Author : FASMA Category : African Stories & Novels
wahala
itama seta sha..
Maysam tace a'a Abba ka kyaleta da halinta kuma ai ba'a meda sharri da sharri ....
Duk wanda ya nufeka da sharri to kai ka saka mishi da alheri ..
Nan ya rumgumeta yace shikenan y'ar Abba na hakura Allah ya isar miki ya albarkaci
rayuwarki hakika ke y'a ta gari ce ina alfahari dake...ameen tace..
Ba karamin burge fulani sukayi ba bare ma Maysam gata yarinya karama aman da kaifin
tunani har taji wani abu ya tsargu mata a rai..
Nan aka dinga bawa Maysam kulawa ta kirki komi se anyi mata kai hatta da cin abinci
inde fulani na wurin to itada kanta zata bata wata irin shakuwace ta shiga tsakanin
su ..kuyangi har mamakin wannan abu suke sunsa fulani da kirki ga tausayi amman
abunda take yiwa Maysam abun azo a ganine musamman Maysam da take y'ar kauye..
Malan Musa ne zaune gaban sarki bayan ya kwashi gaisuwa ..sarki yayi gyaran murya
yace to daman wata alfarma mukeso kayi mana ..
da sauri ya d'ago kanshi ya kalli sarkin se kuma ya meda kanshi kasa yace alfarma
fa kuma ma a wajena?
Sarki yace ai muna nema alfarmar ka bar mana yar ka ne..
Shiru yayi bece komi ba a ranshi kuwa fad'i yake gaskiya bazan iya bar muku ita
ba..
Gani shirun yayi yawa sarki yace dama jiya ne mukayi wata shawara da fulani kan
inde bakayi wa yar ka mijiba to muna nemawa yarima Murad auren y'arka Maysam ... .
To fa fans kun ji wata sabuwa kuma .....
Mu had'u a shafi na gaba insha Allah .. .
Ina kaunar ku fans irin sosai d'in nan
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:25 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ππ
[8/17, 1:27 PM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
15__16
*Saudat Farouq na gode sosai da kaunarki ..na ga mesage d'inki kuma in sha Allah
zan gyara..Allah ya bar kauna..*
Dedicated to All my Fans
15__16
```Manzon Allah (SAW) ya ce''Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce''
Muslim ne ya rawaito shi``` .*
Malan Musa yace yarima Murad da Maysam? A gaskiya da wani ne dana bashi amman ai
yarima ba sa'an auren Maysam bane..
Sarki yace haba Malan Musa dukan mu yan adam ne duk d'aya muke a wurin Allah babu
wanda yafi wani babu fifiko se wanda yafi wani tsoran Allah ...hakane Allah ya bani
mulki amman wannan ba yana nufin na fika sede ko in bakason had'a Zuri'arka da tawa
ne
Da sauri Musa yace wane ni nace bana son had'a Zuri'ata da taku ..tunda hakane ta
b'angare na bashi ...bansan ko ita Maysam d'in zata aminci ba amma fa wani hanzari
ba gudu ba ya kamata kusan labarin ita Maysam din ..
Da sauri fulani tace a'a eh duk Maysam ta fad'a mana komi har irin sharri da akayi
mata wanda tun wancen lokaci nasa aka mata duk wani gwaje2 daya dace kuma
alhadulillah duk kariyar mutane ce .....kuma kada ka damu nida kaina zan sanarwa
Maysam d'in
Malan Musa a ranshi ya ce kenan ta sanar dasu y'ar tsintuwace ..amman duk da haka
suka amince ..to shi inbe basu ba dami ze saka musu da irin son da suke nunawa yar
lelen shi..
A fili kuwa se yace shikenan Allah ya zab'a mana abunda yafi alheri ..
Daga haka ya koma clinik...
Waziri kuwa wanda akayi abun a gabanshi ...yayi wa sarki da fulani kirari sannan
yace ina neman alfarmar fad'in tsokacin bakina game da wannan had'in da ake son
yi ..
Fulani tace fad'i waziri an baka..
Ya kuwa gyara zama yace naga yarinyar nan ba jinin sarauta bace kuma a al'adar
masarautar nan dan sarki se yar sarki hakama yar sarki se dan sarki ..amma agafarce
ni idan na fad'i badede ba ...
Sarki yace hakane al'ada kace ba addini ba dan haka na rigayi dana zab'awa yarima
mata mu hali ,tarbiyya da addini muka bi ,,ina anfanin auren jinin sarautar da ba
tada tarbiyya ..daga haka yayi shiru..
Waziri kam kamar ya mutu dan takaici shi yar shi ya so a aurawa yariman sega wata
yar qauyen qayau zowar rana tsaka ta samu a bulus ..shida yayi shekara da shekaru
yana jira. . ..fakar idon sarki waziri yayi yayi kwafa...
Koda ya koma ya tarar da Maysam tana bacci abunta be tada ita ba ya zauna yana tuna
magaganun da sarki......
Har fulani ta riskeshi nan ..bayan ya kwashi gaisuwa se kuma ya fita yana fad'in
bari na dan zaga cikin gari ..
Ko minti biyu ba'ayi ba Maysam ta farka .arba da fulani tayi a tare suka sakarwa
junan su murmushi ..ga kuyangu wasu tsaye suna mata firfita dukda AC da ke kunne
saura kuwa a zube gabanta ...
Fulani tace ya karfin jiki?
Alhadulillah cewar Maysam ...
Fulani ta kuma cewa a zuba miki abicin kici ko?
Gyad'a kai kawai tayi..
Nan kuyangi suka fara zuzzuba abinci kala2 .Maysam ta kalli fulani tace abincin nan
yayi yawa fa
Batace komi ba ta dauki plate guda me free rice da miyar zogale wacce tasha naman
zabuwa ..spoon ta sa tace ci ko kuma sena baki a baki ne ...
Dariya Maysam tayi tace a'a zan iya ..ansar plate d'in tayi ta faraci ko spon goma
batayi ba tace ya ishe ta ...
Fulani ta anshi plate d'in tare da cewa han na baki a baki tunda hakan kika fi
so...
Babu yanda ta'iya haka take ansar abincin dan tana jin nauyi cewa fulani a'a....
Seda taci rabin tukon fulani ta kyaleta ..tasha lemun abarba wanda yaji kayan
kamshi..bayan ta gama ne fulani ta umarci kuyangi dasu basu wuri jiki na karkarwa
suka fice kafin nan seda suka yanyaka fruit kamar pomme(apple) ..pastèque
(watermelon) dade sauran su..
Fulani tayi gyaran murya tace Maysam ina son muyi wata magana amman bansan ya zaki
dauki abunba..
Maysam ta dauki yanka d'aya na kankanar tace ba komi haba kawai ku fad'i ni na
d'auke ki tamkar mahaifiya ta ..
Sosai furuncin nan yayi wa fulani dadi har taji soyyayar yarinyar ta dad'a nimkuwa
a zuciyar ta ...tace amince warki nake nema na ki auri d'ana yarima Murad ..
Maysam wacce take shan kankana ai kuwa seta kware ta ringa tari ...da kyar ya tsaya
tace yarima Murad fa?ni?gaskiya bazan iya se kuma ta rushe da kuka ta kasa qarasawa
tana kunyar cewa bata son jinin fulani kuma ma a gabanta..
Fulani ma sega hawaye shar yana bin kuma tunta tace Maysam bazan miki dole ba kema
y'a ce kina da inci ...yarima kad'e Allah ya bani ...ina son ganin jikokina kafin
na mutu amma shi yarima aure baya gabanshi saboda wani kuduri nashi ..ina ganin ke
kad'e ce zaki iya zama dashi har ki'iya samun soyyayarshi because na yaba da
hankalin ki nutsuwarki uwa uba kuma da hakurin ki ...shiyasa nake neman
alfarmarki ..
Da sauri ta dago kanta ganin shar d'in hawaye a fuskar fulani da sauri tasa hannun
ta ta goge mata t tana kuka tace kiyi hakuri na amince se kuma .. suka rumgume
junan su fulani tace hakika ke y'a ta gari ce ..ina son ki dauke ni tamkar nina
haifeki .tun lokacin da na fara ganin ki naji kin shiga raina time din daki ban
labarinki na tausaya miki matuka ..ina son ki riqe amana ki kula mun da yarima ....
Duk da bata san yanda ake wani kula da miji ba amma seta tsinci kan ta da fad'in
insha Allah zan kula dashi kuma bazan tab'a cin amanar ki ba...se bayan ta fa'di
kuma se taji kunya tasa hannuta ta rufe fuskar ta .......girgiza kai kawai fulani
tayi tana dan murmushi...
Se bayan sallar asar Malan Musa ya shiga d'akin tana lazumi daga zaune abisa gadon
da alama yanzu ta idar da sallah....addu'a tayi ta shafa ..
Ta juwo tace Abba sannu da zuwa ..
Yauwa yar Abba ya jiki ..?
Da sauki ta ansa ..
Se kuma sukayi shiru har na tsawo yan mintuna ..
Maysam tace Abba kaji abunda momy fulani tace mun d'azu.....?
Ya san de be huce zancen auren ba amma seyace a'a se kin fad'a dan ya k'arda ..
Nan ta labarta mishi komi tana jiran jin mizece ...
Yace kwarai kuwa y'ar Abba ni suka fara tuntub'a kuma na amince ......dan mutanen
nan suna kaunarki suna da kirki da karama ..kuma shi sarkin da kanshi ya nemi auren
ki ....ba muda abunda zamu iya saka musu dashi ..kiyi hakuri ki karb'i rayuwa a duk
yanda tazo miki. ....na tabbata bazasu cutar dake ba....
Kukan daya zo mata ta shafe tace shikenan Abba Allah yi mana zab'i na alheri..
Ameen ya ansa nan suka ci gaba da hirar su irinta d'a da uba.....har magarib
..
Haka akayi ta kula da Maysam har na tsawon wata biyu .alhadulillah kuwa sauki ya
samu har tana taka qafar .....nan suka fara shiryen2 komawa qauyen su ..wanda sati
biyu ya rage a daura auren dan haka sarki ya nemi alfarma kuma Musa ya amince ...
Abunka da gidan sarauta nan aka fara kuskus ...
Waziri ne zaune gaban sarauniya Madina yace gaskiya nayi sakaci dayawa dana san
haka zata faru baza 'aba y'ata yarima ba dana biyewa shawarar ki da dad'ewa... .shi
'isa yanzu nazo mu gama karfi da karfe dan mu cimma burin mu..
Wata dariya Madina ta kece da ita tace ai daman kwad'ayin ka yaja maka kayi ta
jiran gawon shanu ...da kaso ai da yanzu kaine a kadagar Mulkin nan aman wai kai me
y'a ..ai ga irin ta nan ..
Waziri yace a bar tuna baya yanzu de na mika wuya...
Da kyau cewar Madina ...yanzu de babu wani plan mu bari se ya dawo kasar...
Nan suka ringa kuskus wanda bana iya jiwo komi..
.
A b'angaren.Murad kuwa besan wainar da ake toyawa ba ..yana zaune a office dinshi
kiran Me martaba yashigo ......se kawai ya tsinci kanshi da fad'uwar gaba ....haka
ya daure ya d'au kiran....bayan ya kwashi gaisuwa Sarki yace ya zancen mu na zaka
kawo mun wacce kake so gashi har time din ya shud'e aman bakace komi ba..
Sosai kai yayi kamar yana gaban shi yace ayi hakuri ban samu ba..
Alhadulillah to ni na samo maka kuma nan da two week ne dan haka seka fara shirin
dawowa.
Wani mummunar faduwar gaba yarima Murad yayi ..yace...
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:27 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ππ
[8/17, 1:31 PM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
17__18
*Jinjina ga MAMAN SHUREIM hakika kin cancanci* *yabo na ban girma ...Allah ya*
*miki jagora a lamuran ki ....thanks for all .*
. *wannan page d'in* *na kine ke kad'e Fasma tace kiyi* *yadda kike so* *da
shi*. .. _Allah ya qara donkon zumunci _
17__18
```Manzon Allah (SAW) ya ce''Sallar jam'i tafi sallar mutum guda daya da daraja
ishirin da bakwai''
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` .
Wani mummunan fad'uwar gaba yarima Murad yayi dan danan zufa ta karyo mishi duk da
AC da ke kunne yace Dady two week fa ?kamar zeyi kuka .
Me martaba yace kwarai kuwa kuma bazan karb'i excuse d'in kin rashin zowanka ba dan
haka sati me kamawa ina son ka tattaro ka dawo gida....
Beyi iya cewa komi ba se to in sha Allah zanzo..
Sarki yace yauwa Allah yayi ma albarka ...
Ameen yace lokacin idonshi har sun kad'e sunyi ja kamar wuta ..
Suna gama wayar da Sarki ya kuwa dannawa fulani kiran .
Sallama kawai ya iya yi mata ya fashe mata da kuka..kamar wa'i qaramin yaro
Bata hanashi ba seda yayi me isar shi sanan tace Murad ..
Jin ta kirashi da sunanshi yasa ya nutsu ta wayar kamar yana gaban ta dan bata fiye
kiranshi da sunan ba se de inhar maganar dazata fa'da tanada matuka mahimmaci
Fulani tace Murad ina so kayi hakuri ka zama me biyyaya ga iyayen ka ..kasan baza
mu tab'a zab'a maka abunda ze tab'a cutar da kai ba.......ina son ka zama me
tawakali a rayuwarka .....kaza me karbar da kuma yin imani da kaddarar rayuwa au ta
alheri wala ta sharri ....
Na sani ba tun yauba kake kai bazaka tab'a yin aureba .....kasan kuwa aure sunna ce
babba ....Manzon Allah SAW ya na ce wanda baya son sunnata to baya tare
dani ...shin kana son kasance wa cikin mutanen da basa tare da Manzon tsirane...?
Kamar yana gabanta yake girgiza kai ..yace Astagafirullah....Momy kiyi hakuri daga
yau banza sake ba. ....
shikenan Allah yayi mana zab'i na alheri..
Ameeen tace Allah ya maka albarka.....to baza ka tambayyi wacce yarinya ce ba?
A'a Momy duk wacce kuka zab'a min tayi mini dan banida zab'in da ya huce naku....
Shikenan Son Amma ko sunan ta bazaka so sani ba?
Bayason Fulani ta fuskancin wani abun kawai se yace ...ina so mana ..
Sunnata MAYSAM
seda gabanshi ya fad'i jin sunan aman ya dake yace ..shikenan Momy inada aiyuka
anan Office ...next week ganinan zowa in sha Allah..
Cike da murna fulani tace Allah ya kawoka lafiya a ganinta ita ya sauko ya amince
da auren daga nan bata san qarfin hali kawai yake yana danne zuciyarshi..
Ranar wuni yayi yana tuno zancen auren ..gaba daya ya kasa qarasa aikin dayake se
gidanshi ya koma ...yana me bakin cikin wannan al'amari..
.
A b'angaren su Malan Musa sun isa lafiya ...Murza se kaf2 da Maysam take tana
tsoron Malan Musa yayi mata maganar karayar Maysam amma se taji shiru hakan yasa ta
saki jikinta dan duk a ganinta Maysam bata gaya mishi yanda akayi.ba..
Ai kuwa Malan Musa na fita koda massalaci ne to fa seta san duk yanda zatayi ta
muzgunawa Maysam koda rankwashine kuwa...
Bayan kwana biyu da dawo warsu da dare tsakani magarib da isha'i suna zaune suna
hira Malan Musa yace Murza dama akwai wata magana danakeson muyi.
Gyara zama tayi tace ina jinka Allah yasa muji alheri ..
Murmushi yayi ya ce alheri babba ma....
Ai kuwa cike da zumud'i tace har na qagauta ka fad'an mana
Yauwa dama Maysam ta samu mijin aure ne .
Wani turnikeken bakin ciki taji ya taso mata aman ta danne tace miji ..a ina dan
ita jira take taji yace dan shaye2 ne ko kuma wani dan daba ko barawo wanda de
Maysam zatasha wuya..
Ai kuwa yace Yarima MURAD dan Sarkin Mustapha me damagaram..
Kasa boye bakin cikinta tayi har seda tace na shiga ukku ni Murza Yarima Fa?dan
sarki kake nufifa?se kuwa ta fashe da kukan bakin ciki..
Shi abun ma mamaki ya bashi..be iya cewa komi ba se girgiza kai dayayi a ranshi
yace tsanar da take yimata har takai haka?to Allah ya shiryeki inme shiryiwa ce..
Kiraye2 sallah isha'i aka farayi ..Malan Musa bebi ta kanta ba ya fice mosque..
Tana gani fitarshi ta fad'a d'aki Maysam na sallah lokaci se jin saukar dorina tayi
nan ta dinga jibgarta harta kaita kasa ..ita kukan azaba ita kukan bakin ciki..
Ta rasa miza tayi se kawai ta kama dantsen Maysam ta gantsara mata cizo har sau
ukku har ta fitar mata da fata tace walahi baza ki tab'a auruwa ba ..senayi duk
yanda zanyi na hana wannan ma..
Wani sabon kuka ya zo mata ta d'aga hannun da niyar kaymata mari taji Sallamar
Malan Musa da sauri tace yi mun shiru munafuka sauran ki gwada wani alamu har malan
ya fahimci nayi miki wanin abun (kuji fa keda yau har da cizo)...
Maysam kam kwna kuka tayi da ga bisani ta dauro alwala ta rinda jero nafilfi tana
roqon Allah ta mata zab'i na alheri
Murza kuwa kwana tayi tana neman mafita shawara kawai ta yanke taje wurin boka ya
hana auren tunda tasan sharri baze yiyu ba tunda sunga irin wahalar da tasha a
hannuna..da wannan shawarar ta kwana
Washe gari kuwa tayi waMalan Musa karyar zuwa gidan su ta kuwa fice han se wajen
boka ''yankan wuka''
To fa Fans ya kuke gani zata kasance ?Murza zatayi nasarar hana auren nan?
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:31 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ππ
[8/17, 1:34 PM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
19__20
Manzon Allah ( ```SAW) ya ce''babu wata musiba da zata sami musulmi sai Allah ya
kankare masa wani zunubi shi da ita har ma qaya da zai taka ta sokeshi yaji zafi''
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.```
Zaune take gaban wani bakin mutum ba kyan gani shi kanshi abun tsoro ne ...dagashi
se d'an pante irin na mutanen da d'in nan ..kan wannan gashi buzu2 duk ya
cikukuye ..se wani uban ja da hakoran shi suke da..wai shi'' Boka yankan Wuka ''
Murza kuwa ki kyenkyamin shi bata jiba ..ta zauna tana zayyano mishi duk irin
abunda take bukata .....
Buga kasa yayi yayi wani d'an tsubuce2 shi ..ya jima... ya d'ago kanshi ya kalleta
a ranshi yace idan na fad'amata gaskiya aikin nan baze yiwu ba tana iya zuwa wajen
wani bokan yaci kud'intan a banza dan yaran da take son ayi mata aiki akansu sun
riqe addini wani mugun abu baze iya kamasu ba Allah ya karesu ....
Se kawai ya kece da wata arniyar dariya yace aikin da kike so ba baze yiwu ba aure
ba fashi sede a saka tsanar ta a zuciyar shi bayan auren ya saketa...
Jimm tayi tace babu abunda za'a iya yi baya ga wannan?
Wannan shi kad'e ne taimakon da zan iya yi miki kuma ko kinje wani wuri kud'in ki
ne kawai za'aci..
Shikenan amma asa harda dukanta ya ringa yi...
Wata dariya ya sake yi se kuma ya daure fuska kamar bashi ba yace bakida matsala
kud'inki dubu goma ne
Kud'in kawai ta fiddo ta aje ..ya bata wani kulli magani yace a zuba a abinci ko
ana sha a bawa yarinyar...amma ki tabbatar bata yi bismillah ba
Se wani washe baki take ta ansa tana zuba godiya kamar kyauta ya bata ..
Cike da farin cike ta dawo gida ...ta tarar Maysam ita kad'e a gidan..
Kusa da Maysam ta zauna da sauri tayi tsaye tana fad'in inna sannu da dawowa...
Yawwa jeki tatso min nonon shanu ki kawo..
Batayi gaddama ba ta tafi amma a ranta fad'i take lafiya inna yau bata zagen ba
bata rankwashen ba .....
Bayan ta kawo mata Murza tace zo zauna kusa dani ita de mamakin abun take ..
Kulli maganin Murza ta fiddo tace yauwa ga magani nan na anso miki wurin inna
ta ...na tsari ne da kuma mallakar miji ..
Itade Maysam kallon ikon Allah take..
Zubawa tayi ta motsa shi tace ungo shanye shi duka
Karb'a tayi dan ba yadda ta iya tana tsoran taci na jaki in bata shaba ...
Bismillah tayi a hankali takai kwanan bakin ta ...
Murza jitake yanzu ne zatayi bismillar se kawai da karfin tsiya ta kama tayi mata
d'ure(ee kin makaro Inna Murza dan tayi bismillah tuntuni )
Har kwarewa Maysam d'in tayi
Amma ko ajikin Murza ita murna ma take burin ta ya cika...
Ana sauran kwana goma