Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin Accident Complete Hausa Novel by FASMA

Author :  FASMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 32

39K to 42K   out of 94.8K words

nayi suka futo da zumar zata rakashi
aéroport se driver ya kawota school din ......
Suna mota se shagwaba take zuba mishi ya kasa fitowa a motar har aka fara kiran yan
tafiya...
Da kyar ya lallaba ya tafi...
Haka driver ya kawota school din Duk ranta ba dadi amma tana ganin su Mufee da
manta da wata damuwa suka shiga murnar ganin juna..kusan kwanan hira sukayi....
Allah sarki Murad shikam kusan kwanan ido biyu yayi besan haka ya shaku da yarinyar
nan se yanzu a ranshi yace gwanda na tafiyata wajen aiki ...da kyar dai bacci
barawo ya saceshi...
Maysam ma seda ta kwanta ya fado mata a rai se taji duk ba dadi.....
Washe gari suka shiga classr(aji)dayake ba'a wasa tun ranar suka fara daukan
lecture
Murad kam yana gama break ya kirayi Mahmud... Bayan sun dan taba hira yace yauwa
dama ina so kaje kamumun booking din ticket zuwa England .gobe nake son komawa...
Mi Mahmud zeyi inba dariya ya kuwa kwashe da ita yace kai amma fa baka da ta
ido ....ashe daman zaman taya matarka vacance ne kayi .kawai daga tafiyar ta jiya
se yau kace wai zaka wani tafi ..ya kara wata dariya..
Takaici yama habashi magana kawai se ya kashe wayar yana fadin dan sa ido
kawai.......
Awa guda Mahmud ya dauka ya kawo mishi ticket din yana mishi tsiya shide be kulashi
ba yayi fice warshi direct bangaren fulani yayi ....tana kishigide bayinta wasu na
mata fifita ,wasu na matsa mata kafa.....
Yana shigowa fulani ta sallamesu..zama yayi suka dan taba hira ..can ya sako zancen
tafiyarshi..
Shiru tayi na dan lokaci...can kuma setace Allah kaimu goben..amma dan Allah kada
kayi irin na wancen gamin nan tayi mishi nasiha....yayi tsammanin ko zata hana
ma...
Da dare ya sanarwa da Dadynshi ...shima fatan alheri yayi mishi tare da addu'oi...
Washegari yayi tafiyarshi cike da kewar su fulani more exceptionnel Maysam...
.
Maheeba kuwa se jin tafiyar Murad tayi ba karamin tashin hankali ta shiga ba ..nan
fa taga samu taga rashi...ta kuwa azawa Waziri rigimar se sun koma wurin Boka jin
miya jinkirta wannan abun...
Babu yanda ya iya haka suka shirya han se wajen Yankan wuka. ........
Tofa koya zata kaya kuma ?ku biyo ni dan jin cigaban.....
Fans nasan kuna yi min uzuri amman ku kara akan nada ..kwana biyun nan se a
hankali..need your prayer...
Love yo all
Fasma
Ahmed Gumel

Dedicated to all my fans
63__64
```Manzon Allah (SAW) ya ce''Duk wanda karshen zancen sa ya zama La'ilaha illalahu
ce lalle zai shiga aljanna''
Abu Dawuda ne ya rawaito shi.```
Babu yanda waziri ya iya haka suka shirya han se wajen boka yankan wuka....
Suna isa kafin ma su zauna boka ya kwashe da dariya ......bayan sun zauna yace base
kunyi bayani ba nasan mike tafe da ku to ina so ku sani mu muna aiki da hatsabibun
aljannai ne.......
Caraf Muheeba ta amshe da fadin to mi alakar jinkirta bukartar mu da aljanai
kuma...
Wata dariyar ya sakeyi se da ta tsorata yace to ai saboda a watan Ramadan an daure
su aman yanzu kam zasu iya yin komi(kuji wani jahilci kamar shi keda mulkin
duniyar....,Allah ya kara karemu daga halaka ameen) ..yace.ku koma gida kawai
kwanan nan zakuji bayani..nan suka shiga murna tare da godiya ...kudi suka sake
zube mishi wai a sayawa aljanai jini dan su kara jin kafin jikinsu.(hum Allah de ya
shirya .....kowa de yayi ta gari dan kansa koba haka ba my Arfat
...)
Nan suka dawo a karo na biyu zaman jiran asirinsu yaci..Muheeba kuwa har ta fara
training din yanda zata dinga tsala rashin mutunci in ta hau garakal mulki ........
Madina kam sosai ta saka ido dan ko yanzu yan leken asirin ta sun kawo mata labarin
waziri...ita kade tasan irin muguntar data shirya mishi lokaci2 Madina ke sakin
murmushi ita kade... ....
Wannan kenan
Murza kam a can qauye abun ba sauki se abunda ya karu tana yar cokala gurguwar
kafarnan ta zame ma yan garin annnamimiya se hada fadace2 tace ...Malam musa kam
yanzu har kunyar fita yake cikin jama'a ..gashi kuma ya kasa sakinta ..shide
addu'ar shi kullum Allah ya kara karesu shi da diyarshi Maysam daga sharri Murza
gashi kumata ci alwashin se ta raba auren Maysam ko ba dade ko ba jima ...
.
Satin Murad daya kacal ya ji duk garin ya ishe shi bashida wani buri daya huce ya
ga ,Maysam kai shi ko baze ganta ba to ya ji koda muryarta ne. ..tun isarshi da
kwana ukku zuciyarshi ta fara mishi zogi zut2 tun yana share abun har ya fara zama
sérieux.....
Ita kam tana can karatu suke ka'in da na'in itada kawayenta ba kama hannu
yaro.......
Yau kam tunda ya tashi ya shirya ya tafi office ya kasa yin komi gashide a office
din amma ya kasa duba koda patient daya ne ...gashi rythme din zuciyar ya rage gudu
ga wannan zut3 din ya dada da karuwa ba shiri ya daga waya ya danna number offishen
makarantar...
Suna tsaka da cours ya kira offishen wai yana son magana da Maysam ...
Basuyi kasa a guiwa ba suka kirata tunda sunga lumbar ta Englace ...
Tana zuwa tayi sallama a nutse tare da farin ina wuni Mom ,ya gida ,,kai amma nayi
missing dinku ba kadan ba ,,ni fa..
Katse ta yayi da fadin to sarkin surutu ya isa kaka nine ba momyn ki ba. Wai ke
inda aka kira bara ki tsaya kiji waye ne ba se ki hau zuba zance ne
...da Sauri tasa hannu a bakinta kamar yana ganinta tace yaya ''suis désolé (am
sorry) baran kara ba...se kuma tace Bonjour comment vas tu?(ykk) da fatan ka isa
lfy ...
Tun lokacin zuciyar ta dan rage zut3 din har wata Yar dariya yayi seda taji sautin
muryar ya ce lfy yar gidan Momyn ta da fatan kema hama ...
Ya cigaba da fadin dama na kirane naji ko kina karatu yanda ya kamata ...(jifa taku
irin nasu
...)
Dariya tayi tace inayi fa ...to yaya se yaushe zaka dawo har na fara missing
dinka....
Se kawai yaji zuciyan shi ya dawo normal har A ranshi yace ke yanzu ne kika fara ni
kam na...se kuma ya
Katse zancen zucin da fadin a fili really kinyi missing dina ......
Cike da jin dadi tace sosai ma pls wannan karon ka dawo da wuri...
Cike da wayo da dabara yace to ko zaki dayo nan ne da karatunn..
Waro ido tayi se kuma tace a'a nide na fison nan din ......
Shikenan comme tu veux(as your wish) ..ze sake wata magana tayi sautin cewa kai
yaya muna classe fa kasa ka kirawo gashi kasa nayi missing din karatuna...seda ga
baya im mutum be yi karatuba kazo kayi tayi wa mutum fada bayan har da kai cikin
masu hana mutum karatun...tana wani turo baki kamar shantu ...lol...
Budar bakin shi se cewa yayi sede in dama mutum bashida niyyar karatun to inba haka
ba yan mintuna ne zasu sa mutum kasa yin karatu.....''peu importe(any way) se
anjima sanna ki meda hankalin ki akan karatu in kinyi ta daya ni kade na san
kyautar da zan miki...
Wata dariya tayi har seda yaji sautin ta a take zuciyar yaji tayi wasai babu wannan
nauyi2 daya keji bare zut3 tace Allah yayana da gaske ta fada cikin zazzakar voice
dinta..
Seda ya lumshe ido , ya bude su yace sosai yar gidan Momy kede kawai ki dage da
karatu......
Shikenan yaya sena baka mamaki in sha Allah ...
Nan sukayi sallama kamar karya kashe yake ji amman dole ne yasa ya kashen ...
Dama yana office dinshi ne ga aiki baje gaban shi ya kasayi tun safe baya jin
kwarin jikin shi se yanzu daya ji muryar Maysam amma fa zuciyar shi ta raya mishi
da dan kawai sunyi sabo ne har ya dan damu da ita..(oho de )
Tafiya tayi tafiya yau har wata biyu cur da zuwan su Maheeba wajen boka ......ita
kam duk tabi tawani tada hankalinta Mahaifiyar ta kullum na rarrashin ta.....
Yaude kama almara da dare MaiMartaba Sarki da matanshin wato Fulani da Madina suna
zaune a bangaren shi ..yayi gyaran murya ...tare da fadin ina son yi wata shawara
ne....
Su duka suka nutsu ya ce mi ze hana ma hada aure tsakanin Yarima Murad da Muheeba
diyar waziri..
Caraf Momy tace ee fa nima na so yi muka wannan maganar amman tunda yanzu kai kayi
ni kam na amince ...
Wani uban tsalle da Madina tayi se gata a tsaye cuwa su kan su seda suka tsorata
tace wannan ai bama maganar daza a daga aji ce tun wuri ku sake tunani..
Tsawa sarki ya daka mata tare da fadin wannan na rigaya dana yanke shawara ko kiso
ko kar kisio wannan ya rage naki..
Fuuu ta fice ta barsu nan ita kade se huci take tace ni Waziri zeyi wa haka ?ni
zeci wa amana ?tab ....zamu gani ti
Washe gare
a fada ,,kama daga waziri sarkin fada ,sarkin dogarai..etc.duk sun hallara
Sarki yace da waziri jiya mun tatauna bisa kan diyar ka Muheeba..
Da sauri ya rusuna tare da fadin Allah ya huci zuciyar Allah de yasa ba wani laifin
tayi ba..
Ko daya se ma alheri ina de fan
Mi ze hana mu kara qarfafa dangartarmu ne na mu hada y'ay'a mu aure wato Yarima
Murad da yar wajrn ka inde ha ba'yi mata miji ba...
Waziri kamar ya mutu dan dadi yace to ai ko anyi mata za'a iya tadashi barema kam
ba 'amata ba..
Aa'a babu kyau nema aure cikin aure..shekenan tunda batada se a hada ai..
Da sauri waziri yace wani hanzari ba gudu ba shi Murad din yana da sha'awar karin
auren ne(wai tirjin da boka yace yayi ne..)
Sarki yace to ai base yana ra'ayi ba ..kuma dole ne ya yarda da auen..
Kowade na cikin Fada se mamakin wannan al'amarin yake..nan akayi addu'a aka rufe
taron..
Muje zufa fans
Fasma ce
Ahmed Gumel
[9/2, 10:04 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 10:07 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

65__66

_Godiya me tarin yawa zuwa ga Fans din Sanadin Accident ..hakika ina jin dadin_
yanda _kuke bibiyar_ book din _Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa__ ... ..
*Da yawa daga ciki naga sakon nin na shawarwarin ku . .. *in sha Allah* *Zan
gyara .ku sha kuri minku kawai kude ku ci gaba da kasan cewa dani* *Fasma....kuna
da yawa Fans bazan iya zano ku ba amma ai* *kusan ina yin ku irin totaly din nan *
*MAMAN SS sakonki ya isa ga Maysam tace tana yinki* **irin sosai din nan
lol ...Amma fa Maheeba* *tace a gaya miki ta shirya tawagan yakin ta* ...
*Nide ...ido ne nawa... ..na gode da kulawarki* *kwarai Allah ya bar zumunci* ..
*_Ohh My Zarbaby tu me manque déjà ..wish you a good journey na gode da kaunarki
Rabbi ya bar zumunci* .... .
_
Dedicated to My ZARBABY
65__66
```Manzon Allah (SAW) ya ce''yana daga kyawun musulucin mutum ya bar duk wani abun
da be shafe shi ba ''
Tirmizi ya rawaito shi.```
Waziri ya sake cewa ai baza ayi haka ba abari ayi da yardar shi..
hannu sarki
ya d'aga mishi ya ce na gama yanke magana ku fara shirye shirye kaway nan da wata
d'aya daidai da congé Noël(chrismaty ) kenan ..
nan waziri ya shiga godiya tare da mikewa ya fuce da shoki ya isa gida koda ya
sanar wa da Muheeba wani wawan ihu ta kwasa har say da biron da nike rubutu ya
subuce mini ya fad'i nan fa suka wuni cikin murna Muhiba kam harda fara yanda
zatayi yafiya da kasaita take da wulakancin da zata ma mutane
Shirye shirye kam ya kan kam yau har saura ''deux semaines''(sati 2) inda ango da
Maysam basu ma san waynar da ake toyawa ba kay dama gari duka dan ko carte ba a
bugu ba yan gidan su Muhiba da sarki kaday suke shirin su inda ita Muhiba har mai
gayran jiki ta dauko dan a cewarta ta fi so ta fito yass da ita wai ita a nufinta
tana so ta fi mai kama da aljanun nan kyau ni ko nace maysam ko batayi ado ba ta fi
ki kyau ko ba ha ba fan???
Ana haka ne Sarki ya kirayi Murad bayan ya gaishe shi Se Sarki ya sako zancen auren
shi da Muheeba yanda kasan wata saukar guduma haka yaji a kanshi a take ya dafe
setin zuciyar yanainnalillahi..hi .......Sarki ya ci gaba da cewa kuma ina so satin
me kamawa na ganka garin nan ...
Da kyar ya iya hada kalmomin shima da kyar ya fara fadin pls Dady kar...
Da sauri sarki ya katse tare da fadin inde har na isa da kai to ina so kayi mun
biyaya.....
Allah ya zaba muna abunda yafi alheri shikade Murad ya iya fadi.....
Sarki na yanke kiran Murad ya yanke jiki ya fadi a sume.....
Shigowar Mark kenan dan yayi ta kiranshi a waya baya dauka gashi yana son ansar
wani doc me mahimaci shi ya sama ya tako ya zo gidan.....
A sume sheme2 ya ganshi nan fa hankalin shi ya tashi bayan ya kirayi ambulance se
kuma ya fara bashi ''premiers soins(first aid)....
Da kyar ya samu ya farfado ambulance na zuwa aka fice da shi emergency..
kwanan shi daya yana jinya Allah ya tashi kafadarshi...tun agadon ya kirayi
fulani .....tana dauka ya kuwa fashe mata da kuka kamar ba yarima Murad...
Nan da nan jikin fulani yayi sanyi tasan abunda yake yiwa kuka nan ta lallasheshi
tare da mishi nasiha kan yiwa iyaye biyyaya .....
Nan Murad ya ji zuciyar a kashi 100 ,,kashi 40 na damuwar dayake cikin sun
ragu ......
Ita kam fulani bata san mi ya sa ma take goyon bayan auren nan ....barema yanzu
dataji har kwanciya yayi a asibiti dan tasaan irin yanayin ciwon shi in ya tashi
har fidda tsammanin shi ake ...gashi ita bakin ta yayi mata nauyi sosai baza ta iya
cewa bata son ayi auren nan .........
Murad yace Momy Maysam fa??
Dan shiru tayi na yan dakika se kuma tace itama ba'asanar mata ba......dan bansan
yanda zata dauki lamarin ba ...ina son yarinyar har cikin JININ JIKI NA na ke jinta
dan bazan so taji wannan zancen daga bakina ba amma dayake kai mijinta ne se ka
lallabe ta ka gaya mata...
Momy kawai a barta base an sanar mata ba dan ni kai na baza....se kuma yayi shiru..
Nan sukayi sallama...
Haka momy ta shiga saka da warwara ta rasa ya zatayi da Maysam....
Hakade ta daure ta kira offishen bayan an bawa maysam wayar ,nan fa maysam ta shiga
zuba taji Momy se surutu take mata...can de ta tsageta tace Momy lfy najiki shiru
yau ..,...?
Fulani daurewa tayi ta sanawar da Maysam komi bayan tayi mata nasiha me ratsa
zuciya ....
Tunda Momy ta fara magana taji wani abu ya tokare mata wuya ,....da kyar ta tara
nutsata ta nunawa fulani ba komai ai kuwa fulani na kashe wayar ta fara ganin
dishi2 nan ta sulale itama kasa a sume....nan da nan akayi emergency na nan clinik
din makarantar aka shiga bata temakon gagawa ....
Murad kam suna gama waya da fulani ya dannawa Mahmud kira ..yana dauka ko gaisawa
basuyi ba Murad ya fara magana cikin huchi yace wly kada ka sake ka bugo min katin
auren nan kai kar ma ka fadawa kowa .....dan ni bani da tsarin auren mata biyu amma
tunda su Dady sun rantse se sun min auren dole shikenan amman pls''je t'en
supplie'' kada kayi komi ka barsu kawai in ya tambaya kace ee kayi ..haba da girma
na da wayo na ace za'ayi mun auren dole har so biyu....
Ganin yana famar sauka daga kan layi yasa Mahmud taro shi da nasiha ...nan sukayi
sallama tare da alkawarin baze yi shirye2n komi har se yazo...
Suna gamawa ya danna wa offishen makaranta su Maysam kira amma mi se aka sanar
dashi ai batada lafya ...dafe da zuciya yake tambayan mi ya sameta...
Sukace ai tana emergency room basu fito da ita ba....
Nan fa ya lallaba batare da sanin Mark ba ya shige office din shi dayake a likitar
daya ke aiki ake mishi traitement .....
Takardar neman hutu ya rubuta tare da cike kaf wani file dayansa za'a bukata bayan
bayan nan.....direct da kanshi ya kai office din babba su ...dayake sun san yana da
matsalar zuciya kuma abunda yake da bukata kawai gida ...ba tare da bata lokaci ba
yayi mishi signé ya bashi dan su can suna tattala da taka tsan2 kan rayukan yan
adam .kun de sani base na bata lokaci ba ...ko ba haka ba my Momyn Hajia ...
Direct aéroport ya fice amma cikin rashi sa'a be samu flight me tashi yau ba....shi
so yayi ma ya dauki hayar jirgin gaba daya inde zasu kaishi se su ka nuna mishi ai
abun ba daga nan take ba .....hanyar ce ke cike ga iska me karfi ...ga
gajimarai .....Dole yayi hakuri ya dawo zuciyar shi kam banda lugundan zut3 babu
abunda take moshi...kira kuwa yayi yafi a kirga amma maganar dayace tana
emerjency..fada da masifa kam malaman makarantan sun shashi duk da sun sanar mishi
yaune kawai amma se bala'i yake zuba a duk kiran da yayi..musu..
Kai bama su ba hatta Mahmud seda yasa shi zuwan Maradi babu shiri dan a yanda yake
mishi magiyar yaje ya gani mi ya sameta ...har seda shi kanshi Mahmud din yaji
tausayin shi.......
Be tsaya nan ba nan ya kira fulani ya daga mata hankali ita ma ..ta kirayi
makarantar suka jaddada mata ..direct ta nemi izini wajen mijinta sarki dare da
fada mishi lalin da ake ciki...beyi wani gaddama ba ya sa aka shirya musu jirgi
itada Mahmud daya zo sanar mata da ciwon Maysam din tare tafiyar Maradi .....abu
nasu kan kace mi 10min har gasu a Maradi ..direct motocin dasukazo daukan su Clinik
din makarantar suka fice...
Har lokacin babu wani good news ...
A bangaren Murad kuwa se hawaye yaji ya fara zarya a idon shi(haba kada ka bada
maza man ....eh man )nan ya shiga tunani kada fa ya je ya rasata l
Kamar yanda ya rasa SWEETBABYN shi...yana nan har aka kira magarib babu new ..
Se bayan sallar isha'i daya sake gwada kira ya koyi sa'a ya na kira Mahmud yana
dauka ya bawa Maysam dan ta farfado za a kaita dakin futu..........
Cike da zakuwa yace Mahmud how is she now..,?
Muryar kawa taji se jin wani sanyi ya ratsa zuciyarta ita kanta tayi mamaki
hakan ..tace yayana am fine now ..
A tare suka sauke Wata sanyyayar da lallausar ajiyar zuciya ..kuma se suka saki yar
dariya lokaci guda ...yace wai miya sameki ne..
Shiru tayi ..se can tace nima de ban sani ba kawai de s....
Momy ta karbe wayar tare da fadin haba Son ''elle as besoin de se reposer ...so ka
bari in ta huta se kuyi maganar ...marerecewa yayi kamar tana ganin shi ya fara
zubo mata shagwaba....ganin yana son rinja yarta yasa ya kashe wayar...
Itama oganiyar bata so fulani ta katse su ba ........
Washe gari kam asubanci yayi ..karfe tare jirgin su ya keta hazo...
Safe a good journey Murad..
Love you all..

Dedicated to all my fans
67__68
```Manzon Allah(SAW) yace''lallai Allah ta'ala ya haramta wa wuta cin naman wanda
yake fadin

14 / 32