Author : FASMA Category : African Stories & Novels
mishi tambaya
Seda gabanshi ya tsinke amma se mazge Nan ma yace aa
Shikenan Allah ya sauwake amma yaushe ne tafiyan naka??
Gobe nakeson ficewa har na ciri ticket ammafa ko su me martaba ban sanar musu ba...
Tab kanada aiki kaida Fulani yau kenan ,ka sani sarai batason zammanka acan dande
kawai ba yanda ta iyane amma shine se ana gobe tafiyar zaka sanar mata.
......
Kaide bari aboki ni kaina tsoro ne yahanani fada amma zansan yanda zan bullo
mata...
Duna gama hirar ya nufi bangaren Fulani cike da zullumi ...
Tana waya ya tadda ita koda ya kashe kunne se ya gane da Maysam take wayar kuma da
alama kuka take Fulani na aikin lallashi...
Tuni yaji ba dadi jikinshi ya sanyi shikam duk wani zafin ranshi da nuna
shariyarshi akan abu baya iyayi akan abunda ya shafeta ..
So tari beson don meyasa yakeson yi mata muguntar ma akan abunda be kai ya kawo
ba ..da wanine kowata da tuni ya bada umarni an horar dashi ......
Karbar wayar yayi daga hannun Fulani ya kara a kunnenshi ...
Kukan shagwaba kawai Maysam ke xubawa ita ta gaji tayi kewarsu iya gaskiya a
medota gida...
Kiran sunanta kade yayi yasa tayi tsit kamar ruwa ya cinyeta dan tagane me
maganar ..
Shiru ya biyo baya can yace waike wace irice baki iya gaisuwa bane mtsss yayi tsuka
A memakon ta gaisheshi setace to ai baka bani umarnin magana bane..
Kut ya fada ni kike fadawa haka??
Shiru ta sake yi mishi
A bunda ya kular dashi yaceto wly kiji da kyau keda dawowa gida se nan da shekara
idan kunyi hutun karshe banyarda kidawo ba ehe ..kuma wly kika sake kika ki yin
karatun yanda ya dace ummm ni kade nasa irin horan da zan baki dan bazanyi asarar
kudi ba ke inbaki zo ta daya ba wly kada ma kisake ki dawo gidan nan kiyi zamaki
can .. ...
Mi Maysam zatayi inba kuka ba. Sosai ta cika mishi kunne da taratsi harseda ya
kauda wayar daga kunnenshi ...
Yana medawa kuwa ya zunkud'amata wata xungureriyar tsawa yace "Ferme moi ta bouche
idiote" kawai a kanki aka fara school ne da zaki damu mutane ...dama shi
tallak.....
Da sauri Fulani ta wabce wayar ta shiga lallashi ganin ze baro mata aiki da kyar ta
lallabata ta kashe wayar ..
Ta kalleshi da niyar balbaleshi da fada amma ganin idon har sun kada sunyi ja
saboda bacin rai yasa tasoma yi mishi nasiha da yayi hakuri da duniya wannan yawan
fushin nashi baze kareshi da komi ba ...tace shin wai kai baka tawwakali ne ..??
baka karban kaddara ne??
Da sauri ya dago kai yace inayi mana Momy..
Bana tunanin haka Dan da kanayi da kayi da dadewa...shekara nawa da rasuwarta amma
ka kasa sakin ranka kayi rayuwarka yanda ya kamata ...addu arka take bukata amma
bawai da dauki bakin hali ka saka a ranka ba....
A da bahaka kakeba kowa yana yabon halinka jama a na sonka dan kyautata musu da
kakeyi amma yanzu gaba daya ka cusa musu tsoranka a xukatansu ....ma aikatan gidan
nan kama daga bayi dogarai kowa yana tsoran hada hanya dakai...dan gudun horan ka
me tsanani ..shin a haka kake ganin wata rana jama a zasu soka a matsayin
sarkinsu...
Ka canza halinka ka dawo yanda kake kamarda...
Wani kukane yakubce mishi yakuwa zube kasa tare da daura kanshi bisa cinyarta ya
dafe Dede saitin zuciyarshi yana fadin ki yafeni Momy ni kaina na kasa sarrafa
zuciyana ne amma zanyi kokari ki tayani da addu a...zuciyar shi har wani zogi take
mishi
Farin ciki fal zuciyarta
Ta shafa kanshi tace Allah ya shige mana gaba
Ameen ya furta
Ya jima haka sannan ya fara sauke ajiyar zuciya akai2 har ya dawo nml
Nan ya sanarwa Fulani zancen tafiyarshi gobe..amma gamamakinshi se yaga bata nuna
damuwar ta ba se nasiha data qara yi mishi ta dora dacewa yanzu de kai magidan ci
ne dan haka zancen ka tafi kayi zamanka kamarda se lokacin dakoso zowa ma be taso
ba .. haka suka yi ta hirarsu har lokacin sallar magarib yayi ya fice..
A bangaren Maysam kuwa ba karamin kuka tayi ba jin muryar fulani datayi se kuma
gigan nata ya fado mata a rai nan ta lalaci cikin gogin tunanin shi...can kuma tayi
kwafa kamar yana gabanta tace kadeji dashi mutum bashida aiki se zallar
mugunta.haka tayi ta tunanin shi
Wajejen goma na dare ya shiga wajen memartaba sanin adede wannan lokaci to babu
kowa a fadar daga sarki se matanshi dan wannan lokacin iyalanshine
Su biyu kawai ya tarar daga sarki se Madina ..zama yayi ya kwashi gaisuwa sannan ya
sanar musu tafiyarshi sarki ya mishi fatan alheri tare da nasiha.."
Madina ma cike da iya bariki take mishi nasiha wai annan itama ta iya
makirci...amma idan zaka bude xuciyar farin ciki ne fal har shokyn dadi zuciyar
keyi lol..
Nan yayi musu sallama ya fice...
Zo kaga murna wajen Madina har ta kagu tabar wajen me martabar se kawai ta sulale
se dariyar mugunta take..
Haka kuwa akayi seda suka bari dare ya raba waziri yayi turaren a dede kofar dakin
Murad bayan sun tabbatar dayana ciki a cewar su yana fitowa se bin duniya...
A bangaren Murad kuwa bayan yayi komi na al adarshi kamar yanda yasaba se hau gado
amma me tunanin Maysam ya gama cika mishi zuciya daya rutse ido ze dinga jin
kukanta na dazu..banda juyi babu abunda yake tsaki kam da ina kirgawa da rubutawa
da nayi read more 3 lol..
Ganin babu bacci a idanunshi yasa ya doro alwala ya dinga jero nafilfili ...se
wajejen 3 da rabi barawo ya saceshi wanda ya haddasa mishi makarar sallar
asuba ..se karfe shida ya bude idonshi da gudu ya fada tolet yayi wanka tare da
doro alwala yayi sallah..dayake tara jirginsu ze daga se ya fara shirye2n shi..7 da
rabi ya gama tsaf ya jawo jakar kayanshi ya fito ...
Yana ketara kofar dakin wata irin juya ta kwasheshi kan kace mi har ya kai
kasa....ga wani irin ciwan kai daya far me da sauri ya fara ambaton sunan Allah
kadan2 ciwon ya lafa komiya dawo nml amma me gaba daya yaji garin ya fice me a
rai burinshi kawai yaji a wani gari ko wata kasa..
Da sauri yana kayanshi ya fice atsetse yayiwa Fulani bankwana a cewarshi yayi
latti kada ya rasa jirgin
A jikinta takeji kamar kar ya tafi..kamar ta hanashi tafiyar nan
Yana shiga mota driver yaja suka fice a masarautar
Madina da waziri dasuke tsaye suna kallon komi da alamade maganu yaci dan waziri ya
ga har sanda ya tsallaka da yanda juya ta kwasheshi
Madina ta shiga waka kamar haka Mun rabu dakai.....
Mun yi nisa da kai
abadan damu dakai se a lahira💃
Waziri yace wanna haka yake....
FASMA CE✍
Ahmed Gumel
[8/31, 9:55 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[8/31, 9:56 AM] A A Dboy: SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
**Dubun gaisuwa zuwa ga fans din wannan littafi hakika ina alfahari da ku da irin
so da.kauna da kuke nunan .......* **Daya wa daga cikin ku naga sakon nin ku in sha
Allah zakuga* *canji....ina love dinku irin totaly and completly din nan lol*
_Ina ma abota Son karanta novels masu ma'ana ,fad'akarwa nishada'ntar
wa ,etc ...ina me farin ciki gaiyatar ku da ku biyo writers na kungiyar_ *STAR
WRITER' ASS* ... _mun sake fito muku da news novels kamar su_
*NIDA KAWATA &UWAR RUKO part2* _na Momyn Mufeeda_ 😍,
_Da kuma_
*KALAR TAWA UWAR & KARSHEN ALEWA KASA* _na Mimsqueen_ 💋
_Ga kuma_
*MEERAH* _na in law dina Xaynab(queenbaby👸)_
*AMEEMAH &DAJIN SOYYAYA* __na Hadjara (Arfat ba😘)_
_Se kuma_ *SALMAH* _na Usman(miss you a lot❣)_
__Fans Kada ku bari a baku labari dan gaskiya novels din sun had'u masu_ _iya
magana sukace da abaka labari gwanda ka bada......._
*Ina alfahari da ku yan kungiyar Stars Allah ya kara hada kanmu irin éternity din
nan_ 😁*
_Je vous ai pas oubliées mes sis d'amour Maman Haneep..Maman
Shurem...Zainab.Sarah...,Ramatou_ _and my namesake Fatima municipale... Ina kaunar
ku irin sosai din nan..Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa.dama wa dinda ma ba
ambata ba kuna raina_
Dedicated to all my fans😍❤
43__44
```
Manzon Allah (SAW ) ya ce :''me yanke zumunta baya shiga Aljanna ''
Bukhari ya rawaito shi
```
Yana shiga motar driver yaja suka fice daga masarauta direct aéroport (hilin
jirgi)suka tafi zuwan shi keda wuya jirgin su ya daga kamar daman shi kade ake
jira...Mahmud ma tsetseye sukayi sallama dashi anan har yake tambayarshi ko se
yaushe ze dawo amma budar bakin shi ya ce ba rana ...... ..
🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹
Madina da waziri da suke tsaye suna kallon komi da alama de maganin su ya ci dan
waziri yaga har lokacin da Murad ya tsalaka da yanda juya ta kwasheshi...
Madina ta kwashe da wata arniyar dariya ta shiga waka kamar haka
mun rabu dakai...
Munyi nisa dakai
Abadan damun dakai se a lahira💃
Waziri yayi dariya yace wannan haka yake ...saura shegiyar figigiyar matarshi...
Madina tace barni da karamar kwari wannan ai karamin aiki ne....
Rayuwa juyi2 yaude rayuwa ta juyo gare mu sauran kuma ogan ..shima ya kamata a
fara planning din yanda za ayi mu kaudashii.fadar waziri..kenan
Madina tayi yar dariya tace wannan ma barshi a hannuna lokaci kawai nake
jira.....kaide ka zamo kullum cikin shiriii..
Ba damuwa ai ni akowani lokaci a shirye na ke ..keni ko yanzu hakama...
Shikenan da zarar na shirya komi zakaji ni. ...
Nan waziri ya daga waya ya kirayi Murza ya sanar mata ...
Murza dake gadon asibiti tuni farin ciki ya cikata har bata san lokacin da wata
makirar dariya ta subce mata wanda yayi Sanadin tashi M.Musa daga bacci ..ya
kalleta ya girgiza kai .....Itamade kashe wayar tayi tare da yin kwafa
A ranta kuwa fadi take dadi kasheni ..Maysam wannan karan sena zamo ajalin ki..
(kuji fa🙄.)
A bangaren fulani kuwa da sauri ta daga waya a nufin ta kirayi Murad kan ya fasa
tafiyar amma ina baa ta shiga tayi kiran yafi a kirga dole ta hakura ta bishi da
addu'a...
Shikuwa Murad gaba daya ya rasa abunda yake mishi dadi nan ya jingina da kujerar
jirgin ai kuwa se bacci yayi awon gaba dashi... Be farka ba seda suka isa birnin
ENGLAND..shi kanshi yayi mamakin wannan bacci da yayi kuma ga wani irin ciwo da
kanshi yake yi ..hakade ya lallab'a ya shiga taxi ya na isa gida yanemi magani
yasha kuma wani sabon bacci ya sake daukeshi ...wunin ranar de a bacci ya kareshi
ganin abun bana karewa bane yasa ya daga waya ya kirayi wani abokin aikinshi me
sunan MARK kuma daman shike kula dashi idan ciwon zuciyan shi ya tashi.....
Be wani dauki lokaci ba yazo tare da kayen aikin shi...yayi yan gwaje 2
shi .....can ya bashi maganun nuka ya sha .....ya kaleshi yace haba Murad kamar ba
Docteur ba zaka bari ciwon ka ya tashi har haka koma ka sani sare irin
conséquence din daze biyo baya in har ba'yi intervenir da gagawa ba.....idan ma
wani abun ne yayi Sanadin tashinshi to ina baka shawarar idan akwai yuyuwar ka
mallakeshi to kayi gaggawa inko ba hakaba ka dangana dashi amma fa zakasha wuya ko
kuma ma yayi sanadiyar zama ajalinka...
Murad yayi karfin halin yin dariya yace bazaka gane ba ..tunda de yanzu ganinan ai
se kayi abunda ya dace.. A ranshi yace abun dama mallaki nane kawai de bazan so
naci amanar my sweetbabyna ba(🙄kaide kasani iya kacinta de in lokacinka yayi ka mutu
mu kuma musha gumba da nono atoo....,😎.)
Ya rurubuta mishi magani .sanan yace tode a iya bincike na baccika bashida nasaba
da ciwonka mayebe gajiyace ....daga nan ya mishi sallama akan ze tafi siyo maganin
da kuma dan abinci dazeci
Gyada kanshi yayi tare da mishi godiya ........
Washe gari kam ras ya tashi har ya tafi wurin aikin shi sede zuciyarshi bata dena
yime zogi ba ..aiki ya tarar ba kadan ba.yinin ranar kaf a aiki yayishi se gab da
magrib yakoma gida ...bayan yayi isha'i ya dauko wayarshi se alokacin ya ganta ashe
a kashe take...yana kuwa kunnawa kiran fulani ya shigo ..
Da sauri ya daga ya gaïda ta tare da jero mata ban hakuri ..
Daga can fulani tayi dariya tace shikenan ya huce da fatan ka isa lafiya ...
Nan suka dan taba hira tace wai ni shi ko ka sanar da Maysam tafiyarka ?
Seda gabanshi ya fadi shi sunan ta kade ma in yaji se gabanshi ya fadi bare yaji
muryarta ko kuma ya ganta...gaba daya se yaga kamar yar kanwarshi ya daure de yace
to ai Momy batada waya ..
Amma kasan baka kyauta ba ko ko batada waya ai seka biya ta Maradin kayi mata
bankwana ko..to yanzu de ba wanan ba ka kirayi offishin makarantar sesu bata ..
To kawai yace amma fa badan ze kira din ba....nan tayi mishi sallama tare da
jaddada mishi ya kirayi Maysam din..kuma zata kira taji ko yayi ....
Yayi kicin'2 da fuska shifa gani yake Momy ta takura mishi .... babu yanda ya iya
bayan ya kirayi Mai martaba hakade ya kirayi makarantar dayake sun sanshi farin
sani koda ya basu sani ya nemi zeyi magana da Maysam ba a wani bata lokaci ba aka
kirata....
Tana ansar wayar bata tsaya taji me kiran ba tace ina wuni Momy ya gida?
ya.. ....cak ya tseda ita yace ke wai bakida hankali ne bakiji me kiraba kawai ki
kama zuba zance yaja tsuka..mtssss...
Shiru tayi can tace kayi hakuri ban san kaine ba..ina wuni..
Se kuma jikinshi yayi sanyi yace lafiya ....yace da fatan de kina karatu dan walahi
kinji na rantse idan har baki zo ta daya ba to kada ki kuskura ki dawo gida
hutu ...
Tace to..a ranta kuma tace daga kira se masifa
Yace kuma badan kinga na koma ba kice zakiyi abunda kikaga dama zansa a dinga
fadamin duk wani motsinki da kamaki da laifi daya sekin raina kanki
Nan ma tace to(a ranta tace kenan ma baya kasar tayi kwafa)
Nan de yayita banbaminshi
Ita kuma komi se tace to ...
Ya kari fadace2n shi ya kashe wayar ...
Maysam ta koma aji amma tunanin fadan Murad ne fal ranta ....tace waishi baya
gajiya da yiwa mutum fada ne ....komi shi se yayi fada da mugunta ciki........tana
shiga aji ta tatara komi ta watsar tacigaba da karatun ta.....
A bangaren Murad kuwa yana kashe wayar ya dafe zuciyarshi da hannu saboda wani irin
zogi da take mishi ...ya daga waya ya kirayi docteur Mark tun yana daukan abun wasa
har ya fara ganin dishi2 .kan kace mi tuni ya zube nan kasa .........Mark na
shigowa ya tarar da shi cikin wannan halin dataimakon wani abokin aikinshi dayake
su biyu sukazo...suka ciccibe shi sukasa a mota suka nufi hospital dashi ...kafin
su isa tuni ya sume...direct emergency aka shiga dashi.......
Ta fa fans muje zuwade....
Nikuwa nace amma su waziri sunyi aikin banza da suka tsaya a barin masarauta da ai
se susa a shiga tsakaninshi da har mazauna a cikin masarautar tundade gashi ya bar
garin amma kuma ya ci gaba da mu'amalal shi da parents dinshi..amma a ganina fa🙃
Fasma ce🖊
Ahmed Gumel
[8/31, 9:56 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 9:49 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
45__46
```Manzon Allah (SAW)ya ce''duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce''
Muslim ne ya rawaito shi
```
Kafin su isa tuni har ya sume ...direct emercency a ka shi ga dashi ..
Nan docteurs suka duqufa dan ceto rayuwarshi a bunka da turai kayan aiki birjik dan
haka kan kace mi cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo normal ....amma fa idanun
sa a rufe da alama bacci yake.....Be farka ba seda ya kwana yayi rabin wuni har
wata rama yayi ta kwana daya .......Mark na zaune kusa da shi da yake shi ke
jinyarshi ya ga bakin shi ya na dan motsawa kamar me sonyi magana ga kuma idon shi
a rufe suke...
Kusanto kunnenshi yayi dede bakin se yaji Murad na ambatan sunan Maysam....
Maysam...
Cike da mamaki Mark ya dago kai yana kallon Murad dake kwance yace Maysam?to
ko.....
Kafin ya gama tunanin Murad ya fara bude idanunshi Tar ya bude shi se akan
Mark ..yayi karfin halin yin dariya ..
Mark ya kamashi ya kaishi tolet yayi wanka tare da doro alwala ..........yana zuwa
ya saka jallabiya ya kabarta sallolin da ake binshi bayan ya gama Mark ya gabatar
mishi da abinci ....kadan yaci shima dan ya samu ya kama karfin jikinshi ....
yana tsakada ci . Mark ya kalleshi ya ce .....waccece Maysam ???
Tambayar a bazata tazo mishi dan kuwa har seda ya kware .....
Mark ya tsiyayi ruwa yabashi
Da tarin ya lafa yace Maysam kuma ....''.non je ne la connaît pas ''...(ka ban
santa ba)
Mark yayi dariyar gefen baki yace shikenan idan baka santa ba amma ka sani sunan
dakayi ta kira kenan ......
Ya mutsa fuska yayi yace nide ban santa ba ..ya kauda fuskar shi...
Mark yace bazan tambayeka abunda ya tado maka ciwon ba amma abunda zance maka kayi
gaggawar mallakar ko hakura dashi dan kuwa idan ka bari zuciyar ka ta sake bugawa
kamar yanda tayi jiya tofa the best solution se amma ka opération kuma kasan irin
''risque''(hatsari) din dake cikin opération....
Gyad'a kai kawai yayi amma badan ze iyaba dan ko yanzu dayaji sunna ta seda yaji
wani zogi a zuciyar shi ....shi yasa tsanar yarinyar yake kara yawa a
zuciyarshi.......
kwanan shi ukku aka sake shi ya dawo gida ....ran na hudun ma ya koma aikin shi duk
duk dade be wani kama karfin jikinji kamar da ba...
. .
.Abangaren Maysam kuwa karatu take ka'in da na'in ba kama hannu yaro ......dayake
kuma ta hadu da masu son karatu Mufeedah da Mariyam ga kuma ilimi ..duk inda bata
fahim ta ba suke ganar da ita daya ke su sunyi jss1 ..a duk inda ka gansu to fa
zaka tarar suna biya karatun sune na bako ko na arabi........
Akulum kuma Maysam idan ta tuna cewa SANADIN ACCIDENT ne had'uwar su da Fulani har
ta samu gatan zuwa école ga islamiyya taci me kyau ta sha me kyau sannan ta saka me
kyau ga soyyayar uwa da Fulani ke nuna mata ...se kwai ta fashe da kuka tare yi wa
Allah godiya .su Mufeedah de se suyi ta bata baki da hakuri dan su ji suke idan ta
tuna rabuwa da yan gida ne take kukan.........
Haka de rayuwa tayi ta tafiya yau da dadi gobe akasin haka inda yau har su Maysam
suke zana exam na karshen shekara wato pass to jss1......sun dage karatu suke bana
wasa ba ..sati suka jera sunayi se kuma sati me zuwa za'a fada musu résultat se
kowa ya tafi gida hutun wata ukku......lfy lau suka gama question din kuma basu
bata wahala ba ....tsoran ta