ne
nawa a ciki idan Amirah zata zo ko a nan gidan zata sauka ne?”
“Ina nufin ke zaki tafi Gombe idan zata zo, then se ku tsara yanda kuke ganin
lokacin da kowacce zata ringayi a nan din”. Ya fada yana zama a gefena.

Yanzu kam na gane inda ya nufa, wato tsohuwar magana ce ta taso kenan yaje ta sake
masa fanfo akan tanaso ta dawo nan. Zaune na tashi na jingina bayana da Allon gadon
nace “Toh Baban Ali ya zanyi da aiki na kuma? Sannan Yara suma ya za’ayi dasu?”

“Maganar aiki na gaya miki zaki ajiye daman yara kuma dasu zaku tafi duk wadda take
Gombe se su zauna a gurinta”.

“Kan uban nan lallai ma” na fada ina kallonsa kafin naci gaba da cewa
“Yanzu saboda matarka tana so ta dawo nan shine zakace na ajiye aiki na amma kasan
sam wannan ba adalci bane ko?”

“Ke zaki koyamun yanda zanyi adalci kenan, toh ki dauka duk yanda yayi miki amma na
gama magana dole ki ajiye aikin ki Ma’u ki koma Gombe tunda haka na tsara” ya fada
yana kallona.

Seda na qare masa kallo dan na tabbatar da gaskiyar abinda yake fada kafin na
sassauta muryata ganin dagaske neman rigima yake nace

“Haba Baban Ali, ka manta wuyar dana sha kafin na samu aiki nan, mutum nawa ne suke
nema Allah ya zabe ni akan su ya bani amma yanzu lokaci daya kace na ajiye. Da ace
muna da Branch a Gombe da babu musu zan nemi transfer in koma can amma yanzu kawai
dan kana so ka kawo wata ni kuma seka tauyeni kace na bar aiki na ai bakayi mun
daidai ba.

Ni bani da matsala zaka iya dawo da ita ko a cikin gidan nan ne ka bata daki amma
dan Allah kabar maganar aikina ina son sa ban kuma shirya barinsa a yanzu ba”.

“Shikenan tunda kina son aiki ki, seki zaba ko shi aikin ko kuma umarnina” yana
fadar haka yaja bargo ya rufe har kansa nima sena fice nabar masa dakin.
Sam abin ma dariya ya bani lallai akwai match me zafi a gidan nan to Allah ya bawa
me rabo sa’a.

Washe gari tsaf na shirya zan fita aiki, ina tsaye ina barwa Amna sallahun abinda
zata girka ya fito muka kalli juna se cewa yayi

“Kiyi mun tuwo da miyar Kubewa da rana za’a zo a karba”

“Naman rago zaki sakawa Miyar Akwai soyayye ma a Freezer seki diba” na fada ina
zuge jaka ta dan duk a zatona da Amna yake seda naji yace

“Dake nake ba ita ba, daga yau ma karta sake yimun girki kuma kullum za’a ringa
kaimun lunch office” yana gama fada yasa kai ya fita na bishi da saurin. Sanda na
fito yana tsaye a jikin motarsa.

“Ban fahimci abinda kake nufi da nayi maka lunch ba ka manta zanje aiki ne” na fada
ina kallonsa, idan ya amsa ni to motar sa ma tayi magana, ya kunna mota ya bata
wuta, harya taka ya leqo ta window yace
“Banyarda ki dara qofar gidan nan ba” ya qarawa motarsa wuta ya barni a tsaye.

Kamar mara laka haka naja qafafuna na koma cikin gidan, akan kujera na zube ina
sauke numfashi, dagaske dai Bashir yake ya na so ya rabani da aikina kenan. Badan
ina tsoron Allah da fita zanyi sedai duk abinda ze faru ya faru amma yau zan haqura
idan yaso ya dawo naji me yake nufi dani tukunna.

Anty Suhaima na kira ina kuka na shaida mata komai tunda daman da ita muka fara
maganar ai, haquri ta bani tace yanzu zata kira Alhaji qarami ta gaya masa duk
yanda mukayi zanji ba’a rufa awa guda ba kuwa sega kiran Alhaji Qaramin.

Shima din nasiha yayi mun akan na kwantar da hankali na shedan ne kar mu bashi
qofar da ze farraqamu ya tabbatar mun kuma ze kira Bashir din yayi masa magana.

Ban san yaya sukayi ba dan daya dawo be kulani ba fuskar nan dai kamar ta shanu
haka muka kwana kamar abokan gaba. Washe gari dan na gwada Sa’a ta na shirya kuma
akayi dace tafi kuma mutu be ce dani ba hakan yayi mun dadi alamu sun nuna sunyi
magana da Alhaji Qarami kenan kuma ya barni naci gaba da zuwa aiki.

Haka muka cinye sati biyu cir ana wannan yanayin duk iyakar qoqari inayi gurin
kyautata masa dayi masa duk abinda nasan yana so amma kallon banza ban ishi Bashir
ba bare na arziqi haka idan zan kwana ina masa magana baze daga kai ya kalleni ba
ko wani abin yake so sedai ya kira daya daga cikin yaran yayi masa.

Abinda na lura dashi shine harda zugar mutane a cikin abun nasa kuma daman na san
Bashir halinsa ne daukar shawarar wasu indai ka gaya masa abinda yayi daidai da
ra’ayinsa tofa shikenan.

Haka dai nake lallabawa ina taka tsantsan da duk abinda ze qara mun laifi a gurinsa
ga zazzabin da yake damuna kullum qaruwa yake ga kuma sabuwar damuwar Bashir gaba
daya na susuce har wata rama nayi,

A bakin Aliyu naji cewar Monday zuwa Laraba su Bashir bazasu yi aiki ba an basu
hutu, nan da nan nima na rubuta letter akan bani da lafiya naci sa’a akayi mun
approving da wuri dan daman duk wanda ya ganni yaga mara lafiya.

Nan da nan na shiga shirye shiryen yanda zamu gyarota da Bashir dan wannan zaman
doya da manjan da mukeyi bayamun dadi kuma a zahiri na fishi cutuwa sedai nima
qudurce a raina indai yana tunanin abinda yakeyi ne zesa na sakko na bi ra’ayin sa
na ajiye aiki na na koma Gombe ya dakko wata Mata ya kawo nan to kuwa bazan chanza
ba.

Idan da ace wani uzuri can na daban yasa ya yanke hakan zan iya karba amma wallahi
indai akan Amirah ne a wannan gabar na shirya karbar komai.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 31

BASHIR

Ransa fes ya bar gidan ranar dan ya tabbatar da Ma’u bazata fita batareda izininsa
ba. Zuciyarsa ta kasu biyu, wata tana gaya masa abinda yayi daidai ne inda wata
take nuna masa kuskuren abinda yake shirin aikatawa kuma kamar rashin Adalci ne.

Shikansa ya tabbatar da aikin Ma’u rufin asirinsa ne kamar yanda ta fada kudin
jikinsa yake komawa shida yayansa.

Haka yayita juya abun a ransa har ya isa office, Lokacin da suka fita break kiran
Alhaji Qarami ya shiga wayarsa, yayi matuqar mamaki amma daya tuna abinda ake ciki
seya goge mamakin.

A mutunce suka gaisa sannan Alhajin ya fara cewa
“Engineer yanzu Suhaima take gaya mun wata magana wai ko ka hana Ma’u zuwa aiki ne
ko menene dai, nasan halinsu qilan wani laifin tayi maka koh?”

Kame kame Bashir ya shiga yi yama rasa abinda zece masa, se Alhajin yayi murmushi
irin na manya. Yana sane yayi masa haka tunda Suhaimah ta fada masa komai harda
dalilin daya saka yace tabar aikin amma yana so ne yaji gaskiyar komai a bakinsa
hakan da yayi ya tabbatar masa da son kaine kawai irin nasu na maza ya saka shi
aikata hakan.

Seda yayi gyaran murya kafin yaci ga da cewa “Koma mene dai yanzu ina roqa mata
arziqin a barta taci gaba da aikinta, kuma koda gaba wani abu ya sake tasowa nine
uban Asma’u ni ya kamata ka gayawa zan dauki mataki akai” daga haka dukayi sallama
ya kashe wayar.

Sam hakan be yiwa Bashir dadi ba, akan me zata kai qarar sa gurin sa saboda tasan
Alhaji Qarami yafi qarfin yayi jayayya dashi ko ya nemi alfarma a gurin sa yaqiyi,
yanzu gashi saboda qanwar sa ya sauke kai yana roqonsa bayan ko shi aikin nasa da
yake taqama dashi bazar Alhaji Qaramin ce.

Yana hanyar komawa gida suna waya da Amirah Yake gaya mata abinda ya faru

“Amma wallahi Yaya sun ma raina maka wayo, kaida gidanka amma ace dan ka yanke
hukunci wani yazo ya warware shi kawai dan suna da kudi se su ringa zuba iko a duk
inda suka ga dama, gaskiya seka tashi tsaye koda yake aikin gama ya gama ai tunda
har ka bada qofar da zasu ringa yanke maka hukunci a gida kaga gaba baka isa ka sa
ko ka hana ba se a kai qarar ka inda akasan bazaka musa ba” Amiran ta fada kafin
taci gaba da yi masa fanfo

Da yake abinda yake so ne nan kuwa ya hau kai yayi daram akayi sa’a akayi Sa’a daya
tuntubi Bala da maganar shima, da yake duk kanwar ja ce duk irin Abinda Amiran ta
fada ya dora nasa akai, wannan dalili da hujjojin da suka kafa masa na cewa daga
inda wasu suka fara shiga cikin hukuncinsa tsakaninsa da Ma’u toh raini yazo dan
tasan duk sanda ya fada mata abinda be mata ba tana da inda zata kai a tilasta shi
ya chanza, wannan yasa shi ya kasa ganin kyautatawa da duk qoqarin da Ma’u ta ringa
yi na son ganin ta wanke kanta.

Se yake ganin duk ihu ne bayan hari, ta rigada tayi abinda tayi dan tayi ta nuna wa
duniya be isa ba shi kuwa yayi Alqawarin bazata ga gazawarsa ba dan haka su zuba su
gani da kanta zata haqura tace ta bar aikin nan dan babu gudu babu ja da baya.

ASMA’U

Ranar Litinin da wuri na tafi Asibiti dan daren jiya kasa bacci nayi ga zazzabi ga
wani ciwon mara dakyar naga safiya. Ina zuwa bayan likita tayi mun tambayoyi kai
tsaye ta turani lab inda suka dauki jini na da fitsari suka ce na jira a waje.
Minti 30 tsakani Nurse ta kirani dan har an kaiwa Dr result.

Ba qaramin mamaki nayi ba jin wai ciki ne dani dan ko kadan ban kawo hakan ba har
likitan tana tsokana ta wai haihuwa Biyar amma na kasa gane alamun ciki. Seda tayi
mun scanning, cikin sati 9, magunguna ta rubutamun da zasu taimaka mun da zazzabi
da kasalar da nake fama dasu na karba a pharmacy kafin na wuce gida raina qal kamar
an mun bushara da Aljanna.

Ada na ce na gama amma yanzu damun cikin nan naji dadinsa sosai dan nasan shine ze
zama silar daidata tsakanina da Bashir.

Sanda na koma gidan ya fita daman Amnah yareda sauran yara suka fita taje
makarantar ana neman su dan suna shirye shiryen yi musu graduation party.

Ban zauna ba saboda murna duk se naji na warke ma, dakin Bashir na shiga na gyaro
shi tsaf na wanke Toilet na saka qamshi, kafin na nemi guri me kyau na ajiye
takardar test din Asibitin inda nasan hankalinsa ze kai.

Dakina na koma nima na sake wanka na sheqa kwalliya sosai dana san dole na burge
Bashir, Dumamen tuwon da mukayi jiya naci da baqin tea kafin na sakeyin brush na
dawo palour na zauna zaman jiransa.

Se gurin sha biyun rana ya shigo, na miqe fuskata dauke da murmushi na nufe shi
amma kafin na qarasa ya dakatar dani ta hanyar daga mun hannu se na tsaya din kuwa
ina kallonsa ya wuce ni ya zauna akan kujera.

Jiki a sanyaye nima na koma na zauna, idonsa akaina yace “Weekend din nan zaki
Tafi Ita kuma Amirah tazo”.

“Wai dan Allah Baban Ali me yasa kake da son tada zaune tsaye? Ina mun gama da
wannan maganar ko. Nagaya maka ni bani da matsala da zaman Amirah amma banga
dalilin da zesa ni a takurani ace na koma wani waje ba saboda ita, tazo mana kowa
ba zaman ta zatayi ba namene se an shiga haqqina wai” na fada ina yatsina fuska dan
harga Allah na gaji da maimaita abu guda.
Kullum daga ya zauna zancen kenan Amirah zata zo toh ko Addah ce tazo mana ina
ruwan wani.

“Oh hakane, wato kina ganin kin isa kenan a zaton ki dan kin kai qarata ze sa na
chanza ra’ayina ne? Ni ba irin namijin da ze zauna yan uwan matarsa suna tsara masa
yanda zeyi bane kin kuma fi kowa sanin idan nayi niyyar yin abu babu uban da ya isa
ya saka ni ko ya hanani”. Bashir ya fada yana kallon cikin ido na, sena miqe tsaye
nima ina kallon sa nace

“Duk abinda zakayi ya tsaya kaina ni kadai karka ce zaka zagar mun Yaya dan ni
nasan mutunchinsa kuma ko banza wallahi Alhaji Qarami yafi qarfin raini a gurin ka
dan yayi maka abinda duk duniya babu wanda yayi maka shi, ko gani kayi za’a zage
shi kamata yayi ace se inda qarfin ka ya qare”

“Ni kike gayawa haka Ma’u ni kike gorantawa cewa Yayanki yayi mun abinda babu wanda
yayi mun shi ko?”

Shiru nayi masa dan idan na bude baki nasan bazan fadi abu me dadi ba dan gaskiya
Bashir ya qure ni na tabbatar so yake sena zazzage masa galan din rashin mutunchi
daga nan se ya juya duk wani laifi zuwa kaina tunda daman neman sanadi yakeyi, ina
jinsa yana ci gaba da fadar maganganu son ransa ban tanka shi ba qarshe ma nayi
wucewa ta dakina na ina shiga ya biyo baya na yana cewa

“Wato ga mahaukaci ina miki magana kin tafi kin barni a tsaye ko lallai Ma’u kina
so kiga asalin kala ta kenan”.

A fusace na juya nace “wace kalar taka ce tayi saura da ban gani ba Bashir, ai duk
wata fuska ta ka ka rigada ka gama bayyana mun ita na gani na kuma san da wanda
nake zaune dan tsahon shekarun da mukayi a baya Kura ce da fatar Akuya nake zaune
da kai. Daman mutane sunyi gaskiya da suka ce baka tantance halin namiji se randa
ya qara aure.

Wallahi ka bani mamaki Bashir ban taba tsammanin ka a cikin layin maza masuyiwa
matansu butulci ba a lokacin da suka samu wasu.

Dame na rage ka, ta ina na gaza? Dame ita wacce kake fifitawar ta fini?
kullum hanqorona na burge ka nayi maka abinda zaka ji dadi amma a koda yaushe
sakamakona baya zama me kyau anya ka taba sona kuwa?

Karkasa na yarda da cewa ka aure ni ne kawai dan biyan buqatar kanka yanzu da kake
ganin ka samu yanda kake so kake neman ka mayar dani bolar da zaka juye sharar ka
duk a sanda ka debo ta idan ba haka ba meye laifi na? Ko kuma ni ban cika mace ba
nata matancin yafi nawa da yasa kake take nawa haqqoqin dan biyan tata buqatar.

Wallahi Bashir idan baka yi a hankali ba zaka tashi cikin jerin mazan da zasu je
lahira da shanyayyen jiki saboda ka gaza Adalci a tsakanin matanka, idan ma kana
tunanin idan kayi mun abu zan yafe ko ban kaiwa Allah qarar ka ba Bashir yana kallo
kuma se yayi mana hisabi nida ku” nayi maganar cikin muryar da take nuna qololuwar
bacin raina dan gaskiya nakai bango na kuma shirya tarar ko menene tunda naga
alamar Bashir ya fara daukar kawaicina a matsayin sakarci shiyasa yake kawo mun duk
shirmen da yaga dama.

“Ni kikewa fatan na tashi da shanyayyen jiki Ma’u saboda nabaki umarni a matsayina
na mijinki kinqi bi?” ya fada muryarsa na rawa idonsa ya kada yayi jajir har wasu
jijiyoyine suka fito a cikinsu, banji ko dar ba a raina ba na gyara tsayuwata ina
kallonsa ido cikin ido. Se ya girgiza kai yayi kwafa kafin yace

"ASMA'U, ASMA'U, ASMA'U sau nawa nawa na kira sunanki?
Dukda yanda Asma’un daya kirani ya dake ni dan na manta rabon da Bashir ya kira
ainihin sunana amma se na dake, hannu biyu na saka na riqe quguna nace

"Sau uku ENGINEER BASHIR AHMAD" dan ni ma fa ba baya bace a fagen iya fitsara,
kawai dai shekaru da yanayin rayuwa suka sa nayi sanyi amma a wannan gabar dole na
fito masa a ainihin MA'UN BAFFAH ta wadda ya sani shekaru goma sha shida da suka
gabata bawai ASMA'U matar Bashir uwar Aliyu, Jafar, Farida, Abdallah, Ahmad da
Muhammmad ba.

Qara gyara tsayuwata nayi ina kallonsa ganin yanda yake bina da kallon dana
tabbatar na zallar mamaki ne jin yanda ni na kira nasa sunan gaba daya ma Gatsal
bako Sakayawa,

Sena saki wani guntun murmushin takaici, lallai Bashir ya manta dawa yake magana, a
zatonsa nayi tibis ne ko? be san har yau da saurana ba sedai ba’a tabo ni ba.

Kansa ya girgiza yana qoqarin kokawa da hukuncin da zuciyarsa take ayyana masa,
wani sashe na ingizashi akan yayi inda dayan ke kwabarsa da nuna masa zafa ta iya
kwabewa amma idan ya ja da baya ai ma zata raina shi kuma yabi abinda take so
kenan.

Kai ba wannan ba raini biyu ma tunda itama ma AMIRAN zata qara tabbatar wa duniya
be isa da ASMA'U ba tunda gashi ya bata umarni taqi tabi. Se ya gyara tsayuwarsa
tareda qara tsuke fuskarsa da dama can bata da fara'a sam, wani kallo yake jifanta
dashi da yasan yana ladabtar da koma waye amma banda wannan kangararriyar Matar.
Cikin kaushin murya yace

"For the last time ASMA'U ina baki umarnin kiyi resigning daga aikin ki ki tattara
yara ku koma Gombe d....."
"Na gaya maka wallahi Bashir bazan bar aiki na na koma Gombe ba saboda zaka kawo
Matarka Lagos" nayi saurin katse shi.

"Shikenan, Se ki zaba ko auranki ko kuma aikinki" ya fada cikin sautin dake nuna
qololuwar bacin rai yana harde

28 / 80