Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin Accident Complete Hausa Novel by FASMA

Author :  FASMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   25 / 32

72K to 75K   out of 94.8K words

yace miki babu wata kishiyaπŸ™„
halan baki yarda bane`)...

Be shigo gidan ba se wajejan tara da rabi dan ya biya likita sun samu wani
emergency...

Lokacin daya dawo tana wurin su Mufeedah ....sullube wa tayi ta tafi sama abunta..

Lokacin yayi wanka yana kallo a laptop dinshi . ...

Daga bayanshi tazo ta leka computer taga miye yake kallo yana murmushi ne shi kade
haka ....ai kuwa photon ta dana sweetbaby ne a screen din ..ai nan gabanta yai
wani irin mummunan faduwa ta kurawa photon sweetbabyn ido kamar tasan yarinyar take
gani.......namijin kokari tayi ta kewayo direct rufe computen tayi tace mi kake
kallon photo baya gani a zahiri kuma a gabanka ....
Jayota yayi ta fada jikinshi yace hakane to ai naga kin manta dani de shiyasa....

Murmushi kawai tayi ...ta tashi

Nan ta kawo kajin tare da fresh milk da jus se kuma fruit tace zo muyi dinner..

Ya mutsa fuska yayi yace kici kawai a koshe nake..

Tab ai wly wannan bama magana bace oya com'on ..

Girgiza kai yayi yace yar rigimace ke wly ....

Zama yayi ..ta bude kajin kai ba Murad ba ni kaina na hada miyau dan wata irin
suyace tayi musu se tashin kamshin dadi sukeπŸ˜‹πŸ˜‹...

Yace yau kuma soyyayun kaji akayi muna a dinner..

Umm na amarci ne ai dan haka kaci abunka..

Kwashewa yayi da dariya dan shi ya dauka duk wasa ne abun..

Itade kasa ci ma tayi duk ta wani tsure. ...ni kuwa nace kefa kika sa kanki dama
kin ci kajinki dan zasu yi dadi a bakiπŸ˜‹....

Ganin takasa ci yasa ya shiga bata a baki ...da kyar ya samu tayi baki biyu..tace
ya isheta ..fresh milk kawai tasha...
Shikam suyar ta mishi dadi dan haka yaci da dan yawa..

bayan sun gama ta tattare komi takai kitchen ....

Wanka ta shiga tayi tare da alwala ...duk cikin sanyi jiki takeyin komi....umm
turare sun sha kashi anan ta saka wata sleepingdress dinta me kyau ..dogon hijab ta
saka ..lokacin data shiga dakin nashi ...har yayi shirin baccin shi yana kokarin
hawa gadon...

Da sauri tace ya haka kuma ....

Da mamaki yake kallonta yace kamar ya fa..
Ba karamin karfin hali tayi ba tace kayi alwala zamuyi nafila ......kamar yanda
sunna ta tanada

Be kawo komi a ranshi ba dan haka beyi muso ba yayi ya jasu..rka'a biyu
sukayi.bayan sun gama tace banji kayi muna addu'a ba ..shifa yanzu abun ma tsoro
yake bashi .beyi nauyin baki ba.yace wai mikike nufi ne haka..

Murmushi karfin hali tayi tace hakkika zan baka ne yau..

Waro ido yayi ya saki baki da hanci yana kallonta ..

Hannu tasa ta rufe mishi bakin tace miye kuma abun mamaki anan ..

Ajiyar zuciya yayi yace kada ki damu ni na yafe ..

Seda ta cire kumya ta sadda kanta kasa tace to ni kaban nawa hakki tunda kai baza
ka amshi naka ba ...

Zura mata ido yayi yama rasa abunyi ..da kyar ya tattara nutsuwarshi yace are you
fine?kin san kuwa mi kike fada?

Still kanta a kasa tace dama se mutum bashida lfy yake neman hakkishi ne?...kuma ma
ai sabida bana so kashiga wani hali ne...

Besake cewa komi ba nan ya shiga kwararo musu addu'a ...sannan yayi mata
tambayoyi ..
Cike da nutsuwa take amsa mishi ....

Gado suka nufa bayan sun kwanta Murad ya mirgino yayi mata runfa yana shafa
gashinta kanta yace ''es tu sΓ»r que c'est ce que tu veux.....?


Gyada kai kawai tayi dan se yanzu cikkeken tsoro ya shigeta (ayya ai kin makaro
kuma ..ai seda nace kada kiyi kika yi 😜)


Naso kwaso muku rahoto to aman sena ga abun ya fice karfin bironan dan haka sum2 na
fito tare da rufo musu kofar ..

Nan falon na zauna Um kuma kunsa ai mizanyi ...ragowar kajin nan na tasa agaba na
fara ciπŸ˜œπŸ˜‹ ..abuna......daga nan na dinga jin kuka da kananan ihun Maysam..

Ai kuwa mi zanyi inba dariyar ketaba...🀣🀣🀣🀣dama na gaya miki ai kika ki jina .....aman
fa daga baya na nan tausaya mata faπŸ˜œπŸ˜‰....

Asuba tagari 😎😎😎



Muje zuwa `


Ina yinku 😍😍😍


Fasma ce ✍yar mutan zinder
[9/13, 9:57 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[9/13, 7:47 PM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* πŸŒŸβœ¨πŸ–Š
( _Home of spécial 🏑&extraordinary writers_ )


🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

S.W.A✍

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚ *oohh today is a special day for me because it's my birtday ....* 🍭🍩 *happy birtday
😍
to me ..am so Happy..joyeux anniversaire à moi* 😍❀😘😘

πŸŽ‚πŸŽ‚ *happy birtday to you JIDDA Kema* .πŸŽ‰πŸ­



Dedicated to ME FASMA &YOU JIDDA😍❀




πŸ…Ώ99__100




```Manzon Allah (SAW) yace ''kada dayanku yayi tafiya da takalmi daya.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi..```




[15/08/18 Γ  00:00]Nan nima bacci ya kwashe ni ...asubar fari a kunne na akayi
ta ..cikin hanzari ta tura kofar na shige ...Maysam na tsinkaya ta kududun ne a
cikin bargo tana bacci ta aman da kagani kasan bawani dadin bacci takeji ba..inan
tsaye ina kare ma komi kallon da alamade har sunyi wanka dan ko drap din an
canzata ..fuskarta tayi fayau da ita ...se lokacin naga Murad ya fito daga tolet da
alama wanka da alwala yayi ..fuskarshi har wani kyalli agonci take ga wani tsadaden
murmushi da yake saki akai2 .....jallabiyar shi ya saka ya shiga jera nafilfili
tare da addu'oi ga Maysam har akayi kiran sallar farko sa anan ya isa ya zauna
bakin gadon dede setin Maysam .....

Shafa kanta ya dinga yi daga bisani kuma ya kai bakin shi dede kunnenta ya na yi
mata rada..duk kwallafata banji miyake fada mata ba..

A hankali2 ta fara bude idonta da duk suka kumbura alamun tasha kuka kenan ta sauke
su fes kan kyakyawar fuskarshi ....kawai seta saki mishi kuka wanda daga ji na
shagwabane ..shi kuma gogan ya hau ya zauna se rarrashi yake ..da kyar ya
lallabata ta tashi da kyar har wani dingishi take ya kaita tolet ya sake gasata a
ruwan zafi sanna ta doro alwala ......

Shi yajasu sallar ...yau kam da kyar ta samu tayi azkar din ma dan wani mayan bacci
takeji ....bayan sun gama ya jata suka koma gadon bacci duk ya wani mamatse ta ya
rumgume ..tayi kokarin kwace kanta aman ba karfin ga kuma bacci da yaci karfin ta
dan haka ta kyaleshi ......
Shikam kasa komawa bacci yayi kawai tusata gaba yayi yana kallonta wani sonta da
kaunarta na kara shiga cikin jikin shi ...shi kade se sakin murmushi yake..yana
zngura mata albarka

Wajejan bakwai ya fita ya sanar da su Mufeedah kada su jirata bata jin
dadi ....suka hayo suka tarar se kwasar bacci abunta take .....haka suka fice cike
da jimami tare da tunanin ko mi ya sameta ...duk tausayinta ya cikasu ..suma duk
jikin su yayi sanyi ganin Maysam batada lfy.haka sukaje driver ya saukesu ..dan da
farko sunso ma kin zuwa aman se Murad ya nuna musu mahimmacin zuwan su dan insun
dawo se su koya mata abunda aka koya musu.. .se lokacin suka sami dan kwarin
guiwa ..

Murad kam Kuyangi ya saka sukayi mata break masu dan romo2πŸ˜‹..

..nan ya zauna palon yana kallo aman rabin hakalinshi na kanta biri2 se ya
lekata ..yau kam baya jin ze tafi office dan haka yakira Mark ya sanar mishi wife
dinshi bata jin dadi dan haka baze samu damar zowa ba....

Ita kuwa baccin gajiya take ..ba ita ta farka ba se goma ...ta lallaba tayi wani
wanka tare da gasa jikinta se kuma taji dadi ajikinta ...dugawar riga na atampa ta
zumbula tare da wani zabgege hijab a cewar bazata kara saka english wear ba tunda
suna temakawa wajen tadawa Murad. Sha'awar ..aman intayi shigarna babu ta inda ze
ga jikinta ma bare ya takurata

Tan fitowa dariya ta subcewa Murad ganin irin tafiyar da take ...

Haba ai kuwa nan ta duke ta shiga rera mishi kuka .....da kyar ya lallabata ...se
harara take aika mishi

Farfesun ma kadan ci shima dan ya matsa mata ne ..dan bata da appeti ko kadan....

Yau kam Maysam kin zama ma tayi kusa da Murad bare har ta dane cinya yayi2 takiye
mishi kai daga karshe ma kuka ta saka mishi ..dole ya kyaleta ..taje can kujera
dake nesa data shi ta zauna...ga kuma kumyarshi dake dawai niya da ita yau din

Shi abunma birgeshi da dariya ya bashi..

Zaman kurame sukayi ..ita tana kallon tv shikuma ya na kallon ta ..can de yace
waini yau baza ayi mun magana bane ..ni miye lefina bayan keki ka nema kuma na baki
..

..nan ma shiru tayi mishi...

Daga haka seya tashi ze dawo kusa da ita ai kuwa ta saki kuka tana fadin wayoo
Momyna se kasheni wly kada ka matso kusa dani mun bata tunda kayi mun mugunta ..

...guiyoyin shi biyu ya kai kasa yace inace abunda kikeso ne nayi miki ko..

Tana share hawayen tace to daga baya ba nace maka bana so ba amman kayi kunnen
shegu dani ..

Yana yar dariya yace sorry my honey ai banjiki bane kuma ma ni abunda kade naji
shine kawo in sa maka ..dakike ta fada..se sunan yen dakika dinga jerawa na su zo
su temakeki ... .....

Ya mutsa fuska tayi tace nide yanzu ba ruwana dakai dama na sani ba wani sona kake
ba dan na tabbata lahira direct kaso aikani jiyan nan, kawai de kwanane a gaba ..
Gumtse dariyar yayi yace shikenan bazan karaba ...

Se lokacin ta saki ranta ..tace shikenan to kawo yatsarka mu shirya...

Ya beko mata yatsar ....a memakon tayi abunda tace se kawai ta shiga waro ido tana
kallon yatsar ..kamar wacce taga wani abun tsoro

Ganin haka shima ya kai kallonshi wurin dan ganin mitake warawa ido hakane ...ganin
ZOBEN dake yatsar ne take kallo yasa yace yana da kyau ko ?

Gyada mishi kai tayi ..

Yace ko kina sone na bakishi..

A'a abun ne ya bani mamaki dan ina da irin shi ...Abbana ya banishi lokacin dana
za'ayi auren mu

Kai har ma wannan rubutun MΒ² dake cikinta ina dashi ..sede tawa tafi taka kyau da
kyalli dan zinariya ne nawa..kai kuma azurfa ne ..tana yi mishi gwalo..

Mamaki da al'ajabi ya kamashi danshi yana iya cewa shida sweetbabynshi kade ne ke
dasu a fadin duniyar nan ma dan kuwa shi ya saka aka kera musu su ...kuma abunda
yasa yace haka can cikin zoben ba MΒ² bane kade sunan su ne a jiki aman in baka
luraba MΒ² kade zaka gani ..yana kallonta yace ina naki zoben ne ..cike da zakuwa ..

Kai na baroshi can gida cikin kayana dan banason ya bata...

Murad yace to shi zoben naki yana rubutu ne acan cikin shi...

Girgiza mishi kai tayi tace a'a bashida kawai MΒ² kade ajikin....

Ajiyar zuciya yayi dan dama da kamar wahala asamu me irin shi sede me kama
dashi ....nan suka ci gaba da hirar su da su Mariam suka dawo sukayi mata ya
jiki ..bayan Murad ya fitane suke tsokanarta kode ta sama musu Baby ne...

A ranta tace um bakusan jiyane ma aka bude hanyarba ku har ta wani baby kuke ..a
fili kuma seta ce tab baby fa ni yar yarinya dani haka ..ai konayi ciki sena kara
girma ..ku bakuga wuyar da akesha bane wurin haihuwa..

Suka kwashe da dariya Mufeedah tace to dai kada akwana biyu mu ganki da cikin kina
wani cika bakin kin..

Kai bakinki ya sari danyan kashi wly ......nan sukayita barkon cin su hardaga baya
suka koya mata darasin na yau.....

Cikin satin kam soyyayrsu suke ci da cinke kullum suna makale da juna ..Maysam ta
saki jikinta kamar da har da saka kananan kayanta ..sede shima be sake gwada
nemanta ba .. ..

Yau kam ta kama lahadi su duka biyun suna gida...
Maysam ta cakare ta fito da biro da kuma wata notebook lokacin yana aiki a laptop
dinshi ..koda ta zo batayi wata2 ba ta jaye laptop din ta dane cinya abunta ...

Yana kallonta har wani lumshe ido yake dan turaren ta suna kashe mishi
jiki .....kallonta kawai yake..yana admired dinta

Daga bisani kuma yana wani shashafa yace kullum kara kyau kike wife ..

Yar dariya tayi sekuma tayi kissing dinshi a kumatu tace nagode MURADINA ...yanzu
de bawan nan ba lissafi nazo muyi...

Da mamaki yake kallonta yace lissafi kuma...

Umm tace ..se kuma ta fara yi mishi tambaya kamar haka ..shin kana da gidaje biyu A
Maradi ko..,biyar a Niamey ko?
Ya gyada kai ..yace e
Ta ci gaba motar goma gareka ko?
Yace ee
Tace se kuma mall kana ukku a garin nan .da kuma hudu a zinder

Cike da mamaki yace ee

Tace da kuma jirgin ka na nan dana Niamey ko?

Yace wai tsaya a ina kika samu duka wannan bayan Mall dina nan da jirgin dana saya
ko kwana goma basuyi ba kuma kosu Momy ban fada ma ba ..tayaya kika san duk
wannan...

Dariya tayi tace to ai ba ina nasan su bane ..zaka tambaya mi zanyi dasu nan gaba
zaka tambaya ...dan kai da kanka kayi mun alkawarin su..

Cike da mamaki yace ni kuma..

Shikenan bara na tuna maka ranar nan ne lokacin dakake amsar hakkika kace duka
wannan abun ka banisu halak malak ..

Se yanzu tabbase ya tuna..yayi dariya yace to ke yanzu mi zakiyi da duk wanna
abubawa...

Momy zan bawa su ..dan bansan ita waccar matar taka kyautar mi kayi mata ne
ehe ...dan haka zan bawa Momysu ita tasan mizatayi da su..
Dariya yayi mata ganin kishine ya motsa yau din...
Kwantar da ita yayi a kirjinshi yana shafa kanta yace wai miyasa kike kishi da
matar da bakima santa ba...

Da sweetbaby ya kamata kiyi kishinki dan ita keda rabin zuciyana kema kina da
rabi...dan kishiyar da kike ta batu wasa nake miki tun wancan lokacin ..babu wani
aure danayi ....ki saka a ranki daga ke na rufe kofa in Allah ya yarda dan ko nayi
Allah yana gani bazan iya yin adalci tsakani ba...kai na baze iya daukan rigimar
mata biyu ba ni ke din ma da za'a rabaki abani rabinki dan ke kade ma.caza mun kai
kike bare mata biyu..


Wani sanyi dadine ya ziyarce ta tace har ta kara kankameshi gam a jikinta tana
dariya farin ciki tace to ai ita sweetbaby bata nan taya ma zanyi kishi da ita
bayan na san sonta a jinin jikinka ne yake yawo ....bazan iya yin kishi da itaba
soboda kana sonta ..nima kuma duk abunda kake so nakanyi kokarkin na koyawa
zuciyata sonshi ...dan na faranta maka rai...kaga ita tare na ganku bazanso rabaku
da ita ba

..kara rugumeta yayi yana mata godiya ....yace to yanzu se mu fara procedure din
transfert kenan...

Dariya tayi tace wani tranfer ai kuma na yafe maka su dan dama saboda
kishine ...dariya yai.shikenan to ..

Can se yace kinga gift dinki ne...
Kalar tunani tayi tace a'a..

Ok to kije ki sake duba karkashin pilonki zaki gani...

Da sauri ta tashi ta shige...koda ta duba se kuwa taga wani envelop .....doko shi
tayi ta kawo mishi..

Girgiza mata kai yayi yace a'a ai nakine ki bude abunki..

Ai kuwa tana budewa taga takardun gidane se key ....

Zatayi magana yace gift dinki ne ...takardun gidan wannane da kuma key din sabuwar
motar da na sai miki ..kamar yanda al'adar can gida ta tanada ba ..cewa washe garin
daren farko za 'abawa amariya gift na fita kumya ..naso baki taki kema washe garin
to aman ai ranar tazo mun a bazata shiyasa se yau nasamu ...na baki da fatan banyi
lefi ba

Cike da murna ta fada jikinshi tana me jin dadi .tace na yafe ..ai daka barshi ma
dan wannan al'adane ba addini ba..

Murmushi yayi.ya rada mata a kunne cewa ina alfahari da ke babyna...ina tayaki
murna kin kawo mi budurcinki na gode miki Allah ya albarkaci rayuwarki duniya da
lahira...ya biyaki da mafificin alherin sa ...ina sonki wifey ta...

Tana dariya farin ciki tace na gode Allah ya saka da alheri ya kara budi ...je
t'aime plus....

Sosai yaji dadin adddu'ar ....se kuma yace to muje daga ciki ki kara nuna mun
godiyar ki..

Master room ya fice da ita ..na kuwa mara musu baya dan ganin wacce irin godiya ce
da har se anje kuryar naki za'a yita..


Tunda suka shiga suke aikin kissing din su kamar zasu cinye junan su ..nide ina
tsaye ina jira ..dan inde wanna ne naga na saba gani ..ai kuwa abu ya fara kankama
suka shiga romance ..ina ganin haka na jayo kafafuna na fito ..dan kusan ita
soyyayar theori suna fada ne ina sauye muku amma ita pratical ta inda zan fara ma
nake rasawa shiyasa nake bar musu dakin😜.. ...tun shi Maysam ta zama yar hannu a
bunka ga renonshi yasa wani lokaci babu ko kunya itake nema ..soyyaya kam da
tattali junan su duk wanda yagan se sun bashi sha'awa..sun kuma birgeshi ..karfi
dayaji ta medasho mrs romantico ..Mark da Mahmud kam banda tsokana babu abunda suke
mishi..

Babu ruwanshi da inda suke ako ina soyyaya yake gwada mata ..rayuwa tayi musu
dadi ..su duka sunyi bulbul kwanciyar hankali ta zauna musu ..

🌹. 🌹. 🌹
A gurguje pls

Bayan wata ukku

Maysam tayi wani kyau da fari na ban mamaki ..ta kara cikowa musaman kirjinta..har
wani fresh tayi ...Murad kam abun nema ya samu se kwasar garabasa yake .....

Yayinda ita kuma kwana biyun nan da zazzabi take kwana ...

Se kuma wani dan banzan kwadayi abu inde me yaji2 ne to zataci shi ..kwade harda na
banzan..yau ma suna zaune lafiya2 suna hirarsu irin ta masoya ..can Maysam tace my
king zanci hadin boss..

Gyara zama yayi yace miye kuma wani hadin boss..?

Dayake abun na rigima ne se kawai ta rushe da kuka har da shure2 ita kawai hadin
boss zataci.

Da kyar ya shawo kanta yace wai dan Allah miye ne sena fita na nemomiki shi ...

Tace garin kwaki da madara da suga kuma ba'a saka ruwa hakanan ake shanshi..

Dafe goshi yayi yace to ni yanzu a garin ina zan samu garin kwaki ..ai tana jin
haka ta sake fashewa da kuka tace kenan ma baza ka samo min ba. ..wayoo Momyna
ina kike ne..
Babu shiri ya zari key ya fice ..be jima ba se gashi ya shigo ..nan ya hada
mata ..tana ci taji yayi mata dadi .har wani lumshe ido take.dan haka rigima ta
kwanta ......bayan ta gama yace taje ta dauko hijab dinta sutafi asibiti yayi mata
wani test dan tabbatar da abunda yake zargi....

Ai kuwa bayan yayi mata test din ya gano karamin cikin dake makale a mararta na
wata 2 da yan kwana ki...

Tana nan zaune yashigo da test daya karbo daga lab..batayi aune ba taji ya dauketa
yana juyi da ita ...
Can ya sauketa yace am so very happy today..

Tana kallonshi tace what's happen ne...kake murna haka..

Yace toutes mes felicitations na kusa zama papa ke kuma mama a takaici'' tu es
enceinte de deux mois''

Wani waro ido tayi tace what ?ciki?

Yana yin yanda tayi maganar ne ya tsorata Murad ..a ranshi yace kadade fa bata son
cikin ....


.
Love you all😘😍❀

Fasma ceπŸ–Š yar mutan Zinder
[9/13, 7:47

25 / 32