Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin Accident Complete Hausa Novel by FASMA

Author :  FASMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 32

18K to 21K   out of 94.8K words

kade ta ne bayan sun koma kauye yaje ya sanarwa da Malam Musa ...be
wani daga hankalinshi ba yade ce Allah yabata sauki..
Washe gari wajejen goma na safe ta farka da kadan2 take bude idon ta harta bude su
ware ..dan motsa kafafunta tayi aman se taji kamar babu su ..dan danan gabanta ya
bada fat .....da sauri ta yunkura zata tashi aman ta kasa ..se kawai ta fara
ihu.....
Sega infirmieres"likitoci " sun shigo da gudu da kyar suka samu tayi shiru tace
miya kawoni nan ne.
D'aya daga cikinsu tace ina kyautata zaton Accident ne kukayi wanda ya hadasa miki
karaya har biyu a qafar dama se kuma qafar hagun da aka cire miki ita saboda gaba
daya kashishuwan wajen sun ratatake babu damar dori dole seda aka cire ta
Wani ihun kururuwa da ta saki se da ta firgita su ta dunga ihu da fuzge2 kamar
sabon kamu...
Wata nurse tace haba baiwar Allah kamata yayi kiyi hakuri kiyi hamdallah daba duka
bane aka cire miki ko kuma ma da kika rayu baki maceba
Haba ina Murza bata ma san tanayi ba ganin abun bana qarewa bane yasa suka mata
allurar bacci tukon suka samu lfy..
Se sha biyu Musa yazo likitar ..nan docteur yayi mishi bayani halin da Murza ke
ciki..
Banda girgiza kai babu abunda yake....
Ya na fitowa daga office din doctor direct chambre "daki"da Murza take ya shiga
wanda yayi dede da farkawarta ...
Ta bare baki zata fara kururuwa yace ke dakata bakida hankaline ?ko baki san nan
likita bane da akwai marasa lfy?to walahi kiji da kyau inde kika ci gaba da wannan
ihun naki to ina me tabbatar miki gidan Mahaukata zasu kaiki..
Tsit kakeji Murza tayi se wani mazurai take..
Nurse suka shigo duka dan duduba ta suka bata magani tasha ...(su Murza an zama me
kafa
daya ....)
Kafin sati ya zagayo har ta fara jin sauki ....
Labari na kaiwa ga Maysam ta kuwa bi ta tada hankalinta ta ringa rokon Fulani ta
barta taje ...
Da fari Fulani ta kiye mata ganin duka ma yaushe akayi aure harda zata fara futa
amma irin addabar tata da tayi setace shikenan jeki tambayo mijinki inhar ya barki
sekizo mutafi tare dan ban yarda da Murza ba..
Jin haka yasa Maysam ta bata rai tace haba Momy (haka itama take kiran Fulani
yanzu) miye na wani tambayyarshi kawai muyi ta fiyarmu..a zahiri kuwa tsoran zuwa
idan yake take..
Fulani tayi dan murmushi tace baki san mace bata futa seda izinin mujinta ba?..duk
macen da ta futa bada ixinin mujinta ba to tana cikin tsinuwar malaiku .ne har ta
dawo
Nan tayi tajan hankalinta....
Maysam tace shikenan bari na tambayoshi to ta fice daga palon
Fulani kuwa a ranta ba karamin dadi taji ba ganin yanda Maysam din ta dauketa kamar
mahaifiyar ta...
Seda taje bangaren nashi tsoro ya kamata nan ta fara wasisin shiga..ta jima nan se
kawai tayi shahada ta shiga..
Zaune yake bisa doguwar gujera a palon ya mak'ala ecouteur "earpiece "a kunne se
wani karkada kafa yake...
Tun lokacin data shigo fitinenen kanshinta ya sanar mishi da zuwanta amma se yayi
kamar besan da shigo warta a..
Itama tunda ta shigo kallo daya ta mishi ta kauda kai ..
Ta jima nan tsaya tana tsoran yi mishi magana tajawa kanta rankwashi dan bata manta
dana waccen ranar ba..
Ta kusa rabin awa tsaye sekuma ta samu waje ta zauna a kasa ta sada kai
Ganin haka yasa ya tashi ya zauna yace ke dabbar inace daba zakiyi sallama
ba ...kuma ki wani zo kisani gaba bako gaisuwa ke gaki ishashi ko? ...
Itade batace komi ba a ranta tace kai wannan mutumun komi zakayi baka yi mishi
dede..
Shifa yace kada na sake gaisheshi ..amman yau kuma yana fada akan gaisuwar..
Abunda ya harzukashi menan jin tayi mishi shiru ya ce ke yaki nan na tatakaki..
Maysam da shegen tsoro har kwalla ta cika mata ido ta miki ta fara tafiya kamar
hawainiya ..
Wata sangamemiyar tsawa ya daka mata. Ai kuwa bata san lokacin daya gurfana a
gabanshi ba.
Yace....
Sorry fans nida kaina nasan yanxu banayin typing me yawa kuma ina ganin korafe2 ku
banaki d'auka bane....de kuna muna uzuri ..am buzy kwana biyun nan ne..
Love you all fans irin sosai din nan
Fasma
Ahmed Gumel
[8/17, 1:50 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[8/17, 1:53 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

33__34
```Manzon Allah (SAW) ya ce""Allah ta'ala yana da sunaye casa'in da tara,wato dari
badaya,duk wanda ya haddace su, to lallai zai shiga Aljanna "
Bukhari da Muslim se suka rawaito shi.
`
Wata sangamemiyar tsawa ya daka mata ai kuwa bata san lokacin data gurfana a gaban
shiba ..
Yace ke wai mi kika d'auki kanki ne??ee..ya kuwa kai mata rankwashi a kai ze qara
mata da sauri tace yi hakuri yaya kaifa kace kada na sake yi muka magana in har
bakaine ka bada izinin haka..ba..
Wani kallo ya watsa mata yace ohoo kuma shine kika zo kikayi mun kikam kamar wani
dogari kin wani zura min ido kamar manya ya kuwa dungure mata kai yace to wai ma
miya kawokine? Iye me kama da aljanu
Baki na karkarwa muryarta har sarkewa take tace da......ma2 innata ce ba ta da
lafiya shine Momy tace nazo na tambayeka zamu tafi ganinta..
Mi kikace???Momy komi ne?? ..ya sake rankwasheta ya kama kunnenta ya murd'e harda
ciza leb'e yake dan mugunta seda ta saki d'an kara yace wannan Momy nace ni da
sweetbaby na kadai in kika kuskura kika sake kiranta da Momy tooooo yayi kwafa tare
da sake mata kunnen .. ....yace kuma ni ina ruwana da fitarki tunda ba d'aureki
nayi ba??(umm umm Murad to
)
Yaja dogon tsaki Mtsssss KE SORS DE MA MAISON VITE2
Qafafunta har hadewa suke wajen sauri ta fice a dakin seda ta fita ta sauke wata
nauyenyar ajiyar zuciya tana luliya kunnen a ranta tace shi wanna wai hannunshi
baya gajiya da mugunta ne..? Amma de kwanda shi da Murza ..
Bayan fitarta ya lula kogin tunani yace kai ya zamo dolema na koma England wajen
aikina dan kuwa inde har ina tare da yarinyar nan to kuwa seta saka tsohon ciyona
tashi ..ba damar ya tabats se yaji mass shock koda kuwa mugunta ce ze mata da zarar
fatar su ta hadu to se yaji..gwara ya tattara yanashi2 ya tafi kafin ta bullo mishi
da wani
aiki (umm su Murad manya )
tare suka tafi da Fulani lokacin Murza anji jiki duk da taji sauki amma tayi yar
rama...
Irin yanda ta dinga tarerayar Maysam ke kace ta sadudane ita ko da ga ranta tana ta
kisima abubuwa da dama ..dan har yanzu bata bar munmunan qudirinta akan Maysam ba..
Ita kuwa Maysam yarinta me dadi ganin yanda Murza take yimata yasa ta dan saki
jikinta se dadi takeji wai yau ga Murza na mata magana me dadi ba hantara harda
tafawa..
Itade Fulani kallonsu take amma bata yarda da tuban Murza ba.....
Nan kuyangi suka shishigo da kayan marmari da abinci iri2 ..
Murza har wani lashe lebe take dan kwadai taga abubuwa..
Basu jima sosai ba Fulani tace su tafi ..
Maysam badan tasoba sedan batason yiwa Fulani gaddama..
Tundaga wanna lokacin kusan kullum se Maysam tazo ganin Murza i zuwa yanzu ta saki
jikinta sosai da ita...ita kuwa Murza se dariyar mugunta take kasa2..tana fad'in
shigo2 ba zurfi shegiya me kama da aljanu..ai sena rabaki da wannan mijin zakisan
ni Murza yar bala'i ce( Allah de ya shirya)
A bangaren su Madina kuwa Lokacin da sukaji labarin Accident din da Murza tayi
waziri ya garzayo a b'oye...
Nan ta bashi kullin magani tare da gaya mishi yanda za'ayi dashi...suka kuwa sheke
da dariya kamar ba a likita suke ba...nan ya sake zube mata wasu kudin tare da
alkawarin zasu na kula da ita a boye har ta warke garau dan suci gaba da cin karen
su ba babbaka..
Lokacin da waziri ya kaiwa Madina wannan labari ba karamar mjrna tayi ba harda d'an
taka rawa tayi..
Nan suka tsara yanda zasu turara hayakin....wazi
ri yace kinsan shegen nan.akwai shi da son zuwa lambu bayan la'asar ..kinga se a
turara a hanyar..
Wani murmushi Fulani tayi tace aikin ka na kyau kaga yanzu karfe biyu kenan nanda
awa biyu komi ya kammala...shege inbe mutu ba ma to mu kawar dashi daga
masarautar..kaini dama haukatar dashi tasa akayi ..
Waziri ya washe wasu hakoranshi yace ai yanzu aka fara mu gama da wannan se musan
yanda zamuyi dashi nan gaba...
Wajejen uku na rana waziri ya turara hayakin a kofar shiga lambu sannan ya kasa ya
tsare ya hana kowa shiga. Ya zauna nan yana gadin wurin
Har lokacin isowar yarima murad tareda dogarai da kuyangi ...
Shikam waziri ya zube nan yana kwasar gaisuwa tare da zuba mishi kirarin da be kai
zuciba...
Hannu kawai yarima ya daga mishi ya sa kai ze shiga lambun
To fa fans ya kuke ganin zata kaya??asirin nan ze kama Murad kuwa??
[8/17, 1:53 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[8/17, 1:55 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

35__36
```Manzon Allah (SAW) ya ce "lallai su malamai magadan sune Annabawa ,sun gadar da
ilimi,duk wanda ya same shi ya samu babban rabo "
Bukhari ne ya rawaito shi.```
Hannu kawai yarima ya d'aga mishi yasa kai ze shiga lambum...
Amma me se kawai yaji kamar a mafarki ana kwala mishi kira seda gabanshi ya bada
ras jin wata murya me shige data babysweet dinshi na kiranshi da Yaya da sauri2
cikin zafin nama ya juyo se kawai ya ga yar qauyen nan ce Maysam wani turnikeken
bakin ciki yaji ya rufe ya kuwa d'aure fuska tumau ...
Cikin sauri dogarai da kuyangi suka zube nan suna Allah ya huci zuciyar ka yarima
dan sarki jikan sarki ...blabla dan kuwa ranshi yayi matukar baci
Itama Maysam data kula da haka se taki isawa wajenshi ta zube daga inda take tana
Allah ya huci zuciyar ka idan ranka ya bace.dama Fulani ce take neman ka yanzu..
Gadan2 ya nufota
Ai kuwa tace kafa minaci ban baki ba ta zabga da gudu se bangaren Fulani ....
Ranshi in yayi dubu ya bace kamarshi ace an aura mishi wannan yar shilar banda
shirme kauyenci yarinta babu abunda ta iya shi walahi yaga ta kanshi banda auren
dolen da aka yi mishi a memakon a samu babbar yarinya wacce tasan ciwon kanta koba
komi zata iya fidda shi kumya cikin abokanan shi se kawai a aura mishi wannan
aba... shifa yanda take gudu kamar ba Gimbiya matar yarima dan sarki ba ...mtss
yaja dogon tsaki
Harze shiga lambun se kuma ya tuna da tace Momy na nemanshi...se kawai ya juya ya
nufi bangaren Fulani fuskar nan ba annuri..
Takaici be gama kasheshi ba seda ya tarar da Maysam tayi daidaya a cinyar Momy se
kwasar firarsu suke kamar ba surukai ba ..kwafa yayi tare da zama gaishe da ita
kawai yayi ya ci kip...
Murmushi Fulani tayi tasan wannan bacin ran har da kishin Maysam data kwanta a
cinyar sa.....
Maysam kuwa da tun shigowarshi taki ta kalleshi ma bare taga irin mugun kallon
dayake watsa mata..
Fulani tace Murad2
Da sauri ya d'ago kanshi yana kallonta
Tace ya maganar karatun Maysam ne ??ka b'ullo da zancen kuma kayii shiru gashi har
kana shiryen2 tafiya ...
Dan sosa kai yayi yace tana nan Momy..
Nasan da haka inaso nasan wacce makarantar ka zab'a mata ne? ?
Shifa beyi wannan tunanin ba ....yace Momy nace ba da wai a sakata a makarantar
kwana ..
Waro ido tayi tace ban gane makarantar kwana ba...kada ma ka tada zancen nan dan me
martaba ma baze amince ba..
Maysam ma seda ta tashi ta zauna tana wuwurga ido amma jin abunda Fulani tace yasa
tasaki ajiyar zuciya ..
Murad ya marerece fuska yace haba Momy miye aibun makarantar kwana kuma fa ta nan
kusa wato ta birnin MARADI za a sakata ......idan bata ganinku zata fi zagewa tayi
karatu kuma makarantar ta Abba Mahmud ce ..
Jim Fulani tayi kamar me tunani
Da sauri yace kin kwantar da hankalin ni zan sanarwa da me martaba ...
Nan ta dan saki sukaci gaba da hirar su ..
Maysam de badan taso ba tade yi shirune kawai..
Yayi tsaye ya faki idon Momy ya zabga ma Maysam mugun kallo yace Momy a bawa
yarinyar nan tea takawo min ina b'angare na...kan tace wani abu ya fice abunshi
Seda cikinta ya bada kululu jin Fulani tace ta shiga cuisine ta d'ako tea ta kai
mishi..
Ita baza ta iya yiwa Fulani gaddama ba bare tace a 'a bazata jeba
..ba yanda ta iya haka ta d'oko ta nufi bangaren gabanta na bada fat2.....a ranta
tace yau kuma ko wace muguntar zan tarar duba da irin kallon kad'e dayake mun yau
kam seta Allah...
Ta jima nan tsaye taga tana b'atawa kanta lokaci se kawai tayi karfin hali ta
shiga. ....
A bangaren waziri kuwa ba karamin bakin ciki yaji ba ga maganin duka ya turara wai
dan ya kama Murad sosai har kwalla seda yayi saboda takaici Maysam kam ya tsine
mata yafi cikin kwando ..
Haka ya lallab'a jiki ba karfi ya tafi bangaren Madina wacce take jiranshi tun tuni
tana so taji in maganin yaci...
Nan ya labarta mata itama jitayi kamar ta mutu dan takaici tace wai wannan wace
irin jarabace haka ..amma ba komi ka saci jiki yanzu ka tafi wajen Murza inda akwai
ragowar maganin ta baka idan kuma babu to ta kwatanta maka wajen Boka se ka tafi ko
zuwa gobe ne....
Nan waziri ya saci jiki se likitar da Murza take ya koyi sa'a Malam Musa baya
nan...
Murza kam har tafisu shiga damuwa .jin wannan zance ..ta shiga tsine ma Maysam tare
da surha mata zagi da kyar . tayi mishi kwatance. wurin Bokan.. ya tafi da yar
murnar shi...
Je vous aime mes fans
Fasma
Ahmed Gumel
[8/17, 1:55 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[8/17, 1:57 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

37__38
*Ban manta dake ba yayata takai na SARAH ina alfahari dake* *Allah ya bar kauna da
zumunci ina yinki irin sosai dinnan*
*Up up up STAR .W.A hakika ina* *alfahari da ku yan kungiyar mu musamman ma*
*Antyna Momyn Mufeedah* ..
*Hadjara (Arfat)*
*Mimsqueen*
*Ummu Usmane* *(i miss you keda* )
*My in-law Queenbaby* ..
*Allah ya qara hada kammu ina kaunar irin totally dinnan* .
Dedicated to all my fans
37--38
```Manzon Allah (SAW) ya ce "ya na daga alamar kyawun musulunci mutum ya bar bin
duk wani abun da bai shafe shi ba "
Tirmizi ne ya rawaito shi.
```
A bangaren Maysam kuwa tana shiga falon da sallama a bakinta amma setaji shiru wata
hamdalah tayi tare dasakin murmushi jin dadin dabata taras dashiba isa dining tayi
ta aje mishi tea din sum2 cikin sauri tayi hanyar futa amma mi se taji yace ke zo
nan...
Dan danan dariyar jin dadin data ke ta gushe ta tsaya cak ta kasa gaba kuma taka sa
yin baya ...
wata uwar tsawa ya daka mata dan tsoro bata san lokacin data zube nan ba dan
kafafuwanta gaza daukar ta sukayi dan ta razana sosai ...da rarafe ta isa inda yake
tuni har kwalla ta cika mata ido. Tayi kalar tausayi
Se kawai yaga kamar sweetbaby shi idan tayi b'anna wato idan tayi laifi ko kuma
idan taji tsoro ....
Runtse idon shi yayi wata zuciyar tace ka tausaya mata mana ko dan tana kama da
babynka...
Wata zuciyar tace mishi a a kada ka raga mata ai dan tana kama da ita ne ma ya
kamata ka bata wahala kamar yanda take ba zuciyarka duba da tun da tashigo
rayuwarka ta tado maka da ciyon daya dade da warkewa ....beyi wata2 ba yabi umarnin
zuciyarshi ya zare belt dinshi ya zula mata daya yace wannan na qara hawa cinyar
Momy ne
seda ta gantsere saboda zafi.
Ya dadage iya karfinshi se qara mata ...
Mi Maysam zatayi da gudu ta shige jikin shi ta cukukuye shi
Wani mayan shock yaji gaba daya jikinshi ya saki yayi tagal2 suka zube bisa kujerar
palon ...
Maysam wacce tun dazu idonta ke rumtse se yanzu ta bude su jin sun zube ..
Waro idon tayi ta kama bakinta ...
Shi kuma gogan sandarewa yayi sakin baki da hanci yayi ya zuba mata ido bako
kiftawa itama Maysam din kasa janye idanunta tayi dan ta tsorata jiran hukunci
kawai take
Sun jima a haka ita tana son tserewa amma gogan ya kasa ya tsare ya riketa da
hannushi ...kuma ya fada kogin tunani.....
Mutsu2 da take ya dawo dashi da sauri ya tureta taee da hankada ta lokaci guda kuma
ya daka mata tsawa ta fice mishi a daki ..
Gaba daya ya gigita ta ..tama rasa ina ne kofar fitar seda taga ya taso ya nufo ta
cikin tsawa yake fadin "je dis sors de ma maison "
da gudu ta fice kan kace mi har ta isa bangaren Fulani se haki take ..nan kofar
palon ta tsaya tana meda numpashi seda taji normal tukon ta shiga
"heureusement"(luckily) Fulani bata palon direct room din ta tashige a ranta tayi
hamdalah da Allah ya kubutar da ita a hannunshi da taci na jaki yau ta shafa
bayanta tace nasan kila da ya qara min wata da bayan nan ya gama moruwa.....
A bangarenshi kuwa rasa abunda yake mishi dadi yayi kwata2 yarinyar nan ta haddasa
mishi fadawa tunanin babynshi a ranshi yace kai dolema na kaita school gobe2 nan ko
zanma dena ganinta kwata2...yaja dogon tsaki mtssss
Washe garin kuwa suka kama hanyar Maradin dayake tun a daren ya sanarwa Fulani da
me martaba a cewarshi wai an tsere mata a karatun dan haka gwara ta tafi kota cin
munsu
Tun adaren tashirya kayanta tsaf akwati ukku manya komi na bukata ta dauka wanda
kuwa bata da se gobe yarima ya kaita shopping .
A shopping dinma tsayawa tayi bata dauki komi ba seda taga Murad yayi mata jan ido
tukon ta dauki mai da turaruka shima bawai dan batada suba aa kawai dande tsoran
fadan yarima
Shikuma wurin kayan ci ya tafi yasa yaran wurin suna jidowa kamar madara lipton
Milo etc...komi a wadace ya saye dan Momy seda tayi mishi kashe kwakwara kafin su
fito
Haka ya biya kudin aka jida musu a motar da kuyangi duke suka fice se Maradi.
Yana tuki a ranshi yace ya akayi bega yarinyar nan ta dauki pad..wata zuciyar tace
mishi peut etre (may be) bata faraba ma..yace amma walahi angama dani (jifa to mi
ruwanka ciki kawai iyayi
)
Juyowa yayi yana kallonta ..ita kam se sharara bacci take ..besan lokacin dayace
bacci nayi miki kyau...se kuma yace to mi ruwana ciki..tsuka yaja ya cigaba da
tukinshi...(kadeji da gulmarka ehe)
Tafiyar awa ukku sukayi suka iso wani shago ya shiga ya sayo mata simkin pad din
gabad'aya...
Har llokacin bata farka ba..
Wani haushin ta ya karaji
Tana baccita me dadi cike da mafarkai masu dadi taji saukar

7 / 32