Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
mata dukda tasan da zancen komawar amma bata zata da wuri haka
ba kuma ya akayi ma Ma’u ta yarda da tsarin ko kuma gida ze raba musu dan haka
cikin murna tace masa
“Har an samu gidan ne Yaya ko Anty ta yarda zata dawo nan ita?”
Shiru Bashir yayi, abin ya masa nauyi a zuciya yana kuma buqatar wanda ze fadawa
yaji sanyi dan haka besan sanda bakinsa ya subuce yace mata
“Bama tare yanzu mun rabu da Ma’u”.
Duk yanda Amirah take cikin farin cikin maganar tafiyarta lokaci daya komai ya
tsaya mata, “Yaya kun rabu ka saki Anty kake nufi Innalillahi wa’inna ilaihi
raji’un a garin yaya” ta fada tsakaninta dan Allah dan ko kusa ko alama ba abu bane
data taba hasaso faruwarsa.
Dukda take kishi da Ma’u bata taba yi mata fatan a saketa ita ta zauna ba, tasan
irin so da qaunar dake tsakanin Bashir da Asma’u tun tana yar yarinya bata taba
hasaso wani abu da ze kawo rabuwarsu ba idan ba mutuwa ba.
Gaba daya ma seta rasa me zata ce masa, haka sukayi sallama jikinta a sanyaye ta
ajiye wayar tana ta jimanta abin a ranta.
“Ke kuma lafiyar kika rafka taguma kamar wadda ubanta ya mutu” Addah data shiga
dakin ta ajiye kayan shanya ta fada tana kallon Amirah, se Amiran ta janye tagumin
da tayi tace
“Uhm Addah wani abun tashin hankali Yaya yake gayamun yanzu wai ya Saki Anty”.
“Amma ban taba sanin ke dai Asararriya bace sallamammiya se yau Amirah, saboda an
saki kishiyar ki shine kika rafka tagumi kamar wadda akacewa Murtala ya mutu, to
dan uwarki idan ba’a saketa ba ke taya zaki samu fawa a gurin miji kullum kina rabe
kamar wata mara galihu wannan ai abin kiyi rawa kiyi shewa ne ta tafi ta barmiki
gida kiyi yanda kika ga dama bari ma ki gani” ta taqarqare ta rangada guda tace
“Allah na gode maka mun yada kwallon mangwaro mun huta da quda, ai wallahi daman
duk wanda yaci tuwo dani miya yasha, seki fara shiri yaushe zaki tafi can din
yanzu?”
“Wai jibi yace Addah” ta fada a sanyaye dan fa ita bata ga abin farin ciki da sakin
Ma’u ba.
“Toh bari kiga in bazama karbo taimako, idan da wasu kudi a hannunki ki kawo na
hada naje can qasa gidan su Mero wasu yan haya sun shiga tace mun matar tana bori
kuma ta iya aiki bari kiga naje na karbo miki maganin kafi dana mallaka, ai yanzu
za’a fara wasan ita kanta Nafi seta gane shayi ruwane wallahi” ta yayimi hijabi
tayi waje tana ci gaba da handala an saki Ma’u.
Amirah na zauna tana ci gaba da jimaminta Sa’adaha ta shiga gidan, itama dai kamar
Addah harda gudarta tace
“Yo ke Allah ne ya kashe ya baki se ki tashi a tsaye da kissa da kisisina ki
riqeshi gam wallahi, ki kuma san duk yanda zakiyi kar a bar miki yara dan dasu
zakiyi zaman kishin in bata nan ki zugashi ya bata yaranta can su qarata ke kuwa ki
samu guri ki zuba isar ki yanda kike so bakiganni ba shida yaransa se dai in sun
hadu a gidan Hajiyarsa su ganshi, da kisisina na hana ya dakko su ban kuma fito
fili na nuna bazan riqesu bane ba idan mun hadu se inyi ta jansu ina yaushe zasu zo
mana a gefe shi kuma nayi duk yanda zanyi ko ance su kwana baze barsu ba to kema
haka zaki zama dole ki koyi wayo da dabara shine zakici ribar zama dashi.
Haka ta ringa yi mata famfo da hudubar tsiya Amirah kuwa ta hau kai tayi zaman
dirshen nan da nan ta ware Sa’adah ta kwaso mata tarkacen magungunan mata sannan
suka fita kasuwa ta sissiyo wasu abubuwan dan ya tura mata da kudi bayan sun gama
waya.
Addah kuwa daga gidan yar Borin gidansu Dada ta wuce. A tsakar gida ta saka kujera
yar tsuguno Bayan data karbe Lemo me sanyi data gani a hannun Naziru ta kwankwade
tas ta yarda robar kafin ta kalli Dada tace ke
“Ke Nafi na taba ki da arziqi”
“Meya faru Addah, tunda kika shigo daman fuskarki ta nuna akwai labari me dadi”.
“Ki bari kedai, bana dai Allah ya taimake mu, mun yarda kwallon magwaro mun huta da
quda” ta fada tana washe baki,
“Toh fa ban gane ba wane wane gwallon mangwaron aka yar?” Dada ta fada tana gyara
zama.
“Bashir mana Allah ya rabashi da alaqaqai an sakar mana kurwar Da m ya saki
Asma’u”.
Kamar saukar Aradu haka su Dada sukaji maganar, seda ta kalli dakin Alhajin su
Bashir tana fatan ace bacci yakeyi dan da ta san zancen da Addah tazo dashi kenan
bazata bari suyi shi anan ba, cikin qasa da murya tace
“Addah wannan wace irin magana ce babu dadin ji haka shi Bashir din ne ya gaya miki
ko wa?”
Addah kuwa qara gyara zamanta tayi ta ware murya tace “Ke dagaske fa dazun nan ya
kira Amirah yace ta shirya jibi zata tafi dan ya saki Asma’u kinga baya zauna gida
babu mace ba kai Naziru be gaya maka ka siya mata tikiti bane” ta qarasa tana
kallon Naziru da yayi mutuwar tsaye.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Hasbunallahu wani’imal wakeel Amma Bashir Amma
Bashir kai Jama’a wannan abu da me yayi kama” Dada ta kwashi salallami tana juya
hannu hankalinta idan yayi dubu ya tashi, se Addah ta saki baki tana kallonta tace
“Ke ban gane ba, murnar ce tasa kika rasa abin fada ko kuwa tunda dai naga wannan
ai abinda muka dade muna buri ne ko yanzu Allah ya tabbatar mana, kin gani ma yanzu
naje na karbo abubuwa. Wannan Mantau ne yanda tunaninsa ze shafe baze ma tuna da
wata Ma’u ba, wannan kuma kafine da Mallaka na ita Amiran dan kin san ba haqura fa
Asma’un nan zata yi ba yanzu se kiji zata dawo tunda bamu san saki nawa ya mata ba
Allah ma dai yasa uku ne muga ta tsiya”.
Dada dai ba bakij magana, ga tashin hankalin saki da akace an yi ga wannan barbada
da Addah takeyi ta tabbatar duk a kunnen Alhaji Amadu, ita kuwa Addah ta gama su
badadinta ta saka Fainusa da duk jikinta itama yayi sanyi zubo mata abinci.
Ta tabbatar Alhakin abinda su Dadan suke yiwa Asma’u ne Allah ya ke rama mata
akanta gashi nan tana zaune kusan shekara biyar a gida bayan da kishiya taci ubanta
sannan aka sakota, dakyar yanzu ta samu wani suka daidaita gashi yanzu wannan ta
kuma bullowa qila akanta zasu sake ganin wata sakayyar ita dai tsakaninta da wannan
Addah se Allah ya isa kawai.
Ayi maneji kafin zuwa dare in sha Allah 🙏🙏
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 41
Addah tana cin abincinta tana sake gayawa Dada da tayi zugudi yanda za'ayi. Da
tasan halin da Dadan take ciki a sannan ma da tayi shiru tuntuni. Seda ta kwashe
abincinta tas tayi gyasa kafinta dauraye hannunta tana cewa
"Kinga kirashi muji zancen sakin nan da kunnen mu karma qarya shegiyar yarinyar can
takeyi kinsan fa daman ta iya ta, qilan dan fada sukayi kar mu gama murna muji
sabon labari".
"Nidai Addah da kin tashi kinje gida kawai daga baya mayi magana" Dada ta fada tana
waiwayen dakin Alhajin su Bashir daidai lokacin kuwa ya turo kekensa ya fito daga
dakin.
Fuskarsa ba yabo ba fallasa suka gaisa da Addah, ba tareda ya ko kalli inda Dada
take ba ya kira Naziru daya kafe a guri daya kaman gunki yace ya kaishi waje.
A qofar gidan kuwa bayan Naziru ya ajiye a gurin da yake zama suyi hira da mutanen
sa se ya kalli Nazirun yana murmushi yace
"Kaji abinda uwarku da yar uwarta suka aikata ko? Ni sam ba wannan Nafisan na aura
ba ban kuma san lokacin data zama me son kanta da son zuciya irin haka ba. Amma
shikenan, suma ai sun haifa".
"Kayi haquri Baba" Naziru ya fada,
"Kai zan bawa haquri ai Naziru ku da Allah ya jarraba da uwa mara tunani, kuyita
Addu'a Allah ya tsare ku da fadawa hali irin wanda dan uwanku yake ciki dukda shi
da kansa ya jefa kansa ba wani ya aike shi ba, idan kuwa harta tabbata Bashir ya
rabu da yarinyar nan, hmmm Allah dai ya rufa asiri" Baba ya fada yana zaro kudi a
aljihunsa ya miqawa Naziru yace
"Karbomin katin Mtn na kirashi naji, wayata babu kudi".
"Bari na tura maka ta Banki Baba" Naziru ya fada sannan yayi masa transfer katin ya
danna wayar Bashir.
BASHIR
Se da gabansa ya fadi da yaga kiran Alhajin su dan muddin ba abu me matuqar
muhimmanci ba Alhajin baya kiransa sedai shi Bashir din ya kirashi.
Yasan kiran baze rasa nasaba da maganar sa da Ma'u ba labari yaje musu kuma wannan
yarinyar ce zata fada dan se daga baya ma ya shiga dana sanin me yasa ya gaya mata?
Dukda ko ba yanzu ba ai dole zasuji amma qila se kafin sannan ya gama daidaita
komai.
Be daga ba seda wayar ta katse yabi bayan kiran a ransa yana shirya abinda ze fada
masa.
"Barka da Rana Baba" Bashir ya fada bayan da Alhajin ya daga wayar, se ya mayar
masa da cewa
"Barka dai Muhammadu ya aikin ya iyali?"
"Duk suna lafiya Baba, muna cikin aiki ne ma yanzu idan ba damuwa zuwa anjima idan
muka fita sallah sena kira" Bashir ya fada yana goge zufar da tafin hannunsa yayi a
jikin rigarsa, Allah yasa ba wannan maganar Baban ya bugo suyi ba dan besan me zece
masa ba
"Ai maganar tawa gajeriya ce tambaya daya ce zan maka seka ci gaba da aikinka, shin
dagaske ne ka saki Asma'u?" Maganar Baban tayi masa dirar mikiya nan da nan ya fara
in ina kamar wani sabon kurma duk yabi ya rude, dakatar dashi Baban yayi da cewa
"Nutsu mana Malam Bashari tambaya ce fa me amsa da Eh ko Aa amma duk ka rikice
kamar wanda Alqali ya titsiye, kaga aiki kakeyi ka amsamin na kashe wayata
shikenan".
Yanda yayi maganar a dake ya tabbatar wa da Bashir ba a cikin lokacin wasa yake ba,
dan haka dole ya kama kansa kamar qaramin yaro yace
"Eh Amma..."
"Riqe bayaninka ai ka amsamin, yanzu dai ina so naji ka tuna rabar daka zo mun da
zancen zaka auri yar gurin Fattu abinda na gaya maka?"
Shiru Bashir yayi ya rasa ma wani abu ne ya dabaibayeshi,
"Dakai nake magana kayi shiru fa Bashir" Baban ya daka masa tsawar data sakashi
magana babu shiri yace
"Na tuna Baba"
"Me nace maka?"
"Ka tambayeni dole akayi mun nace maka Aa ra'ayin kaina ne, sannan ka sake
tambayata me Asma'u tayi mun nace maka babu komai"
"Daga nan kuma fa?"
"Ka gayamun cewa Asma'u matar rufin Asirice kuma mayafi ce data lullube ni, idan
kishiya zan yi mata naje na nemo yar gidan mutunchi wadda tasan qimar kanta na
hadasu amma na kafe nace ni Amirah nake so".
"Ba shakka kafiya tayi amfani. Tun ba'aje ko ina ba ta rabaka da uwar gidanka uwar
yayanka shida ko, to ka dai bi a sannu Bashir idan bakayi sa'a ba duniya da kanta
zata koya maka karatun da ka kasa ganewa, seka zubda hawaye a lokacin da babu
amfanin da zasuyi maka, ita matar fari komai mugun halin ta tana cin wannan darajar
ta kasancewarta tushiya bare kai da Allah ya datar dakai da samu mace ta gari yar
gidan mutunchi shine kaga ta wannan hanyar zaka gode masa ba madallah, gaka ga
Fattu nan da yarta sun isheka bada misali a gaba" yana gama fadar haka ya kashe
wayarsa.
Sosai yake jin baqin ciki da takaicin abinda Bashir ya aikata, me yasa tun a
lokacin da Asma'u ta nuna bazata zauna dashi ba be goya mata baya ta barshi tun a
sannan ba? Daya san haka zata faru a gaba da koda qarfin tuwa se Bashir ya bata
takardarta a lokacin da ita da kanta ta buqata amma ba'a tara sani da ikon Allah,
shi yanzu da wane ido ze kalli yarinyar da Ahalinta.
Wayarsa ya shiga lalubawa ya shiga neman Number Alhaji Qarami dan a yanzu shine
matsayin uban Asma'u, cikin Sa'a ya samita kuwa ya dannan masa kira.
Cikin mutun taka suka gaisa kafin suka shiga jimamin abinda ya faru kafin yace ya
turo masa da Number Goggo ze kirata da kansa tunda Alhajin yace bata sani ba.
Suna gama wayar kuwa ya tura masa dan shikansa yana ta taraddadin ta yanda ze sanar
mata da wannan labari a irin yanda ta daukaki Bashir kamar dan data haifa.
Cikin sa'a Alhaji Amadu yana kiran Goggo ta daga wayar, bata da lambar ya sani dan
haka yayi mata bayanin shine nan suka sake gaisawa tana tambayarsa jiki da su Dada
ya amsa da duka lafiya kafin suka yi shiru.
"Hajia abu ne mara dadi ya faru amma ina so dukka muyarda da komai muka gani a
rayuwa muqaddari ne daga ubangiji ya na yin abinda yaso a kuma sanda yaso" Alhaji
Amadu ya fada bayan daya katse masu shirun.
Goggo cikin rashin fahimtar inda zancen sa ya dosa dukda tasan dai baze wuce akan
Asma'u ba dan haka tace masa
"Amma Alhaji meya faru ne ban gane maganar da kake yi ba".
"Kiyi haquri Hajia kuma ki fahimceni, magana ce akan Asma'u da Bashir, kinsan da
aure da mutuwa da haihuwa lokaci ne dasu kuma idan Allah ya saukar dasu babu wani
abu da ya isa ya canza faruwar hakan to a wannan gabar ma Allah ya saukar da ikonsa
ya kawo qashen wa'adin zama tsakanin Asma'u da Bashir".
Salati Goggo ta kwaso ta dire, cike da jimami tace "Yanzu yarinyar nan seda ta
kashe auran hankalin ta ya kwanta wai me Asma'u take nema ne a rayuwa? Yarinya ace
zuciyarta babu salama shekaru kusan uku da yin abun nan na zata ta haqura komai ya
wuce ashe ita akwai abinda take qulla kai Jama'a wadannan yara namu Allah dai kayi
musu Albarka".
"Sam wallahi Hajia ba laifin Asma'u bane, bama tun yanzu ba tun tuni duk abinda ya
faru ita akayiwa laifi kuma aka danneta aka sakata yin biyayyar dole saboda ita an
isa da ita.
Shi Bashir din ne dai daman gaban kansa yake yi a komai to yanzu ma ya sake nuna
mana ya isa da kansa ya isa yanke hukunci babu shawarar kowa yayi saki ba tareda
sanin mu ba be kuma gaya mun ba se matar sa ya gayawa yanzu na tsinci zancen a
bakin yar uwar tasa na kirashi kuma a waya ya tabbatar mun da haka akayi,
Dan girman Allah kiyi haquri, munyi magana da Alhaji Tukur yace mun baki sani ba
saboda sun rasa ta yanda zasu gaya miki wannan al'amari shiyasa nace ni bari na
kiraki da kaina na sanar dake Bashir be kyauta mana ba be kuma kyuatawa kansa ba.
Idan Bashir yana da hankali ko dan irin qaunar da kika nuna masa kika fifita
farincikin sa akan na yar da kika haifa wallahi ko zaginsa Asma'u takeyi yaci ace
taci wannan darajar ya daga mata qafa ballantana na tabbatar da ko kallon banza
bazatayi masa ba".
"Karka yi saurin yanke hukunci cewa laifinsa ne Alhaji ita kanta Ma'u yarinya ce me
naci da kafiya, wanda yake zaune da ita ne kadai yake gane halin ta tsakanin mace
da mijinta kuma se Allah, Allah kadai yasan irin quntatawa da baqin halin da take
masa" Goggo ta katse shi a sanyaye dan abin ya dake ta kwarai, Me Ma'u tayi wa
Bashir har haka da yayi zafi ya sake ta.
"Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri" Goggo ta fada bayan dogon ban haquri da
Alhajin ya sake yi mata, haka suka ajiye waya jikinta gaba daya ya mutu,
"Allah sarki Ma'u ita kuma tata Jarabawar kenan akan abinda take so".
Alhaji Amadu kuwa bayan ya gama wayar sa yasa wani saurayi Abokin Naziru da ya zo
wucewa ya turashi zuwa cikin gida, har sannan suna zaune a tsakar gidan Addah na
zuba masifa da besan ko akan me takeyi ba, haka ya gungura kekensa ya shige daki ko
a fuska be nuna musu yasan me akayi ba ya kuma qudurce baze taba yiwa Nafi maganar
ba koda kuwa ita ta kawo kanta da kanta, ze ci gaba da Addu'a Allah ya raya shi ya
kai lokacin da zasu girbi abinda suka shuka, a rabar ne ze silleta tas ya yada mata
da maganganun da suka dade suna ci masa zuciya.
BASHIR
Suna ajiye waya da gaba daya ji yayi rasa me yake yi masa dadi a rayuwa. Har a
yanzu shi bega abinda yayi ba ya kuma san babu me fahimtarsa adan an tashi kowa
bayan Ma'u zebi baza'a duba martabarsa ta matsayin mijinta da ita take takewa ba.
Babu abinda yafi daga masa hankali da a kullum Alhaji yake maimaita masa watarana
se yayi kuka da idonsa akan Amirah wannan ai baki yake yi masa kawai kuma ita
Amiran nan fa ba irin wadda ya sani a baya bace yanzu ta chanza ta gyara duk wasu
halayenta marasa kyau da ake gani a baya ita kuma Ma'un da akewa kallon ta kirki
yanzu ita ce take masa abinda baya so.
koma dai menene aikin gama ya gama saki dai ya rigada ya furta dukda yanzu dai
yaga yayi zari da yayi mata saki har biyu dan daya ya kamata yayi na gargadi amma
dai ba matsala,
ze cigaba da lissafi se ya rage wata daya ta gama Iddah sannan ze ce ya mayar da
ita, Dukda yasan tabbas zeji jiki na rashin Ma'u a kusa dashi abinda be taba koda
mafarkin faruwarsa a rayuwar su ba amma ita ta janyo musu haka, daga ita har shi
dole su shiga gararin rayuwa kafin komai ya daidaita dan ta wannan hanyar ce kadai
ze horata ta yanda gaba ko ance ta sake musa masa magana bazatayi ba bare har ya
bata unarni taqi bi.
Haka ya ringa saqa da warwara har lokacin tashinsa aiki yayi, yasan yanzu yara sun
koma gida, ze barsu daga nan zuwa Jibi Amirah tazo dan ko ya dakko su yanzu baze
iya musu hidimar da suke da buqata ba dole se mace dan haka dai ze ci gaba da ja
har zuwa sannan dan idan yayi shiru kar ta dauka ze bar mata yaran ne.
ASMA'U
Ganin har magriba tayi Bashir bezo da wani tashin hankali ba yasa hankalin tavya
dan kwanta tayi tunanin ko ya haqura ya sakar mata ragamar yaran ne tunda taji
sunce ya dawo harma su Ahmad sunje gidan ya basu Chocolate.
Bayan Isha tana zaune wayarta tayi qara, shareta tayi dan ta gaji da amsa waya.
kamar wutar daji labarin mutuwar auranta ya karade Gombe se kiranta akeyi ana mata
jaje ta rasa ta bakin wa maganar ta fita amma bata raba daya biyu Bashir ya gayawa
matarsa, ko yan uwansa su kuma suka kwaza a duniya daman mutane kuma masu jiran
qiris nan da nan labari ya zagaya.
Har wayar ta qaraci qararta bata ko duba ba can sega Amna ta fito daga daki da
wayarta a hannu ta miqa mata tana cewa
"Goggo ce tace ta kiraki baki dauka ba".
Karbar wayar tayi ta saka a kunnenta kawai