Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
ai ba shiri ta buga wani uban tsalle tayi gefe sedai kafin ta kai
qasa yai azamar riqota dan shi kansa ya tsorata da yanda ta miqe din ba shiru suka
zube qasa, a tare suka saki qara shi ta zafin buguwar rashin tsammani data same shi
ita kuma ta azabar da taji cikinta ya dauka danji tayi kamar dinkin ze bare.
Kuka riris ta saka gana tsoron abinda ze mata gana azaba abinda ya hadu ya qara
qular da Bashir qoqari yake ta tsaya tabar mutsu mutsun amma ita se qara zillewa
take tana ihun yayi haquri a zatonta dukanta zeyi, ganin tana bata masa lokaci yasa
ya daka mata wata uwar tsawa yana ce wa “wallahi ko ki rufe mun baki kona make ki a
gurin ki tsaya mu gani ko kinjiwa kanki ciwo”.
Tsit tayi se shatato kwalla take hannu ta akan cikinta dayan kuma ta rufe baki,
yanda take matsa cikin ya tabbatar masa da tana jin zafi ya saka shi cewa ta tashi
ta biyo shi yayi gaba tana binsa a baya a dudduqe, seda ya kashe fitilun ya kulle
qofa kafin suka shiga motarsa, wallahi badan yana tsoron kar wani abun ya sameta
Allah ya kamashi ba da barinta zeyi jikinta ya gaya mata. Haka ya sake fita daya
saura suka nufi Asibiti shi yana jera tsaki ita tana kuka qasa qasa.
Basu bata lokaci ba dan an tabbatar musu babu komai motsawa gurin yayi amma dai ta
kiyaye irin hakan, Allurar kashe zugi suka mata kafin suka kamo hanya kamar
abokanan gaba har suka zo gida yana tsayawa ta wuce sedai tuna bata da key ya
sakata rakubewa tana satar kallonsa. Har ze shige part din Asma’u shima ya tuna da
bata dakko key dinba dan haka ya qarasa ya bude mata qofar be amsa Nagode din da
take ce masa ba ya wuce abinsa.
Kitchen ya fara tsaya wa ya dauki Yoghurt me sanyi kafin ya hau saman, beyi zaton
samun Ma’u a dakin ba amma yana budewa qamshin Airfreshner dana turarukan baccinta
suka masa sallama besan sanda ya fara sauke aji yar zuciya ba dan har ga Allah
qanshin sun san yaya masa rai.
Akan dan teburin da yake dakin ya ajiye yoghurt din da tarkacen keys dinsa da
wayoyi kafin ya cire rigar sa ya shiga toilet. Wanka yayo da alwala, bayan ya fito
ya shafa mai sama sama ya zura jallabiyya Ya fesa turare lokacin har biyu ta gota
kafin ya kalli Gabas ya tada sallah.
Raka’a biyu yayi a sujjadarsa ta qarshe ya dade yana yiwa Allah kirari kafin ya
dora da istigfari tareda neman zabin Allah akan dukkan al’amuransa ya rufe da
salatin Annabi kafin yayi tahiya ya sallame. Ya dan jima hana lazimin La’ilaha
illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin har seda bacci ya fara fuzgarsa sannan
ya tashi yana jin nutsuwa na saukar masa. Seda ya sha yoghurt din dan yunwa yake ji
sannan ya kwanta ya juyawa Ma’u da bata san da dawowarsa ba baya.
A kusan tare suka farka da Asuba, ya cuna baki Gabas ta cuna Yamma kafin ya miqe
tayi wuf ta shige toilet tayo fitsari tareda chanza pad ta koma ta kwanta kafin ma
ya gama shirin Masallaci bacci ya sake kwasheta.
Da safe ma haka suka tashi, ya hada fuska tam yana zaune a palour yana kallon
labarai ita kuma tana ta kaimawon hada masa breakfast, bayan ta gama ta masa magana
daga “Toh” be sake ce mata komai ba kuma be motsa ba se itama ta share kawai dan
dai fushin ai ba nata bane, idan kuma zancen komawa ne ai indai yar gaskiya za’abi
batayi laifi ba. Dibar Abincinta tayi ta wuce dakinta taci, bayan ta gama ta fito
sukayi kici bus ze shiga zata fito ta rabe masa ya wuce kafin ta fito.
Abincin ta fara dubawa taga yaci da yawa ma tayi dariya a fili tace “na zata shima
cikin fushi kake dashi ai” ta shiga tattarewa ta sauka qasa da kayan. Tana cikin
dauraye kwanukan taji motsinsa ya bude qofa, ta window ta ga fitarsa tana ganin
yanda yai diri diri a tsakanin parts din me kuma ya tuna ya wuce ya kunna motarsa
ya bar gidan.
Ragowan Abincin ta juye ta yafa mayafinta ta kaiwa Amirah. Tana zaune a palour tun
jiyan a nan ta kwana sallah ma duk anan tayi kuma har lokacin bata kwashe kwanukan
jiya ba ga plate din data sake cik tuwo bayan sun dawo shika a bushe.
Ba qaramar kunya ce ta kamata ba ganin Asma’u, duk se taji ta muzanta saboda yanda
Asma’un ta sheqa wanka da wata Atamfa doguwar riga se qanshi take ita kuwa tama
zaune cikin kwanuka da kayan jiya a jikinta seta hau soshe soshen tana gaida Asma’u
da tayi mirsisi kamar ma bata ga komai ba.
Kayan ta dire mata tana cewa ta juye ta bata kwanukan kafin ta duqa ta kwashe na
jiyan a ranta tana cewa “Na san darajarsu bari na kwashe abuna” bata ko saurari
Amiran dake cewa ta barsu yanzu zata tashi ta wanke ba, ganin haka yasa ta tashi ta
shiga kitchen ta juye ta daurayo kwanon da zallar ruwa ta kawo mata. Karba Ma’u
tayi tana cewa “se ki nemi abinda zaki ci da rana tunda naga kin warware” tayi waje
abinta.
Wannan abincin taci tayi nak sannan ta tashi ta dan tattare gurin ta shiga dakin ta
tana qarewa Hadadden Gadonta da aka rushe bedside din kallo. Ita dai yan sunan nan
sun cuceta wallahi dan dai bata hango ranar da Yaya ze sake mata wasu kayan ba
yanzu ma ta samu ya haqura ya sakko daga fushin nan ma kafin wani zance ya biyo
baya.
Wunin ranar zir Bashir a waje yayi shi, itama Ma’u bata zauna ba ta fita harhado
sauran kayayyakin da take buqata da ba’a samu acan dan haka se yamma lis ta dawo
bayan ta biya ta dakko yara. Koda suka dawo ma basu zauna ba kayansu suka hade tsaf
dan gobe Sunday tanason suje su wanke kai da kitso Monday se Lagos.
Sanda Bashir ya dawo yaran sun kwanta Amnah ce kadai idonta biyu tana karatu dan da
sun koma sati biyu zasu fara SSCE, da niyya tijara idan basu dawo ba ya shigo gidan
se Allah ya ceci Ma’u tana kitchen ta jiyo Amna na gaishe shi yana tambayarta
yaushe suka dawo tace dazu. Kitchen din ya leqa suna hada ido ya wani qara shan
kunu tayi masa sannu da zuwa ya daga kai ya fice ya haye sama qasan ransa yaji
dadin ganinta.
Seda suka zo kwanciya ta gama duk hidimominta taji muryarsa yana cewa “akwai abinda
kuke buqata ne?” Seta dakata daga saka hular da takeyi ta kalle shi yana zaune a
bakin gadon yanda yayi maganar yana fuskarta wani guri daban, kallo daya zaka masa
kasan akwai abinda yake damunsa gaba daya yayi laushi.
Kusa dashi ta koma ta zauna, seda ta shagwabe fuska sosai ta tara kwallar qarya a
idonta kafin ta riqo hannunsa, waiwayowa yayi seda ta tabbatar ta saka kwayar idon
ta cikin tasa yanda baze iya kaucewa ba sannan tafara magana tana cewa
“Haba Baban Ali Haba Na Ma’u wai fushin ne haryanzu ina kake so na saka kaina naga
haske bana ganin Murmushin ka? na tuba nabi Allah kayi haquri indai batun Tafiya a
motane na yarda gobe muyi asubanci mu tafi idan kana tare damu nasan babu abinda ze
same mu se ikon Allah”.
Duk yanda yaso ya janye ya kasa dan riqon da tayi masa da kaifin idonta yayi tasiri
a jikinsa, daman dauriya ce kawai amma yana buqatar ta, yana buqatar me kwantar
masa da hankali kuma Ma’u ita kadaice duk damuwar daya shiga a duniya take iya
magance masa ita har in yana tare da ita tana saka shi ya manta komai sedai daga
baya ya tuna shi yasa duk sanda matsala take tsakaninsa da ita yake ji kamar ya
zauce dan babu me masa magani.
Fuzgota yayi jikinsa ya mata ruqo me tsauri tana jin yanda zuciyar sa take bugawa
jikinsa har wani rawa rawa yake, cikin dasashshiyar murya yace “Badake bake fushi
ba Ma’una, me yasa, meyasa ita bazata ji magana ta ba me yasa koda yaushe take
sakani ciwon kai”.
Seda Ma’u ta murguda baki ta harareshi dukda be gani ba a zuciyar ta tace “taya zan
sanin maka ba kai ka kwasowa kanka ba” a fili kuwa seta qara riqeshi cikin kwantar
da murya tace “Kayi haquri” . Yanda ta fadi haqurin yasa yaji tamkar ta watsa masa
ruwan sanyi a zuciyar sa, kissing goshi ta yayi kafin yace “Na haqura Yar Aljanna”.
Cikin tsananin farin ciki ta dago ta kalli kyakykywar fuskarsa tace “To Na kawo
maka abinci, yau duk nasan baka ci komai ba ga fuskar ka nan ta nuna”.
“Muje ki bani” ya fada yana daga ta gaba daya, seda suka sauka har qasa sannan ya
ajiyeta Amnah da ta gama hada littattafanta zata shiga daki tayi saurin saka
littafin a fuska tana tafiya da baya da baya. Rankwashi ya kai mata da wasa cikin
harshen turanci wanda dashi yakewa yaran magan yace “gidan ku me kike yi anan baki
kwanta ba haryanzu”
Dariya tayi ta dan janye littafin tace “Abbi karatu Saura two Weeks mu fara WAEC
fa”
“Ok maza je ki kwanta karki manta kiyi Addu’a” ya fada yana zama akan kujera, seta
juya tana cewa “Good night Abbi”
“Good night Amna” ya fada daidai sanda Asma’u ta fito da plate din daya zubo masa
dambun couscous se kunun aya a Jug.
“Good nigh Mami” Amna ta sake fada, seda Ma’u ta ajiye kayan akan centre table
kafin tace “Good night Amnan Abbi”.
Dariya Bashir yayi yana cewa “fadi ki qara kam Amnan Abbi” murmushi kawai tayi, a
ranta tana jin dadi yanda Bashir ya dauki qanwar tata tamkar yar da ya haifa a
cikinsa dan gani take kamar yana mantawa ma ba yarsa bace, tunda riqon Amna ya dawo
hannunta be taba sauya wa daga yanda ya karbi yarinyar ba ko a fuska, komai ya
tashi yiwa yaran itace farko a matsayin first born dinsa. Cikin dadin rai yaci
abincinsa ta tattara suka wuce Aza rum.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 23
Ranar litinin kamar yanda muka saba tunda muka yi sallah muka hau wanka da shiri
dan jirgin bakwai za mubi ga tazarar zuwa Airport Akko dago Gombe. Shida bata
qarasa ba muna bakin Sienna da ake kwasar mu in munzo ko zamu tafi. Yaran sun gama
shiga ina tsaye daga qofar ina jiran Bashir da yake qara dudduba cikin gidan kafin
ya rufe ina murmushin hirar su Naziru da Ahmad yanda yake biye masa kamar wasu
Abokai.
Ba dade wa Bashir din ya fito yasha Suit kalar Dark Blue farar cikin nan har wani
daukar ido haskenta yake, seda yayi Addu’a ya tofa kafin yaja qofar ya rufe se ya
nufi part din Amirah yana cewa Nazirun “ka kunna motar mana ka tsaya kana surutu”
ya shige nida Naziru muka rakashi da ido.
Ashe tana gidan nayi zaton tun jiya ta wuce gida yanda ta saba ana washe gari mu
tafi take farayin gaba. Cikin motar nima na shiga na zauna ina duba agogon wayata
ganin shidan ta yi harda minti biyar.
Bashir kuwa a daki ya tarar da Amirah hankali kwance tana baccinta, shurin qafarta
yayi ta farka a firgice tana zare ido ganinsa yasa tayi saurin nutsuwa ta shiga
gaishe shi. Be amsa ba ya cilla mata rafar 200 dubu Ashirin kenan yana cewa
“Zamu tafi Naziru ze kawo miki kayan Abinci, wallahi koda wasa kika saka qafarki a
qofar gidan nan ki tabbata kin fita kenan mtsw” ya ja tsaki ya juya dan har yanzu
bala’in haushinta yake ji gashi an hanashi hukuntata.
Harya kai qofa ta zaburo ta biyo shi da sauri dan kuma yanzu hankalin ta ya koma
kan yarta, ga Nononta da suka dameta da ciwo saboda cika, saurin ce masa tayi “Dan
Allah yaya zanje naga Iman” tayi maganan cikin rawar murya kaman kuwa yana jira ya
jefa mata wani mugun kallo kafin yace
“Ya zama kuskure na qarshe da zakiyi tunaninyi ki sake dora hannunki a kan yarinyar
nan, da kina sonta kika jawo mata ciwo sannan tunda aka fita da ita daga gidan kin
tambayi yanda take bare kije ki ganta? Idan ke bakya qaunarta ni inasonta dan haka
nayi miki iyaka da ita kota warke bazan dawo miki da ita ba tunda bake kadai bace
zan kaiwa wadda zata kular mun da ita” yana gamawa yasa kai ya fice ya barta tana
rusa kuka.
Abinda baze ma yiwu ba kenan taya ze raba ta da yarta ce masa akayi bata sonta? Ai
tasan tana Asibiti kuma a kwanakin in ma tace zataje ba bari ta zeyi ba shi yasa
amma wallahi bazata yarda ba dole ma ya barta ta fita kai ita bama zata iya zama a
gidannan ba sedai ta tafi gidansu, ta yarda acan din bazata fita ko ina din ba amma
badai a nan ba.
Tana son magana da Addah amma babu hali, ita ba waya Addah ma haka dukda da tana da
wayar samun Addah bazeyi wahala ba ko a wayar Ummi ne. Tunda suka rabu a gidan Dada
basu sake magana ba bata san yaya Addah ta qare a nata gidan ba tilas kuwa tana
buqatar magana da ita, ya dai tafin ko Nazirun in yazo anjima ta roqeshi ya siyo
mata ko Key pad ce a cikin kudin da Bashir din ya bar mata.
GIDAN ADDAH
Ranar bayan Addah ta bar gidan su Bashir Napep ta hau ya kaita gidanta. Alhaji
Murtala na tsaye a qofar gidan da wasu mutane su biyu Addah ta sallami me Napep
zata shige ya dakatar da ita.
“Yawwa ga Hajia Fatun ma ta dawo” ya fada yana nuna musu ita. Se Addah taci burki
ta bisu da kallo daya da daya amma bata ga fuskar data sani ba dan haka se ta saka
kai ciki kamar bataji maganar da Alhajin yayi ba harta tura get ya dakatar da ita
dacewa
“Wallahi kika shiga gidannan se ranki yayi mummunan baci Fatu” Alhajin ya fada
cikin kakkausar murya. Se Addah taja da baya jiki a sanyaye, to su waye wadannan
kuma? Wane jafa’in ne ya sameta.
Takadda daya daga cikinsu ya miqo mata yana cewa “Hajia gashi sammacine daga kotu
ana qararki akan laifin damfara”.
“Damfara?” Addah ta fada da qarfi tana dafe qirji tareda zaro idanu waje
“Ni Fatu wana damfara?” Ta sake tambayarsu hankalinta in yayi dubu ya tashi.
“Akwai bayanin komai a ciki idan kunje kotu zakiji cikakken bayani kafin sannan
kina iya neman lauya da ze tsaya miki” dayan mutumin ya fada, sallama sukayiwa
Alhaji kafin suka hau mashin din da suka zo suka bar Gurin.
Addah data gama jiqewa da zufar tashin hankali ce ta kalli Alhaji Murtala da yake
jifanta da wani irin kallo data fassara dana tsana da takaici yace “Daman na fada
miki Fatu tun kina dauko magana kina cin riba wata rana se kin dakko ta wanda yafi
qarfin ki.
Se kije ki san yanda zaki kare kanki ko kuma ki fara shirye shiryen tafiya gidan
prison tunda halinki yaja miki” yana gama fada ya shige cikin gida Addah ta rufa
masa baya tana kuka kamar yarinya.
Bata tsaya ba har cikin uwar dakinsa inda ya shiga, Hajia Binta yar tsakiyarsu na
cikin Toilet tana wankewa taji shigowarsu da kukan Addah seta leqo tana cewa “Aa
Alhaji lafiya waye yake kuka... Au Addah kece lafiya dai waye ya mutu?”
“Kiga mutuwa akanki munafuka kuma duk sharrin da kuka kitsa masa sedai ya koma
kanku” Addah ta fada cikin hargagi, dariya Hajia Binta tayi harda tafawa tana cewa
“Ikon Allah se kallo, da alama dai bana an kwaso me zafi”
“Fita ki bamu wuri” Alhaji ya katseta, seta hade fuska tana cewa “kamar yaya Alhaji
in baku guri bayan ni nake da aiki ko Alfarma za’a nema ai ba ta haka za a zomun
ba” kafin yayi Magana Addah ta tareshi da cewa
“Alhaji muje gurina Dan girman Allah”. Shiru yayi kamar baze amsa ba se kuma ya
miqe yayi waje ta bishi a baya yana jin Hajia Binta na fadar maganganun an shiga
haqqinta dan ba haka taso ba, dayace ta fita zata fitan in yaso ta labe inda zata
ji kan zancen tas gashi yanzu ta jashi dakinta.
Addah kuwa tiryan tiryan ta labartawa Alhajin duk abinda ya faru da basussukan
jama’ar data ci da yanda sarqar Hajia me Gwal ta salwanta dama yanda suka rabu
yanzu ga zancen sammaci”.
Takaici ya gama qume shi, shidai Fatu qaddarar sa ce amma ba komai lokaci yayi
daya kamata yayi maganinta ko yaya me taji a jikinta amma yanzu bari a gama wannan
case din tukunna.
“Wanda yaja ruwa ai shi ruwa ze doka, takaddun gidan original suna hannuna gobe se
muje gidan matar aje da Dillalai suyi masa kudi a siyar a biya kowa kudinsa, Allah
ya tsare gaba idan zaki gyaru” ya tashi ya fice ya barta tana ajiyar zuciya dan
bata zaci abubuwan zasu zo da sauqi haka ba. Ita yanzu koma menen ai a siyar a biya
wannan jarababbiyar matar, ita da tunda Allah ya halicceta ko Police station bata
taba zuwa bare a ganta a gaban Alqali gara komeye a siyar a bata kudin su rabu
lafiya. Da wannan ta samu sa’idah har ta iya kwantawa tayi baccin gajiyar da batayi
ba.
ASMA’U
Gaba daya sukuku mukayi tafiyar babu wani kuzari har muka sauka Ikko, a Airpot din
muka rabu Drivern Bashir ya kwashe mu shi kuma ya dauki Shatar Taxi ya wuce office
daga nan. Yanda nayi tsammani gida na nan ya hada kari, bamu ko zauna ba na rabawa
ko wa aikin da zeyi, Ahmad da Muhammad da suka fara mun rigimar wai Yunwa dukda
munsha Tea kafin mu taho ga Cake da sukaci a jirgi se na turasu gidan Anty suna
fita kuwa se gasu sun dawo wai Aliyu da Jafar suje inji Anty, Breakfast ne data
shirya mana ta basu wanda ya zamar mata kamar dole duk sanda mukayi tafiya irin
haka bata gajiya seta kawo mana.
Nan da nan kafin wani lokaci mun qalqale ko ina har kayan da muka dawo dasu kowa ya
jere nasa na amfani kuma an adana su a inda ya kamata.
Bayan Azahar Muna zaune muna huce Gajiya Anty ta shigo su Ahmad na binta a baya da
kulolin Abinci, bata gaji ba wai abincin rana ta kuma kawo mana, matar dai tana da
kirki kwarai nayi sa’ar maqociya.
Kan Dining suka koma Amna ta zubo nawa ta kawo mun cikin palour ina ci muna hira da
Anty suna gamawa kuwa duk suka shige daki wai bacci se Anty ta miqe tana cewa bari
ta barni nima na huta. Tsarabar Kindirmo me kyau da Dambun fura se Kuka da kayan
qamshi na dakko mata daman na ware su daban na hada mata da wani turaren wuta da
Alawiyya yayata take hadawa ta bani yana da kyau sosai mukayi sallama ta wuce gida.
Na raka ta kenan David yaron da Bashir yake aikowa wani lokacin ya kawo saqo ya
tsaya a qofar gidan, kayan amfani ya kawo su kayan miya, veggies, Nama, kifi,
dankali, doya plantain duka dai kayan amfani da za’a nema ya siyo, qofar kitchen ta
baya na bude masa