Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin Accident Complete Hausa Novel by FASMA

Author :  FASMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 32

15K to 18K   out of 94.8K words

kama da aljannu ..waya sanima ko diyar sarkin wani aljanin ce...ta
bankad'e ta ta fice..
Itade Maysam idon wannan shine bata ce da ita komi ba ...se addu'ar neman tsari
datayi ..
Ran Murad in yayi goma ya bace banda tsaki babu abunda yake dan ya tsani african
time....
Gabanshi ne yayi wani mummunan faduwa sakamakon yin tozali dayayi da fuskar Maysam
dake nufo so ...baki da hanci ya saki (kamar Halima da Samira sunga MIP .)ya zubawa
sarautar Allah ido banda wata barakallahou fi.........babu abunda yake ambato wani
abu yaji ya d'asu me a zuciya kafin ya lalibo yaji miye
Mahmud ya katse shi da fadin kallon ya isa haka kada idon su fad'o sanan yasa hannu
ya rufe mishi baki...
Wani haushi ya ji ...Mazgewa yayi ya buga tsaki Mtssss to uban mi zan kallan a
jikin yar kauyen ne ...
Shide Mahmud dariya yayi yace ashe shegen ka iya zab'e wannan kyau har haka gata
kuma yarinya danya sharat haka ..amma kake wani basarwa kamar baka son auren..
B'ata fuska yayi yace ya ishe ka haka fa to..
Kafin yace wani abu su Maysam suka iso..
Mahmud ya fito ya bude mata baya inda Murad yake yace bismillah amarya
Tana d'ari2 ta shiga motar ya rufe ya zagawo ya shiga danshi ze tuka su..
Wani ni'imtaccen kamki shi ya daki hanci Murad besan lokacin daya lumshe ido
ba .....
Itama hakan ta kasance a ban'agarenta a hankali ta bude baki zata gaishe shi gudun
kada tayi laifi amma mi?
Wata jibgegiwar tsawa Murad ya daka mata yace d.....
Wash kuyi manaje da wannan..
Fasma
Ahmed Gumel
[8/17, 1:39 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š
[8/17, 1:41 PM] A A Dboy: ๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

25__26
Manzon Allah ( ```SAW) ya ce''Dayanku ba zaiyi imani ba har sai na kasance ni nafi
soyuwa a gareshi daga dansa da mahafinsa da duk mutane baki daya''
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` .
Wata jibgegiyar tsawa Murad ya daka mata seda ta gigice gaba daya ta qara tsorata
dashi yace...ke dabbar inace da baza ki iya gaishe damu ba.... ohooo ko mu kike
jira mu gaishe kin ko ? Idiote kawai.......
Jikinta har b'ari yake ta sauri tace ina wuninku Yaya..
Muryarta na dakar dodon kunnenshi besan lokacin da ya juyo da kallenshi gareta ba
Aka koyi sa'a ta d'ago kai itama ...idonta cike da kwalla kad'an ya rage su
zubo ...
Habawa idon na sarkewa cikin juna gaba dayansu suka kasa d'auke idon kowa da abunda
yake ayyana wa a zuciyarshi .....
Ita tana yaba irin kyan da Allah yayi mishi ne
Shikam gogan gani yayi tana mishi kama da lovely sister dinshi data rasu a SANADIN
ACCIDENT dasukayi da dad'ewa.....wata irin tsanar ta yaji yana shigarshi dan kuwa
ta tuno mishi kahon zuciyar shi .........kawai beyi wata2 ba ya zabga mata wani
kantameman mari seda gefen bakinta ya fashe yace ''que รงa soit la premiรจre et la
derniรจre fois(wannan ya zama kashedi na farko kuma na karshe) dazakiyi gigin qara
saka idonki cikin nawa kai ko kallona na kamaki kinayi da wannan idon naki me kama
dana mayu to walahi na lafira seya fiki jin dadi shasha kawai kina yar jinjirar ki
amman har kin san ki kafe mutum da ido a ranshi yace walahi Momy ta gama dashi a
rasa wacce za'a aura mishi se wannan yar shilar(ni kuwa nace dama na lahira inde
dan aljanna ne ai dole ya fita jin dadi nesa ba kusa bama ehe )..
Batace komi ba se hawayen dake makalle su ka zubo shar2 ta dafe kuncinta dan marin
ya shigeta sosai ...
Se kuma ya ga rashin kyauta war hakan danshi be cika son dukan mata ba kai ko gani
yayi wani yanayi to ze yi kokarin hanawa ..a ranshi yace to pourquoi na mareta ?mi
tayi mun...wata zuciyar tace saboda tana famar tado maka da tsohon ciwon kane......
Ita kam kuka take me cin rai duda in silence takeyi..
Ganin sun kusa isowa yasa ya bata Mouchoir yace amshi maza goge mun hawayen nan
sanan kuma kiyu mun shiru duk kin wani cikawa mutane kunne da kuka salon ayi zaton
wani abun nayi miki....
Mahmud da bece komi ba tun d'azu yanata tukinshi yace M2 ya zaka daki yarinya sanan
ka hanata kukan ai abun se yayi mata yawa ...
Wata harara daya zabga mishi yasa shi yin shiru....
Maysam kuwa amsa tayi ta goge hawayen sanan ta gogoge jinin na gefen bakinta ..yar
karamar bag dinta ta bude tasa mouchoir din kudun kada ta bashi tayi wani laifin a
ranta tace shi kuma wannan haka kalar tashi muguntar take,?
Babu wanda ya sake cewa komi har suka iso ...
Har ze fita Mahmud yace na roke ka kushi ga tare kamar yanda ko wa yake yi ...fais
รงa pour moi
Bece komi ba ya fita ..ganin haka yasa itama tafito...wani jan tapis me laushi da
fleurs (flowers) ne shimfid'e tundaga dede motar har cikin hall d'in ...
Jero wa yayi da ita suka fara tafiya ...da sauri Mahmud ya sha gaban su yace haba
alfarma fa na nema kuma walahi su momy gaba daya suna ciki...
Tsaki Murad yayi yace to ya kake so ayi ne dan raini kawai..
Dariya Mahmud yayi dan inda sabo ya saba yace hannun ka zaka zagayo ta baya ka rike
kugunta ..itama kuma tayi hakanan se kuma ta kwantar da kanta bisa ka fad'arka
shikenan fa
Zo kaga yanda Murad ke mishi wani irin kallo kamar idon ze fad'o kasa ..sunfi 2mn
amma ko alamun yi beyiba sema wani juyar da kai dayayi gefe
Mahmud yace haba M2 kufa kad'e ake jira..
Tsaki ya kuma ja mtsss sannan ya sa hannun da niyar d'aurashi a kugun amma mi?yana
d'ora hannun yayi maza ya dauke sakamakon wani shock รฉlectrique daya ji ..itama
hakan ce ta kasance a b'angarenta har seda ta runtse idanu....
Shikam Murad abun ba karamin mamaki ya bashi ba dan kuwa wannan shock din idan ya
tab'a late lovely sister d'in shi kade ne yake jin shi ..ya gane hakan ne dan
betab'a sake jinshi ba tun bayan rasuwar ta kuma gashi docteur yasha tab'a mata dan
yi musu magani amma bejishi ba..
Wani haushinta tare da tsanar ta yaji yana qara d'asuwa a zuciyarshi har wani zafi2
ta fara yi mishi...
Kafin ya gama tunani kiran Momy ya shigo wayarshi yana dagawa ta fara balbaleshi da
fad'a taya za'a tara mutane amma dan raini kuki shigowa banci tun dazu kuka
zo...kan yace wani abu ta katse wayar...
Bin wayar yayi da kallon se kuma yayi shahada ya daure ya mazge ..ya tattaro
jarumtarshi ta last year lol ..ya riko kugun ..
Mahmud yace amariyar mu ke muke jira fa..
Hannun na karkarwa tayi yanda Mahmud din yace takuwa kwantar da kanta bisa
kafad'arshi sede dayake ya fita tsayi so duka tsawon nata bakin dede kafad'ar tashi
ne ..nan suka fara tafiya a hankali kamar masu jin tausayi kasar..
Suna shigowa kowa ya zuba musu idanu hall din tak a cike yake da mutane wurin uwaye
daba haka wajen matasa ma..ko wacce se wani gyara zaman dan kwalinta take ko zata
sayu lol....
Dj ya saki kid'a
Masu photo sukace kau ban guri ta ko ina flash kake gani...fulani naga tayi wa
Maysam wani abu da hannu wanda bansan mi hakan yake nufiba ..amma ita wanda akayi
wa senaga ta wani sunne kai tana dan murmushi kasa2 ...jin ta kara manna kanta bisa
kafad'arshi ya sa yajiwo yana kallonta ..haba wannan position ba karamin burge
mutane tayi ba ..
A Wasu kujeru na alfarma masu ruwan zinare guda biyu jikin juna ne suka zauna ...
Nan aka fara programme din da fari aka bada takaitancen tarihin soyaryarsu wanda
duk Mahmud neya shirya kayanshi ........aka umarce su da su fito su taka rawa duda
a tsaye suke dukan su amman zo kaga yanda ake b'arin kudi....
Daganan kuma akace su fito su yanka ''gรขteau ( cake )
tare suka yanka se kuma shi ya fara bata ...dayake ya fita tsayi ..kumashi shi baze
iya dukowa ba se kawai ya dan dagata kadan dede tsawonshi ta saka mishi ..tafi raf2
kake ji ta ko ina
Can na hango yan Star Writer's Ass se wani washe baki suke ana korawa juice..ana
kus2 kasa2 lol
Samira.. Murjanah ..Dala.. Sarah ...Ummi .....Mzz beeberh ...se shoki ake kwasa ana
korawa da juice ....
Daga can bangaren na hango members na zuri'amu fans2 suma se ciye2 suke ....
Anyi ciye2 da shaye2 amma fa na juice duk wanda yazu ya cika tumbinsa sanan duk
wanda ze tafi to se anbashi wata sac me shake da alherai kan
turarenki ..atampopi ..etc...
Se wajejen goma na dare aka tashi wanda a lokaci Murad jiyake kamar yayi fufuke ya
ganshi a gida..
To daza su dawo ma seda yaso yayi musu drama .....Maysam tazo kenan zata shiga
motar ya kuwa daure fuska yace...
[8/17, 1:41 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š
[8/17, 1:43 PM] A A Dboy: ๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช
27__28
```Manzon Allah (SAW) ya ce "fiyyayen musulmi shi ne wanda duk musulmi suka kubuta
daga sharrin harshensa da hannunsa"
Muslim ne ya rawaito shi``` .
Da zasu dowo ma seda yaso yayi musu wata drama.....dan kuwa lokacin da Maysam tazo
zata shiga motar..ya kuwa d''aure fuska yace ke...se kuma yayi shiru sakamakon
ganin Momy da yayi se kawai ya shige motar fuskar nan ba annuri se wani muzzire
yake ...ganin haka itama Maysam da ta shigo taja bakinta gum.....
Koda suka iso da tayi niyyar fita da sauri ya riko hannunta duk da namijin kokari
yakeyi dan ba qaramin dauriya yayiba jin wani irin shock na ratsashi..
Seda yaga shigar Fulani bangaren ta sannan ya jiyo da fuskar nan tashi da har ta
canza kala yace dan tsabagen gulma da munafinci miye na wani biyoni dan shinshin
daa shegen iyayi kika wani shigo mun mota kamar wata bita zai2 nan ya dinga mata
fada ta inda ya shiga bata nan yake fita ba..ya qara da cewa kai ko magana inba
nina baki iznin yimun ba kikayi hum yayi kwafa..
Itade idon wannan shine
Abunda ya qara harzukashi kenan ya kuwa kaimata rankwashi seda kwalla ta cika mata
ido....
Da sauri tace dan Allah Yaya kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba. Na tuba ka
yafen..
Wata uwar harara ya ban kad'a mata yace kima qara kiga yanda zanyi da ke ..ya fice
abunshi.
Sum sum itama ta fito ta fice bangaren Fulani ..a ranta tace Allah abun godiya ...
Washe gari wajejen goma na safe Murad ne zaune gaban me martaba ya wani sunne kai
banyan ya kwashi gaisuwa ..me martaba yayi gyaran murya yace alhamdullilah Son
Allah yanuna mana aurenka ina alfahari da kai nan ya d'anyi mishi nasiha sannan
yace game da tarewar matar kace ....nida Fulani mun yake shawarar kawai ka tafi da
matarka can England .
Wata irin zufa Murad yaji tana karyo mishi kamar baze ce komi ba se kuma yace Ranka
shi dade bawai naki bin shawararku bane amma ni aganina abarta nan se asakata
makaranta tayi karatun nan
Ganin ya fara yin nasara ya ci gaba da fad'in ..because a can karatun zeyi mata
wahala dade anbari ta gama koda secondary ne seta ci gaba a can din...
Ayi mini afuwa idan na fad'i badede ba
Dan murmushi yayi yace shikenan to Allah yayi mana zabi na alheri
Ameen yace sanna ya fice direct bangaren Fulani ya nufa..a ranshi yace
alhamdullilah na rabu da alajakai ..amma inba abun su momy ba ina yar kauyen nan da
zuwa England ....
Kwance take ta d'aura kanta bisa cinyaryar Fulani se hira suke abunsu kamar uwa da
y'arta gwanin sha'awa...
Suna haka ya shigo palon ganin Maysam bisa cinyar Fulani ba karamin haushi yaji
ba...ya qara daure fuska... ..gaidata kawai yayi yayi shiru se wani ku
mbare2 yake...
Da sauri Maysam tace ina kwana yaya ...
Wani kallo yayi mata na irin zamu hadu dinna..ciki2 ya amsa a takaice da lafiya..
Momy ta gumtse dariyata tace wai ni son waya tabo min kaine se gumtse fuska kake..
da safiyar. Nan
Kicin2 da fuska yayi yace haba Momyn ya zaki bari wannan tahau min cinyata
Fulani tayi dan murmushi tace yo inba abunka ba yarima ai yanzu na yayeka ka huce
hawa cinya..ka girma ai yanzu kam matarka ya maye gurbin ka ..kafin itama ta haihu
ta barwa baby place ko?...
Be iya cewa komi ba amma a ranshi yace wai baby ..bade da niba zakiyi ta jiran
gawon shanu
Kuwa .
Maysam kam abun mamaki ma ya bata ta saki baki da hanci tana kallon wannan
shiriritar
kawar da zancen yayi da labarta mata duk yanda sukayi da sarki yanzu ..
Dan jimmmm tayi kamar me tunani
Da sauri yace kuma kinga in anan take zatafi sakewa tayi karatu da kyau ..
Shikenan Allah yasa hakan yafi alheri cewar fulani...
Maysam da tun dazu take jin duk hirar se wani
washe baki take tana mirmushi kasa2 dan akwaita da son ecole
Suna haka sega sarki ya aiko kiran Fulani ....nan ta barsu palon cikin su babu me
magana ...
Fitarta keda wuya ya ce kuwa ke zo nan.d....
Kuna raina fans love you
all
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:45 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š_*
[8/17, 1:45 PM] A A Dboy: ๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน
[8/17, 1:48 PM] A A Dboy: ๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

29__30
```Manzon Allah (SAW) ya ce "ya ku mutane ku tuba ga ubangijinku. Na rantse da
Allah ni ina tuba ga Allah a rana sau dari "
Muslim ne ya rawaito shi```
Fitar Fulani keda wuya yace kuwa da Maysam ke zonan wacce ita har ta kai kofar fita
palon ganin fulani ta fita..
Jiki na b'ari ta zo ya durkusa gwiyoyin ta a kasa ta sada kai kasa tace gani
Yaya ...
K'ara murtuke fuska yayi beyi wata2 ba ya dadage iya karfin shi ya rankasheta a kai
yace wannan na hawa cinyar Momy nane ...ya qara mata yace wannan na gaishe nine da
kikayi dan nace kada ki sake kimun magana matukar bani na baki izni ba...ya qara
mata yace wannan kuma na kallona da kikayi ne....
Ze qara mata da sauri tace dan Allah yaya kayi hakuri bazan qara ba...sega hawaye
shar2
Wasu biyu masu shegen zafi ya sake yimata yace wa inan kuwa na jin dadi da kikayine
dan za'a sakaki makaranta tare da ban hakuri da kikayi yanzu ya hankad'eta yayi
ficewar shi ya barta nan se kwasar kuka take...
Ta jima nan taga ba sarki se Allah ta lallashi kanta ta tashi ta shige room tana me
ayyana abubuwa da dama...
Sarki ma kuwa maganar karatun ce yayi wa Fulani ta ko yi na'am ganin irin farin
cikin da Maysam tayi lokacin da yarima ya sanarwa musu yanzu...
A b'angaren Murza kuwa Madina tasa aka yi mata kiranta ...tana dari2 tsoro duk ya
cikata ta amsa kiran dan duk a ganin ta wuyyar da tabawa wa Maysam ne za 'a
hukuntata
Amma me jin irin mugun nufin Madina da waziri akan su Maysam din har bata san
lokacin da wata bazawarar dariya ta kufce mata ba ta kuwa gyara zama tana sauraron
su daga nan itama ta ta karkace kai ta sanar musu irin yanda take yiwa Maysam har
zuwanta wurin boka seda ta sannar musu
Madina tayi wani murmushi tace shikenan fad'uwa tazo dede da zama in lokaci
tafiyarku kauye yayi zan turo miki da kudi kisa bokanki yayi mini wani aiki....
Murza se wani wangale baki take taji zancen kudi...
Haka suka yi ta tsara makircinsu ...
Murza jitake kamar ta zuba ruwa a kasa tasha jin za akashe mata Maysam ..sun jima
sannan taron makircin ya qare kowa ya kama gaban sa ...
Sha biyu na rana dede aka maida su Murza kauyensu cike da murna dan kuwa Madina ta
saki mata kudi a zuwan ta kaiwa boka ayi mata aiki akan Marud da Maysam ...zuwansu
keda wuya ta kuwa haura hann se wajen boka yankan wuka dayake bata tarar da Malan
Musa ba.....
Zaune take a gaban bokan se wani hangame baki take tana watsa wasu jan
hakoranta...nan ta fad'imi shi yanda suka tsara na akashe su ..
Buga kasa da tsubbace2 yayi kamar na wancan lokacin ...
Ya dubeta yace wannan yara da taurin kai suke dan kuwa ajalinsu ba anan kusa ba
yake abunda zan iya yi muku anan shine kawai rabashi da iyayenshi da matarshi kai
dama masarautar baki daya duk da aikin ba karamin aiki bane dan se azubadda da jini
ma..
Ko ajikinta Murza tace babu matsala a zubar ko na waye inde bukata zata biya ..nan
ta zube mishi rafar kudi wanda ita kanta bata san adadinsu ba a ranta tace nikam
kudi be daman ba inde Maysam zata dawama a wahala...se wani murmushi take...
Wani magani ya bata cikin wani tsumma yace a turara a wurin da aka san ze
ketara .....
Yana ketarawa yanda hayakin yabi iska haka shima in ya bar masarautar baze sake
waywayen su ba har se in ku kuka bukaci dawowarshi........
Ta karbe magani ta fito har da yar rawarta ta kama hanyar gida.....
ta shigo kauyen cike da murna dede wata kwana ai kuwa wata motar yan kasuwa ta
shayo kwanar itama ai kuwa ta kwasheta jikake ragajaf ta zube kasa wanwar...
Fasma
Ahmed Gumel
[8/17, 1:49 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š_*
[8/17, 1:50 PM] A A Dboy: ๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

30__31
*Ina maqiyan Murza ku fito wannan page* *din takuce .....ku fito ku kwashi shoki fa
....lol..*
*Ban manta dake ba my dear Hadjara* ( *Arfat.)..ina godiya da qaunarki Allah* *ya
bar qauna da dankon zumunci...ina yinki sosai ...* *littafinki "AMEMAH " yana wuta
gaskiya* *yana fadakardamu da nishadantar damu Allah ya* *qara basira da zakin
hannu Fans kada kubari a baku labarin* *littafin Amemah dan gaskiya ya hadu sosai*
Dedicated to all my fans
31--32
```Manzon Allah(SAW) ya ce "wanda duk ya yarda da cewa ALLAH shi ne Ubangiji,ya
yarda musulunci shine addini,ya yarda MUHAMMADU(SAW) manzon ne to wannan ya dandani
zakin imani "
Muslim ne ya rawaito shi``` .
Ta shigo kauyen cike da murna dede wata kwana ai kuwa wata motar yan kasuwa ta
shayo kwanar itama ai kuwa ta kwasheta ji kake ragajaf ta zube nan kasa wanwar ...
Ta kuwa bare baki iya karfinta ta saki wani runtamemen ihu sakamakon wani bala' in
zafi da taji a kafafunta ...tuni ta sume dan zafi ..kan kace mi a ka kwasheta akayi
likita baban gari dake kusa da su ..amma mi daga nan ma aka turasu babar likita ta
birnin Damagaram har lokacin da suka isa bata farfado ba..
Nan likitoci suka bata taimakon gaggawa .....sukayi mata allurar bacci dayake dare
yayi daman ..
Dreban daya

6 / 32