Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin Accident Complete Hausa Novel by FASMA

Author :  FASMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 32

54K to 57K   out of 94.8K words

fulani ...tace son kai ne...
Cike da kwarin guiwa jin bata dau abun da zafi ba ya ce nine Momy ..dan Allah ku
yafe mun wly basan miya sa man ba yana fadin yan kuka..
Godiya ta shiga yiwa Allah (SWT)daya kubutar mata da son dinta ....dama ai addu'a
bata faduwa kasa . kuma ```Manzon Allah (SAW) ya ce'' idan zakayi roko ,to ka roki
Allah ,kuma idan zaka nemi temako ,to kanemi temako a wurin Allah.(Tirmizi)
```
sanin bayin kanshi bane yasa tace na yafe muka daman can ban rike ka ba ...nan ta
shiga yi mishi nasiha da ya rike addu'oi dayin sallar nafila..dan ```Manzon Allah
(SAW) ya ce''Addu'a itace ibadah (Tirmizi``` )
Sosai zuciyarshi tayi wasai ...sun jima suna wayar sanna ya kashe tare da fadin se
zuwa safe ze kirayi Sarki dan har sha daya tayi...seda safe sukayi wa juna tare da
gaya mata gashi nan cikin satin nan in Allah ya yarda.....cike da murna kamar karsu
kashe wayar ..har ze kashe se kuma ya sake fadin Momy ina Yarinyar nan take ..
Ganin dare yayi Fulanin kar sarki ya jita shiru dan ita keda duty yasa tace tana
nan she is fine tana can tana wurin karatun ta...
Bakinshi yayi nauyi tambayar a 'ina se kawai ya kashe kiran ..
Fulani dan murmushi tayi tare da fadin ni kam ido ne nawa...
Yana kashewa ya dannawa Mahmud kira ...
Ringing biyu shima ya daga duk jiyake su Mufeedah ne shima...
Amman mi se yaji muryar Abokinshi wanda ko cikin dubunan jama'a ze iya sheda ta..
Cike da zumudi yace M2 kai ne ko kuma kunuwana ne suke mini gizo...
Murad yace nine aboki pls kayi hakuri da abunda....
Be gama ba Mahmud ya katse shi da fadin ai komi ya fice a kiyayi gaba de...shima de
nasihar rike addu'oin tsari na safe da yamma yace ya rike kamar yanda fiyyenyen
Hallita ya umarce mu da yin su...(suna nan cikin HUSNUL-MUSLIM)..
Murad yace hakika ka cika aboki na kwarai Allah ya bar kauna da zumunci masu
dorewa...
Ameen ya amsa ..
Se kuma Murad ya ce kenan de yar gidan Momy bata ci jarabawa ba ko kuma fasa yi
musu tsallaken class din akayi ne dan na tambayi Momy tace tana can wurin
karatun...
Mahmud yace ita kuwa suka samu dan har da mention excellent SANADIN haka har
gwanati ta tura su karatu England itada kawayen ta ...
Yan zu haka suna can. enland...
Tunda Mahmud ya fara bashi labari yake jin dadi har lokacin daya ce mishi wai sunan
nan england sannan hankalin shi ya tashi wani irin bacin rai da kishi suka da
baybaye shi wanda acewarshi martabar aurenshi yake karewa..
Cike da masifa irin tashi yace What?da Izinin wa?...waye yayi mata jagora batare da
izini naba?ya ci gaba da fadin jinake na jima da gayamata cewa bazan barta tayi
karatu anan ba......?
Mahmud shima daya kai kololuwar bacin rai yace..
The more you comment ,the more i typing.. .
Bazan gajiya da fadi muku ina yinku irin totaly din nan
Fasma ce
[9/2, 10:45 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[9/10, 10:28 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* πŸŒŸβœ¨πŸ–Š
( _Home of spécial 🏑&extraordinary writers_ )


🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

S.W.A✍

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

*Alherin Allah ya kaimu muku a duk inda kuke aminan kwarai MOMYN HADJIA & MY
AISHA (NANAS)ina jin dadin shawarwarinku da nuna kulawarku a gareni Allah ya bar
kauna da zumunci me dorewa a gaskiya ina yin ku* 😍😘❀

__ban manta dake ba Garkuwa ina jin dadin yanda kike bibiyar littafin nan Rabbi ya
bar zumunci......_ 😍❀❀❀
_Fans ban manta daku ba kusan ina yinku irin totaly din nan har kullum_ ❀😍




Dedicated to all my fans😍❀




πŸ…Ώ 81__82
``` ```Manzon Allah (SAW) yace''kowane abu me sa maye haramun ne.
Muslim ya rawaito shi
```




[31/07/18 Γ  22:23]
Mahmud ya kai kokokuwa bacin rai ..ya ce to Momy da Sarki suka bada izini..........

Jagora kuma da kake wani tada jijiyoyin wuya nina na mata shi ...,,

Sanna da kake batun ai tasan bakada ra'ayin tayi karatu acan .to mu aljanu ne da
zamiyi aruwar sanii komi kake nufi tunda de mu baka taba fada mana bz.....da kaji
yanda yake maganar kasan cinkin bacin rai yake yin ta.......

Se kuma jikin Murad din yayi sanyi yayi ajiyar zuciya yace sorry aboki ba haka nake
nufi ba cikin sassauta murya yayi maganar

Mahmud ya sauke ajiyar zuciya shima ya ce shikenan amma a tari gaba ...cike da
tsokana ya ce kawai kishi ya wani rufe maka ido har baka san maganar dakake fadi
ba..

Ya leman kuwa yace kishi fa?ni ba wani kishi kawai ina son kare martabar aure
nane...

Dariya Mahmud ya yi daman yayi zaton abunda ze fadi kenan ....

Nan Mahmud ya gaya mishi komi game da makarantar har sunan ta ...

Shi kanshi besan irin yana yin da yake ba yana de amsawa da to...

Shi kuma Mhamud dan ya kara har zukashi ya ce ..bari na baka number ta dan kada
kasha wuya. .

Wani yawu me dacci ya hade yace Mahmud kun kashe ni yanzu har da waya kuka
bata ..fadi yake kamar zeyi kuka ..

Mahmud ya kwashe da dariya ..seda yayi me isar sa har Murad ya hasala dan
haushi ....yace se anjima..

Da sauri Mahmud yace kenan de baka bukatar number ko...to seda safe...

Da sauri yace bangane ba bana so ..?kaji na fada da bakina ne...kawai kaban in zaka
ban kasa2 yake fadin kawai ana so a bata min yar renota a wani zo harda bata phone.
To wai ma itada taje karatu miye na wani bata waya.

Mahmud daya jishi yace da kuwa kasani iphone7 ce..

Kamar zeyi kuka yace wly kun gama dani ina yarinyar nan ina iphone7 miye laifin ki
saimata touch ligth ma.....

Mahmud daya samu abun tsokana yace kai har da fa Whatsapp ,twitter,facebook
etc ..duk ta iya kai tama kware yanzuu...in fada maka kuwa

Katse kiran kawai yaye ba tare da ya anshi numb wayar ma tuni zuciyar shi tashi
bugon zut3. Banda huci babu abunda yake .Mark da ke kusa dashi ya dafa shi yace be
carefuly .mana..bawani abun tada hankali bane kayi hakuri duk da banji miya ce ba
amman ina so kabi komi a sannu.kada kayi saukin yanke hukunci cikin fushi daga baya
kayi da na sani....nan yayi ta tausarshi har yaji sanyi a ranshi ...basu fita ba
daga massalacin har seda suka gabatar da sallar isha'i sanna suka komo kowa ya
nufi gidanshi .. ...

Yana nan kwance bisa makalelen gadonshi har wajejen sha biyu na dare amma ya kasa
bacci kai alamun jima be jiba kawai duk maganganun Mahmud ne ke masa yawo a
kwakwaluwa ..kasa hakuri yayi ya kalli agogo yaga sha biyu har da minti 5. .dan
haka ya danna mishi kira dan yanzu yana da yaki nin sun idar da sallar asuba acan..

Lokaci shi kuwa ya dawo daga masjid kenan yaga kiran Murad ..seda yayi murmushi dan
yasan mussababin kiran .....
Yana dagawa yace kai wai har yanzu bakayi bacci bane ko kuma tunanin yar renon naka
kake....

Seda ya ja tsaki yace ni ba wannan nakira ka fadamin ba ...number zaka bani ..kuma
harry up ina da abunyi..yana wani basarwa wai dan kadama yaga damarshi....

Mahmud yace ka biya tukon....

Kamar ya shiga wayar yake ji yace wai kai wani irin dan rainin wayo ne ...yace ka
fada ko nawane kasan de zan iya saye ko?...

Yace amma de kasan number nan zatayi tsada ko ?dan kuwa me wayar....

Da sauri ya katse shi da fadin ''je t'en supplis''' kaban number nan ..wai mi
natare maka ne a rayuwa da kake son yi mini katsa landa haka ne .....

Mi Mahmud zeyi inba dariya ba yace shikenan bari na turo maka..

No kawai ka gayan yanzuu....

Number ya bashi yana fadin ka gaida mun yar renon taka..

Katse kiran kawai yayi dan yaji haushi ba kanan ba ....

Yana bashi ko save dinta beyi ba ya danna mata kira.....

Haba yaya Murad sha biyun dare ne fa. ...ai lokacin Maysam ta kai goma ma na
bacci....
Seda yayi mata missing call 5 bata dagaba ...

Murad ba uzuri nan ya fara fadin zamu hade ne inba ma raini ba ina kira kiki wani
dauka....tsaki daya ja yafi a kirga ..haka ya kwana da kyar barawon bacci ya kwashe
shi...


Washe gari Tun tashinta da asuba taga miss call 5 amman dataga sabuwar number se
bata meda kiran ba kai daga karshe ma kashe wayar tayi dan yau wani pratical
zasuyi kuma abayan gari sannan ba'a barin su suyi waya shi yasama basa fita da ita
duk ranar da zasuyi...


Murad kam yau har makara ma yayi salllar asuba seda gari yayi dan haske ya farka a
gurguje yayi sallar yayi shirin fita . amman kafin nan ma ya mata kira yafi
akirga yajita swich off....tun lokacin zuciyar ta fara lugude....ya na fita direct
hanyar dazata kaishi makarantar yayi dan yau ko office baya jin ze iya
tafiya..kira yayi ya sanar da Mark cewa baze samu damar zowa ba.....
Cikeda zullumi ya isa makarantar ..be tsaya wata2 ba ya shige wurin shugaban
makarantar ..dayake bawani boyayye bane dan haka tarba ta mussama shugaban yayi
mishi.
Nan yayi mishi bayanin abunda ya kawo shi.

Babu mata lokaci shugaban ya fara bincike...

Can yace ai kwarai a nan take karatu su biyar gwamnatin kasar Niger ta turo
su...amma yanzu basa nan sun fita bayan gari yin wani pratical...kuma gobe ma can
za su tafi...

Ranshi in yayi million ya bace..amma se ya danne yayi mishi godiya tare da fice
wa .....ranshi inba suya babu abunda yake ..a ranshi fadi yake dole ma ta bar
makarantar nan .....


Su Maysam basu suka dawo ba se wajejan shida na yamma . duk sun galabaita......

Suna zuwa ta kunna wayarta da zumar yi wa fulani shagwabar wuyar dasu sha yau...


Gefe daya kuma Mufeedah ce ke soyewar ita da Mahmud ....yanzu kam ba'ace wa komi
dan sun shaku da soyyarsu.. Can yace wai ina kanwata ne.

Gatan nan kusa dani kona bata ne..

Ee yace..
Bayan ta bata suka gaisa ..yace wai mijinki ya kiraye kuwa jiya....

Dafe kirji tayi ta wani waro ido kamar yana ganinta tace wayyo na shiga goma .
kadade fa shine ya kirani jiya .......
Tace ya Mahmud kace tawa ta karemun dan naga number england ce sede ban kawo cewa
shine ba shiyasa ma ban mede kiran ba...

Mahmud yace ki kwantar da hankali ki ..nan ya bata labarin duk abunda ya faru
jiyan.

Wani uban tsale tayi ta dane bisa kan Mufeedah tare da wani ihun murna tace kai
Alhamdullilah ..lallae Allah abun godiya ne. ...

Cike da murna da zumudi har jitake kamar tayi fiffeke ta ganta kusa da yayanta..

Wayar ta bawa Mufeedah tashige bayi abunta ..se taji ma duk wata gajiyar da suka
kwaso ta tafi ..fuskarta banda annurin murmushi babu abunda take. ..


Suna zaune suna wani dan exercice su ukku.....lokacin har goma tayi dan haka suna
gamawa kowayi shinfidar shi dan bawa gangar jiki hakkin ya...

Lafiyar gado suka bi ....can se wayar Maysam ta shiga tsula kara...
Da kamar bazata dagaba dan har bacci ya fara dibanta...
Amman ganin number jiya ce yasa ta wartsake tana mutsitsike ido..tare da zubawa
wayar kallo kurr

Kasa dauka tayi se wani waro ido take kamar wanda tayiwa sarki karya.....

Can de tayi shahada har ta kusan tsinkewa ta daga ...
Da farko yayi niyyar yima mata masifa ..aaaman mi ..tana doka sallama yaji shi har
cikin kokkon brain din shi. A take yaji ranshi yayi sanyi ...muryarta kade data
daki dodon kunneshi seya ji ta mishi kwarjini ....yaji baze ma iya mata masifar
ba..

Seda ya sauke ajiyar zuciya sannan ya amsa sallamar ..
Tofa ita kam har seda ta wani lumshe ido jin muryar shi dan ta sheda Muryar....
Tace yaya ykk?ya two days?ya aiki?ya fama da jama'a?

Wannan karon shima lumshe idanun yayi har besan lokacinda murmushi ya subuce mishi
da fadin haba duk wannan question din wacce zan ansa ne ?dan ayanda take wata
maganz kasa2 ko su Mariam da suke daki daya basu jiyo ta ba

Kamar tana gabanshi ta wani turo baki tace duka.....
Jin shiru yace ..to am fine ...komi Alhamduliilah...

Tunda ya fara magana tayi shiru a ranta fadin take masha Allah ...yaya bade dadin
Murya ba ....ko dayake ma ai daga bakin nan tafito wanda nakeji kamar na saka a
biredi na cinye shi .... .(πŸ™„to mikike jira🀨)

Katse mata tunanin yayi da fadin haka mukayi da ke ne?jinake na dade da cewa
bazakiyi karatu a England nan ba?kuma nace ba yanzu zaki fara aiki da waya ba amma
sedakika amsa ko? to wly..

Da sauri tace haba yaya na ..yaushe rabon da ka ganni,ko kaji murya ta ma seyau
dana ke daukin ka seka shiga yi muni fada...ta fada cike da kissar kamar zatayi
kuka. ..ta cigaba da fadin kuma wly ni duk agajieye ma nake duk bacci ne tak ado
na....pls yaya kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba...am so sorry..


Duk se yaji ba dadi ya tausaya mata yace shikenan bari na barki haka amma fa make
sure zamu cigaba da maganar nan gobe....

Da sauri tace kada kashe wayar nan ni ban gaji da hirar ba...

Yace to ai nima ban gajin ba se de zanje aiki gobe kuma kema gashi pratical
zaku ....

Har zasuyi sallama yace yauwa daman dan na fada miki yanzu kina da abokiyar zama
dan nayi aure.da...

Bata bari ya karasa ba ta kashe wayar tare da sakin wani kuka kasa..2...

Yau itama kam bacci se barawo ne ya saceta ..dan maganar wai yayi aure se dawoma ta
take.....


To fa😳😳😱MURAD aure yayi kuma 😁😁
Kenan de Maysam anyi mata kishiyaπŸ˜…...kai abun nann yayi mun...πŸ™ŠπŸ™ŠπŸ™ŠπŸ™Š


Ina yinku irin sosai din nan❀😍



Fasma ce 😘
(yar mutan Zinder😘 )
[9/10, 10:28 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[9/11, 8:40 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* πŸŒŸβœ¨πŸ–Š
( _Home of spécial 🏑&extraordinary writers_ )


🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

S.W.A✍

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ




Dedicated to my SAMBABY😍❀




πŸ…Ώ83__84



```
Manzon Allah (SAW) ya ce''kunya tana daga cikin imani''
Bukhari da Muslim suka rawaito shi```




[01/08 /18 Γ  22:58]A bangaren Murad shima beyi wani bacci ba. .nan zuciyar shi ta
fara cewa why2 zaka fada mata nee.....ganin baze iya jurewa ba yasa ya danna mata
kira amma har tagama ringing ba'a daga ba ...kai daga baya ma kashe wayar Maysam
tayi ..duk se yaji babu dadi ..wata zuciyar tace mishi yo semi in ta kashe
wayar ...ai k
duk lefin kane dan kana sakar mata fuska ne har taga damar renakai . kawai abunyi
anan ka shareta..kai mima ze hana ka tafiyar wajen su Momy ....

Yana ta wasi2 ...can shi kade yace kai baze yiyu ba .....

Kiran sallar farko a kunnen shi ..tun da ya tashi yake ta danna mata kira amma har
lokaci a kashe ..zuciyar shi ta raya mishi kawai ya iske ta school din mana..ya
kuwa yi na'am da wannan shawarar..

Karfe bakwai da rabi ma acan tayi mishi ..amma cikin rashi sa'a har sun tafi daya
iso ...ranshi in yayi dubu ya bace ..ya shiga motar shi yayi gida dan shiryowa
office.....yana tafiya yana jan tsuka tare da buga sitiyarin motar shikade yake
fadin zamu hade ne ...se kin san ni kika kashe wa waya...


A bangaren Maysam kuwa tun tashita asuba su Mufeeda suka fahimci tana cikin
damuwa ..kwata2 yau bata walwala.....komi cikin fada take yinshi

Kuma gashi ta matsa musu kan su shirya yau bus din wuri zasu shiga ..ganin
yanayinta yasa basuyi wata gadama ba suka shirya ...su aka fara kaiwa wajen dasuke
pratical din.....
Bayan sun iso ..suka jata can wani gu inda babu sauran dalibai ....tsakiya suka
sakata a tare suka dora hannuwansu a kafadarta ....
Suna kallonta Mariam tace what happen to you Maysam ?ko wani a cikin mu ya bata
miki rai ne?

Mufeedah tace haba Maysam kada ki dau halin da naki ba ...tun tasowar mu muna
tattala junan mu ..pls muna me baki hakuri inhar mu muka miki wani abun...ki sani
komi yayi zafi maganin shi Allah. .ki yawaita fadin innalillahi. Wa inna ileyhi
raju'un ...
Kuma ina me kara baki hakuri ..

Da sauri Maysam ta rufe mata baki da hannun ta ..kamar me jira kawai ta fashe musu
da kuka ..

Cike da mamaki da tsoro suke kallonta ..a tare suke fadin inna lillahi.....miyayi
zafi hakane wai Maysam tuni suma idon su har ya ciko da kwalla suka ce pls say
something mana .....


Da kyar cikin gwanji kuka tace yaya Murad ne yayi mun kishiya.. .

Duk se suka ji wani mugun tausayinta ya dirar musu se suka rumgumeta suna
lallashi ..

Mufeedah tace haba tripleM nasan kishi halas ne kuma mun san yanda kike son mijinki
amma kiyi hakuri kuka bana naki bane. Lokaci yayi da zaki fuskanci miji ki ki
bashi kulawar da gatan da kowani namiji ke samu..yanzu da da badaya bane ...kinsa
ciwon kanki ....
Mariam tace sanna shawara da zamu baki anan itace anan shine kiyi koyi da kishi
irin na matan Manzon Allah(SAW) bawai kizo kiyi ta wani tada jijiyo yin wuya ba ki
tada hankalinki ki tadawa mijinki shima ....
Sanna kisani cewa su maza an halasta musu da su auri mata 4 in de har zasuyi
adalci a tsakani ....Shi aure ana yinshi ne saboda asamun nutsuwa na sani kishi
dole ne amma bana hauka ba. ....

Mufeedah ta kara dace wa. Kuma shi namiji inde har yayi niyyar yin auren shi to
kisani ba wai fadanki da maseefar ki ,ko fushinki ze sa ya fasa ba dan a lokacin
giyar amariya na layi da ,,in kinga kinyi nasara da wa'inan to dama Allah can ya
nufa ba matar shi bace..dan namiji in...ko kuma inkiyi wasa ma ya tsinke taki
igiyar..dan dole se kin kauda idonki daga wani abun dan gujewa duk wata fitina..

Mariam tace ina me baki shawarar da kiyi zaman amana tsakanin ki da kishiyar
ki ,,dan kuwa kota cuceki Allah baze barta ba .....

Mufeedah tace sanna ki kasance macen da akullum zata ringa tunatar da mijinta kan
yayi kokari ya ringa kwatanta adalci ..bawai ki zamo wacce tana kallo mijin ta baya
yin dede a tsakanin ku ba amma ki kasa tunatar da shi kai har ma wai ki zanki gani
ko yafi sonki ko kuma kina takamar wai ke wace abace ..to kisani duk abunda kayiwa
wani to kai ma kada ka cire tammahani wata rana se am maka. ..sanna ki sani fadar
ma'aiki SAW ne ke cewa
```Duk wanda yake da mata biyu se ya karkata wajen daya ya bar dayar ,,to zai
tashi ranar alkiyama barin jikinsa daya a karkace''(Ahmad)...```

Tace shin zakiso kiga yayaki a haka ne duk ikirarin dakike cewa kina sonshi?

Nan sukayi ta tausarta har taji komi ya fice har da su dariya databawa suke.....
Yau kam saukar

19 / 32