Author : FASMA Category : African Stories & Novels
...yau akwai
bidiri a gidan nan
Babu kumya yace Ameen Momyna ....
Momy ta sake su tace bari na bada sanarwa familly's meeting yau ..kaga se a warware
komi..
Baki har kunne ya dagawa Momy kai ..ta fice se waywayen Maysam din take..
Itada Mom dake bakin kofa suka fice fada.
Yayinda mamakin Maysam ya kasa boyuwa ganin irin farin cikin da Murad yake ...ga
wani manne mata daya ke karayi ..
Zata yi magana Suka ji kukan jaririn dake kan kadon su na jarinrai..da sauri ya
daukoshi yana kalloshi ...cinyarta ya dora matashi ya bata dabino dan kasar MADINA
ta tauna ta tsarta mishi ruwan abakin...
Bayan tayi ne yace to ki bashi abinci shi yunwa yake ji ...
Seda ya kawo mata ta wankeshi tas sanan ya dedeta mata yanda zata shayar dashi din
😂Maysam ta aza shayarwar da dadi ..da hanzarinta ta fiddo ta sa mishi ai kuwa babu
shiri ta zare tana yarfa hannu tace wayyo ashe da zafi ...
Murad ya kunshe dariya dan kada ta ki ba babyshi nonan yasa ya shiga
lallabarta ....da kyar ta yarda ta bashi ..to sabuwar haihuwa ina wani ruwa ai kuwa
da zafi ya isheta zareshi tayi ...ai kuwa shima ya bare baki yana kuka ...babu
yanda Murad ya iya se ruwa ya bawa yaron ya koma bacci..
Bayan sallar isha'i aka shirya family meeting din gaba daya kowa ya hallara kama
daga sarki fulani .Mom da Dad,Murad Mahmud M.Musa da kuma triple M wato su
maysam ..da kuma babynta Etc..
Su fulani kawai suka san da zancen dan haka bayan an bude taro da addu'oi sarki ya
bukaci Fulani datayi bayanin meeting din gaggawar data saka ayi ..nan fulani ta
shiga yi musu bayani komi daki2 wanda tunda aka fara zancen kowa ya zurawa Maysam
wacce take makale a jikin Murad yaki sakinta tayi dan nesa dashi ma ido ciki da
al'ajabi wanan lamari ..dad kam tunda ya dora idonshi akanta ya tabbatar da jinin
shice dan ga kamaninta nan dana matarshi karara . farin cikin shi ya kasa boyuwa
wanda har seda ya taso ya rumgume Maysam din yana me jin dadi dawowar tilon yarshi
Mom ma ta kara rumgume Maysam suna masu yiwa Allah godiya ..
Sarki ma farin cikin dayake ciki baya misultuwa ..gyaran murya yayi tukon su Dad
suka dan sassauta rikon da suka yi mata ..itade idon wannan shine ta rasa gane mike
faruwa ...
Da sauri ta koma kusa da Murad kasa2 tace pls yaya wai mike faruwa ne ban fahimci
su Mom ba kan cewa ni yar su ce .. Kuma kaima se wani kirana da sweetbaby kake pls
ka fahimtar dani sega kwalla ta cika mata ido ....zeyi magana sarki yace yaki nan
yata zo nan...
Jiki ba kwari ta isa wajenshi shima rumgumeta yayi yana me jin dadi
dawowarta ..sanan ya zaunar da ita kusa da shi yace bari na baki labarin komi
yanzu. Kowa ya nutsu dan jin abunda sarki ze fada wanda manya ciki sunsan komi..
🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹
Asalin su
Elh MUJAHEED shine Sarkin na takwas a wannan masarautar sarki ne me adalci da
gaskiya yanada mata ukku biyu daga ciki Allah ya musu rasuwa kuma su Allah be basu
haihuwa ba se matarsa ta biyu me sunan sarauniya Haj MUNIRA ita Allah ya arzuta
da y'aya har biyu dan ba'a jima da yin aurensu ba Allah ya bata ciki wanda bayan
ta haihu aka saka mishi sunan MOUSTAPHA wato ni. Se kuma bayan yan shekaru da
dama ta kuma sake haihuwar mace wacce aka sawa sunan MAYMUNA wato Mom ...muntashi
cikin jin dadi kasan cewar mu yayan sarki garin .. Nayi karatuna a kasar waje
wanda bayan na gama ne na dawo sarki Mujaheed yayi murabus wanda a ranar nadi aka
hada da aurena nida MARIAMA wato fulani wacce take diya ga sarkin AGADEZ .....
Shekara biyu Allah be bamu haihuwa ba haka muke zaune tunda munsan Allah ne me
badawa..wata rana naje Diffa kaiwa sarkin garin ziyara anan ne na hadu da MADINA
wanda mahaifinta ya nuna yana son hada *zuri'amu* (littafin nida Aisha ) ..
Banyi kasa a guiwa ba dan ina ganin girmanshi da kimarshi yasa na amince da auren.
Ban baro garin ba seda aka daura auren muka tafo tare.
Bayan wata ukku Allah ya Arzutar da Fulani da samun ciki murna ba'ama maganar
bayan wata tara ta haifeshi wanda ko sunan shi ba'ayi ba Allah ya amshi kayanshi
wanda kunsan Madina ce tayi sanadin hakan ..
Haka muka zauna cikin su babu wacce ta sake samun ciki har mukayi shekara hudu
Fulani ta kuma samun wani cikin wanda bayan ta haifeshi aka samishi sunan kakanshi
MUJAHEED wato Murad .. ..tun haihuwarshi be kuma samun wata ishashiyar lafiya ba
kullum muna hanyar asibiti ...duk da irin gata dayake samu bare ma wurin Mom dinshi
wacce tafi shakuwa da kai dan kusan ita ta renaka hakan yasa ka shaku da ita matuka
. inyayi wata rashin lafy . har sa ran bazama ya ta shi ba muke aman daya ke da
sauran kwanakina Allah ya tashi kafadashi ....kanada shekara tara akayi auren Mom
itada dan sarkin Niamey me sunan Elh MOCTAR wato Dad dan haka bayan auren can aka
tafi da ita . da kyar aka rabaku kai daga bayama dole tasa aka meda kai can
wurinta saboda irin shakuwarku ...anan ka gamu da Mahmud wanda yake daya daga cikin
familyn masarautar......
.bayan wasu watani ta samu ciki duk da kanancin shekaruka aman kana tausayawa mom
dinka duk abunda take bukata kafin bayi su mata kai ka yi matashi kamr su yanka
fruit etc.. A takaicede tare kukayi renon cikin ...bazan manta ba ranar wata lahadi
wanda yayi dede da gobe birtday dinka wanda har paty mom ta tsara maka aman ranar
ta tashi da dakuda .. Da asuba dede kiran assalatu ta haifi yarta mace kyakyawa
da ita wanda tunda ka ganta kake murna da jin dadi anyi maka kanwa . daukanta ma
kam seka ga dama kake bawa wanda kaso ko dad din seya lallabeka kake bashi ita
yayinda Mom ta zama yar kallo dan se kaji tana kuka kake badata abata
nono....gashi se fadi kake ranar birtday dinku daya dan haka tare zukuna
patynshi....dama su yan barka basa ma tarkar amsarta....ko sunan ta kai ka zaba
mata na farko wato Mufeeda wai dan kuyi kusan suna iri day shima dad din ya biye
maka yasa yayi na'am da sunan aman se mummunan abu ya gifta ana gobe bikin wato
rasuwar mahaifiyar mu ~Munira~ wanda ACCIDENT ne SANADI suna kan hanyar zuwa
sunan ne ..dan haka akayi suna cikin lami tare da Sawa jaririya sunan MUNIRA wanda
kwarai munji dadin irin karar da Dad yayi mana wanda za'ana kiranta Ummi....aman
kai kam banda zumburen2n baki babu abunda kake yi wai anki sa mata sunan da kake
so ko Ummi baka kiranta dashi ..kai daga baya seka shiga kiranta da SWEETBABYNA..
To fa SWEETABABY de ta tashi cikin gata daka shagwabantata sosai school kawai ke
rabaku shima seda lallaba duk wani abunka yakan karene akan Munira tana da shekara
daya kuka zo ganin gida nan ka bawa kowa mamaki dan kuwa cewa kayi wai aure kake so
kuma Munira za'a aura maka harda su birgima dan ance maka a'a ..... ..ELH MUJAHEED
ne ya lallaba ka tare da tambayarka miyasa kakeson aure ..budar bakinka se cewa
kayi ai school na hana ka zama tare da ita aman idan anyi muku aure shikenan zaka
dena school din kayi renonta.
Kowa na wurin seda ya dara ..nan Elh Mujaheed ya bada wasiyar ko bayan ranshi ..ko
ba dade ko bajima Murad bashida Matar data huce Munira..babu me ja da hakan dan
hakan aka rubuta aka aje..shima dad lokacin be musa ba kuma be nuna kin
amincewarshi ba . . .nan aka lallaba ka kan cewa in kana son auren to fa sekayi
karatu daganan aka rufe maka rigimar ka....
To fa ko agaban waye da sweetbabyna kake kiran ta baka kumyar kowa .itama bata
yarda da kowa se kai .tana kiranka da BABYNA.
Bayan shekara biyu Allah yayiwa Elh Mujaheed rasuwa . munyi rashi matuka ...
Bayan wasu shekarun biyu lokacin kana ss2 kuma ka dada canza mata suna zuwa MAYSAM
koda Mom ta tambayeka ..se cewa kayi ai wani zubin kumyar dad kake Ji
shiyasa ...data nemi sanin ma'anar sunan kuma sekace mata Ai Maysam yana nufin
SWEET ne ..se kuma itama sunan ya birgeta to tunda ga lokacin sunan Ummi ya goge
kowa yake kiranta da MAYSAM din ..se kuma aka shiga shirye2 birtday dinku kai na
cikewar shekaru 14 ita kuma 4 kamar ko wace shekara aman wannan karon ka aza rigima
kan a nan kakeson ayi muku patyn anyi rarrashi aman a banza dayake abun kaddararene
yasa ka kwallafa rai itama kuma yar renontaka ta biye maka kuka hargitsawa Mom da
Dad kwanya babu shiri suka tattataro suka zo nan garin koda mukaji dalilin zuwansu
munyi musu fada sosai kan biye muku da sukayi ..
Anan kuma aka shirya muku wani birtday din banzan kuma mantawa da wanan ranar ba
rana birday din da safe wajejan goma na safe Fulani da Mom zasu rabon temako ga
kauyikan dake kusa damu kamar ko wani bayan wata ukku2 tasoma bari har gobe saboda
birtday aman kuma da ta tuna cewa duk bawan dake karkashin su ya kwana da yunwa
sun shiga hkkinshi bayan su suna cikin wadata dan haka saboda birtday bazatayi
cancel din bada temakon ta ba ..to itama Mom ta kuke seta bita batayi mata musu
ba ...itama Maysam na ganin Mom dinta ta shiga kukan seta bisu ..kai kuma kafarta
kafarka dan haka kaima ka bisu .lokacin dazaku tafine ka fiddo wani zobe wanda
shine gift din da zakayi wa Maysam sosai ya burge mutane dan iri dayane zoben
babbaci kawai nata na zinariya ne nashi kuma na azurfa ne wanda tafiyar su wannan
haji ya saka Dad ya sa aka kera musu shi ....ku duka a mota daya kuke ..lafiya
kukai temakon..se a hanyarku ta dawowa ne tsautsayi ya afka muku wandan kukayi
wani Accident a take dreben motar ya rasu a wurin kukam gaba dayanku an wurwurga ku
wanda kuka sume a wurin ku duka ... Nan bayin da kuke tare su suka nemi baku
temako ..aman abun mamaki shine batan Maysam ko sama ko kasa ..anyi neman duniya
aman babu ita babu alamunta ..
Abu kamar wasa aman akayi neman nesa da kusa babu ita ..har kwararu police aka saka
nemanta aman jikake shiru ..abu de kamar asiri ..seda aka jera sati anan nemanta
aman shiru .....daga baya ma aka tabbatar musu da cewa inde har tana cikin jejin
nan to sede wata ba itaba dan akwai namomin daji a wurin da kyar ne idan zata
rayu ..shiyasama muka dangana da ita muka dauka da ta mutun..
.to fa nan kuma Murad ya bujiro da nashi sallon rashin Maysam dan bashida aiki se
kuka ko kuma ya tisa photonta gaba yana kallo yana magana shi kade ..
Kadan2 ya dawo shiru2 yayi bankwana da dariya fara'a da kuma sakin fuska ga mutane
se kuma wata tsabagen fada da masifa ..abu kadan bayi sukayi ze saka ayi musu horo
me tsanani . school ma ya dena zuwa kullum kumshe cikin kuryar daki ..abun ba
karamin daga hankalimu yayi ba ..ga kuma abangaren Mom itama tun da abun ya faro
tayi AVC take zuciyarta ta kamu wanda yayi sanadiyar kullum suna hanyar kasashen
waje don neman magani...shima Murad da kyar aka lallabshi yayi candy da weak da
izinin Allah ya samu ..ai kuwa muka yanke shawarara turashi turashi England ko ze
samu damar sakewa yayi karatun shida Mahmud aka turasu dan ya samu ya kula da shi
sosai tare da bayi da dogarai ..acan dinma ansha fama kafin ya dan sauko ya fara
karatu aman fa bakar zuciyar nan na nan makalle dashi ..abu kadan ze sakashi
fushi .........
Se anan sarki ya ja numpashi yace to kin ji labarin ki Maysam *SANADIN ACCIDENT* ne
hakan ta faru... kaf palon in ka dauke parent din kowa se sharbar kuka ya ke bama
ya Maysam ba da take ganin abun kamar almara ba..wai itace Sweetbabyn Murad daya ke
matukar so ... Ashema shi ya reneta tun tana ciki ..se kawai ta sake fashewa da
wani kukan wanda Murad babu ko kumya ya zo ya rumgumeta yana lallashi ..
Sarki ya bukaci M.Musa dake cike da mamakin wannan lamari da yayi mishi bayanin
gameda da Maysam din..
Be boye musu komi ba yayi musu bayani yanda ya sameta ..sunyi matukar mamaki jin
inda ya sameta dan da wurin da accident din ya faru da kuma inda ya sameta da
tazara sosai
Sanan ya basu hakuri kan irin abunda Murza tayi mata ... ..
Kowa na daki murna yake bama ya Maysam da ta samu iyayenta yanzu taji kuma irin so
da gatan da suke mata ..ba ..an jima nan ana hira sannan ya aka rufe taro da addu'a
.kowa yayi bangarenshi cike da jin dadi da farin ciki....
To fa oga Murad ya aza rigimar sede Maysam ta koma bangarenshi da zama dan yaga
Mom na son kaita bangaren da suka sauka ..nan fulani ta shiga yi mishi fada ..to
wai ma mi zatayi maka acan bangaren ne dan danyan goyon nan ..aman a memakon ya
sauko se cewa yayi Momy ai waccar wifyna ce wanna kuma ai sweetbabyna ce kinga it's
two person different ..kuma walahi ni banma gaji da ganin ta ba yana yi yana wani
matsawa kusa da Maysam din ..ita kanta Maysam din kunya yake bata bare kuma su
fulani ...daga bayama girgiza kai tayi tayi ficewarta ...
Haka yace shikenan Mom kawai muje can naku bangaren dan nima na kwaura kawai ..Mom
kam murmushi tayi dan tasan za'a rina dan zeyi fiye ma da haka din..
A bangarenma seda ya danne zuciyar shi ya basu wuri su kara sanin junan su aman
bini2 seya leko su ya koma ..
Sha biyu nayi yazo yace to Mom ki ban aron sweetbaby na nima kinga ma dare ya tsala
seda safe ko...
Mom harda yar kwallarta don ya tuna mata lokacin da suna yara ma haka yake mata da
lokacin baccinta yayi zezo ya dauketa koda kuwa mi take mata ..seda safe su
karasa ...dan haka bata musa ba ta sallami Maysam din .wacce take ta zumbura baki
kan ita bata gaji da Mom din ta ba..haka ya lallabta aman mi ai kuwa jaririn yace
besan dare ba nan ya shiga musu kuka abunka da sabuwar shiga itama kawai ta saka
shi gaba tana kukan dan bata son ya zatayi da shi ba ..
Murad kam banda dariya babu abunda yake mata ..can de dayaga da gaske take kukan
yasa ya dau baby yana jinjigashi shima dan ayi se yayi shiru ....
Ta kalleshi tace laa only one ya akayi mi kayi mishine ya dena kuka..dariya yayi
yaceai ke ya biyo a kukan nan dan kwana kike kina kuka kuma ko ambaki nonon ba wani
shiru kike ba ...kuma yanda kika ga yana kuka bakinshi na karkarwa to kema haka
kikayi .
Rufe fuskarta tayi tana fadin kai babyna banda sharri fa..
Wani lumshe ido yayi yace 'repete le encore'
Tace mi din?Baby?
Lumshe idon yayi yana murmushi yace Sweetbabyna ina sonki fiye da raina ...ya
hada su ya rugume su duka....
Daga nan nima nace bari nayi musu sallama ..ko ba haka bata fans?😆😆😆😜😜....
Baride na dan kara samunku labarin..
Maysam tace baby to miyasa lokacin da aka daura muna aure ka nuna mun tsana da
hantara inde har lalle ina kama da sweetbabynka a lokacin ..
Yana mirmushi nan nashi me kashen yan mata yace to ai ko lokacin tsananin kamar ku
ce ta saka nayi tayi miki haka dan duk wani kallon da zan miki ina kara tuno da
itane wanda yke barazanar tada mun da ciwo na ne..bare kuma fatar jikin mu ta hade
senaji zuciya na ta fara Kidan Zut3 shi yasa kika ga bana iya miki muso kan abubuwa
da dama na kanyi loosing din controle dina da zarar idon mu sun sarke da
juna ..ina sonki da yawa sweetbabyna pls idan kinga zan kauce kiyi kokarin nunamunu
hanya dan da rabin zuciya na ne kika bayae gurbin aman yanzu kam gaba dayanta
''elle t'appartienne '' aman am sorry da duk abun da na miki a ba..
Bata bari ya qarasa ba ta hade bakinsu tare da girgiza mishi kai kusan raba daren
sukayi suna hira daga karshe ya rumgumeta sukayi baccin su
Ranar suna yaro yaci sunan MUHAMAMAD anyi shagali iri2 ..da walima kai abun ba'a
cewa komi se san barka ku ma de kunsani base natsaya baku labarin bikin ba .. .
🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹
Wai ina labarin Inna Murza ne?
Allah ba azalumin bawa ba Murza de ta sake rasa kafarta gudar data rage
mata ..yayinda bugan kan da tayi ya haddasa mata tabuwar hankali .hauka turben
takeyi (hum jama'a mubi duniya a sannu kana abun kirkin ma ya ka kare bare kana
shuka sharri adoran kasa. ..kungade Murza duk abunda tayi nufin su Maysam dashi
shine ya kome mata ..dan tayi niyar meda Maysam gurguwa idan baku manta ba aman
Allah ya qareta ..taso haukata su nan nan ma batayi nasara ba ....komi zakayi ka yi
tawwakalli da Allah ....duk abunda kakeyi ya kamta kasani Allah yana jinka kuma
yana ganin ka ..sanan kaji tsoron Allah a duk inda kake ..Allah ya qara karemu mu
da zuri'armu baki daya ameen ya kula shiryar da masu hali irin nata) .an kulleta
anan cikin masarautar bisa umarnin Maysam dan ita tace ta yafe mata kuma ta nemi
alfarmar da abarta nan dan kada ta shiga duniya..Murad ba haka yaso ba to aman
Maysam ta zartar da hukunci babu yanda ya iya . sede muce Allah ya shirya masu
shiryiwa ya sa sa su gane ga duk masu hali irin na Murza da makarabanta wato waziri
da Madina..
🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹
To fa abun na oga Murad ba sauki dan fa ya zama mijin tace ko kuma ma mijin kan
tace dama kusan zuciyarshi a rabe biyu take to kuma yanzu Maysam ta mamaye ta duka
tunda yasan itace sweetbabyn shi..
Yauma kamar kulum suna zaune a palon fulani ..ya wani tankwashe kafafu yana gyara
madarar da za'abawa littlebabyn shi dan baya bari bayi su taba wai acewarshi yafiso
suyi renon kayansu da kansu yayinda da Maysam ta saka babyn tana mishi wasa kamar
wani babba ...Mom ta fara yi mishi fada akan ya dena sake ma Maysam da yawa
haka ..tayaya tana zaune ace shi ze kada madara da kanshi..
Ya wani marece yace kai dan Allah Mom bana son ta wahala da yawa ne walahi a barta
da shayarwarshi kade ma jiki take ji ..ita kam Maysam kanta akasa dan ita kanta
tana mamakin wannan kaunar da Murad yake nuna mata ..Fulani de batace komi ba.
Harkokin gabanta ma take
Mom ta taba hannu tace wai anyya kana cikin hankalin ka kuwa miye na wahala anan
wai ayya ma zaka iya mulkar kasar nan kuwa nan gaba ?
Yana dariya yace kai Mom wani mulki kuma ai bazan iya barin Maysam dinta ba dede da
yan mintuna bare aje ga zancen awwanin da zanyi a fada ..tab ai da kamar