Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   69 / 80

204K to 207K   out of 238.5K words

ita Mamai bazata taba samun farin ciki a gidan mu indai kana so
ta dawo to ka sake ta kawai gidan mu ya koma yanda yake kafin ta shigo rayuwar mu".

Kasaqe Bashir yayi yana kallon Aliyu da jin abinda yake fada, ya saki Amirah fa me
yasa se wannan sharadin ze saka na shawo masa kan Ma'u?
Shida yake qoqarin gyara kuskure shine yake so ya sake aikata wani ita kuma idan ya
sakeya yanzu kuma wata jarabawar ta sake afko masa fa gaskiya Aliyu yayi haquri
banda wannan ya yarda dai ze raba musu gida yanda suke da har na can Gomben ma idan
Amiran ta koma ze raba musu kowa gidanta daban.

Hannun Aliyun ya kama yana sake marairaicew kamar wani kalar tausayi yace
"Haba Aliyu so kake na sake yin wani sakin kenan bayan nayiwa kaina alqawarin ko
dukana mace zatayi bazan sake sakinta ba. Baka san yanda nake ji akan rabuwata da
Maminku ba, Baba fushi yake dani ko magana baya mun yanzu haka su Amiru duk sun
dena kulani saboda abinda ya faru so kake na sake maimaitawa itama Dada da sauran
yan uwana su tsane ni?"

"Ai daman Baba dasu Uncle Amir ne kawai suke son Mami ni ina ruwana idan sunji
haushi kawai in dai kana so Mami ta dawo to kayi alqawari zaka saketa koma zaka
dawo da itama daga baya ni babu ruwana amma yanda aka saki Mamanmu saboda ita itama
taji irin yanda mukaji" Aliyun ya fada kansa tsaye babu wata damuwa a tatttare
dashi.

Bashir kuwa ido ya saka masa yana mamakin a ina ya samo wannan tunanin ko kuwa Ma'u
ce ta fada masa hakan ita take so a saki Amirah sannan ta dawo. Kansa ne ya dauki
dumi, yanzu idan da gaske ya amince zata dawo din ko kuwa kar ta sake rufta shi se
daga baya yayi biyu babu ko daya.

Numfashi ya sauke yana kallon Aliyu da yayi kicin kicin yace

"Na yarda amma se randa aka mayar da aurena da Mamin ku sannan zan cika maka
alqawarin"

"Ka dai san hukuncin cika alqawari" Aliyu ya fada yana kallonsa.

Kai shi abun ma ya zarce mamaki wai yau shi Aliyu ya titsiye haka yake bashi
umarni, ya ya iya? Haka ya rausayar da kai yace

"Na sani kaima se kayi qoqari ka cika naka alqawarin" ya fadi haka bawai dan har
zuciyarsa ze aikata hakan ba. Buqatar sa kawai Ma'u ta dawo idan ya samu bega kuma
wanda ya isa ya sake raba shi da ita ba ballantana wani alqawarin Aliyu can.

Haka ya shiga gida da yaqinin cin nasarar yaqin ta wannan sigar daya samu, yasan
tana da rauni akan yayanta in Allah ya yarda wannan raunin nata shi ze kaishi ga
nasara.

ASMA'U

Ganin da nayi har ana saura kwana uku a koma makaranta Bashir be yi magana ba yasa
na sake tuntubarsa. Ta whatsapp call din ya kirani saboda ni nake so muyi magana
dan haka na daga muka gaisa yake cemun

"Kin jini shiru ko wallahi Ma'u bani da kudi ne, abinda na saka rai dashi ban samu
ba ga shi da saura kafin mu samu salary ina ta dai fafutukar yanda zan samu daga
yau zuwa Gobe in sha Allah zan saka miki"

"Toh Allah ya rufa asiri, ayi qoqari dai kasan su bazasu karbe su ba idan ba'a biya
ba. Ga siyan su takalmi ma da jaka da dan abinda ba'a rasa ba tunda sabon session
ne duk suna da buqatar a canza".
Allah sarki rayuwa shi baya zaton ma ya taba bada kudin wasu jaka da takalmi dan
yawanci idan suna Gombe a shagonta suke zuwa a dakko tunda duk tana siyarwa harda
su Lunch box din da suka dawo nan kuma sedai ya gansu da abinsu, kudin Uniform da
sport wear kadai yasan in suna buqata take gaya masa baya ga wannan sedai yaga tayi
musu.

"Shikenan, yanzu zan tura miki da 1M a fara rage kudin kona mutum uku ne zuwa jibin
se na ciko" ya fada qasan ransa yana so ya roqeta da yasan bazata rasa kudi ba ta
ranta masa amma yana tsoron amsar da zata bashi tunda yanzu kam Ma'un ba ta da bace

"Shikenan toh ka tura amma fa ka tabbata Jibin ka ciko dan ni inaga ma zanje a
chanza lambar nan gaskiya can su ringa tura maka duk abinda ya kamata" na fada
kafin na kashe wayar.

Wani abu naji kamar tausayinsa ya dan kamani, nasan Bashir da hidimar yayansa indai
an gaya masa yanayi ballantana kuma harkar makaranta tunda har ya ce bashi da kudi
toh tabbas bashi dasu din.

Ba'afi minti biyar ba sega alert din kuwa ya shigo, wayar na ajiye na janyo durowar
gefen gado na sega kudin da Ambassador ya bamu ranar nan tunda na watsa su ban qara
bi ta kansu bama dan na manta shi kansa da yace na kira shi ban kira din ba.

A jakata na zuba su da niyar gobe idan na fita zan biya banki se na cire wanda ya
turamun na hada da wadannan na biya musu kudin makarantar kawai daman ai kudin
Aliyu ne sa ci tare da qannensa.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 60



Washe gari Juma'a kuwa da wuri na dauki excuse na kama hanyar banki, seda na fara
Zuwa Access bank na cire kudin daga akawun dina na hada da wadancan kafin na wuce
Zenith inda ake saka kudin makarantar bayan da nayi printing teller da suka tura
mun.

Ina shiga bankin Yusuf ya kirani.
"Ina zuwa dan Allah zan kiraka ina banki ne" na fada bayan da muka gaisa.

"Hajjaju bari nima na turo da akawun a sakamun wani abu mana" ya fada cikin wasa

"Toh shikenan, seka turo ina jira" na bashi amsa ina shirin kashewa ya tareni da
cewa
"Har transaction din miliyan nawa zakiyi da se kinje banki?"

"Kudin makarantar yara ne fa zan saka kasan basa karbar transfer dole se cash
deposit za'ayi"

"Ke kike zuwa biyan kudin makarantar yaran shi Baban su aikin me yakeyi da baze je
da kansa ba ko kema irin matan da suka dauke dawainiyar yara da bata zamar musu
dole ba sukeyi ce" ya fadda cikin wani yanayi kamar na bacin rai.

Murmushi nayi nace masa
"To meye a cikin biyan school fees? Ni har PTA ma ni nake zuwa musu kai komai ma na
makarantar su lamba tace akai"

"To sannu kinyi abin kirki a tafa miki" ya fada kafin yaci gaba da cewa

"Na rasa me mata kuka dauki kanku yanzu wallahi, gani kuke kamar gwaninta ce ko
iyawa ke uwa ki dauki haqqinki ki dauki na uba duk ki hada ki ringayi in ba haka ba
ina ruwanki da harkar makarantar yara?

Iya abinda ya shafe ki shirin su na tafiya makaranta kula da tsaftar su da abinci
shikenan se bitar karatu idan sun dawo gida ko taya Home work ni banyarda haqqin
uwa bane tayi wa yara shi uban aikin me yakeyi idan ya dawo da daddare da baze tara
su yaga abinda suke koyo ba se kece zakiyi??

Abin nan yana bala'in bani haushi, Idan ka fita da safe motocin kai yara makaranta
in ka hadu da goma bakwai matane a ciki biyu daga ciki shine zakaga Driver aka
daukar wa yaran yake kai su se daya ne zaka samu uban da kansa bayan dai qarshe
mutum yace yana sauri ze tafi aiki duk sauri dai qarfe bakwai ma'aikaci yake fita
kuma suma makarantu bakwai ake budesu me ze rage ka idan ka tsaya ka ajiye yayanka
kafin ka wuce naka gurin aiki

Wannan uar dawianiyar da iyaye maza muke kasa jurewa muyiwa yaran mu fa shine
abubuwan da har girman su bazasu manta ba kuma a irin lokacin ne fa kadai kake samu
da zaka tattauna da yaran kasan matsalolinsu amma ina kai agogo sarkij aiki ka fice
ita mata ga aikin gida ta shirya yaran ta rufe gida ta kaisu ta dawo ta dora daga
inda ta tsaya in an tashi ta koma kune zuwa PTA kuna wannan kune wancan duk wa ya
aike ku ne

Kin ganni duk irin Busy da nake yayan Yaya Umar (Yayansa ne daya rasu) in har
kikaga banje na dakko su daga makaranta idan akayi hutu ba to bana qasar ne amma ko
a ina nake se na koma na dakko su ko na kaisu tunda boarding sukeyi haka Visiting
har personal Visiting indai na samu dama ina zuwar musu saboda ni ne matsayin uban
su a yanzu ba kuma naso suga wani abu da akeyiwa wanda ubansa yake raye su sun rasa
suyi kukan maraici saboda Babansu babu abinda beyi mun a rayuwa ba duk matakin da
na kai da bazarsa nake rawa Dan haka tun wuri ki tashi malama ki San Abinda yake
haqqinki da wanda ba naki ba

Ki zauna a inda nake bari na turo yaro yaje ya saka kudin karki kuskura ki shiga
bankin nan kuma wannan ya zama na qarshe da zaki sake zuwa biya musu wani kudin
makaranta idan baze je da kansa ba a barshi" ya qarasa maganar ta sigar umarni.

Haka kuma na zauna a motar bayan ya kashe ya sake kirana mita ce dai yake tayi akan
mata mun fiya zaqewa, se kuma miji ya miqe qafa ya saba da kina masa daga baya kizo
kina qorafin yaqi yayi bayan tun farko baki sabar masa da yayi ba.
"Wai dan ma baka san ya na gudanar da nawa zaman auran ba kenan da ina ga bulala
zaka sak kayimun shege duka irin wannan masifa da kake daga zuwa biyan kudin
makaranta" na raya a raina.
Ba'a jima ba sega kira ya shigo mun da lambar da ban sani ba, uzuri na bawa Yusuf
na daga mutumin yake cemun shine wanda ze karbi kudi ina ina na kwatanta masa ina
da tsaya se gashi ya qaraso da alama ma'aikacin bankin ne dan ga ID card dinsa nan
a wuya.

Seda muka gaisa na dakko Teller na bashi ina zaro kudade daga jaka ya juya ya tafi
nayi saurin dakatar dahsi da cewa ga kudin se cemun yayi wai Teller kawai aka ce ya
karba yai tafiyarsa. Ko minti goma ba'ayi ba se gashi ya dawo da receipt na karba
nayi masa godiya na zaro dala dari biyu na bashiya dakyar ya karba mukayi sallama
na kama hanyar makarantar kai tsaye naje na chanza Teller,

kafin na isa ya ringa kirana yana jaddadamun da naje a cire numberta a mayar data
Bashir ya kashe wayar sa yaqi bani damar da zan masa maganar biyan kudin ma da yayi
oh Yusuf kenan shi ma kowa ya aike shi yin abinda ba haqqqinsa ba oho.

Text na rubuta na tura masa na godiya da irin hidimar da yakeyi da yarana kafin na
rufe da cewar na tanadar masa da kyakykyawan labari ina jiran zuwan sa Lagos

"Ki saka ran gani na a ko da yaushe Allah yasa abinda na dade ina muradin jine daga
bakinki Asmy" ya dawo mun da amsa. Murmushi nayi dan dagaske ji nake ya kamata na
amsawa Yusuf na bawa kaina dama ta gwada sabuwar rayuwa tareda kyakykyawan yaqinin
samun chanjin Alkahiri.

A daren ranar ina kwance a dakina saboda kaina da na danji yana mun ciwo aka
kwankwasa qofa, Aliyu da sauran yaran gaba daya yana gaba suna binsa a baya suka
shigo suka jere mun a gaba na dago ina cewa

"Wane kalar iskanci ne wannan zaku wani tsaya mun aka kamar masu Asambili idan ma
wani abun kuke so mutum daya baze wakikce ku ba wai bana hana ku yimun wannan
gangamin bane?"

Shiru suka mun, na kunna fitila se a sannanna lura da yanayin fuskokinsu gaba daya
babu walwala sun sunkuyar da kawunan su qasa. Wata faduwar gaba naji nayi saurin
tashi zaune ina cewa

Babu wanda ya amsa ba kuma su dago kai suka kalleni ba,

"Ku fice mun bana son wulaqanci ana magana kunyi shiru ku fita ku bani guri" na
fada cikin tsawa dukda qasan raina ina tsoron abinda ya saka su yo wannan gangamin
haka, qafata na sauke qasa da niyyar fafarar su tunda sunqi magana seji nayi kamar
hadin baki sun rushe gaba dayan su da kuka yanbiyu suka yo kaina da sauri suka
runguneni.

"Meye haka ku fada mun dan Allah wani ne ya mutu?" Na fada a gigice ganin irin
kukan da suke yi harda Aliyu da bazan iya tuna rabon da naga kukansa ba.
Gaba daya na rikice jikina har rawa ya dauka a zatona wani abunne ya faru, Farida
na janyo na girgizata ina cewa

"Zanci ubanku wallahi kuyi mun magana menene waye ya mutu a nan ne ko a Gombe?"

Aliyu ne ya zube guiwoyinsa qasa a gabana ya kama qafata yana cewa

"Mami da girman Allah ki dawo gidan mu. Wallahi Mami Abbi yayi nadama ki dawo indai
kina so rayuwar mu ta inganta karki tafi ki barmu da wannan matar, bana bacci Mami
tunda kika bar gidan mu kullum cikin damuwa muke, Abbi baya hayyacinsa su kansu su
Abdallah Mami saboda basu gama gane abinda yake faruwa bane wallahi da ba'a kusa
damu kike ba da yanzu bansan yaya rayuwar mu zata zama ba saboda babu wanda yake
kula damu shi kansa Abbi yanzu neman wanda ze sauta shi ya ringa kula dashi yake
kina kallo se ayi sati ni kadai nake kwana acan gidan kuma be damu da ya san Ina
sauran suke ba, ba'a bamu abinci acan gidan to Mami idan bakya nan waye ze bamu?
ina zamuje waye ze nemo mu idan be gammu ba?"

Kamar wadda aka watsawa ruwan sanyi haka naji nayi shiru ina jinsa su kuma suna ci
gaba da kuka tareda fadar maganganu dan Allah na dawo gidan su.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi jin ba mutuwa akayi ba, amma zancen rayuwar su da
sukayi ya tabani hasaso yanda suke garari tsakanin gidajen nayi a fili na furta
"hasbunallahu wani'imal wakeel" Dagaske da bana tare dasu yaya rayuwar su zata
kasance? Ina zasu je su samu gatan da uwa take bawa danta? Waye ze kulamun da
tarbiyyar su? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ni Asma'u yanzu yaya zanyi duk me
yasa banyi wannan tunaninba nake shirin yanke wa kaina shawara??

Gaba daya kukan nasu ya dagulamun lissafi nama rasa abinda zance musu, dakyar na
iya saka hannu ina bubbuga bayan yan biyu nace

"Ya isa ku dena kuka akan wannan maganar ce zaka tara mun yara saboda wulaqanci ka
saka su kuka kai bazaka iya zuwa kai kadai ka same ni ba se kun tayar mun da
hankali?"

"Mami bani na gayyato su ba ki tambaye su gasu nan duk tare mukayi magana kowa yana
cikin damuwa mun kasa zuwa mu tunkareki shi yasa nace mu taho yanzu ki tausaya mana
Mami mu koma irin rayuwar da muka tashi a cikinta" Gwani na gwanyen ya sake fada.

Seda nayi dagaske kafin sukayi shiru na tattara su suka fita suna sake maimaitamun
na taimake su na tallafi rayuwarsu na koma gidan Babansu, wai harda yan biyu kai
wannan abun ma yafi kama da wasan kwaikwayo tabbas shiri ne Kuma Bashir ne ya
shirya shi. Shiyasa dazu kenan gaba daya suka fita ashe gurinsa sukaje ya yiwo musu
huduba ta nan ya zagayo kenan tunda ya kasa yi da kansa.

Duk yanda naso na share maganar daga zuciyata na aiwatar da abinda nayi niyya tun
farko kasawa nayi da gaske ina tunanin makomar rayuwarsu. Yanzu muna tare bani da
tabbacin idan nayi aure Yusuf ze barni naci gana da zama a nan dukda ya ce ze bari
kuma nasan ko za'ayi yaya Bashir baze bani su ba kai ni kaina bazan kai yayana
Agolanci wani guri ba bayan ubansu nada yanda ze riqe au to yanzu yaya zanyi??

Abu guda uku ne, kodai na haqura na koma gidan Bashir nayi zaman Yayana, ko kuma na
auri Yusuf na zubar dasu ko kuma na hauqra da duk biyun na rungume su mu zaunaba
tareda na sake wani auran ba wanda na tabbatar bame yuwu bane dan baza'a barni nayi
hakan ba to dole cikin zabi biyun farko kuwa na dauki daya, wannene mafita?
Komawata gidan Bashir bayan duk abinda ya faru ko kuwa sabuwar rayuwar da nake
yaqinin samun chanji a cikinta?? Mene kuma makomar Yarana??

Saboda tunani har wani mugun ciwo kaina ya dauka, dare yayi qarfe sha biyu harta
gota amma haka na danna kiran lambar Goggo ba tareda tunanin tsufanta ba karna
tayar mata da hankali nima ina da buqatar magana da uwata ne in nemi shawararta
tunda tana sona tana kuma jin irin abinda nake ji yanzu akan yarana baznaso na
yanke shawarar da zata tauye rayuwarsu a gaba ba.

"Asma'u lafiya? Meya faru kike kiran waya a daren nan" ta fada bayan data daga
kamar me jiran na kirata.

"Kiyi haquri Goggo na tasheki daga bacci" na fada a sanyaye, se tace mun

"Ba bacci nake ba, kin ganni ina ta salloli ne da addu'a wane bacci zanyi yanzu
Asma'u nida nake da buqatu nake da yaya da nake nema musu shiriya kullum a gurin
Allah"

Maganar ta kawai se naji ta sakani kuka dukda bansan kukan na menene ba.
"Goggo dagaske na haqura da Bashir badan na dena sonsa ba sedai kawai hakan shine
maslahar zuciyata bazan taba samun yanda nake so a gurin sa ba zan qare rayuwata
cikin qunci da ciwon rai da baqin ciki shiyasa na zabi haqura dashi amma Goggo yaya
makomar yarana zata kasance idan na auri wani daban na tafi na barsu?

Matarsa ba zata iya riqe min suba bansan yaya tarbiyyarsu zata kasan ce ba musamman
a gari kamar Lagos Goggo dama a Gombe ne akwai wadanda zasu saka ido akan su saboda
su Goggo bazan iya tsallake wa na sake wani aure ba ki bani shawara me ya kamata
nayi?"

Shiru ta mun harna gama magana ina gunsheqara kuka, seda nayi iya yina nayi shiru
kafin tace mun

"To yanzu kira kikayi ki gaya mun zaki koma gidan mijinki ko yaya?"
"Goggo shawarar ki nake nema ban san meya kamata nayi ba" nayi saurin bata amsa. Se
da tayi wani murmushi kafin tace

"To Ma'u ai maganar ki ba tayi kama da ta wadda take neman shawara ba. Cewa kikayi
bazaki iya tafiya kibar yayanki ba to ai seki koma gidan ubansu kawai ki riqe su
daman ba abinda kike so ba kenan duk meye na wani kuka ni kin tayar mun da hankali
abinda befi ki tura mana da saqo a waya ba akan zaki mayar da aure muzo mu taya ki
murna shikenan fa.

Addu'ata kullum Allah yayi miki zabin Alkahiri, idan so nane bazan so ki koma inda
ba'a san darajarki ba tunda har Allah ya fito dake ba kuma wai ke kika nemi sakin
nan ba amma tunda kin zabi ki koma Allah yasa hakan ya zamo miki Alkahiri" ta
qarasa maganar a sanyaye.

Yanda take magana kadai ya isa ya nunamun bata ji dadin abin ba, qarasa hadiye
kukana nayi nace mata

"Goggo ba cewa nayi zan koma gidan Bashir ba wallahi nima na gaji, na yarda bani ce
a gabansa amma Goggo makomar Yarana nake dubawa. Dazu suka zo suka sameni suna kuka
akan nayi haquri na koma gidan su.

Goggo ba'a basu abinci komai na rayuwar su a nan sukeyinsa idan

69 / 80