Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   32 / 80

93K to 96K   out of 238.5K words

zuwa nayi naga kyakykyawar fuskar ki sannan na kawo miki
wannan(ya miqo mun wata farar leda da kwali dan kwali qarami a ciki) ina so na
kwanta da wuri gobe zanje wata Interview kiyi mun Addu’a Allah yasa a dace”.

Karba nayi ina cewa “In sha Allah za’a dace, Alah ya bada nasara”.
“Amin” ya amsa mukayi sallama ya tafi ina juyowa mukayi kicibus da Fahad sun taho
shida Anwar yayan Alawiyya da take bi.
Fahad qanin Hajia Anjin ne shine auta a gidansu, Fari kyakykyawan saurayi me qirar
larabawa ga iya soyayya dan da ace da Fahad na fara haduwa kafin Bashir inaga da
yayi nasara akaina saboda iya tsara zancensa.

Hararar sa nayi ta gefe ganin irin kallon da yake mun yana murmushi kafin nace
“Uncle Fahad ina wuni”

“Karma ki wani ce mun Uncle, yau dai naganshi daman akan wannan Kika qi ni Asma’u
gaskiya kin fado da yawa, har naji sauqin radadin da nake ji tunda nafi wanda ya
kasanin sau dari wallahi kuma har yanzu ban cire rai akanki indai ba gani nayi an
daura miki aure ba bazan cire ran zaki zama mallakina ba” Fahad ya fada yana kafeni
da idanunsa masu kama dana mage, sena fizgi hannun Mimi nayi gaba ina cewa

“Se kayi ta saka ran ai kar Allah yasa ka cire, wai ace ba’a san mutum amma su
kamar mayu sun nace kuma ahakan dai shi yayi mun baku ba”

“Indai akanki ne ki kirani sarkin Mayu ma qarewa kenan Asma’u dan sena cinye ki
hankalina ze kwanta”.

“Daga murya nayi yanda ze jini nace “sedai ka ci kanka dan kurwa ta daci ne da ita”
na murguda masa baki harda fari da ido kafin na shige inajinsu da Yah Anwar suna
mun dariya.

Haka kawai duk wanda yaga Bashir seya kushe mun abuna, su kyau da kudi yake a
gabansu ni ba matsala ta bace ba.

Sannu sannu watanni naya shidewa harya rage saura wata daya bikin mu kuma a daidai
lokacin muka gama jarabawar semistar farko a ND1 zamu shiga hutu.

Sosia hankalina ya kwanta tunda zancen auren mu da Bashir ya kankama nayi fresh
abina na qara kyau da haske musamman ga gyaran jiki da tuni Hajia Umma ta fara
tsuma nan da nan jikina ya sake mudewa ko ina ya cika bazaka taba iya mun kallo
daya ka dauke ido ba se ka qara.

Bashir kansa wani lokacin idan ya kalleni yakan ce “anya Ma’u banyi zari ba kuwa ki
kalli kanki ki kalleni ai se ace dan aiken ki ne ni” in ya fadi haka se nayi dariya
nace
“Kai dai ka godewa Allah kadai dan shi yake yiwa bawa kyauta irin wadda beyi zato
ba.

Ana biki saura sati uku aka kawo Lefen Junaidiyya daga Birnin Tarayya Akwati na
dukan Akwai saiti hudu masu shida shida. Kaya kam sedai ace masha Allah dan komai
yaji harda danqareriyar sarqar gwal dinta yar dubai ga kudin da suka doro akai dubu
dari haka dangi a ka dauka ana ta murna yarinya tayi Goshi sati daya zagayo aka
kawo na Yah Fati da Yah Bilki rana daya suma bangaren kowanne sunyi Bajinta
akwatinan su Dozen Dozen da dubu hamsin hamsin akai.

Na Alawaiyya ne qarshe ana saura Sati daya suma suka dunguma masu algaita nayi
maroqa nayi aka kawo sha tara ta arziqi kai komai dai se sambarka mutane anata
yabawa kowa fadi yake saura Na Ma’u kowa naso yaga Lefeen ama’u yasan ba qaramin
Miji na fallo ba nidai a raina nace kwaji dashi idan ma gulma ce ta qare muku dan
ni banji komai ba da ganin Lefen su na taya su murna kuma ban damu ba dan tuni
Baffa ya gaya mun yacewa Bashir ba se yayi lefe ba ya nemi gidan da ze sakani
kawai, dan haka ma ya bayar da kudi masu yawan gaske yace aje Kano a hado mun duk
abinda Amarya zata buqata sannan duk wata hidima zanyi ta biki Alhaji Qarami yace
na gaya masa ze bani kudin to me ze dame ni kuwa.

Har satin biki Bashir nata fafutukar neman gida, duk yan gidaje masu kyau idan ya
tambaya se yaji kudin ya shallake Aljihunsa gashi kuma a qalla dai yana so ya
samarwa Ma’u muhalli me kyau kodan halaccin da akayi masa a zamanin nan adauki Mace
kamarta daga irin gidansu a bashi babu lefe ai wallahi an gama masa komai.

Dakyar ya samu wani gida anan unguwar su babu nisa sosai, gidan dukda tsoho ne amma
fasalinsa nada kyau 2 bedroom flat ne se babban palour harda Gurin Dining ga
Kitchen da dan qaramin store sannan daga waje akwai wani dan palour haka qarami ga
bandakin baqi a tsakar gidan se dan fili da ze ci mota daya.

Da yake ginin tsohone sunyi dakunan manya a wadace duk girman gado zasu iya dauka
kuma da akwai bandaki a kowanne daki matsalar da babu tiles sumuntine a dakunan
palour kadai suka sakawa tiles din.

Tareda Aliyu suka sha buga bugar neman gidan, bayan sun samu bayan ya biya Aliyun
yace masa ya kamata ya gayawa Ma’u tunda tun wancan satin take masa maganar gidan
dan tuni anje anga na sauran har ma jiya an tafi kafin Abuja da Bauchi na su na
cikin Gomben ne yayi saura, da za’a siyo kaya ma da farko Anty Saratu Babbar
Yayarsu Mace itace akan yin order kayan daman tafi kowa jin takaicin auran Bashir
da za’ayi cewa tayi baza’a siya musu iri daya da Asma’u ba dan tasan Bashir bashida
gidan da za’a zuba su, seda Hajia Babba tayi mata kaca kaca tace kuam karta kuskura
ko cokali abanbanta in yaso idan an rasa inda za’a zuba a bawa Ma’un kayanta ko
siyarwa ne tayi tasan dai an mata yanda akayiwa yan uwanta.

Ita dai Goggo nata Ido, ko Suhaima data kira tayi qorafi cewa tayi babu ruwanta
matar mutum kabarinsa kuma ita bata ga aibun Bashir ba da za’a ce baza’a aure shi
ba.

Washe gari sukaje da ita da Bashir din da Aliyu se Alawiyya yar uwa ta rai da rai.
Ita kam gidan ma ya mata a haka, bandaki ne matsalar dan duk ya dafe nan take a
cikin kudaden data karba ta ware ta bawa Bashir din dakyar ya karba tace a canza
kayan bandaki har tiles din qasa dana bangon a cire, ya hada da abinda yake
hannunsa ayi sauran gyare gyare da fenti idan yaso dakunan se a saka carpet kawai a
ciki,

Haka kuwa akayi a cikin kwana biyu se ga gida ya dawo sabo dan gyara aka masa
gangariya kai bakace tsohon gidan nan bane, ana i gobe kamu kuwa aka je aka jera
mata kayan ta sega gida ya fito shar yaji kaya yan order. Gadajenta biyu Yan Turkey
masu kyau da tsada ga kujeru na alfarma da kayan kallo kai duk wani abu da ake
siyawa yar gata an sakawa Asma’u haka kayan Kitchen sosai Goggo ta gwangwaje su da
kuloli tunda duk Baffa ne yake siyan Electronics iyaye mata su saka abinda babu ai
kuwa tayi qoqari kai baka ce auran Yaya uku take ba.

Tsaf aka shirya gida har yan jere na cewa wai daman qaramin guri yafi kyan kwalliya
se suka ga kamar jerenta na neman yafi na masu manyan gidajen kyau.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 34

Ranar Juma'a aka daura aure na da Bashir, Juma'ar data shiga cikin jerin rana kun
tarihin rayuwata na farin ciki da bazan taba mantawa da su ba. A qa'ida ranar da
aka daura aure a gidan mu ake kai Amare amma mu ba'ayi haka ba saboda Dinner da
manyan Yayyenmu suka shirya zasuyi a daren ranar sauran Yayyen mu mata se tsiya
sukeyi wai an fi son mu su kuwa kamar ana jira da an daura ake kwashe su.

Da yake tun ana sati daya da biki muka san da shirin Dinner, nasan dole sauran
Angwaye zasu gwangwaje suyi shiga ta alfarma tunda suna dashi dukda Bashir ma nasan
ze yi iya qoqarinsa amma baze iya kamo su ba saboda tattalin arziqinsu ba daya bane
su duk masu dashi ne.

Haka na samu Baffan mu na tasa shi da naci seda ya bani shadda yadi goma cikin irin
wadanda yake dinkawa ni kaina bansan kudinta ba kawai dai nasan suna da kyau kuma
ko cikin Mutane ina dadewa banga wanda ya saka irinta ba sefa manyan irinsa.

A gurin Yah Mustapha na samu hula harda takalmi daya siya dan daurin aure saboda
duk gidan mu ya fisu gayu, dakyar ya bani wai order su yayiwo takanas seda mukayi
ma zan biya kudin rabi nidai dana samu suka zo hannuna nace a gudunmawar sa, yana
ji yana gani na masa fin qarfinsu se na bawa Yah Abubakar shaddar nace ya kaiwa
Bashir dinki tunda abokinsa ne yasan Size dinsa na roqeshi dan Allah karya gaya
masa ina so na bashi mamaki ne.

"Ma'u kenan, yanda kike son Bashir kike tattalin sa Allah yasa kar wata rana yayi
miki halin mu na maza" abinda Yah Abubakar ya gaya mun kenan a lokacin da se naji
jikina yayi sanyi.

Gaba daya daman na lura dashi kamar hadi na da Bashir beyi masa ba na rasa dalili
dan har tambayarsa na tabayi yace mun babu komai, da yake daman shi ba mutum ne me
yawan magana ba se na bar maganar kawai nasan idan da Bashir nada wani mugun abu
baze barni na aure shi ba.

Tsaf na hade kayan nan bayan an dawo daga daurin aure angwaye sun shigo aka dauki
hotuna, masha Allah gaba dayan mu munyi kyau kuma ko wacce ta dace da zabin ta se
fatan Alkahiri dangi da abokan arziqi suke yi mana. Suna shirin ta fiya nayiwa
Sadiya qawata rada dan daman ita na bawa ajiyar Kayan tayi maza taje ta dakko su,
seda suka fita tabi bayan Bashir din ta bashi.

Muna zaune a bangaren da qawayen mu anan ta hira irin wadda ko wanne qawayen Amarya
sukeyi idan ana biki, hayani ya na tashi wayata dake hannuna tayi qara, Bashir ne
daman zaman jiran kiransa nakeyi sena miqe da sauri na shige bandaki na kullo qofar
ko naji maganar sa dakyau.

"Ma'una kayan menene wadannan, ina kika samo shadda me bala'in tsada haka?" ya
tambayeni bayan dana gaishe shi.

"Kamanta an jima akwai Dinner da za'ayi, kalar kayan da zan saka ne zamuyi Anko".

"Ina sane har ma nayi dinki nima, mantawa nayi sam ban ma gaya miki kalar nawa
kayan ba ai" ya fada daga daya bangaren, sena marairaice nace

"Se ka ajiye su gobe ka saka idan za'ayi budar kai nidai yau wannan nake so na gani
a jikinka".

"Shikenan an gama Amaryata, na tabbatar yau ke kadai ce zaki fini yin kyau a gurin
nan"
"Haka nake so Angona yafi na kowa, se anjiman idan kunzo, kar dai ku bata lokaci
qarfe takwas zuwa Goma Baffa yace za'a tashi" daga haka mukayi sallama na kashe
wayar.

A filin tsakar gidan mu aka shirya za'ayi dinner, tun la'asar masu decorashan din
da aka dakko suka katange iya inda suke buqata suka fara aikin su, kafin magriba
sun gyara guri tsaf se ka rantse wani babban dakin taro ne.

Seda mukayi sallar magriba sannan aka fara shirya amare, munyi kyau har mun gaji
cikin dinkin riga da skirt na wani hadadden material da akayi mana kowa da kalar
nata da ze dace da shigar Angonta, munsha daurin goggoron mu me kyau dan fa fashion
designer guda aka dakko ta shirya mu dukda a sannan ba'a fara kwalliya me fente
fenten nan ba amma ta tsatso mana kyau da iya abinda ake amfani dasu a sannan.

Har mun saka kayan sarqoqin mu Hajia Umma tace mu cire, saitin sarqa, awarwaro da
zubuna ta kawo mana na gwal qirar dubai wanda sallama ce Baffa yake bawa Iyayen mu
mata kudi su siya mana idan za'a kaiki dakin ki saka shi ta bawa kowacce nata ta
saka nan da nan kwalliyar mu ta qara qawatuwa se walwali mukeyi ta ko ina.

Seda mukayi sallar Isha'i sannan muka fita babban palour inda kafatanin yan gidan
mu mu a lokacin mu talatin da tara ne muka hallara ga Baffa da Matansa Hudu aka
shiga daukar hotunan family.

Lokaci daya hawaye suka balle mun kamar sauran na jira kuwa muka dauki kuka wiwi
wanda nasan na zallar murna ne Baffa kansa seda ya kauda kai gefe ya goge kwalla
ganin irin wannan arziqi da ubangiji yayi masa.

A ko da yaushe kalmar godiya ga Allah bata taba barin bakinsa, ya bashi lafiya, ya
bashi arziqin mata, dukiya da Tarin Yaya ya kuma shirya masa su, sannan be jarabce
shi da wani babban Alkaba'i daya dame shi a rayuwa ba banda qananun abubuwan da
kowanne mumuni ba'a gaza jarabtar su dashi to shi kuwa me zeyi idan be godewa Allah
ba da kuma Addu'ar neman cikawa da Imani dan abinda ya rage masa kenan a yanzu.

Bayan mun gama hoto da yan gida Angwaye ma suka shigo, kowa yayi kyau amma wallahi
Bashir dina ya fisu dan se ya zama tamkar wani wata a cikin taurari kamar yanda na
zama Zara cikin yan uwa na, haka muka sha hotuna musamman da iyaye da manyan yayye
suka fita aka bamu guri nan muka baje kojin mu aka dauki hotuna kala kala kafin
muka dunguma zuwa gurin dinner.

Taro ne akayi shi a tsare harda Baffa duk fulatancinsa seda Yayyen mu suka tilasta
shi ya dan zauna a teburin da aka shirya masa da Aminan sa da be ma san an gayyato
su ba, ganin su ya sa ya saki jiki haka iyayen mu mata Goggo ce dai seda aka kai
ruwa rana dan seda muka yi mata hawaye nida Yah Bilki sannan ta fito se wani jan
mayafi take tana rufe fuska yanda kasan ita kadai ce bafulatana a gurin.

Cikin Awa biyun nan akayi komai aka tashi, anci an sha abinci na alfarma qarshen
dai yan gayun Yan Abujan ma sun yaba gashi komai a tsare babu kida balle ayi rawa
irin slow music din nan aka saka kawai aka ci abinci aka dauki hotunan tarihi seda
aka fara watse wa nema qannen mu suka dage se an saka musu kida ai kuwa waqa biyu
aka saka Baffa na hango yanda aka hade mata da Maza ana rawa yace a kashe kowa ya
tafi haka muka kwana ana ta hirar taron nan dan babu qarya munji dadin sa.

Washe gari da wuri aka miqa mu. Munsha kukan rabuwa, Junaidiyya aka fara tafiya da
ita dan jirgi sukabi qarfe goman safe suna tafiya yan Bauchi ma suka dauki Amaryar
su, kafin qarfe biyu an tafi kai Yah Bilki da Yah Fati ni kadai nayi saura tunda
kusa da gida ne.

Seda aka dawo daga kai su aka baro wadanda zasu tsaya musu budar kai kamar yabda
kowa yasan Al'adar mu ta Gombawa, anayin sallar La'asar nima aka kwashe ni se gidan
su BShir inda za'ayi budar kai na.

Seda aka damqani a hannunsu, ga kayan garar da kashi biyu akayiwa ko waccen mu, ta
gidan su miji daban tamu daman tun da akai jere kowa an kai mata gidan ta sannan ga
turame da kwanuka harda Saitin Gado da akeyiwa Uwar miji seda akayiwa kowacce
babban Gado dan Dubai haka aka kai musu.

Bayan sun biya kudin budar kai da Turmin zani da tabarma nan qanne da abokan wasan
Bashir suka fara zuwa kowa ta ajiye kudinta se ta fadi sunan da ta sakamun, wannan
yar farar yarinyar da muka gani randa muka zo gurin Bashir ta taho da gudunta da
naira goma a hannunta.

A inda taga ana ajiye kudin ta ajiye kafin ta kama mayafina cike da rashin ji har
tana neman ture mun daurin dankwali ta bude fuskata tana cewa "Na saka mata ANTY"
mata suka dauki guda kowa ya yaba da ganin kyakykyawar Amaryar Bashir, hannunta na
kama na zaunar da ita nace "Yaya sunanki?"

"AMIRAH" ta fada tana yar dariyar yarinta, nan da nan naji ta shiga raina saboda
ina da son yara daman gata yar fara kyakykyawa da ita.

Anyi Budar kai lafiya seda aka kira sallah aka tashi, yan uwana sun mun kara dan ba
qaramin kudi suka zuba mun ba haka dangin Bashir ma ba laifi sun mun liqi sosai
bayan an gama qawayena suka tattare mana kudin mu muka koma dakin Bashir inda nan
aka gyara aka sauke mu.

Anan muka kwana se washe gari muka tafi gidan mu daga ni se Bashir dan daman ba'a
raka amarya mu iya kacin su gidan su miji se ku qarasa keda shi kawai.

Soyayya me tsafta suka shimfida a cikin gidan auran mu, ban qara tabbatar da Bashir
yana qaunata ba se a yanzu dan a aikace yake nuna mun duk abinda bakinsa baya iya
furtawa.

Cikin sati daya da mukayi wata irin shaquwa me qarfi ta sake shiga tsakanin mu dan
kullum muna manne da juna babu inda yake zuwa se masallaci da yayi sallah kuma ze
dawo gida kuma har zuwa sannan babu wanda yazo mana kullum gidan mu a kulle muna
ciki muna kashe juna da soyayya.

Matsalata daya da Bashir dan irin taya aikin nan da naji ana cewa Angwaye na taya
Amaren su shi bayayi, yana zaune zanyi komai na sedai na kawo masa idan muka ci
abinci yana zaune zan tattare kwanuka naje na wanke qarqari ya zo Kitchen din ya
tsaya ina aiki muna dan hira idan yan maganar na kansa kenan dan Bashir be fiya
magana ba, miskiline seta raya masa sannan ni kuma gani da dan banzan surutu dole
da qarfi da yaji tasa yake biye mun wani lokacin kuma na qaraci maganata idan na
ishe shi ya jani ya kashe bakin maganar da Zazzafan Kiss shikenan.

Seda muka kwana goma sannan muka fita, da yamma Aliyu yazo da yar motarsa one door
daya siya dan shima ya samu aiki tuni kuma da yake bashida wani nauyi akansa
shiyasa har ya iya siyan mota.

Muna tafe yana tsokanata wai me nake bawa Bashir a dan lokaci haka yayi kumatu ya
yi haske shima ze zo a ringa samma sa miyar Amarya ko ze dan farfado nidai murmushi
kawai nakeyi irin najin kunyar nan har muka je gidan su Bashir.

Cikin farin ciki Dada ta karbe mu harda Anty Amina Babbar yayarsu da bata koma
Bauchi ba tunda tazo biki. Haka sukayi ta jana dan saki jiki nidai ina ta sunkuyar
da kai, da Dada taga haka se ta tashi ta barmu ai kuwa na dan sake dasu dan basu da
duhun kai nan da nan muka saba mukayita hira. Dab da Magriba Alhajin su ya dawo,
seda sukayi sallah kafin Anty Amina ta rakani muka gaisa se saka mun Albarka
yakeyi.

A gidan mukaci abincin dare sannan Aliyu ya dawo muka tafi bayan na ajiye musu
tsarabar da na kawo na manta ta a motar Aliyun ina jin Dada na Tambayar Bashir mun
shiga gidan su Addah kuwa yace Aa, tace yayi qoqari ya kaini mugaisa.

Da muka fita a zatona zamu shiga gidan mu dan tun tuni a qagare nake, saura qiris
ma na dauki Fainusa dazu muje amma dai na danne .
Ganin da nayi Mun dau hanya har mun wuce gidan yasa na tabo Bashir

32 / 80