Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin Accident Complete Hausa Novel by FASMA

Author :  FASMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 32

30K to 33K   out of 94.8K words

(Waya baki izinin yin wannan shigar .).....
Hannunta dafe bisa kumcinta tace Momy ce ta say mun da muka tafi shopping
Wani marin ya sake sauke mata yace Momy ta ce ni kade sekuma sweetbaby na .......
Da gudu ta fice cikin room ta bar shi nan tsaye ......
Dadin ta daya da Kuyangi tun lokacin da sukaga Murad ne su ka ficewar su
Shima hanyar stair yayi ya shige daya daga cikin dakin sama ....koda ya shiga dakin
ya jingina da kofar ya rasa miyake mishi dadi zuciyar shi na wani irin zafi sai
kawai hawaye ya fara zarya a fuskar shi wanda besan dalilin yinshi ba .....nan ya
tsaya ya ringa tariyo scene din su ta yanzu da yanda take kuka wanda shi yafi kona
mishi rai dan koba komi bayason ya ga mace na kuka bare shine sila ...wata zuciyar
tace mize hana ka tafi ka lallasheta kada ma Allah ya kamaka da laifin cin zarafin
ta, gashi kuma kaikade ta sani a garin..gata yarinya ...ya tuna nasihar Fulani cewa
ya daure ya kulada Maysam ya ringa tausaya mata mareniya ce.....sanin irin zafin da
mutum keji idan ya rasa wani nashi dukda yasan seyakai zuciyarshi nesa sannan ze
iya kula da ita amma ze kwatanta ya gani..
Da sauri ya fita ya shiga dakin dayake tunanin tana ciki ...
Yana shiga ya hangota kwace bisa gado se kwasar kuka take ....
Gefen gadon ya zauna yace ke....
Da sauri ta tashi zaune tana kallonshi fuska cike da hawaye tace na'am..
Hannu ya biko mata yace zo ...
Da sauri ta rarafa tazo
d'orata bisa cinyarshi yayi yasa hannu ya goge mata hawaye yace kukan ya isa haka
nan ...
Can yace bakisan ke matar aure bace ....
Cike da shagwaba tace na sani man...
Yace to shine kike irin wannan shigar bayan da maza cikin gidan .....
Tace to ai naga basa shigowa ,ni kuma bawani futa nakeyi ba shiyasa ai .....
Ajiyar zuciya yayi yace shikenan kikiyaye kisan irin shigar da zakiyi ...ina fatan
de ba haka kuke shigar nan ba a school....
Nan ma tace a'aa bayan mun yi hutu ne Momy ta say mun a matsayin gift dan nazo ta
biyu ...
Yace to nima ki shirya gobe na kaiki shopping ki zabi abunda kike so dan kin yi
kokari amma fa kiyi kokari ki ringacin ta daya se kuma jibe mu huce can gida...
Wata dariya ta kubce mata jin zasu taga Momyn ta fulani har yar karamar wushiryar
ta tafito tare da fararen hakoran ta wanda kyawunta da tsantsar kamarta da
Sweebabyn shi ta fito besan lokacin da ya rungumeta tsam a jikinshi dudda ya ji
shok din amma wannan karon sema ya kara matseta a jikinshi har seda tayi yar kara
tukon ya dan sassauta mata ...
Ta raba jikinta da nashi tace yaya
Jibifa kayanka sun bace bazaka canzasu bane?
Ya kalla tare da mikewa da ita a hannushi yace mutafi to na fidda...Da ita suka
shiga har dakin ya ajeta ya ce ina zuwa ya dauki kayanshi yashiga tolet seda yayi
wanka tare da doro alwala jin an fara kiran sallar magrib........koda ya fito ta
dan gogge wurin dayayi yar kura tana ta kiciniyar sake zanin gadon amma ta kasa
shimfidar kasancewar yayi mata girma se turo baki take ...dariya yayi ya kama ya
shimfida ya gyara tana kallonshi se dariya take mishi yana gamawa ya yi hanyar fita
tare da fadin kiyi ki gama kiyi sallah ..tace to ...
Shikam be dawo ba se bayan sallar isha'i ..a zaune ya isko ta ta saka tv gaba se
kallon dessin animรฉ take a ranshi yace i lalle yarinya ce ....direct dining yaje ya
zauna kuyangi sun zube abinci iri2 table din a shake yake taf da abinci dana
sha .....a raina nace mutum biyu kade fa kawai zasu ci abincin nan amma ko mutum
goma aka bawa to na tabbata se sunci sunyi saura.....wani nacan kwana ma zeyi
beci .ba.Allah de shi kyauta...
Ganin bata alamun zowa yace ke zonan.kiyi serving dina inke bazaki ciba ......dan
shi ko a gida baya barin kuyangi su zuba mishi sede Momy ko kuma in bata nan ya
jira har lokacin dazata zo ..in kuma a England ne to wannan shi ze zuba abunshi..
Cike da shagwaba tare da turo baki dan bataso ya katse mata kallon ba .....
Tana zuwa ta bude ta zuba mishi ...ta kama hanyar komawa ...yace ke zonan ...ya
zare mata ido yace zauna kici maza ...ganin ta saka abincin gaba ta kasaci yace ci
mana...
Dan kadan ta taba ta tashi ta koma fallon .....
Bayan ya gama shima falon ya zauna tare da canza tasha zuwa discovery ch .....tun
tana kallo har bacci yayi awon ga da ita...
Shima sha daya nayi ya kashe komi tare da daukanta ya nufi daki da ita...
Love you all
Fasma
Ahmed Gumel
[9/2, 9:53 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š_*
[9/2, 9:57 AM] A A Dboy: ๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

53__54
Story&Written
by
*FASMA*
Dedicated to all my fans
*Queenbaby ina kika shige ne kwana biyu keda Ummu Usman..?Allah de yasa all is
fine....munyi* *missing dinku matuka .. pls come back soon...*
*Dubun gaisuwa zuwa ga yan kungiyar mu na STAR ,W,Ass .hakika ina alfahari daku *
Allah* *ya qara hada kammu* ...
*
*Ina yinki irin totaly din nan tawan Arfat ba ....ina jin dadin yanda kike kula
dani da nunan kauna Rabbi ya kara dankon zumunci** ......
53__54
```
Manzon Allah (SAW) yace''tsakanin mutum da shirka da kafirci shine barin sallah
kawai''
Muslim ne ya rawaito shi.```
Da asuba ta rigaye shi tashi tayi mamakin ganinta a dakinshi ...direct tolet ta
nufa ta doro alwala ta kabarta sahlan nafila dan har yanzu lokacin sallar asuba bai
yiba ...
buda idonshi yayi ya saukeshi akan ta tanata lazimintz yayi matukar mamakin ..jin
an fara asalatu yasa shima ya doro alwalan yayi raka'atanil fajr ya na gamawa ya
nufi masallaci don yin sallar asuba
Itama tashi yayi tayi ..
Bayan ya dawo ta duka har kasa ta gaidashi
Ba yabo ba fallasa ya amsa ...nan ta fido alkur'ani ta fara tilawa tare da
azkar ....shima zaman yayi sukayi tare sanan ya jata suka koma .gado dukda de kowa
a sharenshi yake kwance
.
Bai bude ido ba se wajejan goma na rana ......beyi mamakin rashin ganinta
ba ...wanka yayi ya fito cikin shirin shi ..
Tana zaune ita kade ta saka tv gaba ya fito .......
Kare mata kallo yayi daga sama har kasa shigar riga da wando ne a jikinta na
english wear ......kayan ba karamin kyau suka mata ba .....ga ba dan kwali a kanta
kitson nan ne ''tsinar shimkafa'' akanta duk ya zubo bisa kafadinta .....da sauri
ya dauke kanshi jin zuviyar shi ta fara sauya kid'a ...
Direct dinning ya nufa ..ya zauna...
Tana ganin haka ta bishi itama ...
Arish da pepper soup ta zuba mishi da wainar shimkafa se ruwa tea .......ta sakashi
gaba tana kallo ....
Be dago kai ba ya fara ci tare da fadin ke har kinyi break dinne ..?
Ina Maysam bata ma san yanayi ba ta tafi duniyar tunani ....a ranta tace ita bata
taba ganin mutum me kyau irin yayanta Murad ba kamarsu daya da babanshi .......
Dago kan da zeyi jin bata amsa meba ai kuwa idonsu suka sarke jikin juna ...dama ya
kurbi tea ne ai kuwa se ya sarke shi ya shiga tari ba shiri .........itam a kuma
seta rikice gaba daya ruwa kawai ta iya bashi yasha tare da dan bubbuga bayanshi
irin yanda taga anayi....
Da kyar tarin ya tsaya yace dama an zo ansaka mutum gaba ba dole ya sarke ba...
Tayi dariya tace kasan mi yayana ..........?
Ya gimtse fuska yace miye ne....?
Se jikinta yayi sanyi tace a'a bakomi shikenan ma......
'Dage kafad'u yayi irin ''je m'en fou''(i don't care)din nan.... ...a ranshi yace
yarinyar nan sena dena sake mata fuska dan kada ma ta rena ni.irin wannan
kallon ....
Be gama tunanin ba ta tashi ta barshi nan .....
Ya bita da kallo tare da tabe baki yaci gaba da cin abincinshi amma jikinshi yayi
sanyi....
Falo ta zauna se turo dan karamin bakinta take wai ita adole tayi fushi ......
Bayan ya gama ya dawo falon ya kalleta shi abun ma dariya ya bashi yanda take turo
bakin .....
Cike da wayo yace to ni natafi shopping din ........tunda kinyi fushi ai seki zauna
tsaran gida yayi hanyar fita a palon ....
Da sauri ta mike tare da sakin fuskar tace kai yaya bafa fushi ne nayi ba...
Ya juyo yace to ai naga se wani turo baki kike kamar shantu...
Bubbuga kafa ta farayi akasa irin na shagwababun yaran nan ...
Ba karamin birgeshi tayi ba dan haka sweetbabyn shi keyi .....
Tsayawa yayi yana kallonta ganin abun bana karewa bane yace to shikenan jeki ki
shirya kizo mutafi ....kuma cinq(5)mn na baki...
Da gudu ta fice dakin ....... Bata jima ba tafito cikin shirin ta na atampa riga da
''jupe''(sket) se dan gyale data yafa ....tana fito wa yayi mata nuni da hannu data
je ta sako hijab...batayi musu ba ta koma ...hijab din ya fice gwiwar ta .....
Suna fitowa dogarai suka fara kwasar gaisuwa ansar key din yayi daga hannu driver
ya shige itama tana ganin haka ta shiga ...suna gani ya shiga mota suma suka fara
haramar shiga sauran motocin amma se ya daga musu hannu ya na nufin baya
bukata .......
Ba karamin mamaki dogaran sukayi ba amma babu yanda suka iya haka suka dawo..
Har sun shiga mota yace ke wai bakida nikaf da safa ne?
Girgiza mishi kai tayi......
Dan jim yayi sannan ya tada suka tafi ...
Shopping mall ya kaita kayan kam babu irin wanda bata dauko ba kama daga
lesh ,,,atampa ....daganan suka nufi bangaren turare da man shafawa ...ganin be
dauki komi ba yasa ta dauki wasu mayun turare tare da mayyukan su da sabulunsu har
kala biyar duk na maza se kuma irin set din na mata shima kala ukku...
Bayan sun gama layin nikaf da safa ya nufa ..ya jibgo mata yana fadin ko a school
ne to ki tattabatar kin saka safar nan ...ehe...
Ita de to ne nata bayan sun gama ya kaita wurin wasan yara ...
Yana daga gefe se wasannita take a ranshi yace wannan ba aure ba aka mun raino de
aka ban .....
Kai ranar yakaita wurare daban2 ..se la'asr likis suka dawo ..bayan sunyi sallah
direct dinnig suka nufa dan sun kwaso yunwa......
Set din turaren nan kala biyu ta doko ta bashi tace naga baka sai komi ba shi yasa
na dokoma...
ba karamin mamaki yayiba nan ya amsa tare da fadin ashe. de bakida rowa ..
Dariya tayi tareda rufe fuskar ta..
Shima dan murmushin gefen baki yayi ...
Washe gari kuwa sha daya na safe ma acan tayi musu inda suka bar dogarai da kuyangi
zasu shigo motocin su dawo dan su jirgi suka biyo ,,,dukda yasha kauyanci wurin
Maysam..dan ita jirgin ma se ranar tayi mishi kallon gaba da gaba ...
murna wajen fulani ba'a ma zancan girke2 iri2 tasa aka yi musu ...sosai taji dadin
yanda Murad ya rage hantarar Maysam a daya daga cikin dakunan fulani Maysam ta
sauka yayinda Murad ke nashi bangaren ...
Da dare bayan sun futa ta fito da turaren ruka ta bawa Fulani set biyun na mata da
buyu na maza tace wannan naki ne keda dady ne (Sarki) se kuma wannan ta fiddo wasu
set din iri daya guda biyu tace wannan kuma daya na Abbana ne dayan na inna
Murza...
Zo kaga Murna wajen Fulani kamar wacce batafi karfin kayan ba ..nan ta ringa saka
mata albarka..dan gaskiya taji dadi kuma ta yaba da hankalinta..
Shima me martaba ba karamin nuna jin dadin shi yayi ba tare da saka mata
albarka....
Lokacin da aka jewa da Malam Musa da wannan alheri har kukan murna da jin dadi yayi
ya saka mata albarka yafi cikin kwando...sab'anin Murza da bakin ciki saura kiris
ya kashe ta wunin ranar tayi shine tana tunanin yanda zatayi da Maysam tsaki
tayishi yafi sau a kirga a ranta tace wannan yana nufin kenan tana can tanjin dadin
rayuwarta ko....?can tace kai wly da sakema wai abawa me kaza kai ....
Madina sosai ta sawa lamuran waziri ido ta baza bayinta ko ina dan ganin mi waziri
ke barkatawa dan yanzu yama dena shigowa part dinta .. Aranta tace kowa yaci tuwo
dani to miya yasha...
.
Su Murad kuwa Tunda sukazo tare suke yawo duk inda yayi tana binshi dare ne kawai
ke rabasu ba karamar shakuwa da juna sukayi.ba....har Mahmud yana tsokanarshi da
cewa kode ya fada tarkon son Maysam ne...
Shikuwa se ya yatsine fuska yace ina abunso anan dan farin nata ko dan dogon hanci
da karamin bakin ze jani...yaja tsuka ...yace yarinyar da ko kirgen dangi ma bata
faraba ina abunso a jikinta .....
So daya ne nakeyiwa Sweetbaby na..wannan itama tanacin alfarma fulani ne yo banda
wahalar raino ma ba abunda nake....
Mahmud ya sheke da dariya yace gaskiya nawan ka iya tsara mutum .fa.....da wani ne
na tabbata ze kama zancen nan...amma yo ai ko irin kallon dakake binta dashi ko
makaho ze gane bare aka zo ga zancen kishi .....
Murad yayi kicin2 da fuska yace a'aa ya ishe ka hakafa inayin haka ne dan kare
martabar aure tunda de an rigaya an auramin ita babu yanda zanyi ne...
.
A bangaren Maheeba kuwa ba karamin tada hankalinta ba tayi dan ita se yanzu tasan
Murad yanada mata duk da taga yarinya ce karama aman kyaunta ya tsora tata...
Nan fa ta dagawa mahaifinta Waziri hankali .....babu yanda ya iya haka yayi shiri
zuwa ga Murad da zancen.......
Zaune yake shida Maysam datake kan cinyarshi se wasa take da sajen fuskarshi tana
dariya yayinda shikuma yake daddana waya a lambu ga kayan marmari cike a
gabansu ...
Ganin waziri yasa Maysam sauka ta zauna a kasa kusa dashi...jin ta sauka yasa ya do
kai ya kalleta seyabi inda take kallon ..tsinkayo waziri yayi yana magana da
dogaran dake kofar shigowa lambu...
Iso akayi wa waziri ...bayan ya kwashi gaisuwa se kuma yayi shiru ...Murad ma shiru
yayi mishi dan yan Mulkin sun motsa ..
Can Waziri yace ranka shi dade inason yin magana dakai ...
Hannu ya daga alamun ya fadi yana saurarenshi ...
Kallon wurin da Maysam waziri yayi ..cuwat ta mike zata basu waje..Murad ya dawo da
ita kan cinyarshi ....
Waziri a ranshi yace tirkashi wata zufa ta karyo mishi .....
Can yace dama zancen wajen y'ata ne....ina son ka aureta ....
Ba Murad ba hatta Maysam da sauri ta dago ta kalleshi ...Murad ma kallon nashi yayi
yace....
Wash kuyi manage da wannan...
Bansan haka masoyan wannan book din keda yawa haka ba ...a gaskiya ina alfahari
daku Rabbi ya bar kauna da zumuncin mussaman yan group din HAUSA YOUNG NOVEL na
facebook ..ina jin dafin yanda kuke nuna kaunar ku ga book din nann...ban manta da
kaiba Ahmed Gumel ...godiya me tarin yawa Alherin Allah ya kaimaka a duk inda
kake......sauran groups ban manta dakuba kusan ina yinku irin dayawan nan
...
Fasma ce
Ahmed Gumel

55__56
```
Manzon Allah (SAW) ya ce''me zuwa gyadar da marar lafiya ,ya kama wata hanya daga
hanyoyin aljanna har yaje ya dawo''
Muslim ne ya rawaito shi``` .
Ba Murad ba hatta Maysam da sauri ya kalleshi....Murad ma kallon nashi yayi se kuma
ya kalli Maysam wacce tuni yanayin ta ya sauya......
Ido cikin ido ya kalli waziri yace ''non je n'en ai pas besoin''(a'a bana bukata)
wannan bashi ne karo na farko ba dakazo min da zancen auren y'ar ka amma ina son
wannan ya zama na karshe .....yace kanacin darajar tsufan kane da wani ne da nasa
an hukuntashi. .ya cigaba da fadin idan dama wannan ce maganar dakazo muye to kana
iya tafiya na sallame ka ....
Waziri ba karamin mamaki yayi ba haka jiki ba kwari ya tashe ya zazzage wandonshi
ya fice a ranshi kuwa fadi yake taya hakan ta kasance bayan boka ya jaddada mun
yuyuwar hakan....har ya bar lambu yana tunanin wannan al'amarin ....
Yana tafiya Murad ya kalli Maysam dake cinyar shi duk tayi wani kicin2 da fuska duk
da karanci shekarun aman taji zafin furucin waziri....
Yace yade yar gidan Momy ke baki san fushi baya miki kyaune ba .yanda fa kika son
kunun safe kirtup din nan to haka kike in kinyi fushi.........
Babu komai ta ce mishi tare da yin haramar tashi daga cinyar dan inhar ta tsaya to
zata iya fashewa kukan da ita kanta bata san dalili ba...
Dawo da ita yayi ....yace ke bason iskanci to mi akayi miki ne daza kiyi tawani
turowa mutane baki ya shantu....
Dama me nema se kawai ta fashe mishi da kuka tare da tashi da gudu ta barshi
nan ....
Shi abun ma mamaki ya bashi ....
Tashi shima yayi ya mara mata bayan.....
A palon fulani ya tarar da ita se kukan shagwaba take zubawa fulani kuma tayi2 ta
fadi mata abunda ya sakata kuka amma taki fadi ,,,,se aikin rararshi take ....
Bata san da shigowarshi ba se jin gaida fulani .data ji..
Tsit kakeji tayi ,,,tayi saurin tashi tare da fadin Momy bari na shiga ciki
Tana shiga ba ko kunya Murad ya bita dakin ...
Abun ba karamin mamaki da birgewa ya bawa fulani ta bisu da addu'a kara samun zaman
lafiya tare da kara hada kansu .tayi dan murmushi....
Shi kuma ya na shiga yaganta a kwance bisa gado tana kuka ciki2...bisa daya daga
cikin kujerun dakin ya zauna yace ke taso kizo nan ...
Firgit ta tashi ta zauna tayi rau2 da ido ...
Yace ke wai bada ke nake ne ba ''viens ici''(zonan)
Jiki ba kwari ta taso tazo tana murza ido tace gani yaya...
Daga zaunan ya dauketa ya dorata bisa cinyarshi ya goge mata hawayen ....yace wai
mi yasaki kuka..
Shiru tayi mishi ...
Can yace zaki sha chocolats ?
Ta girgiza kai alamun a'a
Yace to alewa fa?
Nan ma tace a'a
Ace cream fa?
Naman ta girgiza kai...
Yace to mikike so ?
Ta ce ba komi ....
Shikenan amman kukan nan ya isa haka kada ki jawa kanki ciwon kai...
Ta ce to......
Algyabar ya fidda mata yace to maza je kiyi wanka dan kiji dadi jikin ko kinaso na
miki ne?
Kamar da wasa tace e'e...
Be tsaya bata lokaci ba ya fidda mata kayan suka shiga tolet din ya wanko ta tas ya
dado ta a towel .....
Koda ya fito ya lura duk kayan jikin shi sun bace da ruwa komawa yayi tolet din
kafin yace ki tabbatar kin saka kayanki kafin na fito .sanan ki tafi dakina ki
dokomin kaya comlet guda......dan baze iya fita da kaya a jike haka ba ..kuma shi
baze bari har su bushe a jikinshi ba....
yana fitowa ya ganta kwance bisa gado bacci ya kwashe ta Abunka da sauran kuka....
Allah yasoshi akwai irin rigar wankan nan a tolet din kuma tanada tsayi dan har ta
fice mishi guiwa .......
Abun takaici yama rasa yama zeyi ...shima gadon ya hau ya kwanta kan kace mi bacci
yayi awon gaba da shi...
Ta rigyashi tashi ya saka kayanta ta dau wayarshi ta fara game abunta dan ita tama
manta da wani doko ishi kaya.....
Tana tsaka dayi kiran Mahmud ya shigo batayi wani dogon tunani ba ta dauka tayi
sallama tare da fadin ina kwana yaya Mahmud....
Cike da

11 / 32