Author : FASMA Category : African Stories & Novels
ta.
Bangaren Abbanta ta nufa dan yi musu bankwana shida Murza sun jima Mallam Musa yana
yi mata nasiha da kuma ta kare mutuncin ta da na aurenta ...
duk sai jikinta yayi sanyi taji kamar ma ta daina tafiyar amman tuno wa da tayi
yayan ta na can sai ta samu kwarin guiwa har zuciyarta tafara azzalzalata dan
zumudi
Dakin Murza ta nufa da niyar yimata ban kwana amma mi cak ta tsaya a dede kofar
shiga palon banyi aune ba naga hawaye sun fara zarya a kumatunta cike da mamaki na
matso na kara kunne na dan ji mi yasata kuka sai naji Murza tana waya tana fadin ee
kadan ma suka gani wly ni nan zan zama ajalin Murad de Maysam (kuji fa da allah
kamar ran a hannunta yake ) da ba ma rashin sa'a ba da yanzu sun dade da mutuwa
ai...,
ke nifa haukata shi naso ayi yabi duniya bama a raba shi ba da dangin ba fadar
madina da ga bangaren layi ,
shewa Murza ta kwasa tace wannan shine target din mu na gaba sai kinyi uwar dakina
shugaba Madina matar sarki shugaban masarauta gaba daya kai ko makirar Fulani ba ta
isa ta taka miki birki ba dole ne ki taka wanda kikeso a garin nan dan duk wanda
yayi miki kan kara za kiyi mishi ta itace abuga dake a barki anan waziri ma yayi
nashi babin an shafe shi.
Dafe kirjinta Maysam tayi cike da mamaki da kyar ta lallaba ta koma bangaren fulani
dede zata shiga taji muryar Mahmud na fadiwa Fulani kaf abunda yafaru shida Murad,
yakara da fadin amman fa ina ganin ba a hayyacin shi ba yake dan a gaskia wanan
al'amari akwai ayar tambaya a ciki
jim Fulani tayi tana jinjina maganar sai kawa Maysam ta fado ba ko sallama tana
gwanjin kuka cinyar Fulani ta fada ta saki wani sabon kuka mai cin rai cike da
tashin hankali fulani ke tambayarta miya faru .?
kukan yakasa tsayawa ta shiga fadin Momy kada kiyi fushi da yayana ba laifin shi
bane wly sune kuma sunce ma sai sunga bayan mu nida shi
Cike da tsoro Fulani da Mahmud sukace suwa din?
Yanzu nan naji Inna Murza tana waya da wata Madina matar sarki nan ta kwashe kaf
abunda taji ta fada musu.
Mahamud dey mamakine ya cika shi har yawun bakinshi ya kafe ya rasa mi zai fadi.
Fulani batayi wani mamakiba dan dama bata yarda da tuban Murza ba kuma ta gane sare
Madinar da take fadi sai tayi shiru.
A fusace Mahmud ya tashi yana fadin kafin su kasheku ni bari nakashesu ..
,dakatar da shi fulani tayi da fadin zauna muyi magana
Bayan ya zauna tayi mishi nasiha kan illar a bunda yake son aikata wa takara da
fadin ''maintenant on a aucune preuve en notre disposition qui va prouver leur
actes. .
Mahmud ya ce''Mais Momy ,Maysam a tout entendu non?.''
Fulani ta sake fadin''Meme si elle a tout entendu c'est sa parole contre celle de
Madina kuma ma babu wanda zai yarda saboda iya makircinta dan tana gwada kamar ta
goya Murad gaban mutane in baka mantaba waziri ma fa yaka yafada amma babu wanda ya
yarda ....
Yanzu de mu fara da kubutar da Murad din daga baya se musan yanda zamu bullo
musu....in su da adiri suka dogara to mu da Allah muka dogara
Nan Mahmud ya bada shawarar ayi ta saukar qur'ani tare da zuwa makarantu su taya su
da addu'a...ya kuma cewa muma kuma zamu rage bacci mu zanki rayashi da nafilfili da
addu'a ..
Sosai sukayi na'am da shawarar nan .....
Maysam tace Allah ya bamu nasara akansu..nima na samu Mijina ya dawo kusa
dani..muyi....
Tsit tayi ganin irin kallon da suke mata ..
Se lokaci ta tuna ashe fa a gaban Surikarta fulani take ..ai da gudu da shige
kuryar daki tana dariya ga kunya kamar kasa ta nutse ta shige ..
Dariya Mahmud ya shiga yi mata ...
Fulani na fadin yaki dawo y'a ta ai bama yar haka dake...
Amma ina Maysam ta ware ..
.nan Mahmud yayi mata sallama tare da jaddada mata gobe2n nan zesaka a fara saukar
alqur'ani..sanna ya fice.
Fulani tabishi shi ma da addu’a dan a gaskiya samun aboki kamar Mahmud a yanzu se
an tona..
A ranar su duka ukku baccin da sukayi kadan ne dan kwana sukayi suna rayashi da
nafilfili da addu'a Allah ya basu nasara akan su Murza ya kubutar da Murad da ga
sharrin su ...
Love you all
Yawan comment dinku shi ze bani kwarin guiwar yin typing me yawa
Fasma ce
Story&Written
by
*FASMA*
*I miss you my Arfat and my in law Xaynabqueen ..wai ina kuka shige ne kwana
biyu ...Allah de yasa you are fine*
Dedicated to all my fans
79__80
```Manzon Allah(SAW) ya ce''wanda duk yayi imani da Allah da ranar lahira to ,ya
fadi alheri ko kuma yayi shiru.
Bukhari da Muslim suka rawaito shi..```
[29/07/18 à 18:40] Washe gari Maysam ta fito cikin shirin ta dan jirgin 10 na safe
zasu bi . zuwa Niamey daga can kuma su daga zuwa England
Da ka ganta kasan tana cikin damuwa .,,duk ma se take ji kamar ta fasa tafiyar nan
duk jikinta yayi sanyi ...gashi wanda take zumundin son zuwa England dan shi ,din
ma Murza sun mishi Asiri .
Haka tayi break sokoko da ita duk Fulani na lura da ita ..dan haka seta ja ta jikin
ta da nufin lallashi
Ai kuwa kamar jira take ta kuwa fashe mata da kuka.
Itama Fulani se zuciyar ta karaya duk se taji ba dadi .....
Haka tayi ta lallabata tare dayi mata nasiha me ratsa zuciya .. ..
Da kyar tayi shiru har fulani na tsokanar ta da fadin ko se ta goyaki ta ne zatayi
shiru....
Nan ta kyalkayale da dariya..
Fulani tayi mata jagora fardar sarki tayi mishi bankwana ..sosai ya yi mata nasiha
shima ..
Suna fitowa fulani ta. bata wata tsaleliyar waya ,,koda na leka na ga iphone,7,..zo
kaga Murna wajen Maysam yau tayi waya ..dan dama Murad ne ya hana a bata ,to amma
yanzu halin tafiya yayi sanadin an bata..
Fulani tace duk number kowa tana ciki na samiki..
Maysam ta kauda kai tare da fadin har ta yaya na ...
Fulani tayi kamar bata gane ba tace ai ..na samiki har ta yayanki Mahmud...
Tayi kicin2 ta fuska tace Momy ta mijina fa nake nufi ...
Fulani tayi dariya tace tofa an zo wurin masu miji manyan to har ita na saka
miki...kai har da photunan shi na tura miki dan daman sun cike mun waya..
Maysam tace kai Momy kin ceci zuciyana fa da yanzu zance a turo min dan ko bacci
zanyi sena saka ka photon a .. ...se kuma tayi shiru da sauri tasa tafin hannuta
tana kare fuskarta dan Seda tayi maganar taji kunya amman ta mazge dayi mata
godiya...ita kanta bata san dan mi yasa ba bata iya controling din kanta wani
lokacin..
A gurguje ta shiga bangaren Abbata tayi mushi sallama haka ta daure ta shiga Dakin
Murza tayi mata sallamar.
Kamar gaske tana wani dariyar yake wai ita dole yanzu son Maysam take ,,a zuciyarta
kuwa fadi take ina nan kwanan nan zaki dawo gida kici Ubanki shegiya kullum se kara
kyau take kamar yar sarkin aljanu..
Itama Maysam sakin jikinta tayi kamar ba'ta ji komi ba ..amma addu'a ce fal
ranta ....
Haka suka rabu da fulani duk kwalla ta cika mata ido inda Mahmud zeyi mata rakiya
har AEROPORT DIORI HAMANI na birnin NIAMEY......acan suka hadu da sauran kawayenta
Su Mufeedah suma sun iso duk da yan uwansu nan suka gaigaisa ....suna na zaune aka
fara kiran passengers ..haka suma su Mufeeda suka rabu da familly ,
,,Mahmud yana nan har jirgin ya daga ..
Wata yar dantijuwa. na gani ita da mijinta wacce tun lokacin da ake kiran passegers
naga ta tsurawa su Maysam ido bata ko kiftawa. mijinta na mata magana aman bata ma
san yana yi ba . hankalinta rankatakwab yana. Wurin su Maysam din.....Mijin ta na
mata korafin su huce tun dazu amman hankalinta baya ma wajenshi shima ya meda
kallonshi ya ga miyene ya dauke mata hankali haka amma lokacin su Maysam tuni sun
shige jirgin ....
Suna nan har se da jirgi ya tashi naga ta sauke wata nauyayar ajiyar zuciyar...
Da sauri mijin ya kalleta yace ya akayi ne ?ko jikin ne...?
Girgiza mishi kai tayi kamar karamar yarinya tace a'a naga wata yarinya ne me kama
da Baby na...
Shima ajiyar zuciyar yayi ya ce ya kamata yanzu yaci ace kin sakawa zuciyar ki
hakurin rashinya ta ....shekara nawa kuma kusan kullum se kinga me kama da ita ....
Da sauri tace a'a wannan ta banbata da sauran wanda nake gani kullum..
Dan murmishi takaici yayi yace kamar kullum kenan haka kike cewa ...kiyi hakuri ki
rumgumi kaddara ..idan har tana raye Allah ya bayyana mana ita ..
Ameen ta amsa amma kam ta kwallafa rai a kan yarinyar dan ta so tayi mata magana
kamar yanda take yi duk wacce taga tayi kama da Babyn ta..
Sun juya da niyar tafiya ..naji Mahmud ya ce Mom,da,Dad... parent din SWEETBABY
ne.ashe..
Juyo wa sukayi suka ga Mahmud ne ..
Nan ya gaishe su cike da.ladabi ..
Suka amsa suna fara'a ..
Mom tace que est ce que te venu faire ici. ?
dan sosa kanshi yayi yace matar Murad ne na kawo zata fice England.....
Dad yace a'aa Masha Allah..
Mom tace kash yau ma babu rabon zanga ta ashe ko dayake fulani taso ta turota kafin
ta fice to se akayi rashin sa'a muna Paris.hakama lokacin da akayi aure bama
kasar..da nasan yau ne tafiyar ma ai da tun jiya zamu dawo dan naga matar d'ana..
Su Dad sukayi yar dariya sukace ai gaba da yawa zaki ganta. Wata rana
Itama dan murmushi tayi tace hakane to Allah ya nuna muna ya kuma sauke ta lfy .
Suka ce ameen...
Nan Mahmud ya yi musu sallama tare ya fice dan yana son a fara yi mishi saukar tun
yau dan karfe da zafi2 ake dukanshi.
Suma driver ya huce su gidan su.
A raina na ce kenan de su anan Niamey suke. .
Ko sarki fulani bata sarna mishi ba halin da Murad yake dan bata da wata
sheda .....
To daman gata da temakon talakawa dan kowani wata biyu ko ukku se an kai tamako
kauyika ko Mutuwar SWEETBABY ma suna hanyar kai temako wani kauyen ne sukayi shi.
Wanna abu ba kamramin faranta ran sarki yake ba shiya sa ma kullum sonta yake kara
shiga zuciyar shi sabanin Madina da ko yan Uwanta bata son temakawa bare wani ..
Shiyasa ma yanzu da sarki yaga kusan kullum se an kai wa makarantu taimakon se beyi
wani mamaki ba dan shi ya aza ta sauya takun ta ne na temakon....
Har ranar suna fada da dare su ukku yake tsokanar ta da fadin wai kode dan taji
labarin zeyi ta ukku ne yasa take shiga da ficen nan dan addu'ar ta amsu ya fasa
auren. ..
Madina da bata san irin wannan wasan ba ta kuwa dafe kirji tace na shiga ukku .
aure fa kace ka tsufan nan mi zakayi da wata macen.kuma shine ni ba'a gaya mun ba
se yanzu tana wani kumbure2...
Share zancenta sukayi sema
Fulani da ta son tsokanarta kawai yake ta amshe karaf da fadin muna maraba da
ita ...fatan zaman lafiya nake maka tanayi tana wani kashe me ido ..tace kuma ai
har yanzu dan saurayi shatak yake ,,ni kam bana ganin tsufanshi.....
Takaici ya kusan kashe Madina daga zaunen banda zabgawa fulani harara babu abunda
take ..
Sarki yace wannan haka yake nima kullum kamar yar sha bakwai nake ganin ki ...wai
ma miye sirrin nan ne .um yan matana...
Fulani tayi wani far da ido ta ce to kawo kunnenka kaji..
Babu gadama ya kuwa dan karkato kunnen shi yana dariya ..
Cike da shaukin so da kaunar junan su ta kuso da bakinta zatayi me rada dan fa su
sun manta da wata Madina na wurin...(kuji wani salon soyyayar tsofi ko )
Se ji sukayi Madina tayi tsaye tana fadin tsofe2 daku amman kuna wani abun kamar
kananun yara ...wannan ai ko Murad baze yi abunda kukeyi ba tanayi tana dokawa
fulani harara....
Fulani a ranta fadi take ...ke kike ganin mun tsufa amman ai ita soyyaya bata
tsufa..( to fa kunji tsofafin ko?)....
Fulani mikewa tayi tana fadin seda safen ku dan Madina keda girki yau..
Sarki yace zo ki fada mun mana kafin ki hucen ...
Fulani na dariya kasa2 ta ce to ai ya fice sede wani jikon..kuma
Kallon zamu hade naga yana jifanta dashi...
Wanda ya kara harzuka zuciyar Madina ..ta shige kuryar daki fuuuu ..tana fadin
jarabbabiya kawai.macce se jarabar iya kissa mtssss.
( Madina kina sha'anin ki fa )
..
Su Maysam sun isa England lafiya ..daya ke gwamnati ce ta tura su kafin ma su isa
har an turo musu bus din dazu dauke su dan ba su kade bane suka samu promotion din
ba....
Direct babbar university England aka akaisu ..nan aka rarraba musu dakuna su anan
cikin hostel din makarantar...
Amman cikin rashi sa'a se ba a hadasu daki daya ba ...Mariam da Mufeedah da wata
dakin su guda se kuma Maysam da wasu yan mata suma dakin su guda..
To fa nan ake yinta Maysam ganin an ware ta da su..da kyar da siddi suka shawo kan
yan matar sukayi changé da Maysam.ta koma daki daya da su Mariam.dadi kamar ya
kashe su ...
Tun washe gari suka fara zuwa lecture dan har an fara da sati suka zo ..dan haka
babu zancen hutu ma ...
Class dinsu guda wato medecine dan sunce mutuwa ce kawai zata raba su ..komi nasu
iri daya ne kai har dressing dinsu ma iri daya suke yi .kuma kullum zaka gansu da
hidjab din su basa yarda su fito hakanan duk da suna garin turawa....., .suna taka
tsantsan da rayuwar su ...sun meda hankalin su ga abunda ya kawo su..
Ba kadan ba suke birge ba mutane da basu sha'awa dan duk gani suke trijumelles
ne(yan ukku)......
Yanzu har sun cinye 1 mois da zuwa ..suna ta karatun su cikin kwanciyar hankali
banda Maysam data tsanan ta tunanin ta oga Murad ...shi yasa ma basa barinta ta
zauna ita daya koda da second daya ne dan yanzu zata saka photon Murad a gaba tana
ta tunanin shi..tun abun baya damunsu har yazo kuma yana yi dan sunsa miyasa Murad
din be nema ta ba suma kullum cikin taya ta da addu'a suke...
Yau ma kamar kullum su Mufeedah sun dan fita suka bar Maysam a daki tana dan
exercice..
Amma mi ko minti daya basuyi ba da futa ta ture komi gefe ta fara sa'arta wato
kallon photon..
Shigowar su kenan ...suka ji Maysam na fadin ita kade wly duk ranar da muka hade da
kai ko to sena tsotse bakin nan tas ..dan gaskiya Allah yayi hallita a wurin
nan ..dan lips din nan shine ake kira Kiss me babyn nan ..ita duk jitake a ranta
tayi maganar
Tana kallon photon tana doka murmushi.
Mi su Mariam zasuyi in ba dariya ba suka kuwa tun tsire da ita har tasaki baki tana
kallonsu dan bata san mi suke yiwa dariya ba
Mufeedah ta matso tace inda muga irin lips din nan da ake ta wani yabawa haka...
Wani waro ido tayi tace wai kuna nufin dama a fili nayi maganar nan ne..
Mariam tace a'aa a Mafarki ne..
Gaba dayan su suka saka dariya ...haka suka ci gaba da rayuwar su .cikin jin dadi.
.
A can gida kuwa sauka yi ake ba kakkau tawa ..
Haka kawai ranar wata juma'a Murad tun safe ya tashi da wani matsene cin ciwon
kai ..lokacin yana likita ne dan haka ya tattara ya dawo gida amma ciwon kamar
karashi ake ...
Ba bu zato yaji bakin shi yana abaton addu'a wanda rabon daya ce yayi addu'a kai
koda bayan salla ne to ya manta...
Kan kace mi bacci ya sure shi ..bashi ya farka ba se wajejen sha biyu da rabi na
rana duk wani iri yake jinshi kamar wanda iska zata dauke shi yake ji fayau2
kawai....ganin lokacin sallar Juma'a yayi dan haka wanka yayi ya fice Masalaci duk
da akwai yar tazara dashi da masallacin. Amman har yanzu kan be bar mishi ciwon
ba...
Tunda sheik din ya fara huduba jikin shi yayi sanyi duk se yake jinshi imcomplete
kamar wanda ya rasa wani abu a rayuwar ya ke ji dan akan yin biyyaya ne ga
uwaye...ake hudubar..
Haka jiki ban kwari har akayi sallar ..suna gamawa mutane suka fara tafiya dan ba
wani yawa ne da su ba daman...
Amma shi Murad nan ya tsinci kanshi da ya zauna ...yana yiwa fiyyenyen Halitta
SALATI ..
Mark dake share guda yana kallon shi duk mamaki ya cika shi ...duda yasan wannan
al'adar shi da Murad ce in akayi Sallar juma'a nan zasu zauna suyita istigifari
tare da salatin Nabiyi ..to aman fa shi Murad ya dade da fasata ..dan ana gama
sallar yake tafiyar shi...
Be gama tsinkewa ba seda yaga an tada sallar la'asar anyi shi da Murad din dan ba
kullum ba yake ziwa masallacin ma agida yakeyin sallar shi...
Shi kam Murad tun da ya fara yin Salatin ya ji zuiiyar shi ta nutsu ..wani rin
nishadi yake ji yana bin duk illahari jikinshi
Kasa hakuri Mark yayi ..bayan sun gama sallar ya matsa kusa da Murad din yayi mishi
sallama nan suka gaisa ciki da fara 'a Murad din yake amsawa ..
Mark de ya boye mamakin shi dan ba kamar kwanakin baya ba da sama2 suke gaisuwar
ma..
Nan Mark cikin dakewa yace yau fa duk kawani sauya mun ...
Murad yace mi ka gani ne.....
Mark daman kamar jira yake nan ya kwashe komi ya fada mishi har da zuwan Mahmud din
da yanda sukayi dashi ...
Inna lillahi wa inna.ileyhi raji'un ... A bunda bakin Murad ke memetawa kenan .....
Be gama tsinkewa ba seda yaga babu numb familyn shi ko daya a wayar shi ...
Mark yayi karfin halin fadin ai ka canza layi tun da dade wa....
Hawaye kawai ya shiga zarya a idon shi yama rasa abunyi ya kuma rasa miya sa shi
yin haka gaba daya baya iya tuna komi......
Mark daya fara dan zargin wani abu se yaji tausayin shi ya kama shi dan shi dama
yasan da walakin goro cikin miya ...Murad dayake tsananin son familyn shi aman
farat daya ya yanke duk wani contact dinshi da su ...
Nan Mark ya shiga yi mishi Nasiha tare da jan hankali kan ya rike addu'a don ita ce
takobin mumuni....
Daga haka Mark ya bashi shawara ya kirayi su fulani yanzu ..
Kallon agogon hannushi yayi ya ga hudu na yama kenan yanzu goma na dare ne a can ..
Amma duk da haka ya danna number fulani dan ya haddace ta a zuciyar shi tun da
dadewa...
Lokacin fulani tana shirin fita zuwa wajen sarki..kiran ya shigo..
Ringing a na biyu ta daga duk cike da zumudi dan taga number england ta aza Maysam
ce ta ari wayar kawayen ta kira...dan haka tana dagawa ta fara da fadin asallama
yar gidan Momyn ta .....
Murad daga can a ranshi ya shiga dan tunani nan da nan zuciyar shi ta fara aikin
zut2 dan tuno mata da Maysam...katse shi fulani tayi da fadin hello..
Cikin da sanyi jiki zuciya na mishi fat2 ya amsa sallamar tare da fadin Momy
nine...
Wani farin ciki marar misultuwa ya ratsa zuciyar