Author : FASMA Category : African Stories & Novels
jin dadi ya amsa nan ta dunga zuba zance
Hayaniyar ta tadashi daga baccin ...da sauri ya anshe wayar ya kara akunnen shi jin
Mahmud se ya kashe wayar...ya zare bata ido yace waya baki izinin daukan wayata
ne...
Ganin ya fara hayayyakoo mata yasa tayi kalar tausayi tace kayi hakuri bazan kara
ba....
Bece komi ba ya fara dube2 ko ze hango kayann...can yace ke ina kayan ne....
Wani waro ido tayi tare da fara yarfe hannu tace kayi hakuri na manta ne ...
To kuma yanzu mikike jira ?
Da sauri ta mike tayi hanyar fita ...
Dakatar da ita yayi yace ke haka zaki fita .babu hijab..
Kallon jikinta tayi riga da jupe ne na atampa....
Da sauri ta dawo ta dauka ta fita tana gungunin shi wannan yaya cikin bangare dayan
ma se mutun ya saka hijab...
Bata ankara ba taji yace ke uban miye kike cewane?naji kamar kince yaya....
Jikinta har bari yake baki na karkarwa tace cewa fa kawai nayi kai yayan nan nawa
akwaishi da kirki2...
Murmushi kawai yayi dan yajita sarai.......
Kayan ta kawo mishi se kuma ta tsaya ...
Ya kalleta yace ke fice mun a daki ko kina tsaye zan sa ne...
Turo dan karamin bakinta tayi tace to ni shine ka kalleni hakanan harda yi mun.
Wanka ...to nima kawai ka saka ina nan ..kaga kenan mun joje ko...
Wani kallon bakida wayo yayi mata yace ke ni sa'an wasan kine?ina wasa da kene?
Dariya ta kyalkyale tace to shikenan ni na tafi ma....
Ta fice abunta tana fadin ma hadu ne the next time...
Shikam yanzu mamakin kanshi yake yanda yake sake mata ...baya ma iya mata fada
sosai....zuciyarshi tace kawai de kanayi ne saboda farin cikin fulani ne....se
kawai yayi na'am da hakan....
Yana gamawa direct inda yasan ze samu Mahmud yayi ....,ya koci sa'a yana nan..bayan
sun dan gaigaisa irin ta abokai..se kawai Mahmud ya kwashe da dariya yace kai
mutumen kana bada wuta fa....
Cike da rashin gano mafitar hakan yace kamar yafa?
Mahmud yace a'a ba komi naga yar raino ce harta fara taya bacci ya fadi cike da
zolaya....
Wani dogon tsuka mtsssss yaja yace kaifa dan iskane .....towai ma idan ma hakane
miye na sawa mutum ido ne?gwauro da kai amma ka iya sa ido...dan Allah a daure ayi
aure ko sa ido ze ragu...
Kwashewa da dariya Mahmud yayi yace shikenan zance Maysam ta samo min yar reno
kamarta kaga se mu gamu mu reno su ko.....
Ganin abun ya fara zama iya shege yasa Murad fadin idan zaka fadan dalilin kiranka
to ka fadan odan kuma ba haka kaga tafiyata...
Gimtse dariyar shi Mahmud yayi yace shikenan ...nan suka firar su ...ganin haka
yasa na fiyo ta marawa Waziri baya shima
.
A bangaren waziri kuwa kasa fadawa diyarshi abunda ya faru yayi ..se kawai yace ta
shirya itada mahaifiyar ta su rakashi wani gu...
Basuyi wani musu ba suka shirya han suka kama hanya ...suna tsaka da tafiya ya gaya
musu komi har Maheeba zata fara bambami waziri yace a'a tsaya ai yanzu haka wajen
boka zamu daku kuji mike faruwa da kunnenku...
Ajiyar zuciya Maheeba tayi tace yauwa Sekayi Abbana....suka tafa itada
uwarta.......
Suna isa basu wani ji tsoro ba duk da cikin daji ne ga datti ga komi....
Suna zuwa kafin ma su zauna Boka ya sheke da wata karuwar dariya .....bayan sun
zauna se kuma yace na san mike tafe daku ba sekunyi bayani ba Dan mutanen mu sun
sanar damu komi....hahahahha....
Ya cigaba da fadin ku kwantar da hankalin ku ...yaron ya zo muna da taurin kai seda
muka sha jinin jarirai ukku amma. Shiru...shiya sa zamu biyo mishi ta bayan fage
Kude ku aje hankalinku gu daya ku saurara Sarki da kanshi ze yi maganar auren idan
kana so kuma zama ka iya dan turzawa ka gani ....shi da kanshi zece se anyi
aurennnn....
Maheeba tawani kwashi shoki daga nan zaunan tace se kayi Boka aikin ka yana
kyau.waya ganni a garakal mulki...hhhhh..
Boka ya cigaba da fadin muna bukatar jarirai ukku daya fari,daya baki da kuma
masara (yan japon,),,se kuma jinsi shanu suma haka ,,,rakumma kuma na saudia ...
Caraf Mahaifiyar Muheeba ta carafke da fadin wannan ai se ku yankan wuka zade mu
bada kudi se a tura akawo ......
Gyada kai Boka yayi se kuma yace wani hanzari ba gudu ba ...
Dam gabansu ya bada...
Yace se kunyi taka tsan2 kada ku bari asirin nan akar yashi ....da kuwa kai da ke
ya nuna waziri da matarshi yace idan ya karye komi ze iya samun ku dan haka ku
kiyaye.......
Dariya naga sunyi sukace hakan bazama ta faru ba...nan suka zube mishi makkudan
kudi suka tafi cike da farin ciki.da ......
A hanyar su ta dawowa ...Muheeba tace Abba ai mun mance da wannan matar tashi me
kama da aljanu ai da mun gama ta da boka itama...
Waziri yace ki kwantar da hankalin ki ki bar batun yarinya keda mulki ne ze kaiki
mi gaminki da ita iya kacin ta de ki bata oder kuma dole tabi...
Ee fa hakane Abba ....nan sukayi ta hirarakin su har suka iso..
Fulani kuwa ganin Maysam tana son koyon girki yasa ta sakata a makarantar koyon
girkin har na tsayon wata daya wanda zeyi dede karewarta dede fara Azumin
Ramadan ..dan acewarta tana yiwa Maysam kwadayin ta samu ladan aure a wannan wata
me albarka koda ko iya girkin ne da gyara gida zatayi.....
Kan kace mi tuni ta fara kwarewa dayake akwai ta brain....tun tana taya fulani dan
ita take shiga cuisine din da kanta ta dafawa sarki abinci inde har ita takeda
girki a cewarta mulki baze hanata samun wannan ladan ba.. kai akazo wani sa'in ma
Maysam ita take musu girkin ....
Ana haka har watan azumin Ramadan ya kama.....
I love you all
Fasma
Ahmed Gumel
[9/2, 9:57 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 10:00 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
57__58
```Manzon Allah (SAW) ya ce''ku kawata mazaunanku da yin salati gare ni ,lallai
salatinku gareni haske ne a gare ku ranar Alkiyama''
Hakimu ya rawaito shi.```
Ana haka har watan azumin Ramadan ya kama....
Gaba daya Maysam ta koma bangaren Murad kwana kawai ke kawo ta bangaren fulani....
De temakon bayinta take yin komi ...shi har mamakinta yake dan kuwa yanzu ta koyi
komi kama daga shimfidar gado komin girmanshi gyaran daki ,wanki tolet kam ko wata
babbar se haka ...
Tare suke shan ruwa suyi buda bakin su tare bayan sallar trawi kuma ta dawo ta
tayashi hira ..kai atakaice de sun dan shaku ,,dukda har yanzu sweetbabyn shi na
nan makale a zuciyar shi hasalima yanzu ya na jan Maysam jikin shi ne dan tana
tsananin kama da ita ko shagwabar ma gani yake iri dayace kai wani zubin mantawa ma
yake cewa wai Maysam ce a gabanshi dan jinshi yake kamar yana tare da
sweetbaby .......shiyasa ma duk wata mugunta hanttara ya dena mata har Mahmud yana
tsokar nar shi dan kuwa kusan duk futar da zeyi tare suke yi da Maysam idan
Kuwa wajen abokanen shine to se ya barta a cikin mota ya kunna mata game ya
bata ......
Azumi kam tun tana jin wuyar shi har ta saba yanzu dayake acan garinsu bawani yi
take ba Murza bata ma barinta a cewar al'adar qauyen seka fara menstrue ko kuma
anyi maka aure sanna zaka fara duk da de ita inde har Malan Musa na gari to kuwa ze
tadda ita tayi......
A kwana a tashi ba wuya yau har azumi ya kai biyar ....bayan sallar la'asr Murad ya
shigo gaida fulani bayan sun dan taba hira fulani ta kalleshi tace wai ya najika
shiru har yanzu ne....
Ya dago kai yana kallonta da alamar tambayta kwance a fuskar sa yace wani abun ne
akayi ....
tabe baki Fulani tayi tace kana nufin baka san akan mi nake zance ba?
Cike da shagwaba yace to ni ina zan sani ne ?
Shikenan to zancen kai sucre(sugar)ne gidan sirrin kanka ne a bisa al'adar garin
nan idan azumi ya kama to duk wani saurayi ko magidanci zeyi kokari ya kai sucre
gidan surikin shi ....
Gyada kai yayi yace shikenan zuwa gobe zan saka akai musu .....
Caraf fulani ta katse shi da fadin kai ya kamata ka kai da kanka dan hakan yana
cikin al'adar kuma yana nuna ka mutunta su....
To fa nan ake yinta yayi kicin2 da fuska sannan yace Momy kisan fa bana son futa
zuwa wani gari a mota gudun kada....
Daga mishi hannu tayi tace kada ma ka soma ka shirya ai Allah ne me
karewa .....idan kanaso kada ka fadawa kowa se Abbanka ....ko Waziri da Dogarai se
zuwa safe kawai zaka sanar musu da tafiyan ....
In sha Allah babu abunda ze sameka se alheri kada ka damu Allah yana tare da
kai ......muma kuma zamu tayaka da addu'a .....
Shikenan Momy Allah ya shige mana gaba ...
Ameen ta amsa ..nan suka ci gaba da hirar su ...
Har ya tashi ze fice tace kada fa ka manta Maysam gida biyu gareta wato can da nan
gidan..
Waro ido yayi yace nan kuma ....
Ee ta amsa ...
To ai momy naga kunada shi isheshe ne mi kuma zakuyi da shi ...
Dariya tayi tace al'adar kenan ..sannan inada tawa tsarabar da zan bayar zuwa safe
kafin ka tafi ka turo a dauka......
Dariyar yayi shima yace ok Momy ki kwantar da hankalin ki inde sucre ne se kin
ture.....
Yana fita ya kirayi Mahmud yace su hadu yana son ganin shi....
Minti biyar ya dauki Mahmud ya iso ...nan Murad ya sanar mishi da komi.....
Mahmud yace kwarai wannan haka yake. ..yanzu kawai ka bari zanyi wa wani magana
zuwa dare se ya kawo.......kamar katon nawa ya kamata muyi oder...
Murad yace kace kawai ya kawo 50. .....se na bawa Momy 25 ...can ma 25 ....ko ya
kake gani....
Mahmud yayi dariya yace yayi tunda ko ankai za'a rarrabawa yan uwa da abokanan
arziki....
Shikenan kawai kace ya kawo .....
Tun nan yayi kira ya sanar tare da jaddada yau yake son su.....
Bayan sallah isha'i kuwa sega oder da sukayi abangaren Murad aka jibge su .....
Maysam na fenêtre(window)tana kallon ikon Allah tun abun yana bata mamaki har ya
dawo bata tsoro.......
Murad kuwa seda ya bari an tashi a fada sannan ya iske mahaifinshi
bangarenshi ..nan ya sanar masa da komi ..ba karamin farin ciki yayi ba tare da
saka mishi albarka sannan yace da safe a bude magazine a dauko bahun shinkafa
20 ..na makaroni ma haka.........
Godiya yayi kamar shi akayi wa kyautar ..
Yana komawa gida ya tarar da Maysam na tilawa qur'ani dan kuwa tun lokacin da
wannan watan ya kama kullum cikin tilawar karatun ta take ...idan yana nan suyi
tare ...ko tv sun dena kunnawa sede idan wa'azi ne zasu kalla
Zama yayi shima yana sauraren zazzakar muryarta har wani lumshe ido yake....
Can ta rufe quranin ta kalleshi tace yaya wai wa incan sucre din hala sadaka za'ayi
dasu ne...?
Ba tare da ya bude idon shi ba yace na Abbanki ne gobe zan kai mishi ...
Be shiryaba kawai se ji yayi ta haye bisa cinyarshi tare da zagayo hannuta a
wuyanshi tace dan Allah zanje ....
Girgiza mata kai yayi alamun a'a ..
E kuwa nan ta fara zuba mishi shagwaba ...
Bude idon dayake ya saukeshi cikin nata tarrrr...wani zut yaji zuciyar tayi da
sauri ya rufesu ruf...yace shikenan ki shirya se mu tafi amman fa ki sani in baki
fito da wuri ba zan tafiyata ne...
Da sauri ta gyada mishi kai cike da murna ta rungume shi eeee se kayi yayana ina
godiya
Kara rumgumeta yayi yace se kinyi yar gidan Momy...nan sukaci gaba da tilawarsu har
lokacin rakata bangaren fulani yayi ....
Maysam kam tunda tayi sahur bata koma bacci ba guddin kada ya tafi ya barta...
Lokacin da Madina ta samu labarin wannan tafiyar ba karamun bakin ciki ba dan
lokaci ya kure mata bare ta cire musu burki kamar kullum ga Waziri ya juya mata
baya....banda kai komo babu abunda take a dakin ...ta jiza yatsa wani zubin ta cije
lebe...
A bangaren waziri kuwa koda ya samu labari be wani tada hankalinshi ba dan su yanzu
jiran Boka kawai suke yayi aikinshi ...dan ko rakiya beyi musu ba..
Fulani kuwa kamar yanda tace da safe zata bada ta ta gudunmuwar kuwa atamfuna , ,da
shadda ,yadina ta bada kala biyar biyar ga Malam Musa da Murza dukda de badan
halinta ba taci albarkar watan Ramadan ne...se kuma wasu atamfofin sun kai 20 tace
a rabawa matan garin....nan ma Murad ya jerowa fulani godiya kamar shi aka bawa ko
kuma dangi shi ......
Maysam se Murna ake yau za'aga Malan Musa ...haka suka kama hanya wacce ta dauke su
awa daya da rabi kafin su isa ...
Malam Musa besan da zuwansu ba yana kofar gidanshi se ganin motocin yayi ga yaran
garin se ihu suke suna bin motocin...kafin ma su iso ya sheda motocin da sauri yayi
tsaye yana jira yaga wanene yazo...
Dogarai suka fara fitowa sunata gyara kimtsi da kyau ......
Mahmud ya fara fitowa se kuma Murad ...yana nan tsayen suka iso da ido Mahmud yayi
mishi alamar dasu duka su gayshe shi ...wani kallon bakada wayo Murad yayi mishi...
Shide Mahmud har kasa ya duka yana gaida Malam ganin hakane yasa shima fara dukawa
da sauri Malam ya taro shi da fadin a'a ya isa haka ma ya rumgumeshi...nan Malan
yace su shigo daga ciki...har ya juya ze shiga yaji an cukuiyeye shi daga
baya..juyowar da zeyi yaga Maysam dinshi ce rumgumeta yayi shima yana dariyar farin
cikin ganinta itama jitake kamar ta mutu dan murna..
Suna shiga yace ta shiga ta dauko tabarmi a dakinshi...
Biyu sabbi fil ta doko ta shimfida se dariya take ..
Bayan sun zazauna suka sake gaisheshi ..Maysam kam ta wani lafe kusada Malan ...
Can sega Murza tana can yawonta taji labarin zuwan su Maysam aai kuwa ta kamo
hanyar dawowa tunda taga motocin tasha jinin jikinta ..dan ita ji take koro Maysam
din akayi kamar yanda suka tsara batasan komi waziri ya canzashi...
Tana shigowa idonta ya saukan kan Maysam da inba farin sani kayi mata a da ba to
kuwa baza ka ganeta ba.....wani abu taji ya tokare ma ta wuya bata gama wartsakewa
ba taga ana jido kayyayeki...mutuwane kawai ya rage mata tayi..a lokacin saboda
bakin ciki.
Nan sukayi mishi bayani tare da sakon Fulani dana Sarki..zo kaga murna wajen Malan
Musa har rasa inda ze sakasu yayi nan aka sanarwa da me gari...kan kace mi anyi
bambami kowa yazo ...haka aka taro a kofar gidankamar wani taron aure dayake ba
wani yawane dasu ba haka mazan garin sukayi layi kowa yazo se abashi bahun shimkafa
dana makaroni ,suga simkin nan me 5 aciki da turmin atamfa....can na tsinkawo
Murtala(da fatan de baku manta shiba)duk ya wani jeme ya manyata saboda wahala..dan
kuwa yanzu haka matanshi biyu da yara ukku....layi yazo kanshi can ya tsinkayi
Maysam dake kusa da Murad se dariya abunsu suke..wata kwala ta taru a idonshi a
ranshi yace yanzufa da Maysam matatace,,,, yace har yaude ina sonki Maysam
dita(kuji fa )haka jiki ba kwari ya amsa ya fice yana me dana sani....haka har aka
gama me gari ma komi biyu2 ya dauka amman dukda haka komi seda yayi saura har Malan
Musa yace asake rarabawa mutane. se Mahmud yace a'a kawai ya rikesu ai daman shi
aka kawowa ganin damane yasa ya raba..
Bayan sunyi azahar suka kamo hanya kamin la'asr sun iso ....lfy Lau suka iso
.
Hakade rayauwa tayi ta tafiya yau har azumi saura kwana goma à de de wannan lokacin
kuwa Murad ya kai Maysam yayi mata shopping bana wasa ba kama daga
atampa..lesh,abaya...etc...iya Murna Maysam tayi tamishi godiya har ya gaji da
amsawa ....
Kwatsam ranar ana sallah saura kwana ukku ko hudu shida Maysam suna bangaren Fulani
.suna ta hira can de fulani tace waini Murad ya akayi banga kayan sallar Maysam
bane? gashi sallah na matsowa kada taje ta rasa dumki...
Sosa kai yayi yace kai Momy duka ma yau ko sati ba'ayi ba nakaita ta shopping kuma
fa duka komi na sai mata..
Fulani tace to ai wannan ra'ayin kanka ne ba kayan sallarta ba ne...
Ya gaida kai kawai ..
Tace yauwa kaga ni to... yanzu se ka kaita ta zaba da kanta .
Maysam wacce tun dazu tana jinsu aman batace komi ba se yanzu tace kai Momy a
barshi kawai sena bada wanda ya semin din dimkim..
Fulani tace bata san zancen ba ...
Haka ya fito tana biye dashi a baya ,,,,.mota suka shiga..driver be zame ko ina
bisa umarnin Murad ba se wurin da ake seda pant da breziya duk dade basu wani fara
fitowa ba.. da kuma takalmi da jaka dan dama sune kawai be sai mata ba.... Itade
idon wannan shine nan ya biya kudin aka zuba su a leda ya barsu nan dogaren dake
kofar supermarché din su suka kwaso kayan aka laftasu a booth.
Bayan sun dayo ne yace to gashi na se miki kayan sallarki yana fadan haka ya fice
dan Mahmud ya dameshi fa kira...
Kuyangin ta suka kwaso kayan suka kai bangaren Murad suka zubesu a dakin Maysam na
nan bangarennn...
Bayan sun fice ne ta fara duba kayan wata dariya naga tayi se kawai ta musu wuri a
inda ya dace...
Love you all irin totaly din nan
*FASMA*
*Ashe haka masoyan wannan book din kukeda yawa haka...kai amma naji dadi ina
alfahari daku alherin Allah ya kaimuku a duk inda kuke wa inda na sani da wa inda
ma ban sansu ba ... Allah ya bar kauna ya kara dankon zumunci...ina yinku irin
sosai din nan ...*
Dedicated to all my fans
59__60
```Manzon Allah(SAW) ya ce''ka bar duk abinda kaga ya shiga maka duhu ,ka kama
abinda yake warai a wajenka
Tirmizi ya rawaito shi.```
Bayan sun fice ne ta fara duba kayan wata dariya naga tayi se kawai ta musu wuri a
inda ya dace...
Yau da gobe se Allah yau har daren sallah gaba daya Maysam ta sauyawa bangaren
Murad sanffari ..ta juya dakin shi kanshi ogan gyaran ya burge shi ....
suna zaune bayan sallah isha'i shida Mahmud suna ta hira can yace inji de baka
manta da alkawarin ka.....
Murad yayi kasake yace ummm inajin na manta de dan tuna min man....
Tab ..to bari na tuna ma kace duk lokacin da kayi aure to ranar sallah zaka gayyaci
goma daga cikin abokanan mu ....
Se lokacin ya tuna yace kai amma kacika aboki na kwarai na gode kwarai kawai yanda
za'ayi ka gayyaci wanda suka daci ni bari na sanarwa da Momy ...nan suka
rabu....yana me jin dadi samun aboki irin Mahmud
Yana shi gowa ya tarar da Maysam tayi daidaya a cinyar Fulani..se shagwaba take
zubawa.
Shigowar shi ma bata sa Maysam fasa abunda take.yi ba...ya zauna ya gayshe da
fulani...Maysam ta dago da nufin gaidashi taga ya zabga mata harara ta turo dan
karamin bakinta tace Momy kin gandhi ko...
Kafin Momy tace wani abu....se kuma cuwat ta tashi taje tana famar hayewa cinyarshi
......
Be hanata ba ta kuwa haye ko kunyar fulani bata jiba ...shima kuwa ko aka se ma ya
shiga yi mata rada a kunne ai kuwa se ga shi tana kyalkyalewa da dariya .....abun
se ya burge fulani