Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   72 / 80

213K to 216K   out of 238.5K words

halinsa nada.

Message na turawa Yusuf akan idan ya kunna wayarsa ya kirani dan Allah da gaggawa
ina so muyi magana ina turawa kuwa wayar ta mutu babu chaji dan jiya damuwa bata
barni na jonata da daddare ba se yanzu da ta mutu na jona na sake kwanciya dan gaba
daya jikina da zuciyata babu dadi.

Haka na wuni da taraddadin abinda zeje ya dawo, ban kuma bi takan wayata ba, daman
kiran Yusuf kadai nake tsammani me muhimmanci tunda naga kuma har gurin La'asar be
kira ba nasan qila suna Chamber ne tunda yau ranar aiki ce zuwa dare dai duk tsiya
nasan ze ga saqona kuma ze kira, dole nasan yanda zanyi na dakatar da maganar nan,
ko bazan koma gidan Bashir ba to sedai na haqura da Aure dan ban hango cewar zan
iya tafiya nabar Yayana a hannun Bashir da Amirah ba.

BASHIR A DAREN JIYA
Cikin wani irin yanayi ya fita daga gidan Ma'u ikon Allah ne kawai ya qarasa dashi
dakinsa ya fada kan gado dafe da kansa da yake barazanar fashewa, yana jiyo muryar
Addah da take tambayarsa lafiya amma be kulata ba ya wuce.

"Ya Allah, ta yaya Ma'u zata auri wani bayan ni? Ta yaya haka zata faru?" Abinda
yake maimaitawa kenan yana riqe da kansa da yake juya masa, wayar dake cikin Aljihu
ce ta dauki qara, a fusace ya cirota.

Amirah ce, se a sannan ya tuna dazu da Yamma Samuel ya kaita Awo kuma haryanzu bata
dawo ba toh kiran me take masa? Qarshe baze wuce qorafi ba ko kuma tana buqatar
kudi kawai seya kashe kiran ya hefa wayar kan gado ya kwanta tareda riqe kansa yana
maimaita Innalillahi a ransa.

Bugun qofar sa da ake kamar za'a ballata ne yasaka shi tashi a hasale, idan kuwa
daya daga cikin yaran nan ne babu abinda ze hana jikin yaro gaya masa basu san
halin da yake ciki ba zasu zo su takura masa da bugu me zeyi musu.

Saurin Ja da baya Addah tayi ganin yanda ya bude qofar kamar ze make ko waye a
wajen, kafin yayi magana ta miqa masa wayar ta tana cewa

"Ungo, Amirah ce daga Asibiti ni bangane kan maganar ma da take yi ba gashi dai
kaji da kanka".

Hararta yayi kamar baze karba ba dan baya san qarin wata damuwa akan wadda yake
ciki amma se dai ya miqa mata hannu, idan dai kuwa rainin hankalinta ne tabbas
akanta yau ze sauke duk tarin bacin ransa.

Cikin muryar Kuka Amiran take cewa daga cikin wayar
"Yaya ina ta kiranka baka dauka ba qarshe ma ka kashe wayar"

"Malama bana son sakarci da rashin hankali ko ni yaron ki ne da dole idan kika
kirani sena amsa? Idan baki da abin fada dallah ki kashe waya kinsa anzo ana bugawa
mutum qofa kamar wanda ake bi bashi" yayi maganar a hasale yana hararar Addah data
saki baki tana kallonsa dan a fuskarsa kadai ta karanci akwai matsala.

"Yaya kazo Asibiti akwai matsala, likita yace wai cire cikin nan za'ayi ni ban gane
abinda suke nufi ba dan Allah kazo" Amirah ta sake fada cikin kuka.

Tsaki yaja me qarfi yace
"Toh su cire mana ni ina ruwana, badai bazaki kiyayi shaye shayen magunguna
barkatai ba ai baki gaji da cin wahala ba, Allah ya bada sa'a" ko a jikinsa ya
kashe wayar ya cillawa Addah abarya ya juya daki.

Duk abinda ya sameta ai su suka ja, yana ankare dasu kullum basu da aiki se jiqe
jiqen magunguna tayita dirka harda wanka da hayaqi yi take shiyasa ya dena cin
komai a gidan dan besan me suka zuba ba maganace kawai beyi musu ba tunda ai koma
menene jikinta ne ze gaya mata bana wani ba.

Yana shiga dakin wayarsa ta sakeyin qara, a fusace ya dakko ze kasheta gaba daya se
yaga Likitan da Amirah take gani ne dan haka ya daga.

A taqaice suka gaisa likitan yace masa yazo Asibiti saboda akwai matsala babba,
bashida zabi tunda yanzu daga bakin likitane haka ya dauki muqullin mota ya fito
dakyar yake daga qafarsa saboda ciwon da kansa yakeyi ga jiri yana gani.

Sanda ya isa Asibitin sosai ciwon kansa ya qaru saboda abinda ya tarar, Jaririn da
yake cikin Amirah ya mutu a yanda sukayi hasashe ma kusan kwanaki uku kenan yanzu
dan tsahon lokacin datace ta dena jin motsi kenan samma saboda tsabar shirme da
rashin sanin ciwon kai irin nata ta zauna wai se ranar awonta ta zagayo sannan
zataje Asibiti tayi qorafi.

Tagumi kawai yayi yana kallon Likitan da yake zabga masa masifa kamar ze dake shi.
"Wane irin shirme ne haka Engineer kamar wadanda baku da ilimi? Mace da ciki wata
bakwai ace kiyi kwana uku bakiji motsinsa ba kuma ki share guri kiyi zamanki a gida
ba tate da tunin komai ba?

Tun farko me yasa ma da ta fara zuwa Awo tayi mana qarya?
Ta gaya mana Haihuwarta daya shine wanda akayi mata Cs babyn ta mutu daga baya se
yanzu ne zata zo tana wannan shine karo na uku banda Bari daya da tayi wace irin
yarinya kake zaune da ita da bata dauki lafiyarta da muhimmanci ba.

Tun farko da mun sani zamuyi bincike mu gano matsalar yanzu kuwa lokaci ya qure dan
Babyn ma ya rigada ya mutu a cikin ta yanzu za'ayi inducing nata ne muna fata ta
iya haihuwa da kanta tunda babu wata matsala amma ko dan gaba dole ku kiyaye.

Da akwai abinda muke kira da Rhesus factor, wani protein ne ake samun sa wajen
kwayar jini (red blood cells) wadanda suke dashi nasu yana zama Positive + yayinda
wadanda basu dashi yake Negative -.
Idan ya kasance mace me Rh + tana dauke da cikin Jariri da yake Rh + to babu
matsala zata haife shi lafiya.

Amma a duk sanda ya zamana cewa an samu banbancin wannan Rh factortsakanin uwa da
jaririn da yake cikinta ma'ana uwa ta zamana cewa bata da wannan protein Rh -
jaririn cikin ta ya zama Rh + a nan ana samun matsala saboda idan kwayoyin halittar
su suka cudanya suna daukar na jaririn kamar abokanan gaba dan haka zasu saki
makaman da zasu yaqeshi wannan yana janyo rasa jaririn da ake dauke dashi idan
jininsu ya hadu.

Dan haka a duk sanda mace da take bata da wannan protein a cikin jininta (Rh
negative mother) ta samu ciki idan aka tabbatar da hakan da akwai allura da ake yi
masu ta Immune globulin domin kare faruwar hakan toh abinda yake faruwa da matarka
kenan wanda da tun farko mun san labarin matsalarta da munyi qoqari gurin ganin
hana faruwar hakan a gaba amma yanzu lokaci ya qure sedai ayi Addu'a Allah ya kawo
masu Albarka a gaba".
(Kuna iya neman qarin bayani akan Rh factor saboda dau da yawa mata na da wannan
matsalar da take janyo musu mace macen jarirai a ciki ko yayin haihuwa wanda ba
kowanne Asibiti bane suke da kula da kwarewar da zasu binciki hakan, Allah yasa mu
dace ya bamu yaya masu Abarka).

Wannan ake kira goma da Ashirin, Haka Bashir ya samu guri ya zabga tagumi bayan da
duk ya gama cike ciken takaddu tareda biyan kudin da ake da buqata.

Amirah kuwa na can a labour room an saka mata ruwan naquda ana ta gumurzu, se gurin
qarfe uku na dare Allah ya yanke mata dan har sun fara tunanin shigar da ita Tiyata
se kuma ta haihu jaririnta kamar sauran me kama da Bashir jikinsa yayi tibis saboda
zafin ciki, sosai ta ringa kuka su kansu Nurses din sun tausay mata irin wuyar
dataci gashi dama Babu ya rigada ya rasu, ana nunawa Bashir yaron kansa da yake
masa bala'in ciwo ya sara yana miqewa jiri ya kwashe shi daga nan be sake sanin
inda kansa yake ba.

ASMA'U
Har aka kura sallar magriba banji kira ko wani saqo ya shigo wayata ba, ina idar da
sallah na qarasa jikin soket din dana saka chajinda mamamkin meya faru yau gaba
daya ace babu wanda ya kirani? Ai ko daga Office nasan baza'a rasa masu kirana ba
dukda na tura da saqon cewar bani da lafiya.
Tsaki naja tare da zama ganin ashe duk wannan abun wai ban ma kunna soket din ba,
kunnawa nayi nan da nan wayar ta dauka, na tashi na cire hijabin jikina daidai nan
aka qwanqwasa qofa na bada izinin shigowa kafin na koma gefen gadon na zauna.

Aliyu ne kansa a qasa ya shigo da sallama na amsa masa ciki ciki ina kallonsa nan
da nan raina ya fara baci dana tuno irin kukan da suka Zo suka ringa yi mun
shekaran jiya hankalina ya tashi ashe duk shiri ne sukayi da ubansu.

"Mami dan Allah kiyi haquri wallahi badan Abbi yace mu roqeki mukayi ba dagaske
Mami muna so ki dawo gidanmu saboda"

"Rufe mun baki Aliyu, ni zaka rainawa hankali ka hada baki da ubanku kuzo ni ku
daga mun hankali ko? Daman abinda kuka shirya kenan kuzo ku yaudareni na koma gidan
ku yaci gaba da wulaqantani yana cin mutuncina ko?" Na fada cikin bacin rai. Seya
rarrafo ya kama qafata fuskar sa dauke da hawaye yace

"Wallahi Mami ba haka bane, dagaske Abbi yayi nadama kuma shiya roqeni akan mu
taimaka masa ki koma gidan mu bansan me yasa yayi abinda yayi jiya ba Mami. Ni
kaina raina ya baci banji dadin abinda ya faru ba kuma yanzu na yarda Mami duk
hukuncin da kika dauka akan sa kinyi daidai na fahimci Abbi nada wani dalili nasa
da yake so ki koma gidansa ba wai dan ya chanza daga halinsa nada ze dena bata miki
rai ba.

Kiyi haquri dan Allah karkiyi fushi dani bansan abinda ze kumayi kenan ba da ban
yarda na shiga maganar ku ba".

Shiru nayi naqi kulashi, ya ringa magiyar sa yana hawaye seda na mula kafin na
dauke kwallar da nima suka fara zubo mun ina kallonsa nace

"Aliyu ina son komawa gidan ku saboda ku badan ina son cigaba da zama da Abbin ku
ba kuma na yanke shawarar haka duk kuwa da abinda ya faru jiya saboda idan na barku
bansan wace irin rayuwa zaku fuskanta ba Idan bana nan dukda bana zaton samun wani
chanji na daban a gidan amma na zabi na bar duk wani farin ciki nayi rayuwa daku
dukda tun farko daman bani na zabi barin ku ba shiya rabani da ku amma laifina kuke
gani"

"Mami ban taba ganin laifinki ba saboda tun banida wayon nasan irin zaman haqurin
da kikeyi da Abbi da yan uwansa. Wallahi Mami lokaci da yawa ina ganin idan nine a
matsayin ki bazanyi irin haqurin da kike yi ba kuma kullum ina Addu'a Idan na girma
karna zama irin Abbi.

Amma bazamu so ace iyayen mu basa tare ba koma menene, na zata abinda ya faru zesa
Abbi ya canza, har Alqawari nace yayi mun akan idan kika yarda kika dawo ze saki
Anty Amirah amma shine jiya yazo yayi wannan abun, gashi nan Yanzu shima abin ya
dame shi tun jiya daya fita daga gida ma be dawo ba bamu san a inda ya kwana ba"

"Aliyu koda wasa karka kuskura naji maganar banza ta shiga tsakaninka da Amirah
balantana har kayi sanadin da auranta ze mutu, ina ruwanka da ita duk abinda ya
faru meye nata a ciki da har zakace se an saketa idan zan dawo?"

"Mami wallahi duk abinda a yake faruwa itace, ko sanda Abbi ya sake ki ita ta
zugashi, ranar muna hanya ya kaimu makaranta sukayi waya ita taringa fada masa
maganganu shine ya dawo ya sake ki" ya fada kamar zeyi kuma

"Karka sake fadar haka kuma babu ruwan Amirah dan bata isa ta saka shi ko ta hana
shi yin abinda yayi niyya ba dan haka karkace zaka tsaneta ko ka cusawa yan uwanka
tsanarta saboda kuna tunanin ita ta fitar dani daga gidan ku.

Rabuwar mu daga Allah ne, idan ya qaddara zan dawo gidan ku zan dawo idan kuma bani
sauran rabon zama a tsakanin mu haka zamu haqura. Abinda nake so dakai Aliyu kaine
babba duk abinda kayi dakai zasuyi koyi ina so ka zama babban kwarai ka yi abinda
qannenka zasu gane na kirki suyi koyi da kai.

Bana so ka dena wannan rashin kunyar da kakeyiwa mutanen da suke zuwa gurina ba
irin tarbiyyar da nayi muku ba kenan, ka kuma kula da qannenka. Bana so naji wani
abu akanka dan idan sauran sukayi suma nasan laifinka ne kaika saka su ko kuma kana
gani baka tsawatar muku ba.

Daga yau gaba daya zaku koma gidan ku da zama cin abinci da komai acan zaku ringa
yi bance karku zo nan ba amma maganar kwana ko yin wani abu na soke gara ku koma ku
koyi rayuwa a gidan ku dan be zama lallai naci gaba da zama tare da ku ba.

Kuyi haquri haka Allah ya shirya mana idan muna da rabon ci gaba da zama tare zamu
dawo wata rana" na qarasa ina daga kaina sama saboda jin wasu hawaye suna neman
zubomun kamar yanda shima Aliyun yake kuka.

"In sha Allahu Mami zanyi duk abinda kika ce, kuma na yarda Mami duk zabin da kika
dauka kiyi, ko auri Uncle Yusuf yana sonki kuma shi ba irin Abbi bane kuma daman ko
baki fada ba ina so na gaya miki zamu koma can gidan gaba daya saboda ko jiya ina
jin su suna cewa sun koreki muma a hankali dukka se mun bar gidan Anty Amirah da
yaran da zata haifa kadai ne zasu zauna a gidan dan haka zamu koma amma Banda
Farida Mami kinga ita kadai ce ba tare zamu ringa kwana ba, gara ta zauna a nan
babu wanda ze ringa kula da ita".

Ajiyar zuciya nayi na kama hannunsa ya dawo kusada ni tareda rungume ni ina shafa
kansa nace
"Karka sake cewa zakayi abu saboda wani kuma ni ba korata sukayi ba zaman da Allah
ya rubuta tsakanin mune lokacinsa ya qare bawai yin wani mutum bane sannan basu isa
suyi muku komai ba se abinda Allah ya tsara,

Gida kuma ai gidan ubanku ne duk inda kukaje kuka dawo baku da inda yafi shi Dan
haka ku kwantar da hankalin ku babu komai in sha Allah"
Nasiha naci gaba dayi masa cikin laluma har aka kira salar isha'i kafin ya tashi ya
fita, wayata na jawo na kunna kafin na miqe na shiga bayi na kuskure bakina tunda
ina da Alwala na fito.

Har na zura hijabi zan tada sallah wayat tayi qara sena koma na dauka dan kiran
Yusuf nake tsammani, bana so a samu wani akasi gara muyi magana dashi a dakatar da
duk wasu shirye shirye tunda ni bazan iya tunkarar Baffa Isiya kai tsaye ba amma
shi Idan yace a daga lokaci ai dole a daga.

Tsaki nayi ganin Alawiyya ce take kira, nasan ma idan na daga raina ne ze baci, se
kawai na ajiye na tayar da sallata, ko kafin na idar an kira wayar yafi sau
Ashirin, ko kyakykyawar Addu'a ban iyayi ba na Shafa saboda jin yanda kira yake
sake shigowa qirjina na dukan uku uku na janyo wayar ina mamakin meya faru haka?
Ban sake shiga rudani ba seda naga duk kiraye kirayen na yan gidan mu ne harda Anty
Suhaima itace ta kira qarshe ma.

Ina qoqarin bin kiran na jiyo muryar Anty daga palour tana tambayar yara ina ina
matar datace ko ta qofar gidan ta nabi seta mun rashin mutunci ita ce kuma ta
biyoni to me yake faru ba?

Wayar hannuna ce ta fadi gabana ya yanke ya fadi dana tuna dazu fa naji Aliyu yana
cewa wai Bashir be kwana a gida ba har yanzu be dawo ba kuma karfa Ace Bashir ne ya
mutu shiyasa ake ta mun wannan kiran.

Jikina na rawa na tsugunna na dakko wayar tsabar yanda na rikice ma kasa dannata
nayi daidai nan kira ya sake shigowa lokaci daya Anty ta turo qofar dakin ta
shigo. A tsorace na kalleta na kalli wayar hannuna, Alawiyya ce dai take sake kira
na sake kallon Anty a maimakon naga tashin hankalin da nayi zato a fuskarta sema
wani murmushi da annuri na gani ta nufoni da sauri ta rungumeni daidai sanda itama
Alawiyya dana daga wayarta ta rangada mun wata uwar guda da ta sakani saurin janye
wayar daga kunnena saboda yanda abin yazo mun babu shiri.

Kamar hadin baki sukace
"Alqawarin Allah ya cika, yau Asma'u ta zama matar Yusuf mutu ka raba in sha
Allahu".

Yanda kasan wadda aka zarewa laka haka nayi baya na zauna dabas akan gado ina
kallon Anty dake kyakyata dariyarta ga muryar Alawiyya ma daga cikin wayar tana ci
gabada zayyo nata zancan nidai jinsu kawai nake amma kamar a mafarki, Aure fa naji
suna cewa kuma nida Yusuf anya sunsan me suke fada kuwa? Kodai labarin zuwa
tambayar auran sukaji basu fahimta daidai ba.

"Amarya fa ta tafi hutun rabin lokaci inaga mu zamuci tukuicin nan dan da alama
bata san da labarin ba" naji Anty tana fada bayan data saka wayata a kunnenta, gani
nayi ta cire ta saka a speaker naji Alawa tana cewa

"Kin tuna me kika ce mun jiya, idan auranki da Yusuf Alkahiri ne Allah yasa idan
sunje yau a daura a take to kin gani idan ma gatsali kika yiwa Allah kinga ya gwada
miki ikonsa babu abinda ya gagare shi dan haka ko kisha ruwan sanyi kiyi murna ko
ki nemi fiya fiya duk tsiya in kin mutu ma haka za'a ce Ma'u Amaryar Yusuf ta mutu
se naga qarshen qiyayya kuma" ta kwashe da dariyar mugunta.

"Kinga yar uwa barta kinji aini wannan abu yamun dadi Allah dai ya sakawa da duk
wanda ya daura wannan aure da gidan Aljanna ya raba shi da sharrin mahassada da yan
sa'ido dan ya gama mun komai a rayuwa abu daya ya rage mun yanzu na tafi gidan
Bashir na isar masa da labarin Farin ciki" Anty ta fada ina jin yanda suka kwashe
da wata muguwar dariya su biyun kafin ta kashe wayar ta ajiye tana cewa

"Ma'u Amarya Ma'u Amarya ai yau tukuicin Yallabai daban yake na wannan labari aradu
sena kaishi duniyar dadi na dawo dashi ke yau ko sunan sa baze iya tunawa ba, bari
naje kar a rigani fadawa Bashir labarin nan dan ina fitowa naga shigowar motar sa
qila yanzu ya taso daga aiki" ta fice abinta tana dariya ko lura da yanda nayi
suman zaune ma batayi ba ta qara gaba abinta.

ITA QADDARAR AURE, MUTUWA DA HAIHUWA ABU NE DA YA KE KASANCEWA A LOKACIN DA ALLAH
YA NUFA KO ANA SO KO BA'A SO.

ALQAWARIN ALLAH YA CIKA A LOKACIN DA KOWA BEYI ZATO BA MA'U TA ZAMA MATAR YUSUF
TABBAS HAQURI YANA TADDA RABO DUK DAREN DADEWA

HAKA ZALIKA SAU TARI ABINDA MUKE SO YAKAN ZAMO BA ALKAHIRI BANE A RAYUWAR MU KO A
IYA NAN NA AJIYE ALQALAMINA NA TABBATAR DA SAQO YA ISA INDA AKE SO AMMA MUJE ZUWA
SAURA QIRIS

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 62

YUSUF

Baze iya misalta irin murna da farincikin daya tsinci kansa a ciki ba jin abinda
Ma'u ta fada. A sukawane ya fice daga gidan yana shiga motarsa Driver yaja suka
tafi,

Tun kafin su

72 / 80