Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   31 / 80

90K to 93K   out of 238.5K words

yanzu se jiran sakamakon SSCE
mukeyi.

A dan tsakanin Baffa ya taramu, daman munsan maganar bazata wuce ta aure ba dan
haka tun kafin ranar kowa ta fitar da zabin ranta dan dukkan mu wannan karon yan
Aure ne maci gaba da karatun a can.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa ni, Alawiyya, Yaya Fati, Yaya Bilkisu se
Junaidiyya mune yan candyn Bana, cikin sakin fuskar da Baffa yake da ita a cikin
iyalansa muka dan taba hira kafin ya gabatar mana da maqasudin kiran namu.

“Na kiraku ne dan naji ra’ayinku dukda dukkan ku nasan kunyi jarabawar shiga Jami’a
me kuka zaba aure ko kuma Bokon za’a ci gaba?”

Seda muka kalli juna muka qara sunkuyar da kawuna kafin muka hada baki gurin cewa
“dukka gaba daya muka zaba Baffa”.

Alhaji Qarami da yake gurin ne ya shiga tsokanar mu da cewa “wato gaku cinye du ko
zaku ce wani dukka kuka zaba to baze yuwu ba sedai ku dauki daya” se Baffa ya katse
shi yace

“Aa bana so karka takuramun yara, shiyasa bana saka iyayenku mata a cikin magana ta
dan karma wata ta tilasta su fadar abinda ba ra’ayinsu ba shine kai yanzu zaka zo
kana tsokanarsu ko, gasunan se su gaya maka su waye surukan naka idan yaso se ka ci
gaba da bincike muga abinda hali zeyi”.

Da daddaya kowa ta fadi sunan rabin ranta, nice ta qarshe harda gyara zamana na
bude baki zanyi magana Alhaji Qarami ya tare ni da cewa
“Ai ke nasani Amaryar ta Excellency ko?” (Yusuf kusan abokin Alhaji Qarami ne dukda
a shekaru Alhaji Qaramin ya girme masa sosai, yaro ne a cikin manya da Allah yayi
masa nasibi sosai a rayuwa, Asalinsa dan Bauchi ne kuma guri daya suke aiki da
Alhaji qarami a Abuja tunda yaga Ma’u yace a duniya nan shi yaga mata haka kuwa
take garashi kamar kwallo amma be sare ba kullum yana kan binta.
Yanzu haka ya shiga siyasa ne ya tsaya takarar Dan Majalissar Taraiya dan yace se
ya kai har shugaban qasa in Allah ya yarda shiyasa suke kiransa da Excellency).

Lokaci daya na hade fuskata kamar ban taba murmushi ba ina kallonsa nace “Ni Bashi
bane Alhaji Qarami ai na gaya masa ni ina da wanda nake so”.

“Haba Ma’u yanzu kice bakyason Yusuf duk yanda yake bala’in sonki kullum cikin
hidimar ki yake yana hanyar zuwa gidan nan” Alhajin ya fada, sena tunzura baki gaba
kaina a qasa nace

“To ni nace yayi mun ne ai tun ranar da ya fara zuwa na gaya masa nacin sa ne yasa
kashi ci gaba da zuwan ai”.

Ze sake magana Baffa ya tare shi da cewa “ya isa Muhammadu barta ta fadi zabinta
babu dole a al’amarin aure”.

Karkacewa nayi ina murmushi nace “Ni Baffa Yaya Bashir nake so”.

Se Baffa ya kalli Alhaji Qaramin da son qarin bayani, cikin takaicin qin zabar
Abokinsa da banyi ba yace “Wai wannan yaron Bashir Abokin Abubakar dan gidan Alhaji
Ahmad na qasan layin nan take nufi”.

“Toh toh na gane dan waje Amadu me Mota kenan toh ai babu laifi se aje a cigaba da
addu’a Allah ya tabbatar mana da Alkahiri gaba daya”(Inkiyar Baban su Bashir ce
saboda ya tabayin Direban Babbar mota yana saurayi tun sannan ake kiransa haka)”.

Godiya mukayi wa Baffa kafin muka fice kowa ranta qal.
“Amma Ma’u baki kyauta ba tayaya Babban Yaya ze miki magana ki musa masa” Bilkisu
ta fada bayan da muka yi gaba nida ita, sena kalleta nace “kiji ki Yah Bilki da
wata magana, so kike nayi shiru haka kawai a cuceni yanda yake so na auri abokin
nan nasa tsaf ze iya zuga Baffa, yanzu kuwa dana fada a gabansa kinga ai nayi
maganin abun”.

“Dukda haka da kin sani bari kikayi ki same shi ke dashi ki gaya masa, kuma ni
wallahi nafi miki sha’awar Yusuf din ma gashi Kyakykyawa dan gaye ga Kudi”.

“Ai se kije ke ki aure shi nidai bana so” na fada ina harararta, Alawiyya data
qaraso gurin mu
Tayi caraf tace “ga ma Uncle Fahad banza duk samarinta na arziqi ta rasa wa zata
zaba se wannan me girman kan tsiyar da ita kadai yake yiwa murmushi a gidan nan”.

Hayayyaqo mata nayi ina cewa “Eh shidin na zaba ba’a son Fahad din saboda dan
uwanku ne baza’a aureshin ba sedai haushi ya kashe ku, Nida Yaya Bashir kuwa nan
gani nan Bari yan baqin ciki sedai su mutu”

“Allah ya baki haquri ni ba da wata manufa na fada ba ta Bashir” Alawiyya ta fada
dan ita baiwar Allah ba ruwanta bata iya wa fitinata. Banza na musu nayi shigewata
daki ban qara kula kowa ba inajinsu suna ta maimaita zancen kowa aka gayawa se yayi
mita na rasa me yasa basa son Bashir.

Idan ma lissafin su bekai sauran manemana Arziqi ba ni wannan baya gaba na dan
Arziqi da rashinsa duk nufine na Allah, zaka iya auran mutum yana dashi ya tsiyace
ko kuma ka aure shi bashi da komai daga baya ya samu wadatar nidai kwanciyar
hankali nake nema kuma a gurin wanda kake so yake son ka kadai zaka same shi.
Dan haka inason Bashir ko a bukkar kara ze ajiye ni na yarda zan rayu dashi har
qarshen rayuwa indai akwai so da qauna ba matsala.

Cikin dan lokaci maganar auran mu ta taso kuma a daidai lokacin makarantu suka fara
sakin Admission, Alawiyyah da daman ATBU ta saka saboda daman saurayinta dan Sarkin
Bauchi ne lokacin har ina tsokanarta nace Allah yasa se ta samu Admission acan kuma
yaqi auranta toh Allah ya taimaketa ta samu ga batun aure ma har an kawo kayan
nagani inaso na alfarma abinka da gidan sarauta.

Ni, da Yah Fati da Yah Bilkisu harda Junaidiyya duk GSU muka cike su ukun dukka
sunansu ya fito a first Batch kowa ta samu course din da take so amma ni har aka
saki second batch babu sunana bayan kuma gaba daya ma makina ya fi nasu a Jamb din.

Har aka fara Registration Admission dina be fito ba qarshe har makarantar seda
akaje amma wai babu sunana sukace wai sedai a sakani a yan Alfarma a bani wani
course din daban nace bana so abarni kawai inda rabo badi sena sake Jamb haka kuwa
akayi se Alhaji Qarami yace bazan zauna ba ko Diploma ce naje nayi kafin wata
shekarar nan da nan kuwa aka samomun diploma a Computer Science na fara.

An kawo goron Yah, Fati da Yah Bilki suma anan cikin Gombe ne suka samu nasu
mazajen duk yayan Babban gida nida Junaidiyya ne ba’a rigada an kawo ba ita dai
anzo tambaya Dan Abuja ta samo yaron wani Minister abinda ya dakatar da kawo kudin
ma wai Babansa ne yayi tafiya se qarshen watan da muke ciki zasu zo.

Ganin duk anyi maganar su amma nida Bashir shiru yasa hankali na ya fara tashi. Sau
biyu ina sake masa magana bayan da aka bashi damar ya turo amma se yace na qara
masa lokaci akwai abinda yake jira gashi kuma a kwanakin gaba daya ma ya janye da
zuwa gidan mu musamman da Yaya Abubakar baya nan, daman shi a Kano yayi service se
Allah ya taimake shi gurin suka riqeshi.

Seda muka ci sati kusan biyu Bashir yana mun wala wala har takai Baffa ya sakeyi
mun akan yaji shiru saboda yana so a hada gaba daya a aikawa da gidajen mazan sa
rana shiyasa yake so yasan shirin Bashir din.

Ranar dana gaji da zilliyar tasa takanas na kama hanya muka tafi gidansu tareda
Alawiyya wadda da dakyar ta yarda zata rakani, muna tafiya tana zagina wai in banda
asara ga Maza da suka amsa sunansu suna bina amma na nace se wani Bashir gashinan
yana wulaqantani kuma tsabar rashin zuciya na dauki jiki zan je gidansu. Nidai ban
kulata ba har muka shiga gidan.

Kai tsaye Dakin Dada muka shiga, da yake daman na saba zuwa gaishetan se hakan be
zama wani abun mamaki na daban ba. Mun sameta tareda Yayarta wadda naji suna cewa
Addah da yaranta guda biyu babbar bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba se
qaramar itama zatayi hudu haka.

Matar nada matuqar kirki ga faran faran da Jama’a nan da nan ta shiga hidima damu
musamman da taji ance budurwar Bashir ce bakinta har kunne take tambayar wacce daga
ciki aka nuna mata ni.

“Wai wai zuqi masha Allah, ashe yanda Bashir yake sunkuyar dakai har ya iya zabo
mace haka kai Allah ya nuna mana lokaci musha biki, sannunku sannunku” haka tayi
tayi dauke wannan ajiye wannan nidai kaina yana qasa ina ta Addu’ar Allah yasa ya
shigo amma har mukayi kusan minti talatin shiru bayan kuma sanda muka shigo na ga
qofar dakinsa a bude alamar yana gidan.

Naziru qaramin qaninsu ne ya shigo, ya qaraso inda nake da dan gudunsa ya zauna
yana gaishe ni da yake muna shiri dashi sosai, seya miqe da gudun sa yace “bari
naje na gayawa Yaya ga Anty Ma’u tazo” be dade ba se gashi sun dawo tareda Bashir
din muna hada ido na tabo Alawiyya nace mu tafi daman jiran da nake kenan nasan
dole ai ze bimu.

Mukayi musu sallama bayan mun ajiyewa Dada ledar dana zubo turarukan fesawa dana
wuta da sababbin kudi yan hamsin hamsin na dubu biyu Addah ta dauke ledar tana zuba
mana godiya kamar ita aka bawa mudai muka tafi.

Seda muka danyi nisa da gidan sannan Bashir ya biyo mu, sama sama suka gaisa da
Alawiyya tayi gaba ta barmu, se ya kalleni yana cewa “Jiya munyi waya amma baki
gayamun zaki zo ba”

“Me yasa zan gaya maka tunda baka son mu hadu yanzu, daman zuwa nayi in gaya maka
dan karka ji a gari, tunda dai ka gagara turowa zan bawa wadanda suka shirya dama.
Na kuma gode da batamun lokaci da kayi da duk alqawarirrikan qaryar da kayi mun
akan zamu rayu tare” ina gama fadar haka nayi gaba na barshi a tsaye ina jinsa yana
kwala mun kira nayi banza dashi.

A zatona ze biyo mu amma har muka je gida babu ko sahunsa, abinda ya qara qona mun
rai ya tabbatar mun dagaske kenan daman Bashir yaudarata kawai yayi ba aurena zeyi
ba yasa na gama fadawa a soyayyarsa sannan yanzu ze gudu ya barni. Ranar haka na
kwana ina kuka, gashi ko a waya be kirani ba, babu wanda yabi ta kaina a gidan,

Hajia Anjij cema da safe da ta ga yanda idona ya kumbura ta jani tanayi mun nasiha
da nayi haquri, lokaci da yawa abinda muke so be zama lallai shine Alkahiri a gare
mu ba dan haka na fawwalawa Allah, idan Bashir mijina ne se munyi aure idan kuma
Allah be yi ba duk nacin mu sedai mu haqura.

BASHIR

Tun lokacin da Asma’u ta gaya masa zancen an ce ya turo gida se maganar ta rabe
masa biyu, bangare daya na farin cikin ya kusa mallakar Ma’unsa se kuma daya
bangaren tashin hankalin da me ze aureta?

Har yanzu bashida komai be kuma bawa wani ajiya ba, dan aikin da yakeyi dubu goma
ce ake biyansa a wata wadda dawainiyat karan kansa ma ba isar sa takeyi ba ga
qannensa suma da qananun buqatunsu tunda Babansu yayi ritaya, kudin garatutinsa
suya har hada yake dan juyawa ana samun abinda za’ayi cefane a gidan yanzu gaba
daya duk burinsu akansa suke na ya samu aiki toh ta ina kuma ze fara daddago
maganar aure.

Kullum da wannan zulumin yake kwana yake tashi ya kuma rasa dawa zeyi shawara baze
iya tunkarar Abubakar ba, Aliyu kuwa tun tuni daman ya gaya masa ya rabu da Asma’u
dan tafi qarfinsa toh se a yanzu ya ga gaskiyar abinda yake fada din amma kuma baya
jin ze iya rabuwa da ita saboda sonta ya riga yayi masa irin shigar da fitar rai ce
kadai zata iya raba shi da shi wannan dalilin ya sa yake zille mata dan ganinta ma
kullum qara rura wutar sonta yake a zuciyarsa sannan ya rasa ta yanda ze fahimtar
da ita halin da ake ciki.

Maganar data gaya masa dazun ba qaramin tayar masa da hankali tayi ba, gaskiya
bazata sabu ba. Dole ya nemi mafita dan yana ji yana gani baze iya zuba ido wani ya
raba shi da Ma’u ba ya rusa duk wani tsari da mafarkin sa akanta.

Jiki a sabule ya koma cikin gidan, palour Dada ya shiga ya tarar dasu ta zazzage
turarukan tana ta santinsu gaba daya ta kwashe se kwalli daya ta barwa Dadan wai ai
kullum ana kawo mata na yau rabonta ne kudin ma seda ta raba biyu ta dauka, ganin
yanda Bashir ya shigo kamar kazar da tasha ruwa yasa suka dakata suna kallonsa.

“Lafiya Bashir ka shigo kamar wanda aka zarewa qashi” Addan ta fada tana kallonsa,
se ya ja guntuntsaki yana kallon Dada yace “Dada maganar da mukayi dake akan sunce
mu tura ne, kinsan tare ake so a hada dana sauran toh shine yanzu tayi fushi har
tana cewa kawai zata bawa wasu dama tunda ban shirya ba”.

“Me zanji haka magana babu dadin ji, kai yanzu Allah ya kashe ya baka shine ka
tsaya salubanci da sunce ka tura din amma ba’a je ba to uwar me kake jira?” Addah
ta fada tana gyara zama.

Shiru Bashir ya mata, dan shi kwata kwata baya so tana shiga sabgarsa ma, Dada ce
tace
“Toh Addah kin manta har yanzu be samu aiki bane, aure ai baze yuwu ba babu abinyi
dame ze riqe matar?”

“Sannu Nafi, kai Allah Nagode maka da Halin Nafi. Wane irin aiki kuma kuke magana
mutumin da Allah ya kawo masa hanyar arziqi, yanzu in banda rashin tunanin irin
naki har kwa tsaya kuna zancen wani aiki ga babban aiki ya samu.

Ka samu yarinya irin wannan daga babban gida tana sonka kuma iyayenta sun yarda
zasu baka qarewar aiki harda gida da mota se an hada maka nasan kai dai kawai ka
tura ayi magana asan dagaske kake seka gaya musu baka da aikin yin Aradu zasu samo
maka tunda yarsu tana sonka.

Kai ashe Nafi kina dab da ja mana Asara kai Jama’a Allah kayi magani”.

Kallon ta kawai suke har ta gama hayagagarta, se Bashir ya miqe ya fice a ransa ya
na qudurce kawai ze gayawa Alhajin su aje, idan yaso su abar maganar nasu bikin
zuwa sanda Allah ze sa ya samu madafa tunda ya rarraba CV dinsa a gurare yanzu
jiran tsammani kawai yake yi. Kasa zama yayi a gidan ya fice, yana so ya kira Ma’u
kuma yana tsoron abinda zata sake gaya masa Allah Allah kawai Yake Alhaji ya dawo
ayi wacce za’ayi kawai.

Addah kuwa ci gaba tayi da surutan ta har tana cewa Dadan idan ma maganar kudi ce
se a nemo Bashi ayi komai da an gama biki abinda ya samu a tattara a biya.

“Kiji ki Addah wane irin bashi ana zaune qalau dan Allah, babu komai idan Allah ya
nufa matarsa ce to se kiga Allah ya kawo hanyar da za’ayi komai cikin rufin asiri.
Haka suka rabu dai Addah na sake jaddada aje ayi maganar nan kar su bari damar nan
ta wuce su.

Bashir kuwa Alhajin su na dawowa da yamma ya shaida masa, ba tareda wani ja inja ba
kuwa ya amince shima abinda yace Allahn daya taso da maganar ze hore yanda za’ayi
komai cikin rufin asiri, tun a daren ranar ya tashi qaninsa ya aikashi gurin Baffan
su Asma’u akan a basu dama zasu kawo goron gaisuwa, a take kuwa yace duk sanda suka
shirya suzo, washe gari kuwa suka hadu da Qannensa guda biyu da Amininsa daya
sukaje aka kai gaisuwa.

Tarba me kyau suka samu daga gurin Baffan da yayyen Ma’u biyu manya, nan da nan aka
qulla magana sedai sun nemi alfarmar a qara musu lokaci akan wata shida da Baffa
yace ya yanke ranar auren.

“Kasan haryanzu Alhaji be samu wani aiki na gaske ba, yar buga buga ce kawai akeyi
ana dai saka ran samun aikin nan kusa, abinda yasa muka zo din ma saboda kaga kar
aga kamar wasa ne abun” Aminin Baban su Bashir Malam Salisu ya fada.

Se Baffa yayi murmushi yace “Babu komai Malam Salisu in sha Allahu babu abinda ze
gagara, kuje kuyi shirinku iya abinda ya zama dole sadakine se ya nemi muhallin da
ze ajiyeta duk abinda ya kakare masa yazo ya sameni babu komai” suka yi sallama
suna ta godiya, haka suka koma gida suna ta yabon dattako da karamci irin na Baffa,
dan lokacin da sukaje gidan daya daga qannen Baban su Bashir din har yana cewa anya
za’a barsu su shiga kuwa shi Bashir me ya kaishi dakko abinda yafi qarfinsa.
ASMA’U

Ina kwance ina ta baqin raina tun jiya har yanzu ban ware ba, gaba daya na rasa ya
ma zanyi dan bazan iya hasaso rayuwa da wani namiji da ba Bashir ba. Addu’ata kawai
Allah ya mantar da Baffa karya kuma tado mun da maganar har zuwa sanda zamu samu
mafita.

Ina cikin wannan tunanin Baba Jummai shugabar masu aikin gidan mu ta shigo dakin ta
sakar mun guda a tsakiyar kai, da saurin gaske na toshe kunne ina zare ido ita kuwa
se sake rangada abarta take ragowar na taya ta.

“Uwar dakina ta zama amarya mun shaida mun tauna goro da alawa Allah ya nuna mana
randa zamu sha taushen daurin aure” ta fada kafin ta sake kwasar wata gudar.

Wani mugun bugawa qirjina yayi, waye ya kawo goro na? Na shiga uku kardai fa Baffa
ya amsa wa wani daga cikin manemana magana.

Dafe qirji nayi na qara fito ta idanu waje nace “Baba Jummai gorona aka kawo dawa?”

“Wato Uwar dakina kina nan da halin ki na tsokana, baki ma san waya kawo goron ba
kenan, to wannan Me gidan da baya dariya ne Engineer kike ce masa kowa” Baba Jummai
ta fada.

Se naji kamar an kwararamun ruwan qanqara a tsakiyar kaina, wata wawuyar ajiyar
zuciya nayi kafin na koma na kwanta ina yiwa Allah tasbihi. Gaskiya Bashir ya
shammaceni.

Waya ta ce ta dauki qara, a jikina na ji cewa Bashir ne, seda na tura baki kamar
yana gabana kafin na daga wayar.

“Amaryata” ya fada cikin qaramin sauti, shiru na masa ina ta faman juya baki kamar
yana gaba na ina jinsa yayi murmushi yace “Fushi ake yi dani ko Ma’una ayi mun
afuwa. Gani a qofar gida nazo bada haquri”.

“Ni bazan fito ba” na fada cikin muryar shagwaba, se ya marairaice shima yace

“Haba mana Amaryata so kike yi na kasa bacci dan Allah ki fito na ganki mana kafin
nan da wata shida na dauke ki gaba daya ki zama tawa”.

Rufe fuska ta nayi ina murmushi nace “Dagake bazan fito ba, nima ai jiya banyi
baccin ba kaga mun yi 1-1 kenan ka tafi se bayan sati uku zaka sake ganina”.

“Kice kawai sena zare sannan, ki taimaka mun nidai ki fito na ganki ko minti daya
ne ki koma na yarda”.

Seda naja masa rai kafin na zura dogon hijabina har qasa na fita, a palour na tarar
da Goggo da su Nasir suna kallo naja hannun Mimi yar dakin Hajia Umma ce muka fita.

Bashir na tsaye daga bakin Get gurin masu gadi, har wurin naje nace masa”A nan ka
tsaya maimakon ka zauna, muqarasa toh”.

“Aa Gimbiya daman

31 / 80