Author : FASMA Category : African Stories & Novels
daya kada tazo ba ta daya ba saboda har yanzu bata
manta da sharadin Murad ba...
A wannan lokacin kuwa Fulani har ta gaji da fadan rashin zuwan Murad tayi fadan
tayi fushin ta gaji kullum maganarshi daya ce cewa zezo .....kai daga baya in ta
kirashi da sun gaisa seyace mata yana dakin tiyata ko kuma aikin sun mishi yawa ze
kirata da ga baya kuma ba kiran zeyi ba..tun abun baya damunta har yazo
yanayi....se de kawai ta bishi da addu'a..
Shima anashi bangaren yana so yazo dan yayi missing dinsu barema Maysam zuciyarsa
na matukar son ganinta amma besan miyasa baya son dawowa garin ba ba .....gashi har
yau zuciyar na mishi zogi lokaci zuwa lokaci......
. .
A bangaren Waziri kuwa duk ya bi ya fige ya rame saboda diyar shi MAHEEBATOU dake
cikin mawuyacin halin sakamakon kama mahaifinta wato waziri cewa da sa hannushi
akayi wa Murad asiri ya bar kasar ita kuma tunda ta taso ta mallaki hankalin kanta
bata da wani buri da ya huce ta ganta a garakal mulki tanayin yanda taso kamar
Madina dukda de tanada kuyangi har biyu amma ita tafi so ace gaba daya masarautar a
hannunta take........lokacin kuwa hanya daya take ganin zata bi ta cika burinta
hanyar kuwa itace ta auri Murad idan sarki ya mutu tana da yakinin yarima Murad shi
ze gaje shi tunda shi kade ne danshi na miji ...
Mahaifinta waziri ya daure mata gidin se abunda take so takeyi kasancewar ita daya
Allah ya bashi bayan shekara da shekaru da yin aure shi yasa ya dauki karan so ya
dora mata .duk abunda zatayi baya ganin laifinta ....koda ta sameshi ta sanar mishi
burinta se ya goya mata baya ...a lokacin ya samu me martaba da yanaso akara hada
zumunci wato a hada yarima Murad da diyarshi Maheeba aure ...
Sarki ya sa aka kira Murad a lokacin sannan ya sanar masa idan har yana da ra ayin
aurenta ..
Bude bakin Murad yace a'aaa kiri2 yace shi baya sonta ...wannan magana tayi matukar
batawa waziri rai amman ya danne zuciyarshi...
Koda ya sanarwa da diyarshi yanda sukayi se kawai ta fashe mishi da kuka har dasu
birgima ..... .....duk da haka seta fara shigewa tana nuna mishi so ...shi kuwa
Murad be masan tana yiba duk inda yayi se taje ........ganin haka yasa ya tattara
ya koma England da zama bayan ya sha fama da fulani.....
Wannan tafiyar tashi gaba daya Maheebatou ta fice a hanyacinta dan a rayuwarta ba a
saba ce mata a'aa ba dole tasa waziri ya turata kasar Mali karatu wajen dangi
mahaiyarta da alkawarin idan ta dawo ze cika mata burinta .....
To fa ranar da tazo ne ta riski Maihaifinta na zancen asirin shida
mahaifiyarta ...tun lokacin ba agane mata ba ..dan dama saboda cikar burinta ta
dawo....
Ganin abun bana qarewa bane Waziri ya wanke kafarshi ya tafi ya sanarwa Madina
halin dayake ciki ..amma Madina fir ta kiya ..babu irin rokon da beyi mata ba kan a
karya asirin Murad ya dawo daga baya a san yanda za'ayi aman tace bata san zancen
ba ..
Rai a bace ya fito kamar wanda zetashi sama a ranshi yace baki san ko biye miki
danake saboda Maheeba bane dan na samu na zama sarki sena barta ta taka wanda take
so...
Haka ya isa gida yanata banbami amman mi abunda ya tarar ya kara daga mishi hankali
dan kuwa Maheeba numpashinta ya dawo sama2...
Ba shiri ya fita ya kama hanyan se wurin BOKA gobe da nisa ...
Makuddan kudi ya zube mishi nan yace yana son a karya asirin Murad ya dawo gida
kuma idan ya dawo kawai a daura aurenshi da diyarshi Muheeba...
to fa fans kunji wata kuma.....
Shin ya luke ganin zata kaya ne?
Fasma ce
Ahmed Gumel
[9/2, 9:49 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ππ_*
[9/2, 9:50 AM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
47__48
```Manzon Allah (SAW) ya ce'' ciyarwar mutum ga iyalinsa sadaka ce''
Bukhari ya rawaito shi.```
Makuddan kudi ya zubewa Boka gobe da nisa yace yana son a karya asirin Murad ya
dawo gida kuma idan ya dawo kawai a hada aurenshi da yarshi Muheeba...
Boka Yayi wata mahaukaciyar dariya seda waziri ya tsorata can kuma ya daure fuska
ya ce ina jin dadin aikin ka ......saboda akwai zubar da jini ...
Waziri ya zaro ido yace jini kuma
Ee na jarirai ma kuwa idan har a nason aikin yayi kyau ...
Waziri yace ayi komi ma idan de har burin er leleta ze cika sannan kuma wani
hanzari ba gudu ba ina son abani maganin da zata mallake shi se abunda tace za ayi
nan ya sake zube mishi kudi ..
Boka yayi dariya yace an gama ..yayi yan zubace2n shi ..ya dauko wani kullin magani
yace wannan a abin ci kona sha za'a zuba mishi amma fa a bari har a daura
aure ......sauran aiki mutanen mu zasu cika shi da zarar sun sha jinin jarirai
komai ze wakana kaide kawai abunda zakayi shine ka cusawa Murad auren da zarar ya
dawo ....
cike da murna ya karbe maganin ..har ze tafi la'anan nan Boka yace kada ka tado
zancen auren a kwanakin nan dan kauda duk wani kokwanyo na mutane ka barin a samun
koda sati ne da dawowar shi sekace mishi kana so ya auri yar ka ...kafin nan mukuma
zamu cusa masa kwar jinin ka da ba ze iya cewa a'a ba ..
Cike da murna ya tafi gida jin harda shawara boka ya bashi ....
Muheeba dake zaune se hirar su suke ita da mahaifiyar ta har da shewa ...ai kuwa ta
najin sallamar mahaifinta ta koma ta kwanta ta fara numpashi sama2.......(tab a
raina nace ashe gaba ma da gabanta makircin wani yafi na wani)
Da sauri ya isa kusa da ita yace sannu Muheeba .....ki kwantar da hankalin ki
wannan karon Murad na kine ...kinga wannan ya fiddo kullin magani yace na mallaka
ne..
Caraf ta bude ido aman saboda makirci de taki tashi ta zauna tace Abba zan auri
Yarima Murad na hau kadagar mulki ? ........
Waziri yayi dariya ya ce sosai sannan ki shirya wa zowar shi kwanan nan yana kuma
zuwa se.aure kawai ...
Ai bata san lokacin da ta tashi zaune ba ...tace wai Allah da gaske?
Yace haba yar lele kin bazan miki wasa da irin wannan batu ba ....
Nan murna ya cika ta har ta fara hangota tana ba kuyangi order se kawai ta fashe da
dariyar farin ciki ..
Ganin haka ya waziri fita ya nufi fada ciki da murna yasa yar leleshi
farinciki.....
Yana fita suka tafa itada mahaifiyarta tare da yin shewa tace kai mama kin iya hada
plan da ba dan nabi shawarar ki nayi cutar karyan nan da baze je a karya a sirin ba
...
Tace kede bari y'ata ai rayuwar ce seda haka ...
Suka sake yin shewa tare da tabawa kamar ba uwa da diya ba ..
.
A bangaren Maysam kuwa yau aka basu vacation bayan an bawa kowa sakama konshi inda
Mufeedah tayi ta daya Maysam ta biyu se kuma Mariam ta ukku sunsha kyautikika ..ita
de Maysam gaba daya tayi sanyi ta san ba ita ba zuwa hutu gida duk wanda ka gani
cike da dauki yau zata tafi gida banda Maysam ...
Mariam aka fara zuwa dauka sanan motar su Mufeedah tazo ...tananan tsaye motocin
fulani suka fara zowa daya na bin daya har goma dan kuwa fulani da kanta tazo
daukarta ... ......
Maysam na hango fulani ta kuwa zanbad'a da gudu ta rungumeta ....
Sun jima a rungumen fulani ta dagota tace Maysam ya banga kayan ki ba?
Ta dago kai idanun ta har sun kawo ruwa tace Momy banyi ta daya ba ta biyu naci..
Fulani tayi murmushi tace kai amma kinyi kokari fa congrats dauther...
Maysam tace Momy kin manta da sharadin Ya Murad ne....
Fulani tace sharadi kuma?dan ita har ga Allah ta manta
Maysam tace yace idan har banzo ta daya ba to bazan zo vacation ba..
Fulani ta bata rai tace bari batun shi je ki hado kayanki mu tafi...
Da sauri ta zube nan kasa tace Momy ki mun rai ki barni nan dan walahi ko kiranshi
na karshe seda yayi mun warning... Sega hawaye shar2 ..
Fulani ta dagota tace kada ki damu zanyi mishi bayani...
Maysam tace kiyi hakuri Momy badan bazan iya bin umarnin ki bane a'a kin huce haka
a wurina bana son shiga tsinuwar mala'iku ne dan cewa yayi bada izinin shi ba inde
har banyi ta daya ba nazo hutu.....ko satin nan a islamiyya malam ya kara jaddada
mana irin sab'awa iyaye ko miji bala'in dake faruwa da mutun
....
Ran fulani ya kara baci a ranta tace ta yaya ma ze gindaya mata irin wannan sharadi
kan wani banza dalilin shi da beda tushe ....nan ta zaro waya ta shiga neman layin
shi amma a kashe...tayi kira yafi a kirga amman bata shiga...ta kalli Maysam tace
shikenan amma bazan iyabarinki a school din nan ba koda kuwa da kuyangi..ki had'o
kayan ki na kaiki bade shi garin ne yace bazaki bari ba?
Ta ce eee
Fulani ta bada order a ka debo kayanta aka saka a booth ...suka fice ...
A motan kam fulani tasha surutu har suka iso wani tamtsamemen gida ....tun kofa
gidan abun kallo ne bare cikin ba'ama zancen ...katon gidane na gani na fada duk da
babu kowa ciki se me gadi da me bawa fleurs (flowers)ruwa amma fa ko ina tsap2 nan
kuyangi suka fara goge2 masu shara nayi masu daura abinci ma nayi ..fulani da
Maysam kuwa shopping suka tafi kafin su dawo komai is ready.
Se biyar na yamma fulani suka fara shirin tafiya bayan a zube mata kuyangi bakwai
dan yi mata komi se digorai biyar ...
Tofa nan ake yinta dan kuwa Maysam kuka take shab'e2 fulani ma daurewa kawai take
dan ji take kamar tayi mata kukan sede ga bayinta nan kusa ba dama ...da kyar ta
samu ta lallaba ta tafi....
A mota kam fulani duniyar tunani ta fada tana yaba kaifin hankalin Maysam ,,gata
karama da ita ta tuna lokacin da take ta fadan rashin samun Murad a waya ...cike da
shagwaba Maysam tace kai Momy ki barshi haka mana may be yana wani aiki
ne ......wannan kira haka se ya 'aza ko ba lafiya tayi dan murmushi...
Madina da Murza kam basu san wainar da waziri yake tonawa ba se saukar Murad suka
gani a masarauta...
Madina kam bakin ciki ya kusan kasheta abunda bakinta ke fadi kawai ta yaya haka ta
faru?...ras gabanta ya fadi data tuna da waziri tace kadade shi ya batan planning
dina tayi dariyar gefen baki tace zan kuwa bincika......
Zo kaga Murna wajen fulani bakinta ya kasa rufuwa dan murna ....haka ma me martaba
sarki ...
Murad kam tunda yazo yake baza idanu yaga ta ina zega Maysam ama shiru kwanshi biyu
yaga baze iya hakuriba ya tuntubi lfulani da zancen dan yasan de yanzu anyi hutu a
ko'ina
Kamar me ciwon baki ya tambayi fulani ina Maysam take yana wani babasarwa waishi a
dole be damu da itaba....
Fulani tace tana Maradi mana.ya sake jefo mata tambayar basuyi hutu bane?
Ta kalleshi tace sunyi mana tun satin jiya ...
Da sauri ya kalleta yace to tana ina ne ?
Fulani tace tana gidanka na Maradi tareda kuyanginta da dogarai ..
Quoi(what)!!??ya fada cikin wata irin voice ta......
...
Ina sonku fans
Fasma ce
Ahmed Gumel
[9/2, 9:50 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ππ_*
[9/2, 9:53 AM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
49__50
```Manzon Allah (SAW) ya ce''hakika Allah ba ya kallon surorinku da dukiyoyin ku
amma sede abinda ya ke kallo shine zukatanku da ayyukanku''
Muslim ya rawaito shi``` .
Da sauri ya kalleta ya ce to tana ina ne?
Fulani tace tana gidanka na Maradi tare da kuyanginta da dogaran ta....
Quoi(what)?ya fada cikin wata irin voice. ...se kuma ya sassauta murya tunawa
dayayi da fa Fulani yake magana ya danne bacin ranshi baki na karkarwa yace Momy
wanne daga cikin gidan ?
Cike da nutsuwa ta kalle shi tace gidan ka dake unguwar ''sabon gari''wato babba
gidanka ba....
Besan lokacin da ya waro ido ba yace haba Momy gidan nan fa na ginashi ne saboda
sweetbaby.na ne sega hawaye shar2 kuma ai.....
Kafin ya karasa ta tare shi da fadin wai anya Murad kana cikin hankalin kuwa ?yo
inba haka ba taya zaka gina gida akan wacce bata ma doron duniya ...
Rararafo wa yayi ya dora kanshi a cinyarta tare da dora hannushi dede zuciyarshi
yace Momy har yanzu zuciya tace ta kasa yarda cewa sweetbaby na ta mutu a kullum
gani nake kamar zata dawo gareni ko na ji ma kamar tana kusa dani.....
Fulani ta shafa kanshi tare da goge mishi hawaye tace kaci gaba dayi mata addu'a
dan shi take bukata daga gareka bawai ka dorawa laifin wani akan wani ba.......
Bede ce komi ba se ajiar zuciya dayakeyi a jere ...
Can kuma kamar wanda aka ciza ya tashi ya zauna cuwat yace Momy dawama kikace kin
bar wacan abar..?
Fulani ta gane sare amma seta mazge tace me wa kenan?
Cike da shagwaba yace ita fa !!
Fulani tana sonyin dariya amma ta danne tace idan baza ka fada min waba abar
maganar tunda de ni ba yar modi bace bare nayi arwa......
Kamar zeyi kuka yace Maysam fa nake nufi......
Au wai da ita ....to tare da bayyinta take.........
Ya dan sauya fuska yace ina de fatan dogarai masu tsaron mata aka bata ?
Fulani kam se gimtse dariyar ta take tace ka taba ganin dogarai mata ne?
Yayi dan shiru can yace to wai ma miyasa bata dawo gida hutu ba?
Wanna karon fulani ji tayi kamar ta dokeshi a ranta tace ashe shi ya ma manta da
sharadin shi ya bar baiwar Allah da wahala...
Tade daure tace to batayi ta daya ba ta biyu tazo...
Yayi fuskar tunani yace to mi alakar zowanta da ta biyu datayi..?
Fulani tace iii lale fa dole ka tambayya to sharadin daka ginda ya mata ne kan in
bata yi ta daya ba to kada tazo hutunnnn..
Shi se yanzu ya tuna ya dan shafa kanshi yace aii hakane ashe........yace Momy bari
na dan zaga gari.....
Tayi murmushi tace a dawo lfy .....
Har yakai kofar futa falon ya juyo yace kuma Momy dogarai nawane suke can din....
Fulani danta tsoratashi tace su goma kacal ne ....
Bashiri yace goma fa?
Tace to ko sunyi kadan ne a tura mata wasu?
Zuciya na tafarfasa yace Momy goma ai sunyi yawa ina laifin biyu ko daya ma....
Murmushi kawai tayi ta shige room dinta ganin inta biye mishi seya kashe mata aiki
da tambayoyi..
Fita shima yayi rai a jagule se yaji baze ma iya fita yawon ba ....lambu ya tafi
wai ko zeji dan sassauci amma ina inya tuna maza goma ke can tare da Maysam se yaji
wani zut a zuciyarshi gaba daya ya saka kanshi a damuwa ya kasa sukuni wani bangare
na zuciyar yace wai mi kake yi hakane?to wai ina ruwana in maza dari ke tare da ita
tundade ba santa kake ba....wata zuciyar ta kitsa mishi ai ba wani damuwa bane kayi
da ita kawaide kana kare martabar aurenka ne haka yayi ta saka da warwarar shi ...
Bayan sallar la'asr ya nemi izini ganin me martaba.....
Bayan an bashi izinin shiga ya shiga ya zauna fulani da Madina na kusa dashi sun
sakashi tsaka da alama de wata magane ce suke wacce ta shafi shagulgulan gidan...
Bayan ya kwashi gaisuwa sekuma yayi shiru ganin haka Sarki yayi dariya yace da
alama de akwai magana a bakin ka yarima MURAD me jiran gado...yayi y'ar dariya
Wannan furuci ba karamin ta dawa Madina hankali yayi ba ta kasa boye kishinta har
seda fuskarta ta nuna wanda fulani kade ta lura da hakan bata ce komi ba se girdiza
kai da tayi dan inda sabo ta saba.....
Shima yar dariyar yayi tare da dan sosa kai yace dama2 ina son zuwa Maradi ne yanzu
se ya sadda kai.......
Me martaba sanin matar shi Maysam nacan ya sa be wani tambaye shi daliliba sede
yace baza kayi hakurin gobe ba tunda yamma ta farayi..
Caraf ya ce ai jirgi zanbi ne.
Fulani bata san lokacin data dara ba
Madina kam fadi take kuyi ku gama na dan lokaci ne...kamaci sa'a a jirgi ne da a
mota ne da cire maka burki ka mutu kowama ya huta
Sarki be sake cewa komi se addu'ar sauka lfy dayita jero mishi tareda sakon gaisuwa
ga Maysam
Nan yayi musu sallama ya fice fulani ma addu'ar tayita mishi ..
Yana zuwa jirginsu ya daga se Maradi ...
.
A bangare Mubeeba kuwa dadi kasheta ne kawai beyi ma amma iya murna da nuna jin
dadi tayi shi ..ita a yanzu hartaga ta zama matar yarima me jiran gado .....itada
ummarta karansu suke ci ba babbaka waziri ma hankalin shi ya kwanta ganin yar shi
ta ji sauki...
Muheeba kuwa tuni ta fara cusa kanta wajen Murad duk da yana korarta tare da yi
muta wulankanci amma kamar bada ita yakeba a cewarta ta bashi time ne kan ya shigo
hannu .....
.
Biyar da rabi ma acan tayi mishi ..yana sauka motoci suka zo daukarshi daya ke
dogaran a sanar da su zuwanshi.direct gidan shi na sabon garin suka sauka...
Tunda suka shigo unguwar gabanshi ya fara fat2 ai suna sshigowa gidan ma gaba daya
ya dan rikice da kyar ya seseta kanshi ya fito direct hanyar falon ya nufa ya na
zuwa yayi knoking ....
Maysam dake zaune tana shan ace cream ga ta saka Tv gaba ...ga kuma biyu daga cikin
kuyangi daya na matsa mata kafa dayar na bata labari me noshadantarwa da saka ban
dariya.....
Jin knoking yasa tace waye ne...setaji ba amsa....
Aka sakeyi da har daya daga kuyangi zata bude Maysam tace a'a' bari na bude da
kaina...
Da ace cream dinta a hannu ta bude kofar ...wa zata gani inba Murad ba wani waro
ido tayi irin na kaga abun tsoron nan ...tace y..
Ina kaunar ku fans ina jin dadin yanda kuke bibiyar novel din Allah ya bar kauna da
zumunci me dorewa ...ina sonku irin totaly din nan
Muje zuwa
Fasma ce
Ahmed Gumel
51__52
```Manzon Allah (SAW) yace''fiyyayen musulmi shine wanda duk musulmi suka kubuta
daga sharrin harshensa da hannunsa''
Muslim ne ya rawaito shi```
Da ice cream dinta a hannu ta bude kofar ...wa zata gani inba Murad ba wani waro
ido tayi irin na kaga abun tsoron nan tace yaya se kawai robar ice cream din ta
fadi daga hannunta gabadaya ta bata mishi kafa .........
Kara zaro idanu tayi tace yaya kayi hakur........
Kafin ta gama fada ya sauke mata yatsunshi biyar a fuskarta ....har tayi taga2
kamar zata fadi ...se yayi saurin fizgota ta fada jikinshi ...
Wani mayen electric shok yaji yabi jini da jijiyarshi kamar de na kowani lokacin
idan har fatar jikinsu ta hade da sauri kuma ya hankada ta yace ''comment oses tu
t'habiller de cette faΓ§on ?