Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   6 / 80

15K to 18K   out of 238.5K words

ga ta inda zaki ringa
kaiwa uban naki gulma idan na taba kudinsa” ta fada bayan Ruqayyan ta fita daga
kitchen din

Oho bata ma san tanayi ba dakin ta ta nufa a ranta tana ayyana tabbas akwai wata a
qasa dan ita dai tafi shekara Goma rabonda taga Hajia tayi girki da kanta Baba
Zulai ce take yi musu ko kuma ita idan taba gida. Ita zata iya cewa ma idan kaga
Hajia a kitchen to an gama Abinci ne idan harda na Baban zatayi barbade daga baya
ma daya gane yai Allah ya isa yama zo kuma ya dena cin abincin kwatakwata se baya
bayan nan taga ya dawo yana ci.

Ita kuwa Hajia tana sauke tuwo ruwan Tea ta mayar ta saka lipton dinta da kayan
qanshi sannan ta zuba jiqon Wizy, bata matsa ko ina ba seda ta kammala tsaf ta hada
komai ta kai kan Dining sannan tashi ga dakinta tai wanka ta fara jero Qara’in
salloli.
Seda akayi Isha Alhaji ya shigo, kai tsaye part din Amarya ya shiga dan akwai kayan
daya manta da safe da ze tafi kasuwa yana so ya dauka kar gobe ya sake mantawa. da
mamaki ya kalleta dan ya zata ta tafi aiki tunda tace masa Night Duty ne da ita.
tana ganinsa ta miqe

“Yawwa Alhaji dama kai nake jira tun dazu”
“Lafiya Abida baki tafi aikin ba? Jiran me kike mun?” Ya fada yana kallonta. Seta
miqa masa wayarta kawai ba tareda tace komai ba, karba yayi yana duba screen din
sega video Hajia Balaraba tana kici kicin zuge jaka, baya jin me take cewa amma fes
yaga sanda ta ciro leda ta guntsi rubutun ta feshe kofar dakin Amarya ta tafi”
Se ya miqa mata wayar dason jin qarin bayani.

“Wallahi Alhaji yanda ka gani dinnan kasan ka fita ka barni kaina yana ciwo dan
haka sena kwanta dan ban ma samu zuwa Barkar Haula da nace maka zan fita ba, se
bayan La’asar na ma idar da sallah na tashi zan leqa na karbo Kati se naji motsin a
bude qofa, in duba ta window fa shine naga Maman Suhaila na wannan ta tsaya tana
maganganu tareda bude jaka wayata na hannuna ni kuma shine na kunna video saboda
kar a maimaita irin ta wancan karan data zuba magani akace qarya nakeyi yanzu dai
ga Hujja ka gani da idonka, nidai ban fita ba koma na menene kai kadai ka tsallaka
shi se kasan yanda zaayi azo a karya dan bazan yi ta zama a daki ba kona fita a
sabautani a banza”.

Wani irin tuquqin baqin cikine ya rufe Alhaji har huci yakeyi, wato duk Allah ya
isar dayai wa matar nan bata daddara ba kenan? Shin wai se Yaushe Balaraba nutsu
tasan Annabi ya faku ne ita dai duniya ce kawai a gabanta to kuwa Insha Allahu
Allah baze sake bata ikon maidashi halin data jefa rayuwarsa a baya ba shi wallahi
badan kar duniya ta zageshi ace ya saki matar sa auren shekara Arba’in ba da rabuwa
zeyi da ita ya huta amma yanzu babu wand ze dubi abinda ta aikata masa shedai a
dora masa laifi ace Ya wulaqanta Uwargidansa.

Cikin fushin daya gaza boyewa ya fita, mintina kadan ya dawo tareda wani yaro ya
shigo palour ya bar yaron a kofar dakin tareda nuna masa gurin yace ga inda zeyi
fitsarin nan yaro kuwa ya tsula abunsa Alhaji ya fita ya nuna masa famfo ya taro
ruwa suka sheqe a gurin nan da nan ya wuce daman tiles ne. Ciki ya dawo yace da
Abida ta biyo shi yai gaba tana baya se palour Hajia Balaraba.

Tana zaune ta hakimce akan kujera ta sheqa kwalliya ta garari ta kuwa yi kyau sosai
dan Hajia Balaraba akwai kyan jiki da gayu kai bazakace tabawa Hamsin baya ba. Tana
ganin Alhaji ta miqe da fara’a da nufin tarar sa sedai ganin Amarya a bayansa yasa
ta gintse fuska a ranta tana tunanin meya faru kuma dan ita bata ma lura da yanayin
fuskar Alhajin ba.

“Balaraba me kika zuba a qofar dakin Abida?” Ya tambaye ta cikin kaushin murya.
Qirjinta ne ya fara luguden daka zuciyarta kaman zatayi tsalle ta fito saboda
razana, ya akayi ya sani to ko wani ya ganta ne? Ita dai a hasashenta babu kowa a
gidan dan Tunda da zata fita seda ta saka muqulli ta kulle haka data dawo dakanta
ta bude kofar, koma menene bazata bare a gano ta dole tasan yanda zata kare kanta.

Qoqarin daidaita nutsuwarta tayi tana daure fuska tace “Bangane me kake nufi ba
Alhaji wani sharrin kuma aka sake qullomin yau ma? Ni duk yau ma ban fita daga part
dina ba bare har naje qofarta na zuba abu”.

Kallon takaici da tsana yake binta dashi, se ya miqawa Abida hannu tayi saurin miqa
masa wayarta. Video yayi playing ya miqawa Hajia Balaraba dake ta taraddadin me
nene a cikin wayar Abidan, ai seda ta kusa Sakin fitsari a gurin saboda kidima nan
danna zufa ta shiga keto mata.

“Wane La’anannen ne ya dauki wannan video” ta fada bakinta yana rawa tsabar yanda
ta rikice, zata sakw magana ya miqa mata hannu ta bashi wayar yana cewa

“Kici gaba Balaraba sharri dan aikene ki sani duk nisan indai kika aika shi
watarana seya dawo miki, tunda har kin raina Allah ya isar da nayi miki akan in
kika sake yimun wani abu ko wani daga cikin iyalaina shikenan na barki da Allah
kuma matakin qarshe dazan dauka shine wallahi Balaraba idan kika sake zuwa gidan
wani malami kika aikata wani abun sihiri a cikin gidan nan kai na ko kan wani nawa,
na sani ko ban sani ba to ki sani a bakin aurenki”

Cikin tsananin razani ta dago ta kalle shi dan bata taba zaton tsaurin hukuncin ze
kai haka ba, ta bude baki da niyyar neman sassauci yace “Karma kice komai dagaske
nake kuma ba igiya daya ko biyu ba dukka ukun nake nufi idan kuma kika aikata a
bayan idona ba tare da na sani ba muka ci gaba da zaman aure dake wannan kuma na
barki da Allah shi ze bimin haqqin zaman zina da kika sa nayi ba tare da sani na
ba” yana kaiwa nan ya shige dakin sa da yake a part din nata, Abida ma jiki a
sanyaye ta juya ta fita aka bar Balaraba da dora hannu aka tama tasa kuka zatayi ko
ihu?

Wannan shi ake kira da An bata biyar goma bata gyaru ba (Dama ai duk wanda yace
tukunyar wani bazata tafasa ba tabbas tashi ko dumi kuwa ba zatayi ba).


Lagos
Seda Ma’u ta cike satin nan daya raya cif aka sallameta, da safe bayan Bashir da
yara sunzo sun tafi tacewa Dr ya sallameta haka. Da kanta ta karbi Discharging
later ta hada yan kayanta kafim ta kira Uber ta cale gida (tsiyar garin da baka da
dangi kenan).

Koda ta isa gidan bata zauna ba seda ta gyara ko ina tsaf ya dawo mata yanda take
so sannan ta shiga hidimar dora girki kuma, aikin ya jata da yawa dan har bayan
La’asar sannan ta kammala komai ta jere akan Dining kafin ta koma dakinta kuma ta
fada wanka. Tsaf ta shirya cikin wani hadadden cotton lace Army green da akayiwa
dinkin Fitted gown datai bala’in yi mata kyau ta fito mata sauran quruciyarta.
Indai gayune dole a cirewa Ma’u hula wannan ko a zamanin yammatancinta babu kamarta
a kaf qawayenta tana da kyau ta kuma iya daukar wanka ga farin jini Allah ya mata
abinda ya sa ta zama ta daban kenan da sauran.

Daurin nan ta kawo shi gaban goshi bayan ta fake gashinta qasa qasa sannan ta saka
cogenta ta qara feshe jikinta da turaruka ta shiga juyi a gaban mirrow dan ta burge
kanta da kanta ballanta na Kuma Bashir ya ganta tasan duk yanda yake qyashin ya
yaba kwalliyarta yau kam se idanunsa sun fado qasa qilan a garin kallo.

Mint flavored chewing gum ta jefa a bakinta kafin ta fito palour ta samu kujerar
dake facing kofar shigowa ta dora daya kan daya tana girgizasu tana danna waya ba
koyi minti biyar da zama ba ta jiyo tsayuwar motarsu, seta qara gyara zaman ta
dakyau tana sauraron shigowarsu.

Aliyu ne a gaba dauke da Laptop bag din Bashir se school bag dinsa daya goya a baya
se ga sauran a bayansa. Gaba daya suka nufe ta cike da murnar ganinta a gidan,
Aliyu ne yace

“Mami this house can never be complete without you Allah Mami da baki nan ji nake
kamar a kango muke kwana amma yanzu tundaga qofa kawai naji it feels like home
again ashe kece kika dawo ciki”

Dukan wasa ta kai masa tana cewa “Oh Ali yammata kam se sun bani da dadin bakin nan
naka Allah dai ya nuna mun lokacin” se ya rufe fuska wai shi kunya yana cewa “Kai
Mami ki dena kunya nake ji”
Gaba daya suka saka dariya, se a sannan ta daga kanta ta kalli inda Malam Bashir
yaci burki tunda ya shigo, seta qara fadada murmushinta tana cewa

“Aa Baban Ali yane ka tsaya ka shigo ka zauna mana ko ka qara sa ciki”.

Bashir
Numfashinsa ne ya dauke na wani lokaci sanda yai arba da fuskar Ma’u, tayi masa
kyau matuqa gaya da har ya kasa iya cire idanunsa daga kanta. Maganar da tayi ce ta
fargar dashi kamar dama me jiran umarninta kuwa se ya taho, kusa da ita inda Farida
ke zaune ya daga Faridan cak ya zauna a gurin tareda dora ta a cinyarsa kafin ya
maida kallonsa kan Asma’u yace “to naga ne hankalin ki yana kan yaranki kamar ma ni
baki ganni ba” ya fada yana kafeta da kallon nan nasa me saka Yammata fadawa
soyayyarsa ba tare da sun shirya ba.

Irin kallon da shi ya ringa qara rura garwashin soyayyarsa a zuciyarta har ya tada
gagarumar wuta da hauyau ba’a samu ruwa ko iskar da sukayi nasarar kashe ta ba.

Seta tsura masa nata kyawawan idon tana hango abinda zuciyarta ce kadai take da
tafsirinsa, a cikin idanun Bashir kadai take iya hango tsabtatacciyar qaunarta
wadda babu Algus ko digo a ciki amma ginshiri da baqar izzar sa suke hana bakinsa
iya furtawa. Har gara gangar jikinsa takan gaza bashi hadin kai gurin boye sirrin
zuciyar tasa dan a duk sanda suka hadu gangar jikinsa na sarrafuwa ne kawai bisa
umarnin zuciyarsa bawai kwakwalwarsa da take nan kamar wadda akeyiwa hayaqin wiwi
ba, yanzu yai abin arziqi an jima ya tafka na tsiya.

Ganin irin kallon qudar da Abbi da Mami sukewa junansu ya saka Amna kama hannun
twins manyan kuma suka tashi gaba daya kowa suka shige dakinsu, miqewar Farida daga
kan qafarsa ta ankarar dashi, seya janye idanunsa cikin son basarwa shima ya miqe
yana ce mata

“Zan samu abinci kuwa? Gaba daya yau coffee ne kadai a cikina”

“Ai fa ga Kuku ta dawo dole ka nemi abinci babu tambayar ya akai na taho ni kadai
ban kiraka ba balle jin ya jikina” ta ayyana a zuciyarta, a fili kuwa seta ce “kayi
wanka first, ga abinci nan yana jiranku” se ta miqe ta nufi dakin su Amna.

Se ya rakata da ido kuwa kamar zasu fado din, yanda take juya qugunta da ya fito
sosai saboda yanda rigar ta bawa komai haqqinsa ga qarar takalmin qafarta da yake
ji kamar qararrawa a cikin qwaqwalwarsa. Wasu busassun yawu ya hadiye tareda lasar
lips dinsa da suka bushe kafin yace “Hmmm” (inji me ciwon haqori 😂😂😂) karaf a kuwa
a kunnen Asma’u daidai sanda take tura qofar dakin su Faridan

“Idan baka chanza hali ba Bashir wata rana sedai ka farka ka ganka a kabari
Maganganun da kake dannewa sun shaqe maka wuya, ayi mutum bakin na son magana amma
baqin rai ya hana shi Allah yai mana magani dai”.

Guri ta nema ta zauna dan ba abunda zatayi a dakin dama ta tashi ne kawai dan ta
bashi damar kallon kwalliyar tata da kyau. Ahmad daya fito daga toilet alamar wanka
a ka masa ta shiga shafawa mai kafin Muhammmad ma ya fito, tsaf ta shirya su, kafin
su gama an kira Sallar Magriba dan haka tace suje suyi Alwala ita ma ta fita dan
zuwa tayi a bakin qofa suka kusa cin karo da Bashir wanda da alama shima wankan
yayi ya chanza kayansa zuwa Jallabiyya Baqa da tayi bala’in masa kyau duk da
kasancewarsa ba fari qal ba, Bashir nada kyau irin na Maza me sanyi daya hadu da
kwarjinin da Allah ya bashi.

“Kayi kyau Baban Ali” ta fada da zuciya daya dan ita bata iya munafunci irin nasa
ba kuma rashin yabon kwalliyarta be taba sare mata guiwa akan ta denayi ba.

Kallon ta yayi yana dan Murmushi kafin yace “Koh?”
Seta amasa masa da sarar sa tace “Uhm” tana qoqarin kauce masa a ranta tana mita. A
zaman shekara Goma sha shidda baza ta tuna ranar da a karan kan Bashir ya budi baki
ya yabi kwalliyar ta ba tun tana qorafi idan tayi se ta tambayeshi tayi kyau sannan
ze yaba har ta gaji ma ta dena, yanzu da yaranta suka girma kuwa indai tayi
kwalliyarta se sunce Mami kinyi kyau shiyasa ma ta dena damuwa da yabawar Bashir
dukda abun da zafi amma ya zakayi (Mazan hausawan Mu Allah ya shirye ku dai 🥺🥺).

Wuce shi tayi ta shiga dakinta itama ta daura Alwala shi kuma ya hada kan yaran
suka fita. Data idar da sallah zama tayi ta qara gyara fuskarta dakyau sannan ta
fito, sun zauna a Dining da gani ita suke jira dan haka ta qarasa gurin.

Seda tayi serving kowa sannan ta zauna suka fara cin abinci kowa na santi karma
Bashir yaji labari dan kunnensa har motsi yake. Besan yawan abincin daya nada ba
seda ya qara saka serving spoon ze debo abincin a karo na uku bayan wanda ta zuba
masa yaji wayam aiko suka kwashe da dariya suna kallonsa. Seya bata fuska kamar
yaro yace

“To ai yunwa nake ji for almost a week fa bamu ci abincin Mami ba, please Mami
karki kuma tafiya ki barmu, we are so sorry mun ji jiki wallahi, we missed you
alot”.
“Zobon da Asma’u ta kurba ne ya sarqe ta ba shiri ta watso shi tsabar yanda mamakin
kalaman Bashir suka nemi kasheta a zaune.

“Bashir dai data sani ne yake wannan maganar?” Kai ita kam badan ciwo ba dadi ba da
tace ta ringayi duk wata ko Allah ze saito mata Bashir zuwa abinda ta dade tana
fata.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 8

To Aka ce mata da Miji se Allah dan kuwa Ma’u da Basharin ta suna qulewa a daki
sukai muqus aka shiga sharafin soyayya dan dama an dade ba’a hadu ba qarshe har
makara tashi bacci sukayi. Safiyar ranar duk su biyun da ka kallesu zaka san suna
cikin walwala.

Ta cancada kwalliyarta da skirt and blouse na Atamfa komai ya fito se juyi take
tana saka kwakwalwar Bashir jijjiga. haka ta hada musu breakfast me rai da lafiya
suka ci suka wuce makaranta dukda sam be so yau ta zama ranar aiki ba ya so ace
suna gida yau yaci duniyar sa da tsinke ya more amma ba komai ai Gobe Friday zasu
hadu.

Suna fita Qarasa yan abubuwan da suka rage mata tayi kafin ta shiga dakin ta ta
kwanta dan huce gajiyar da Bashir ya tara mata, “Bashir is too good” ta ayyana
aranta. Wato yasan ta yanda duk ze wanke laifinsa ta wannan fanni gwanin malami
neda ta tabbatar samun irinsa se an tona.

Tana tsaka da tunanin shauqin daren jiyan ta jiyo qarar door bell da kuma ringing
din wayarta. Wayar ta fara jawowa ta duba, Anty ce matar ogan Bashir dake Flat din
da yake kallon nasu, seta miqe tareda daukan Qaramin mayafi dan dankwalin kanta ya
zame.

A palour suka zube tare da Anty da ta farayiwa Asma’un tsiya tun daga qofa”

“Kai Ma’u kinga wani kyallin goshi da kike daga fitowa daga Asibiti har za’a maida
wani kenan”. Daria Asma’u tayi tana cewa

“Haba dai ai na gama nikam wadan nan ma sun isa Allah ya raya mana sisi na kwai zan
ci gaba dayi”

“Inafa kika gama kedai ki shirya dan qila wasu biyun ne a tafe”

“Ba amin ba Anty” ta tare Antyn.
Gaisawa sukayi kafin Antyn tace mata

“Shekaran jiya na dawo wlh se dare ma nashigo Honey yake cemun Ai kina Asibiti ba
lafiya, har zamu zo jiya da magriba kuma yace sun hadu da Baban Aliyu a Masallaci
ya ce masa kin dawo gida”

“Eh wallahi jiya da rana aka sallamoni ai gaskiya Anty kinsha gida kusan 3 weeks
fa” Asma’u ta fada.

“Ki bari kedai zama nayi na huta nayi gyara sosai dan anan ba wani lokaci kake samu
ka baje yanda kake so ba mutum na saka maka ido” cewar Anty tana bawa Asma’u hannu
suka kashe

“Kai Anty a ringa tausayin Baba na dai karki qarasa mana tsohon mu”

“Ke barni fa dole na kwaci kaina sarai kin san Uwargida na bata wasa da gyara dole
nima na zage kar a raina ni.

Hira suka shigayi Anty ta shiga fito da abubuwan da tayo wa Asma’u tsaraba tana
cewa “Gashinan se a ci gaba da gashi ban ce ki raga masa ko na second daya ba atoh”
suka tuntsure da dariya Asma’u tana cewa “Anty baki da dama”. Se wurin 12 sannan ta
mata sallama ta tafi bayan ta rakata qofa ta dawo tana tattare kayan zuwa dakinta a
ranta tana qara jin qaunar Antyn dan yanda ta dauketa take kula da ita kamar
qanwarta da suka fito ciki daya.

Anty Suwaiba matar Engineer Abdullahi Gusau ce ogan Bashir.
Itace Matar sa ta biyu uwar gidan ta ma anan Lagos take da zama amma ba unguwarsu
daya ba. Mace ce me tsananin kirki dukda ta dan girmi Asma’u amma yanda take
mu’amalantarta kaman qawaye ko shaqiqan yaya da qanwa suke dan tunda suka fara
haduwa jinin su ya hadu da Asma’un.

Ita kanta Asma’u tana ji da Antyn dan Ita tunda suka hadu rabon da tace ta siyi
wani abun gyara da kudinta, a koda yaushe Anty cikin yo musu aike kaya gangariya
daga Zamfara garinsu take kuma duk sanda Asma’u ta tambayeta nawane ta biya seta
nuna bacin ranta. Ta kance da Asma’un
“Ni a qanwa na dauke ki, banida kowa a Lagos seke yanzu”.

Wasu daga cikin kayan ta fitar ta fara amfani dasu a ranta tana hasaso haduwarsu da
Malam Bash dan tasan yau kam se tafi jiya Armashi. Kafin ta gama an kira sallar
Azahar dan haka tayi alwala tayi sallar sannan ta kwanta zuwa La’asar kafin tasan
abinda zata dafa musu kuma.

Couscous tayi musu da miyar hanta ganin lokaci ya qure, setayi marinating kifin da
zata gasa musu su qara dashi zuwa can anjima kafin a kwanta. Yauma batayi wasa ba
gurin cin kwalliya ta daukar magana dan har tafi ta Jiya. Wasu riga da skirt ta
saka na kanti Oxblood da suka kama jikinta kamar tanayin nishi zasu yage. Bata
daura dankwali ba ta faka dogon baqin gashinta daya sha gyara se qanshi yake yi
kafin tabi kowanne lungu da saqo na jikinta

6 / 80