Author : FASMA Category : African Stories & Novels
''La'ilaha illallahu''don Allah''
Muslim da Bukhari ne suka rawaito shi``` .
Washe gari kam asubanci yayi ..karfe tara jirgin su ya daga se Niger......direct
Maradi ya sauka .....Mahmud kawai ya san da zuwan shi shima se dan ya zo daukan shi
ne.....
Momy na break kawai se jin salamar Murad tayi ...ba karamin mamaki tayi ba ..
Koda ya shigo direct bakin gadon da Maysam ke bacci yaje ya zauna abunshi ....kura
mata ido yayi yana kalonta seya ga ta rame mishi......dukawa yayi yayi kissing din
goshinta ....
Mahmud da ya shigo yanzu ya duka ya gaida Momy ya tambayyi ya me jiki .......duka
cike da mamaki take amsa mishi ta nuna mishi Murad ......
Mahmud dariya yayi yace to idan ka gama rashin kunyar seku gaisa da Momy..ko.
Waro ido yayi yana kwallon wurin da Momy ke zaune dan fa shi har ga Allah be san
tana dakin ba ...idon shi ya rufe kawai wajen son ganin Maysam...
Se kuma ya zame ya zauna kusa da Momy yana aikawa da Mahmud sakon harara......
Mahmud yayi musu sallama ya fice abunshi yana meyi wa Murad gwalo....
Kicin2 yayi da fuska .......yana sosa kai yake gaida fulani ya kuwa sadda kai
kasa.....
Fulani har cikin ranta taji dadi ganin hankalinshi ya fara kwantawa da kuma karkata
zuwa Maysam .....
Murmushi tayi ta shafa kanshi tace sannun Son kasha hanya fa ...ga break nan kayi
dan da alama direct nan ka sauka.....
Yana fa jin yunwar amma dan shagwaba ya saka kayan break din gabanshi amma yaki
zubawa...
Fulani ta gane shi sare ta kyaleshi ....tace zuba mana kaci...
Shagwaba ya shiga zuba mata wai shi baze iya serving din kanshi ba........
Suna haka Maysam ta fara buda idannuta da addu'ar tashi daga bacci ta tashi ta
sauke ido ta tar bisa fuskar Murad ....
Itama bata wani lura da fulani ba tace yayana ....tana kokari saukowa...
Da sauri ya isa bakin gadon suka rumgume juna ... Se Maysam ta fashe mishi da
kuka ....
Tashin hankali da sauri ya dora ta cinyar shi yana tambayar ta mi ya same duk ya
wani kidime....
Cike da shagwaba tace ba kai bane..
Ni kuma ya nuna kanshi cike da tsoro dan shi besan miyayi mata ba...yace mi nayi
to...
Shirme irin na Maysam se cewa tayi bakai ne kayi tafiyar ka ba ni kuma nayi missing
din ka..
Dariya yayi har da dan sauti yace to shikenan ai gani nazo ko ....
Dogarai dake tsaron kofar dakin suka cika da mamaki jin dariyar Murad nan fa aka
shiga kallon kallo dan su manta da suga murmushin shi tun kafin suyi wannan
Accident din da SWEETBABYSHI ta rasu....wanda suka jima a masarautar
kenan ....sabbi zuwa kam cewa ma suke baya dariya ..
Dora kanta tayi bisa kafadarshi tare da fadin sannu da zuwa yaya...
Karan hancinta ya ja yace yauwa yar gidan Momy...
Tana dariya jin sunan daya kirata dashi ai kuwa daga idon da zatayi sukayi ido hudu
da fulani .... Waro ido tayi sekuma cuwat ta yi tsaye ...ta sadda kai kasa ...
Shi besan mi ya sata yin haka ba ...se ya fara kokarin meda ita bisa cinyar ...
Nan fa ta fara tirje2 tana fadin kin ganshi ko Momy ...ni ka kyalleni..
Gumtse dariyar data taso mishi yayi ganin wai kunyar Momy takeji..
Sake mata hannu yayi ..da sauri taje kusa da Momy ta zauna kai a kasa ta kasa
dagowa ..tace Momy ina kwana...
Itama fulani dariyar tayi dan abun nata abun dariya ne..tace lfy lau ya kwarin jiki
...
Murad ya ce daga baya kenan seda kika gama rashin kunyar taki zaki wani zo kisa jin
kunya..
Shure2 kafa ta fara tana kukan shagwaba ..
Fulani tace a'a kyaleta daga zowa kada ka takuran yarinya...
Gwalo tashi ga yi mishi jin fulani ta goya mata baya ..yun kuri yayi kamar ze
kamota ..
Da sauri tayi hanyar tolet ta tana fadin momy barin wanka ..
da sauri shima yake shirin mara mata bayan ..fulani da tayi kasake tana kallon
shi ..wannan rashin ta idon har ina ....ganin fa da gaske shiga zeyi ya sa fulani
tsayar dashi da fadin to barin in barmuku dakin nan ..tun kan abun yayi nisa..
Cike da shagwaba yake fadin haba Momy tayata ne fa zanyi ...saboda batada lfy ...
Murmushi kawai tayi tare da girgiza kai ...
Koma wa yayi ya zauna yana ta zuba wanda duk yawancin maganar Maysam ce..
Tajima ciki har Murad ya fara korafin da mitar cewa kada fa aje ko zamewa tayi ..ko
....
Itade fulani najin shi bata tanka ba ...
Tana fitowa daure da towel dinta da hidjab .....shi da kanshi ya shirya ita...
Ya jayota ya zaunar suyi break tana kokarin serving dinsu ...Murad bako kunya ya
rike hannun Maysam din yace bari na zuba mana ke da bakida lfy...
Shiyayi serving din su kuma shike bata a baki ..
Fulani a ranta tace ashe dama shakiyan cine ..zama ka iya serving din..
Ganin abun bana karewa bane se ta hau waya ..da sallama ta fara ..suka gaisa da
alama de mace ce...sun dan taba hira take sanar mata da gata a likita ma matar
Murad ce bata ji dadi ba .... Matar ta jajanta mata ...fulani tace yanaki
jikin ...?
Tace to alhadulillah
Can kuma se ta bawa Murad wayar yana karawa bayan ya gaisheta ya shiga zuba mata
shagwaba har tafi wacce yake yiwa fulani..najide ya kirata da Mom.....
Ita kuwa Mom din ta lalace wajen lallashi ...
Daga baya ya bawa Maysam wayar ya cemata Mom din SWEETBABY nace a...
Hannu na karkarwa ta amsa tana nanata sunan cikin ranta dan ita jitake yana nufin
yarinyar da ze aura ce SWEETBABYN.....
Sallama tayi tare da gaisheta..
Muryarta kawai Mom taji amma seda gabanta yayi wata irin mummunan faduwa ..da kyar
ta nutsu ta amsa mata ..tace ya jiki....
Tofa the same Maysam taji itama..da kyar tace naji sauki alhadulillah...
Mom tace yaya sunanki ne..
Maysam sunana se kawai ta tsinci katan ta son yi kuka wanda bata san dalili ba....
Ganin haka yasa fulani karbar wayar ..itama muryar Mom din duk ta sauya ...nan
sukayi sallama ..
Murad ya goge mata hawayen da suka zubowa yace mi yasaki kuka.. ....
Babu komi kawai tace dashi
Wunin ranar anan sukayi shi...Maysam taji sauki sosai ganin Yayanta kusa da ita
amma kasa zuciyar ta tana son sanin wacce ce Mom da Kuma Sweetbabyn nan....
Irin rigima ta Murad ta aka basu Sallama ya kuwa turbune sede Maysam Ta koma gidan
su na nan Maradi .duk da daman wannan satin za a sake su hutun chirsmate(Noël)..
Fulani ma turbune wa tayi ganin in ta biye mishi suka koma gidan kada soyyayar su
yasa su manta ma da ta na school.....kuma gashi tayi2 su huce tare yaki yace se ya
cinye satin shi anan ...haka Fulani ta koma dan cigaban shirye2 auren ...
Murad na ganin tafiyar Fulani ya je ya doko Maysam suka ci gaba da rayuwar su irin
ta yaya da kanwa masu ji da .
Abangaren Madina kuwa taci alwashin hana auren nan tunda har waziri yaci amanar
ta ....jakadiyar ta tura musamma garin su Maysam wajen Murza kan tana son ganinta..
Murza ta kuwa yiwa Malam Musa karyar za'ayi wa Maysam kishiya zata tafi amatsayinta
na uwa (ni kuwa nace kode UWAR RIKO ba ..littafin Momyn Mufeeda )
Bangaren fulani ta sauka dan kauda duk wani shakku ..lokacin Fulani na can Maradi
ma...Murza..seta saci kafa ta faki idon mutane ta shiga bangaren Madina...
Nan Madina ta kwashe duk irin cin amanar da waziri yayi musu...
Murza har kukan bakin ciki tayi wai taga samu taga rashi ..ta kuwa share hayenta
tace ki kwantar da hankalin ki akwai wani sabon Boka wai shi Matsafi aikin shi shi
yakan Adda ne bama wuka ba...
Madina tayi wata dariyar mugunta tace aikin ki yana kyau shiya sa nake son haraka
da ke...
Kudi ta zube mata tace kuma kice a kashe mana shi ma gaba daya ..in hakan bata samu
ba ...to ayi muna irin na wacen ....a tura shi can kasar da baya dawo ba... Murza
ta fice ..daga nan ma wurin bokan ta fice ...kai gaskiya fa wannan yafi wacen zaman
hatsabibi da shu'umanci. .....
Bayani Murza tayi mishi bayani ta zube mishi kudi.tare da gaya mishi irin aikin da
suke bukata...
Wani kulli magani ya bata yace wannan a zuba akofar da shi Waziri ze
tsallaka ..kuma yabata wani yace wannan kuma a zuba mishi a bun sha ....yana sha
aiki ze ci dan daman kwarjini ne yake musu..
Ya basu wani yace wanan kuma a turarashi da zarar Murad ya shiki hayaki ..yanda
hayaki yabi iska shima haka zeyi.....ya kwashe da dariyarr...yace ga dubara ta
nunawa Waziri komi ya huce seta cuceshi daga nannnnnnnnnn..(
jifa...Allah de shitya)
Cike da Murna ta kawo wa Madina wannan labari ta bata magani ta komawarta kauye
cike da kayan alheri da Madina ta bata...dan har lokacin Fulani bata dawo . ...
. ba
A bangaren Murad kuwa saukar QURAN ya saka ana mishi anan Maradin tare da bada kudi
makarantu da massalatai dan yi mishi addu'a ganin abun akwai tambaya ciki tunda ba
tun yau ba ake son ya aureta amma daya nuna bayaso ba'a matsa mishi ba se yanzu
rana tsaka a tilasta mishi...shiya sa yayi haka koma de minene to yazo mishi cikin
sauki....
Haka Har suka cinye satin su kullum shida yar gidan Momy...wanda yayi saura kwana
takwas auren
shike kaita school ya medota ......Mufeeda da Mariam ma ba'a barsu a baya
ba ..lelanta suke kamar mi..?da aka sake su ma hutu ma kamar su bita suke ji da
kyar suka rabu..
Lokacin da zasu tafi so tayi taki binshi dan bazata iya jurar ganin auren
shi ..amma matsa matan da yayi yasa ta biyo shi .dan dole...
Koda suka zo ma beyi wani yunkurin yin komi ba....kuma da alama ma bashi da niyyar
yi
Murna kam ku san kashe Maheeba tayi ganin Murad yazo ita har ta ga an daura ..se
wani d'ada'aga kai take wai ita a dole futur wife din yarima me jiran gado.
A yaune kuma Madina take shirin aiwatar da kudirin ta..
Love all fans
[9/2, 10:07 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 10:16 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
69__70
Story&Written
by
*FASMA*
*Ho.ho.ho MIMSQUEEN hamshakiyar shahararar marubuciyar ..ina murnar tayaki karasa
littafin ''KARSHEN ALEWA KASA ''hakika kin nishadan tar damu kin fadakar
damu ..Rabbi ya kara miki daukaka .da Baseera tare da zakin hannu ..sosai muka ji
dadin littafin nan Readers kada kubari abaku labari ...zamuyi missing dinshi ..Amma
abun murna da farin ciki shine muna nan tare dake a KALAR TAWA UWAR wanda shima ya
dauko dadi and other dazasu biyo baya..muna biye dake ..love you irin totaly din
nan.*
Dedicated to all my fans
69__70
```Manzon Allah (SAW) yace''kauracewar musulmi da dan uwansa musulmi kamar zubar da
jininsa ne''
Ahmad ya rawaito shi``` .
Hakan kuwa akayi Madina tasa akayi mata Kiran waziri ...dede kofar shiga falon ta
kuwa barbada maganin ,,,,da farko yaso yaki zuwa amman ganin in betafi ba zata iya
kulla mishi wani sharrin yasa ya tafi amma a ranshi fadi yake komi za'ayi sede ayi
amma bazan biye mata ba kan auren nan ...tunda aka zuba maganin aka hana kowa
shigowa bare fita ....bakam2 waziri ya shigo babu wata bismillah sallamar ma se da
ya tsallaka har ya tura kanshi sanan yayi ta ...(a raina nace ai kuwa hakan be dace
ba kana namiji ke koma macen ..wai se ka tura kai cikin falon mutum tukon zakayi
sallama..kasan a wani hali zaka tarar dashi..ne... Ko dayake may be daga wazirin
har Madina basu karanci hadisin ma'aiki SAW daya ke cewa''baya hallata ga musulmi
ya leka gidan ko dakin wani ba tare da izini ba..Bukhari ya rawaiti shi....
...kuma ai ita madina ta sake mishi fuska har haka)
tunda ya shigo yaji jikin shi ya saki haka ya karaso ya zauna ..
Madina ta shiga tsarashi cike da makirci da nuna cewa komi ya fice a wajenta har da
nuna jin
Dadin ta ga wanna auren koma ta na goyon bayan shi kan abunda yayi
Wai shi me diya ..se kawai ya saki jiki da ita nan ya shiga ga zayyana mata yanda
auran ze gudana ...
Madina daga kasa se dariyar mugunta take mishi kai daga karshe ma tace ta dau
nauyin kayan dakin amariya ...
Abunda ya kara tunzura waziri da yarda da ita ....kamar gaske tasa aka kawo mishi
lemo . abunka ga wanda murna ta cika shi ya ma manta da Madina ce matar
Sarki ...Kawai be kawo komi ba ya bude cikinshi ya kwankwadi lemun shi .....yana
gamawa sega kiran wayarshi ya shigo ...Maheeba ce da sauri wai yazo zasu kara
tattauna wa ya fita tare da yi mata sallama ...
Yana fita Madina tayi wata makirar dariya tace dani kake zancen ...
A bangaren su Fulani kuwa ita da Sarki suna zaune suna hirar su dan tunda akayi
maganar auren Murad da Maheeba ya sa Madina ta dena shigowa .akai2 ...suna tsaka da
hirar Fulani tace daman akwai wata magana dana ke son muyi akan auren nan ...a
gaskiya yanzu bana goyon bayan auren nan kai hasali ma nifa ban masan yanda akayi
na amince ba ba ...kuma ....jiya da dare kawai nayi wani mummunan mafarki kan auren
nan ...nide gaskiya a fasa tunda de ko kati ba'a buga ba bare ace garin yasan mi
ake ciki ...kuma ko jiya jiya nan da safe babu irin magiyar da be munba ...kasan
kuwa har kwantar da shi akayi a england ciwonshi yayi wani mummunan tashi Allah de
kawai yasa da sauran kwanakin shi nan gaba ...da yanzu mun ras ...se kawai ta kasa
karasa kuka yaci karfinta ..
Sarki ma hankalin shi ba karamin tashi yayi ba ..yace nima de kin sosa mun inda
yake mun k'ayk'ay dan har ga Allah bazan ce ga yanda abu ya faru ba kawai de na
tsinci kaina nane da amincewar auren ....amma yanzu kirawo mun shi a waya shi Murad
din muji ta bakinshi...
Kallon lokaci tayi taga goma har gifta amma dayake maganar me mahim manci ce yasa
kawai ta danna mishi kiran ...
Lokaci kuwa yana bangarenshi shi da Maysam se shagwaba take zuba mishi kan seya
kaita shopping gobe Se burgima take ajikin shi duk ta yakuna mishi kaya..
.shi kuwa ya kyaleta ne dan yasan yanzu babu idan zashi dare ne ...kuma shi badan
baze iya kaita bane a'a kawai futar ce ma baya son yi kwata2 dan baya son ya gamu
da wani ma Wanda ya san zancen wannan aure ...
Suna haka kiran ya shigo shiit yace da ita ya dau kiran da sauri ganin lokaci ya
san ''quelque chose ne va pas'' lamo tayi a jikin shi tana jira ya gama ta cigaba
daga inda ta tsaya....
Cike da ladabi ya dauka ya gaishe da fulanin..
Bayan ta amsa tace ya zo nan fada dadyshi yana son ganin shi ....
Da sauri Maysam ta shiga ta dauko mishi wata riga .jin Sarki nason ganinshi ...kuma
be kamata ya fita da rigar nan haka ba..
..lokacin data dauko har yakai kofar fita dan sauri..
..
Itama Da sauri tace yaya tsaya..
Ya tsaya tare da juyowa yana fadin minene kuma cikin fada....
Turo baki tayi tace to ba riga na kawo maka ka sauya ba..
Shi se lokacin ya tuna da rigarshi ashe duk ta yakune se kuma jikin shi yayi sanyi
gani tayi fushi...karba yayi ya saka ita kuwa ta anshi waccar din tayi shigewarta
wai ita nan tayi fushi...
Girgiza kai yayi ya fice dan lokacin bashi da time din biye mata...
Su biyu ne palon kamar yanda ya zata nan ya kwashi gaisuwa wajen dady ...
Sarki ya ansa cikin sakin fuska ...se kuma yace dama game da zancen auren ka ne
yasa nayi kiran ka
Kafin ma yaji mi za'ace ya shiga bawa Sarki hakuri kan shifa baya son auren nan
hasalima auren dole ne ake shirin yi mishi har da yar kwallarshi....
Sarki yayi jim yana kallonshi..can yace to dama dan mujine ta bakin ka ..tunda baka
so baza ayi ba ..kana iya tafiya...
Nan kuma hankali shi ya tashi dan jiyake ko yayi fushi ne...ya shiga bada hakuri ..
Sarki yace a'a daman muna da niyyar fasawa ..to mun tambayaka ne dan kada aje ko ka
fara sonta...
Da sauri ya kalle shi yace ..so..?fa Dady ai ni so daya kawai nayi Shima wa
SWEETBABYNA.
Fulani tayi dariya a ranta tace ita kuwa Maysam din fa...kayi ka gama mude idone
namu ..
Sarki yace to shikenan kana iya tafiya Allah yayi maka albarka . .
Nan fa kawai ya rumgume Sarki yana zuba godiya harda kwalar murna ...
Fulani ma ta shafi kanshi tace hankali ya kwanta ko....
Cike da farin ciki ya fice ...
Sarki ya kalli fulani yace wai ashe har haka yake kin auren nan jibi fa ko lokacin
auren shi da Maysam be nuna kin amincewarshi ba haka..
Fulani tace ashede da mun cutar da dan mu da kanmu ...
Sarki yace Allah ya kara tsare mu tare da yi muna zabi na alheri aduk lamuran mu
Ameen fulani ta amsa .
Wani sauri ya ringa zunkudawa kamar wanda ze tashi sama ..
Yana zuwa ya ma manta cewa Maysam tayi hushi dashi kawai tana zaune se ji tayi yayi
sama da ita yana juyi ..
Itade tana mamakin miyasa ka shi murna haka take ..
Yana sauke ta yace ''devine quoi? ''(Ci aruwa?)
Tana turo baki tayi kalar tunani ...tace na baka gari
Yace to an fasa aurena da Maheeba ....
Be gama fada bama tayi wani uban tsalle me game da ihu ta dare bisan shi tana me
jin dadin wannan abun...
Nan fa dadi kamar ya kashe su ...ya kirayi Mahmud ya sanar mishi ...
Shima ba karamar murna yayi ba .
Murad yace ki shirya gobe mufita yawo ba shopping kade ba ....
E fa murna ta gamewa Maysam bibiyu ...
Can yace ta tashi ya rakata bangaren fulani ..
Nan Maysam tace bata san zancen ba ..kawai dan yayi mata wayo ne yayi tafiyarshi
shi kade ya barta... ji wani shirme....
Be hanata ba ... Ta shige dakinta na nan bangaren tayi wanka tasaka kayan baccin ta
..ta feshe jikinta da turare kamar yanda fulani ta koya mata ta nufi dakin
Murad ...shi lokaci har ya kwanta tazo ta makalkale shi wai ita tsoro take ji be
cema komi ba ya gyara mata kwanciya ...duk da har yau inde sun samu contact body
tofa se yaji electric shok din nan sede yanzu ba sosai ba.....
Cikin dare biyu na dare Murad ya raba jikin shi da shimfidar ya doro alwala ya
shiga nafilfili da addu'oi da godewa Allah kan wannan sauyi lamari daya samu .yasan
daman addu'a bata faduwa kasa ..ko ba dade ko bajima ...
Wajejan uku na dare itama Maysam ganin shi yana salla yasa ta tashi ta doro alwala
ta shiga nafila .
Ba su suka kwanta ba se bayan sunyi sallar asuba tare da yin azkar dinsu ....ta
kuwa kara shige mishi jiki..bacci me dadi ya a won gaba da su
Wayewar gari lfy Maysam et Murad...
Ina masoyan Maysam ku fito mu ganku. To ..
Mi ye makomar Waziri da iyanlanshi ?kuma
Ina yinku irin totaly din nan
Fasma ce
*FASMA*
joyeux anniversaire my sam ..wish you all the best ..que cette année soit une année
de bonheur,