Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin Accident Complete Hausa Novel by FASMA

Author :  FASMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 32

21K to 24K   out of 94.8K words

ruwan sanyi a fuskarta
firgit ta bude ido kamar zatayi kuka amma ganin dodonta ne seta sadda kanta kasa..
Suna isa makarantar dayake abun na sune nan aka cicika komi ya zuba kudin shekarun
shidda dazatayi wato secondary
da kudin furniture dana uniform duka komi ya biya
Har dakinta kuyangi sukakai mata kayanta ......daza su tafi da kyar suka rabu da
kuyangin...barema da jakadiya rumgume ta tayi se rusa kuka take...
Lallashin ta tayi tace kiyi hakuri naso zama nan kai hatta fulani taso a baki koda
kuyanga dayane amma yarima yace aa a barki ai school kikazo ba hutu ba .shiyasa
nakeso kidage kiyi karatunki banda wasa..kada kiyi kuka kijawa kanki ciwon kai dama
gana safe dakikayi wajen rabuwa da fulani...
Share hawayenta tayi tace shikenan zan baku mamaki in sha Allah ..
Yarima murad seda ya biya gidansu Mahmud ya gaisar da iyayenshi sannan suka kama
hanyar komawa
A bangaren su waziri kuwa samako yayi ya nufi wurin boka amma har yamma be samu
wajen ba ya gaji likis dole ya hakura ya dawo gida
Ya labartawa Madina komi wani bacin rai taji tace mu bari har murza taji dan sauki
se muje ta nuna muna amma kada ya fice satin nan dan asabar din nan ze koma England
nan da 6 jours kenan......
Kuma wani babban bakin ciki yau yayi tafiya shida kucakar matarshi abunda ya kullar
dani ma shine da kanshi ya jasu ashe dana sani da munyi anfani da wanna damar mu
qara cire musu burki..
bansan da tafiyar ba seda zasu tafi shima a bakin jakadiyata naji koda na fito tuni
har sun bar cikin fadar ..takaici kamar na mutu...
Waziri ya jinjina kai yace ba komi zamuyi nasara nan gaba..
Love all fans
[8/17, 1:57 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[8/17, 2:00 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

39__40
Cen karkashi makoshinta ta furta Bonsoir(g.eveni
ng) yaya
shima can kasa2n ya amsa da bonsoir ,daga haka babu Wanda ya sakeyin magana se
Haider da matarshi da suke ta tsokanar su ,,koda suka iso suka firfito suka kama
hanyar shiga hall d'in Wanda cike yake da mutane da Sauri Haider ya matso ya mishi
rad'a akunne dayake a bayan su suke se yajuyo ya buga mishi harara daga bisani kuma
yaja tsuka ,ya juwo ya sakalo hannuchi cikin na Manane da Sauri ta kalle shi zata
yi magana amman se taga fuskar nan a murke dan haka tawha jinni jikinta ta kyale
ita se asannan ma ta lura da couleur (color)d'in kayansu iri d'aya ne sede shi
shadda farace tasha aikin hannu se meko take,ya kafa fula ja da kuma takalmi ja
shima ,a ranta tace ashe ya Rid beyda laifi dan kayan nan sun haskashi(hum Manane
duba da kyau de dan ba kayan bane suka fiddo shi cqn daman shi me kyaune),,
Shima cikin ranshi fad'i Yake ashe yarinyar nan tanada Kyau Masha Allah se de
karancin shekarun ta(hum kwade ji da gulmar ku),tun shigowasu DJ ya saki
kid'a ,bayan sun zauna ,Safara ta matso tace wow wai kun ganku kuwa ?gaskiya
shigarnan tayi muku kyau ,dan wannan ''idée'' d'in ya Adam ce,,
Sambaby ta matso itama tana fad'in ashe da gaskiyar mutane da suke fad'in kuna kama
sosai nima se yau na k'ara gaskatawa,
habawa eh..kuwa Manane se tafara turo baki cike da shagwab'a wanda ta zame mata
jiki take fad'in haba sambaby ina kama anan ni wly na fishi kyau..
shiko tsayawa yayi yana kallonta....
bayan jawabe2 DJ ya buk'aci ce su dasu tashi su nan taka rawa,
suka fito tsakar hall d'in suduka de a tsaye suke se d'an d'aga kafa dasuke,yen uwa
da abokan arzuki se kari suke musu ,cqn Sega A.Razak ma yazo yana musu kari yana
kuma musu fatan alkhairi tare da fatan samun zaman lfy
,ita ko tunda ya iso take murmushi ,ganni haka yasa Rid bata fuska ,se kawai ya
jata suka koma wurin zamansu har aka tashi amman fuskar nan tumau(umm Doc Rid
manya)..
Dayake dagan nan za'a huce da ita gidan ta dan haka bayan antashi daga patyn Motar
su Momy aka sakata ,a hanya suka k'ara yimata nasiha ,itakam banda kuka ba abunda
take
,da suka iso cikin gidan suka sata fitowa da kafar dama ,tare dayin addu'a ,haka
suka Sakata har d'akinta Sannan suka barota tanata kuka,su Sambaby ma tafiyar su
sukayi dan har 23h ta fice,..
Shima be shigo ba se wajejan 23h40,koda ya shigo gidan ko takanta bebi ba ya shige
d'akin shi ,bayan yayi wanka ya d'auro alwala yayi sallolin shi.ya sanya kayan
baccishi.har ze kwanta se kuma ya ga rashin dacewar hakan danko bâ komi k'anwarsa
ce gâta kuma yarinya..dan haka se ya fito ya nufi d'akin nata''',a sa grande
surprise'(to his surprise) tana kuka har lokacin ya girgiza kai ya iso kusa da ita
yace Manane, tad'ago ta kalleshi ,yace kukan mikikeyi ne haka?
tace babu komi,
ya kuma cewa 'as tu faim?,' (kina jin yunwa? )ne ,
tace a'a ,OK to jeki kwanta kibar kukan nan haka dan kada yasa miki ciwon kai,tace
to
yatashi yana fad'in bonne nuit (good night),yana fita ta tashi tayi wakan tayi
alwala bayan ta ida Sallah ta hau gado ta kwanta ,nanda nan bacci ya sureta,...,,,
Asuba alheri Manane...
Kiran sallar farko ta bud'e idonta..ta shiga toilette ta d'auro alwala tayi
nafilfili ta zauna tana azkar bayan anyi asaltu ta gabatar da raka'atanul
fajar,bayan anyi Kiran sallah ,tayi sallah asuba sannan ta Budé Alkur'ani me Girma
ta fara karantawa..
koda ya dawo daga masallaci d'akin ta ya nufa dan tayar da ita amman tun a kofar
yaji sautin muryarta tana karatu .nan ya shagala da sauraranta dan karatun cike da
nutsuwa da tajwidi take yin shi tare daba kowani harafi hak'inshi ,,se wajejan 6h30
ta rufe takoma gado dan wani bacci me nauyi ne a idonta...
Bugon kofar palon,da akeyi ne ya farkar da' ita koda ta bude Yesmine da Mushana ne
da kalolin abinci sukace inji Mom.ta amsa tace kushigo ku zauna bari na shiga nayi
wanka,
hayaniya da karan TV ne ya tasheshi daga baccin yayi tsaki ya tashi ya shiga wanka,
da ya fito yayi yan shafe 2 shi ya saka wata shadda ‹'cendre'' (ruwan toka) y'a
fito ya isko su Yesmine a palon suka gaishe shi ya amsa.
Ya hanhanga yaga bata palon se ya shiga dakin nata, karan ruwa yaji a toilette din
tabbacin tana wanka kenan, se ya aje wani abu abisa gadan ya fita,
koda ta shirya ciki wata atampa rose(pink) ta futo suka yi break bayan ta gaisheshi
ya amsa ,
Daya kare se ya futa dan akwai abokanen su na américa,kuma yau zasu koma ,dan baka
yatafi yi musu godiya da kuma salama,, da fitarshi ba jimawa Safara ta shigo suka
gaisa tace Manane Rid be baki wata kyauta yanzu ba ?
Kyauta kuma !?? Tami ?
Tace tashi mu shiga ciki suna shiga ta sake tambayar kyautar miye wai ?
Ita Safara se daga filo take tana fadin ai aladar kasar wanan ce, washe garin aure
ango yayiwa amariya kyauta idan har ta fita kumya.....
Aranta tace yoni da ba abunda ya shiga tsakanin mu dashi wata kyauta zeban..?
Bata gama tunani ba Safara tace amishi nan ga taki kyautar, na bude? kode amshi ki
bude da kanki,..
hannu na rawa ta amsa koda ta bude clé (key) ya fado na mota, ta mikawa Safara tace
laaa key d'in mota ne gashi.
Safara ta washe baki ta na dariya tare da fatan alheri har bata san tayi subul da
baka ba tace kai gaskiya Manane yayan nan naki na sonki da yawa.
Ita de kallonta kawai take, safara ta futa da clé don nuna wa sauran *Zuri'ar* (hum
koya akayi ya mata kyautar mota ? nasan de be huce shawarar Haidar ce .) haka ta
wuni bak'i nata shigowa,,kuma kowa yayabaa kyautar daya yi mata,se fatan Alkhairi
ake musu.
Haka suka cinye sati guda kullum da bak'in dasuke zuwa gidan dan haka Manane a yen
kwanakin duk manyan kaya take sakawa ,,tun bayan satin kuwa ta rage sasu ta koma sa
english wears d'inta dan daman a takure take
,Doc Rid kuwa kusan kulum cikin yima fad'a yake amman in ya shiga ta wannan kunne
se ya fita ta d'ayan ,harde ya gaji ya dena kulata..dukda dama ba wani Abu ke shiga
tsakanin su inba gaisuwa ba..
Hake de suke ta zaman doya da manja a gidan daga gaisuwa ba abunda ke hada su seko
insu hadu a dinning, dan har yanzu daga gidan Mom ake kamusu abinci yau sati 3
kenan.
Yau ma kamar kulum daya fito donyi break, be ganta ba, har ya gama beji ko motsinta
ba, har ze futa seyaga ya dace ya leka ta ko lafiya ?
Tunda ba haka ta saba yiba, dan kusan kullum kamshin turaren wuta ke tadashi ,amman
yau palon ma be samu shara ba bare ayi zancen turaren wuta....shigarshi d'akin keda
wuya ya ganta a kwance a kasa hannuta rike a ciki se murkususu take ga kuma hawayen
dake zarya a fuskarta, da sauri ya iso yace Manane miya sameki ?
Dakyar take iya yin magana tace periode ne, yace ina maganin ki yake ne ?
Da kyar tace na barshi gidan Mom, yayi tsaki ya daurata bisa gado ya fita, ya shiga
dakinchi, koda ya duba cikin trouser din maganan nuwanshi babu maganin nata don
haka ya hada allura ya dauki tea me kauri a cup ya shigo dakin nata, kukan nata har
ya fara futowa yace tashi kamar bata jishiba dan batada karfi juyawa dan haka da
kanshi ya jingina ta ya bata tea d'in sannan ya juyata ya mata allura. Nan danan
bacci yayi awan gaba da ita, ya rufa mata bargo ya fice.
Koda ya fita gidan Umma ya shiga, bayan ya gaishe ta yace ina Yesmine ne ? Tana
daki, to daman dan taje ta taya Manane zama ne dan bata jin dadi... Wayoo ,yanzu ya
jikin nata?da sauki alhadulillah..Ok Allah yabata lafiya. Amin ya fita. Yana fad'in
na tafi Umma dan inada cours(lecture) yanzu ya fita sauri2(Cours kuma ?to kara tu
ya koma? komi?
Koda ya dawo daga aiki ya iskota a palon ya tambaye ta ya jiki ,,cike da jin kumya
tace naji sauki,to Allah ya kara baki lfy,tace ameen..
Ciwon be saké tashi ba se bayan sun dawo saga gidan Elh Fayçal daga cin abincin
dare..dawo warsu da kamar Awa ya saké tashi tun kan yayi tsanani ya ha'da allura
danyi mata,amman se ta fara mishi kuka da magiyar kan ya bata magani a memakon
allura,,
Hakade Seda sukayi 3jours yana jinyarta tukon ta warware(gaskiya kina bani tausayi
Manane)...
Muje zuwa...
Fasma&Aïcha
[8/17, 2:00 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[8/17, 2:02 PM] A A Dboy: ```Manzon Allah (SAW) ya ce "Duk wanda yake so a bashi
tsawon rai,a kara masa yalwar arziki,to yabi iyayensa kuma ya sadar da zumuntarsa "
Imamu Ahmad ne ya rawaito shi.```
Waziri ya jinjina kai yace ba komi zamuyi nasara nan gaba.....
Madina tace Allah ya kasan yaron ne taurin rai ne dashi
(Hum to lokacin mutum beyi ba taya ze mutu inba jahilci ba irin naki hum)
Maysam kam koda akayi mata interview se suka sakata a js2 a memakon js1 dayake
Allah yayi ta brain ..basuba ni kaina taban mamaki amma wannan kadan ne daga ciki
baiwar da Allah yake bawa tsirakun mutane...
Dakin da aka kaita gado ukku ne a ranta tace kenan mu ukku ne a dakin nan kodan
kayan dataga kusa da gadajen ya tambbatar mata da hakan...
Nan ta zaune ta rafka tagumi tana tunanin rayuwarta .....tace ko yanzu Abbana
miyake??ko yaci abinci??ko ya tafi kasuwa ...i miss you Abbana.....
Se kuma tace Allah sarki inna Murza ko ya jikinta yanzu ???
Sekuma ta tsallako tunanin Fulani ai kuwa nan shar3 hawaye ya fara zarya a kumatun
ta tace har na fara kewarki Momyna hakika kin cancaci yabo baki sanin ba amma kika
sani a jikin ki har kika auran danki kwaya tal ..kin nunamin so, kauna inasonki
sosai fulani Allah meyin yanda ya so *Sanadin Accident* na samu Momy na fita daga
kangin wuyar Murza ....Allah ya saka miki da alheri...tana haka se kuma tunanin
yarima Murad ya fado mata tace shin ko ya isa gida yanzu? ??ko ya ci abinci??ko
miyake yanzu se kuma ta saki murmushi wanda ni kaina bansan ma anarshi ba .....se
kuma naga ta tsuke fuska tace mi nawa nayin tunanin shi mtss banda mugunta da keta
mi ya iya da wata fuskarshi me kyau ......yana wata tafiyar shi ta takama kodayake
yarima ne dole yayi .........haka ta lalace tana ta tunanin ta data tuno wannan se
ta tuno wacan..
Dafa tan da akayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunani .....
Firgit ta juyo taga waye...
Wasu yan mata biyu ne baza su fuce sa aninta ba ..
Wanda ta dafa ta ta sakar mata murmushi tace ya haka kedaya kuma kina tunani
Itade da ido ta bisu
Tace ""je suis Mariam Moctar ...
D'ayar ma tace nikuma Mufeedah Muhammad ......kefa? ?? Suka fadi a tare jin bata ce
musu kala ba
Tace nikuma Maysam Musa by name..
Wani aji kike cewar Mufeedah ...
Js2 ta fada a takaice...
Waro ido sukayi a tare sukace ashe ma ajin mu daya ....sekuma suka shiga murna
Nan sukayi dan sabo har suka qara gaya mata sharrudan makarantar da yanda suke
gudanar da karatun daga takwas na safe zuwa daya na rana school ne daga ukku zuwa
shida na yamma islamiyya ne.....
Haka kuwa akayi ukku nayi suka saka uniform na islamiyya suka fuce harda Maysam din
dayake kama daga furniture, uniform duka a school din ake baka....
A bangaren oga kuwa bayan ya koma gida gaba daya ya tsinci kanshi cikin
kunci ..besan ya akayi ba amma kwata2 a ranar be runtsa bacci ba ya na rufe idanu
se kawai yaga fuskar Maysam ..shi kade se juyi yake yana tuna scene dinsu na
jiya ..yaja tsaki yafi cikin kwando ..ranar kam se barawan bacci ne ya saceshi
abunda ya jima beyi ba kenan tunanin wani abu ya hanashi bacci shiyasa tsanar
Maysam ta dada ruruwa a zuciyar shi...
A bangaren Fulani ma se taga yau gidan yayi mata fadi da babu Maysam dukda basu
wani jima tare ba kuma ga kuyangi dasu na debe mata kewa amma Maysam ta daban ce a
wajenta..
Washe gari kam sukuku Murad ya tashi har seda Fulani ta tambayeshi ko lfynshi amma
se ya fake da kanshi yake mishi dan ciwo..(hohho su Murad manya)
Maysam kam cike da zumudi ta tashi tun wuri tayi shirin ta na school uniform din ba
karamar karbarta yayiba rigace har guiwa da wando har kasa ruwan toka se dan baby
hidjab fari tas ..nan ta fara bubude kayayakinta ..dan ta samu ta karya ..ita kanta
ta yaba da sayayyar da Murad yayi mata dan kanyan sunyi yawa ma a cewarta .....can
ta hango katan abu ta janyo shi taga an rubuta Pad sanitary .....ta dinga jujuyashi
a ranta tace komiye wannan kuma oho ..haka ta mishi wuri ta aje sanna ta jere
kayanta tsaf cikin wardrobe dayake ba wani girma ne dashi ba dan kahaka sauran
kayan ta bardu nan cikin bags...
Haka suka nufi aji su ukku bayan an tashi lokacin islamiyya nayi suka tafi tare
kafin dare Maysam ta gaji likiis mi su Mariam zayi inba dariya Mufeedah tace zaki
saba muma da farko haka mukaji...
Bayan kwana biyu Maysam karatu ya fara zafi karatu take ainun basuda time idan ka
gansu suna fira to lokacin baccine amman a yinin rana in basa aji to suna
blibliotheque (library) ko kuma suna exercise itada su Mufeedah ...takan tuna
Abbata da Fulani lokaci zuwa lokaci dan yanxu batada ma times din tunanin
Yarima kuwa besan ganin dayake mata yana mata mugunta kad'e ma wata rahamace a
zuciyarshi tun bayan tafiyar Maysam ciwon zuciyarshi yake famar tashi ..dole ya
fara shirin koma wa England dan ganin doc dinshi a cewarshi gwara ya tafi tun kafin
abun yayi nisa..hum
Ai kuwa su Madina najin tafiyar Murad ta tashi haka aka d'auki Murza da kafar
karyaya aka nufi wurin boka da ita dad'insu d'aya Malan Musa ya tafi kauyensu
d'auko musu wasu yan abubuwa se kawai sukayi anfani da damar suka kad'a han sewajen
Boka yankan wuka ...
To fa fans
Kuyi hakuri da wannan ina sonku fans
[8/17, 2:02 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[8/31, 9:55 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

Dedicated to all my fans❤

41--42

```Manzon Allah (SAW) ya ce "
Zaka sami mafi lalacewar mutane a ranar kiyama mutum mai fuska biyu, wato wanda
yake zuwa wajen wadannan da fuska, kuma ya zowa wadannan da wata fuskar "
Muslim ne ya rawaito shi.
```

Zaune suke Murza da Waziri gaban boka yanka wuka bayan sun zayyana mishi irin
rashin sa ar da sukayi sannan suka bukaci da a sake basu wani wanda ya fi wanca
dan waziri seda ya nemi a salwantar mishi da rayuwar Murad da Matar shi Maysam ..

Boka ya sake jaddada musu rashin yuyuwar hakan tukon suka amshi irin na farkon ...

Waziri yace in san samu ne kai koda yana kasar to ya qauracewa garin nan de har
lokcin da time dim mutuwar shi yazo se kawai mu salwantar da ran nashi...

Bokan ya basu maganin amma da sharadin insuka sake maganin nan me kamashi ba baze
sake basu wani irinshi ba tunda sakakin su yayi yawa ..kuma ma ko.wancan lokacin da
kyar suka samu ran da sukayi sacrifice dashi kuma ga wani ran mutum biyu yanzu da
aljanin da ze muku aiiki zai asha ......

Waziri har wani shoki yake kwasa jin za amusu aikin da yarima ze bar
masarautar ..makkudan kudi suka zube mishi
shikuma la' anannan Allah ya basu maganin tare dayi mudu bayani kamar na wancan
lokacin ....

Cike da nishadi suka dawo gida inda aka dawo da Murza likita.

Ta kalli waziri tace wani hanzari ba gudu idan shi yarima Murad ya bar kasar ya
za'ayi da iya maysam din dan ganin tabar masarautar nan??

Wata dariya waziri yayi yace yo inba abinki ba ai da zarar ya tafi ya jima to ina
kyautata zaton dole a raba auren tunda ba miji kinga seta kuma wurinki ko??
Ee fa hakane kai amma naji dadi haka sukayi ta saka warwarsu

.Allah yasota dan har lokacin Musa be dawoba..

🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹

'

Murad kam abun duniya sun taru sunyi mishi yawa besan haka zuciyarshi take son
ganin yarinyarnan ba da be turata makarantar nan ba gashi yanzu lokaci ya kure
mishi ....dan haka se ya samu Mahmud da zancan amma ya boye mishi cewa rashin
Maysam ne kawai ya fadimishi yana son komawa dan ciwanshi yana famar tashi

sosai Mahmud ya tausaya wa abokin nashi yace amma ya akayi hakan ta faru bayan ka
jima bakayi shiba har muna tammahanin ka rabu dashi??

Girgiza kai Murad yayi yace nikai na bansan ya akayi ba

Kode yana da nasaba da aurenka Mahmud ya sake jefo

8 / 32