Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
besan
abinda zata sake aikatawa ba dan haka yabi bayanta dan ya katse mata duk wasu
fukafukan rashin kunya data daura a jikinta.
ASMA'U
Turo qofar da akayi ce ta sakani waiwaya da saurin ina ja da baya dan nasan Bashir
ne, seda na matsa ciki dakyau dan na cire takalmana daman na riqe qugu da hannu
biyu kafin cikin tsiwa nace
"Wai meye kuma meka manta a gidan nan da zaka ringa shigomun duk sanda kaga dama
gaskiya baze yuwuba, yara ne na baka abinka baka da sauran hujjar da zata ringa
kawo ka cikin gidana dan haka yau ta zama rana ta qarshe da zaka sake sako wadannan
qafafun naka anan" na qarasa maganar ina girgiza jiki kamar wata me fada da
Sa'arta.
Da hannu ya nuna ni kafin ya nuna kansa yace
"Ni kika mara ko Ma'u? Ni kika mara saboda a matsayina na mijinki ina tuhumar ki
wanda ya dakko ki a mota da aure na a kanki ya kawo ki gida shine kika daga hannu
kika mare ni"
"Malam ka dai gyara kalaman ka tsohon mijina dai ko ka mantane saki biyu masu kyau
ka hada ni dasu kaga kuwa yanzu ni matar me rabo ce, shima da ka gani Bazawarina ne
yana cikin sababbin yan takara wanda Allah ya bawa sa'a shi ze dauka..."
"Ya isheki Ma'u" ya dakamun tsaqar data sakani yin shirun dole ina sake matsawa
cikin palour dakyau saboda gudun kota kwana. A fili nake ganin harzuqar da yayi da
tsananin bacin ransa wanda ko dazu dana mareshi banga hakan ba.
"Qarya kike yi ke tawa ce kuma dan ni kadai aka halicce ki, Wallahi kika sake
danganta kanki da wani Namiji Ma'u se na miki abinda baki zata ba" Bashir ya fada
cikin daga murya da har seda Faridah da Amna suka fito daga cikin dakinsu amma
kallo daya ya musu suka maida qofar garam suka kulle.
"Saboda na sake ki ne yasa kika samu lasisin da zaki ringa yawo a gari maza suna
daukar ki a mota ko kin manta da cewa har yanzu kina cikin iddar aurena, to kici
gaba da yin duk abinda kikaga ya dace dani dame mu zuba mu gani wanda zeci riba,
amma ki tabbatr duk dan iskan da na sake ganinki dashi se munyi shari'a".
"Kayi shari'a dasu awanne dalili Bashir saboda sunyi maka me" na fada ina binsa da
kallon sama da qasa, ba abinda ya bani dariya irin daya ce wai ina cikin iddar
auransa.
"Saboda sun tsaya da mata ta alhalinbata gama iddah taba" ya bani amsa yana
kallona. Seda nayi dariya kafin na dauki jakata ana ajiye na bude na zaro takardar
Asibiti ta shedar barin da nayi, daman yau nayu niyyar tura masa da ita dan jiya
Goggo ta sake kira ta jaddadamun na sanar masa gudun rigima.
Takardar na miqa masa ina cewa" Bashir nida kai fa Allah ya raba tsakani, gashinan
ka gani da idonka tun wuri ka goge wannan tunanin na wata iddah daga zuciyarka dan
tuni Allah ya yaye mun.
BASHIR
A mugun kidime ya daga kai ya kalli Asma'u bayan daya karanta abinda a ka rubuta a
jikin takardar, kalmar Abortion' (Abortion itace medical term na bari ba
Miscarriage ba 😨 kar yan uwansu Addah suce Ma'u ta zubar da ciki 😂😂) din da kawai
ya gani ya saka wata zufa ta shiga tsatstsafo masa gaba daya ma se yaji iskar gurin
tayi masa kadan se ya shiga fifita da takardar hannunsa yana cewa
"Ma'u ki gaya mun gaskiya tsakaninki da Allah bari kikayi dagaske ko wasa kikeyi".
"Lallai Bashir, kaga alamar wasa anan gurin ne ko kuwa, baqin cikin ka ya saka
shima cikin yaga baze iya zama ba ya kama gabansa ka kalli date din dakyau ka gani
in yaso seka hada sadakar uku data bakwai duk kayiwa Yar dan inaga ma macece" na
fada irin ko a jikin nan nawa amma can qasan zuciyata ina jin zafin rasa aurena da
cikina da nayi.
"Wallahi Ma'u na mayar dake, na maida auran mu fada miki ne kawai banyi ba" Bashir
ya fada cikin yanayin da yake bayyanar da tashin hankali da yake ciki, ni kaina a
kidime na kalle shi, duk yanda nake son Bashir nake qaunar zama dashi se naji
hankalina ya mugun tashi da jin kalamansa na wai ya mayar dani, a rude nace masa
"Yaushe ka mayar dani Bashir yaushe ka yi hakan kuma wanene shedar ka"
"Tun ranar da na karbi su Aliyu a daren na qudurce a raina na mayar dake amma ban
gayawa kowa ba" ya sake fada ya na matso inda nake, senaja baya da sauri ina sauke
wasu tagwayen ajiyar zuciya nace
"Idan ma ka mayar dani ban komu ba Bashir tunda baka gayamun ba kuma baka gayawa
kowa ya zamar maka shaida ba sannan ni a washe garin ranar daka sake ni Bashir a
ranar nayi bari ka duba daye din da yake jikin takardar nan idan ma baka yadda ba
kaje clinic din da kanka zasu tabbatar maka.
Dan haka tsakanina dakai yanzu be wuce zumunchi irin na wadansu da wani abu ya taba
hadasu ba shima albarkacin zuri'ar da take tsakanina dakai, bayan wannan ka qaddara
Bashir baka da wata alaqa dani a rayuwa ba ka kuma da hutumij da zakayi mun
katsalandan a rayuwa.
Mun rabu rabuwa ta har abada ka gogeni daga cikin lissafin rayuwarka dukda nasan ka
dade dayij hakan" shiru nayi da maganar da nakeyi jin kuka yana neman kufce mun,
bana buqatar na karaya a gaban Bashir balantana har yayi tunanin akwai sauran
burbushin soyayyarvsa a zuciyata.
"Asma'u karki ce haka, ta yaya kike zaton alaqar mu zata yanke kema kinsan wannan
bame yuwu ba bane, muje a kinyi barin na yarda kin fita iddah amma ai da sauran
igiyar auran mu ko yanzu zamu iya zuwa Limamin masallacin can ya mayar mana da aure
nasan ko Engineer Abdullahi ze yi miki walicci ni kuwa na isa na karbarwa kaina
aure, dan Allah mubar maganar nan Ma'u bazan iya ba, bazan juri ganinki tare da
wani mutum ba zuciyata zata fashe" Bashir ya fada yana sake damqe takardar dana
bashi.
Tsaki nayi dan naga abin nasa ma tsagwaron rainin hankali ne dan haka na kalleshi
nace
"Bashir fita zamu rufe gida"
"Naji zan fita amma ki gayamun kin yarda za'a mayar mana da aure ko gobe ne tunda
yanzu dare yayi, na sani Ma'u kina sona bazaki taba iya rayuwa babu ni ba dan haka
mu manta da komai mu koma wa auran mu kinji Ma'u".
"Bashir kenan, wato kasan ina sonka bazan taba rayuwa babu kai ba ko ashe tunanin
ka kenan shiyasa ka ringa garani kamar kwallo baka san qima taba bare daraja, ka
auro muj qanwar bayana da nagama shan wahala akanta sannan ka fifita ta sama dani
daga qarshe a dalilinta ka hada ni da saki ka rabani da yayana ko duk saboda kana
tunanin ina sonka bazan iya rayuwa babu kai ba tunda tare aka daure ruhinmu aka
jefi cikij duniya ko?
To bari kaji, ka qaddara kaine numfashina kasan dai idan babu shi babu rayuwa ko?
To dana koma zama dakai Bashir na zabi na mutu akan ka, idan sonka shine Ajalina to
ka je ka fara irga kwanakin da suka ragemun dan wallahi Bashir na gama auranka na
gama zama dakai ko kaine autan maza sedai na mutu ban sake aure ba, mugu me saka
soyayya da qiyayya wanda be dauki dan Adam a bakin komai ba" na qarasa maganar kuka
yana kwace mun sena shige dakina na bar Bashir da yake jinsa kamar an sare masa
qafafu tsabar yanda jikinsa yayi sanyi.
Kuka na ringayi kamar zan shide, Allah ya sani ina son Bashir na kuma san har
duniya ta nade da bazan dena sonsa ba amma in Allah ya yarda ko zan mutu na haqura
dashi.
Bani Bashir yake so ba, alfarma yayi mun ya zauna dani tsahon shekarun nan saboda
ina son sa badan shi a qashin kansa yana sona ba.
Meyasa ban taba gane hakan ba se a yanzu, me yasa tuntuni nake daukar kalaman
yaudarar sa a matsayin so ashe duk na ya cimma wata manufa ne yanzu daya gama samun
yanda yake so a rayuwa gashi nan ya fito mun sak a halayyarsa ta gaskiya.
Hannayena na daga sama ina kukan nace
"Allah kaine shaidata naso Bashir saboda kai badan wani abu ba kamar yanda kayi
mana umarni da mu so mutum dan Allah sannan na kyautata masa da dukkan iyakar
iyawata a zaman aurena dashi, Allah kagani halin dana shiga Ubangiji na roqeka kayi
mun sakayya da mafificin Alkhairinsa, idan kuma bani da rabon samun farin cikin
Namiji a rayuwata Allah ka sanya mun dangana har zuwa ranar dazan koma gare ka" na
shafa Addu'ata kafin na shige goge hawayen fuskata amma sun kasa tsayawa, haka na
shiga bandaki, ina wanka ina kukan harna gama na dauro alwala nayi sallar magriba
da Isha.
Ina kam abin sallar ina ci gaba da kaiwa Allah kukana anan bacci yayi awon gaba
dani ban ma sani ba.
BASHIR
Ikon Allah ne kawai ya kaishi gida yana shiga ya zube akan kujera yana sakin
numfashi a jere a jere tamkar wanda yayi gudun kilomita goma. Gidan shiru da alama
duk sun kwanta yaran haka Amiraj beji motsinta ba daman tunda ya dawo dazu ta bashi
shirmen abincin data dafa yayi mata tijara ta shige daki baya tunanin ta sake
fitowa hakan ma dadi yayi masa dan tabbas idan sukayi ido hudu da ita a yanzu dai a
yanda yake jinsa din nan to komai yana iya faruwa.
A daddafe ya tashi ya shige dakinsa yana jin yanda kansa yake juya masa kamar an
kunna fanka ga wani abu me maiqo da yake taso masa kamar zeyi amai haka ya zauna a
qasa gefeb gadonsa ya hada kai da guiwa ya rasa ina ze kama abin duniya ya hadu
yayi masa yawa
"Dana koma gidanka na zabi na mutu, idan sonka shine ajalina Bashir kaje ka fara
irga kwanakin mutuwata dan na gama auren ka" kalam Ma'u suka ringa masa tilawa a
kwakwalwa.
"Allah karka jarabce ni da wannan, Allah ka sani bazan iya dauka ba, nayi kuskure
Allah dan darajar Annabinka Muhammad SAW kayi mun sassauci karkasa wannan ya zamo
mun qaddadar da bazan iya dauka ba Allah karka rabani da Asma'u" sambatun da ya
ringayi kenan shikadai kamar zararre, wayarsa ya zaro faga aljihu ya fara laluban
numbobi, waze kira ya gayawa damuwarsa? Waye ze bashi sharar yabda ze gyara wannan
kuskuren tun kafin dare yayi masa.
"Bala" hannunsa ya tsaya akai, ba bata lokaci kuwa ya dannan masa kira cikin Sa'a
bugu biyu Balan ya daga yana cewa
"Engineer Mijin Asma'u, na Amirah ko dubu ta taru"
"Bala akwai matsala, ina cikin masifa ina cikin tashin hankali ka taimaka mun ka
gaya mun yaya zanyi na fita wallahi zan iya rasa raina Bala akan wannan tashin
hankalin" Bashir din ya katse Bala kamar ze fashe da kuka ko da yake tuni ma ya
fara na zuciya kawai dai hawayen ne suka qi fitowa a fili".
"Subhanallahi Bashir meya faru badai korar ka akayi daga gurin aiki ba?"Bala ya
fada
"Wallahi gara na rasa aikina Bala, gara na bayar da komai dana mallaka a rayuwa ta
da abinda nake shirin rasawa"
"To menene meyake faruwa kayi mun bayani yanda zan fuskanta se musan ya zamu kamo
bakin zare wane abune haka daya fi dukiya muhimmanci a gurinka Bashir?" Bala ya
sake tambayarsa a tsorace dan gaba daya kalaman Bashir din firgita shi sukayi.
"Asma'u, itace Bala, Ma'u tafi mun komai zan kuma iya bada duk abinda na mallaka
akan fansar ta, Zan iya bada raina akan Ma'u ka sani Bala" Bashir ya fada dakyar
dan qirjinsa ya fara yi masa nauyi, wani irin zafi zuciyarsa take masa kamar wadda
ake watsawa ruwan zafi, Tsakin da Bala yayi ne ya katse masa tunani kafin Balan ya
ci gaba da cewa
"To me Ma'un tayi maka yau kuma yanzu? Kai wai kullum baka da aiki sena kawo qarar
Ma'u ne haba ni wallahi na gaji da jin Ma'u tayi Ma'u tace idan ka gaji ka saketa
kawai kowa ma ya huta mana".
"Bala na saki Ma'u shine Bala'in da nake ciki a yanzu ta gama iddah kafin na mayar
da ita kuma tace bazat sake komawa gida na ba ta gama aure na" Bashir ya fada kamar
ze fashe da kuka.
"Kace ka saki Ma'u harta gama Iddah Bashir" Bala ya tambaye shi da son tabbatar da
daidai yaji ko kuwa kunnensa ne yajiyo masa abinda ya dade yana fatan faruwarsa.
"Dagaske nake Bala na saki Ma'u saki biyu kuma tayi bari a washe garin ranar dana
saketa kaga kenan iddarta ta ciki ka gayamun ya zanyi na shawo kanta ta haqura mu
koma auran mu wallahi ina son matata idan na rasata zan iya mutuwa ka sani Bala"
Bashir ya sake fada a matuqar raunane.
Bala kuwa seda yayi matuqar qoqari gurin danne farin cikinsa kafin ya aro damuwar
qarya ya saka a muryarsa yace
"Ashsha Mutumina ya akayi haka a garin yaya? Amma dai koma yayane aikin gama ya
gama yanzu sedai nemi mafita kuma ayi fatan Allah ya kiyaye na gaba.
Kana ji ko ni nasan Ma'u duk fushin da zatayi ba wani me yawa bane kasan irin son
da takeyi maka, dan lokaci kawai zaka bata dakanta idan ta sakko zata nemeka ku
daidaita kaima kasan duk abinda zata fada buyagine kawai amma Ma'u bazata iya
rayuwa babu kaiba kowa ya shaida hakan"haka Bala ya cigaba da dorashi a keken bera
har seda ya yarda kafij sukayi sallama.
Suna kashewa kuwa Bala ya daka tsalle yana cewa
"Allah na gode maka, badai kai wawa bane ka raina ni'imar da Allah yayi maka zaka
gabe kurenka wallahi muje zuwa yanzu aka fara wasan Ma'u kuwa nasan bazan same ta
ba amma tunda kaima ka rasa ko haka aka tashi wasa nayi nasara kuma in sha Allahu
bazat taba dawo maka ba".
Allah sarki Bashir shi kuwa Sosai kalaman Balan suka kwantar masa da hankali dukda
wani bangare na zuciyarsa yana so yaqi karban hakan dan a yanayin da Ma'u ta nuna
tabbas yaga chanje chanje da yawa a gareta yana kuma jin gaskiya ta fada a
maganganunta amma yasan so ba qarya ba, ba kuma ya zaton Ma'u zata taba tsanar sa a
rayuwa ta bakin Balan zafin abinda ya mata ne ya sakata fadar duk wasu maganganu
amma idan ya bata lokaci ta huce yasan zasu daidaita.
Da wannan ya lallashi kansa ya koma kan gado ya qudundune yana so ya manta
maganganunta amma ya kasa ga wani irin tsoro da tashin hankali dayake shigarsa a
duk sanda ya tuna kalaman ta na dazu har wani zazzabi yaji yana neman kama shi.
Anya ze iya bin shawarar Bala na ya bata lokaci harta huce dan kanta? Ya lura idan
mafa fushin tayi ba kadan bane dazu fa har mari yasha, kai ina baze tsaya ya zuba
ido yana kallo kwado ya masa qafa ba, a wannan gabar dole ya ajiye girman kai ya
kwato Ma'u tun kafin yan iskan mazan Lagos su hure mata kunne.
Haka yaringa hada lissafi yana warwarewa, a ranar dai yanda Bashir yaga rana haka
yaga dare sabanin Ma'u da ta shaqi bacci me cike da mafarkai masu dadi.
Washe gari haka ya farka kamar bugagge, ga damuwa ga rashin bacci lokaci daya gaba
daya suka nuna a jikinsa seka zata yayi sati yana jinya idan ka ganshi. Amirah ma
dai yau ta kama kanta, danfa jiya da daddare jijara yayi mata ta gaske akan taliyar
da har daddawa ta saka mata gashi taji kifi amma loma daya Bashir yayi ya ture ya
ringa surfa mata cin mutunchi wai bata iya komai ba haka yaran ko dandane basu ci
ba suka gudu gidan uwarsu acan suka kwaso abinci tana kallo suka ci suka bata guri
kuma haka ta share gudun sake yin wani laifin a gurinsa.
Da safiyar ma harda hawaye seda tayi da tana hada musu abin kari, doya da kwai ta
soya sannan ta dafa zallar ruwa ta jefa Lipton ko arziqin kanimfari da citta be
samu ba alhalin gasunan tunda ya siyo bata ko kwashe su daga kan inda ta ajiye ba
bare ta zuba komai a ma'adanar sa.
Haka ta gama hada abincin nan kafin dukan su su fito, tana tsaye yaran suka fara
fitowa tacewa yan biyu suzo suci, harta fara hada musu shayi Aliyu yana fitowa ya
kada kansu suka tafi gidan Maminsu suka bar Amirah tsaye tana binsu da kallo tama
rasa abin cewa.
Fitowar da Bashir yayi ta sakata waiwaya wa ta kalleshi, a kallo daya ta hango
damuwa qarara a fuskarsa amma ina ba wanann ne a gabanta ba, yana zama a Dining din
ta dira masa qorafin sunqi cin abinci Aliyu ya jasu sun fita ita dai ya kirasu dan
bazata hana kanta bacci tasha wahalar banza ba sannan suqi ci in kuwa ba haka ba
zata ajiye musu daga yau har gobe se sun cinye sannan zata sake yin wani girkin.
Bashir daya gaji da jinta, ga damuwar da take kansa ga ta surutun data tsaya masa
akai tanayi ya ture plate din data saka masa doyar ya tashi dan daman sam cin yunwa
kawai zeyibawai dab ta masa irin yanda Ma'u takeyi ba, jiya beci abincin dare ba,
ya fita ya nema ya ga babu motar Ma'u a waje abinda ya kaishi gidan kenan yana
tsaye se gata ta dawo yayi wannan mummunan ganin haka ya kwana da yunwarsa gashi
yanzu kuma tasa abincin ya fita daga ransa saboda qorafi.
"Yanzu Yaya ina maka magana shine kaima zaka ture ka tashi ni me aka mayar dani a
gidan nan ne a tilastani nayi girki sannan aqi ci wallahi bazata sabu ba ba kuma
zan iya ba" Amirah ta fada tana shan gabansa.
"Amirah ki rabu dani, ki kuma kama kanki a cikin gidan nan idan ba haka ba zaki ja
nayi miki abinda zaki zo kina dana sani tunda duk ke kika jefani a masifar danake
ciki, matsa mun daga hanya na wuce" ya fada a hankali amma sautin maganar ya sakata
shiga hankalin ta.
Da gani akwai abinda yake damunsa idan kuma ta matsa tasan tabbas zeyi abinda ya
furta din dan haka ta matsa masa tana qunquni qasa qasa shidai ya fice ya barta a
tsaye.
Yana saka qafarsa a waje idonsa suka sakeyin mummunan gani a karo na biyu, Asma'u
ysaye da wani basamuden Beyerabe suna dariya ga jakarta a hannunsa ya riqe mata
yana mata alamar da tayi gaba ta shiga motarsa kamar wani saurayi yazo daukar
budurwarsa zasu fita ita kuma se washe baki takeyi ta shiga motar yana tsaye
mutumin da besan ko waye ba yaja suka wuce Bashir daya dafe motar sa jin jiri yana
neman watsar dashi a gurin.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Ma'una ce nake gani a gaban motar wasu mazan
daban bayan ni Allah me na tuba ka yafe mun kuskuren da nayi ban butulcewa Ni'imar
ka ba wallahi sharrin zuciya da shedan ne suka ingizani" ya fada yana jin ina ma ya
samu hawaye ya zubo masa ko ya samu sauqin radadin da zuciyarsa takeyi masa daga
jiya zuwa yau, yana tsaye har besan sanda yara suka fito daga gidanta