Author : FASMA Category : African Stories & Novels
hadin
boss kasa2 yake mata maganar aman ba karamar kunya ya bata ba dan se gani take
kamar fulami na jinsu ..dan haka seta saci kalon fulani se taga hankalin ta baya ma
kansu dan haka cikin sauri sum2 ta fice ..shima Murad ya mara mata. Baya..harda yar
rawarshi
Duk abunda suke fulani na lure dasu kuma taji dadin hadin kan da suka samu tare da
kaunar junan su ..nan ta kara yi musu addu'ar Allah ya qara basu zaman lafiya da
zuri'a dayyiba...
Suna kuwa zuwa ta aza mishi rigima dole ya hada mata dama ya taho mata da garin tun
can...tare suka yi wanka ..sede tun kafin su kwanta aka fara kiran sallar dole yayi
alwala ya fito masallaci itama tayi tata nan gida tukon suka bi lafiyar gadon....
Haka suke kullum a tare makale da juna ko a gaban fulani be hana wa ya nuna mata
soyyaya itade ji take kamar kasa ta tsage ta shige dan kumya shi kuwa ko a kwalar
rigarshi ..
Fulani ma kam se de ta kau da kanta daga wata rashin kumyar tashi .....
Bayan sati da dawowar su suna palon bangaren su ..Mysam dake zaune a cinyarshi
tana zuba mishi kukan shagwaban da bashi da dalili ...can ya kalleta yace to ki
nutsu muyi wata magana..
Tsayar da kukan tayi ta tattaro hankalinta gaba daya wajenshi..
Gyaran murya yayi yace ya zancen zoben ki ne naji ki shiru ne...
Dafe goshi tayi tace laaa Muradina ai na manta da shi aman bari naje na dubo shi
dan yana dakina dake bangaren Momy...
Murad yace mutafi to na raka..ki
A tare suka shiga dakin ..aman sukayi ma zoben neman duniya basu samu ba...ita kam
har ta gaji dan neme2 da tayi..
Kamota yayi ya zaunar yace ta bari shi ya ci gaba danema ..aman de kin tambbata
anan dakin yake ..
Tana meda numpashi tace ee to ina de kyautata zaton anan din yake sede bana tune
inda na saka shi ne
Ci gaba yayi da ne ma aman shiru...
Can sega fulani ta fado dakin jin sukurniya a dakin ..turus tayi ganin Murad da
kanshi ke neme2..
Tace son lafya kuwa...
Jiki a sanyaye yace Momy zoben wife muke nema ne..
To amemakon ka saka kuyangi suyi se kai da kanka ..
Momy baza ki gane ba ..zoben ne ai bana so wani ya ganshi kafin ni..
Girdiza kay tayi da abun nashi se shi......tafiyar ta tayi ta barsu nan..
Jikinshi duk yayi sanyi dan yaso yaga zoben nan yau..aman dole ya hakura ..
Maysam tace am sorry hubby na baka wahala..ina ga fa na barshi a Maradi da mukayi
patyn mu na karshe ina ga yana can ..
Ajiyar zuciya yayi yace shikenan ki shirya se mu tafi sati me kamawa ...cike da
murna tace to dama kuwa har nayi kewar su Mufeeda..
Aman kuma ganin damuwa a fuskarshi yasa taja shi zuwa bayin dakin dan duk ya hada
zufa abunka ga wanda be saba wahala ba..
Wanka suka yo ..tanata janshi da hira ko ze saki ...ta koyi nasara har da dariya ya
shigayi yama manta da wani zobe ....nan tashiga yi mishi cakulkuli suna ta dariya
abunsu...daga nan kuma wasa ya fara canzawa a zafafefe Maysam ke aikawa Murad da
sakon ni..(kai yarinyar bakida ta ido fa😅.).na so yau na doko muku aman se rasa ta
ina zan fara dan yarinyar nan ta fice tunani na ..ina ganin haka na canza takuna na
ja musu kofa .dan pratical se manya ..
...
Sede Kash basu samu zuwa a satin ba dan asibityn na nan masarauta suka dinga samun
emercency kuma duk na fanin shine ....ga doctor din me kula da wurin baya
nan ..dole tasa ya kama aiki har zuwa lokacin dawowar doctor din..dan clinik din
tasu tafi sauran kayan aiki .shiyasama duk wani emercency daya gagari sauran se
aturo su nan...haka ya hakura kullum cikin buzy yake ..ga kuma rigimar Maysam a
gida... ..itace goyo ,kokuwa ta aza mishi kukan se yayi mata doki ,kai shirme da
rigima iri2 take mishi ..
Seda yayi sati biyu doctor din ya dawo ai kuwa a washe gari suka daga se
Maradi .fulani kam tayi fada a cewarta zasu wahalar da cikin ...kuma ga bikin
Mahmud aman jin acan Maradin za'ayi komi.....kuma taga Maysam ta nuna tana son zuwa
dan aure su Mariam saura one week .na Mufeeda kuma ..kwana goma ..seta kyalesu...
Ba karamar Murna sukayi ba da ganin junan su ba...
Wani abun mamaki be huce zoben dabaya nan ba ..shima duk sun burcike dakuna sun bar
kuyangi da aiki amam babu zobe ...Maysam har da kwallarta ganin ta batar da
zoben.....kai daga karshe ma Murad hakura da zoben yayi ..tunda daman da kamar wuya
ace na sweetbabyn shi ne..shiyasa ya rarrasheta aka bar zancen shi
Maysam tun zuwan su ta shiga hidimar bikin Mariam da dan cikin ta se shiga da fice
suke itada Mufeeda ..in sun mata magana tace to suwa zasuyi in bata kama ba..
Se kuma dare in yayi ta addabi Murad da jikinta ciwo yake mata dole se yayi mata
massage..shi kanshi wani lokacin mamakin kanshi yake yanda yake biye mata ..(hum
macen kenan Murad😝)
Har lokacin kuma Mark be taba zuwa ganin *zab'in iyaye*(littafin my my Fatima yar
kasarmu😍) n shi ba ..yaude Dadyn shi ya ritsa shi ..tunda yake ta mishi fada be
dago ba se yanzu .dayashiga bawa dadi hakuri.hum wai kunsan waye Mark kuwa?
Ku biyo ni de
..dole yaja Mahmud ya rakashi ..da yake ya dawo shima ...dan Murad yana can yana
fama da Maysam dake dan zazzabi gajiya
Mark ke jan motar dan shi ya san gidan......koda sukazo sukayi horn me gadi ya bude
musu kofa ...
Shi de Mahmud ya cika da mamaki dan yasan san nan gidan su Mariam ne
tripleM...aman se beyi magana ba
Mahmud yace to ka kirata ta fito mana..
Ya tsine fuska yayi yace nifa banida numberta hasalima rabona da ita tun tana yar
mitsitsiya da ita ...
Ya kuwa kwashe mishi da dariya...yace kana da aiki kam
Suna fito wa daga motar akayi sa'a sega wani kaninta yazo ze fita..dan haka suka
aikashi ciki ...
Iso akayi musu anan palon ..ummanta da yayunta ne a palon dan haka har kasa suka
gaishe su..sanan wata kanwarta tayi musu rakiya bangaren baki...
Mariam kam tun lokacin da taji wai Ma'aruf yazo ..se ta tsinci kanta cikin bakin
ciki dan aganin ta ai reni ne wanan ace se ana sati sauran aure sannan ze
zo ..badan ummata bace ta gaya mata da bame sata fitowa..
Wani katon hijab ta saka babu ko kwalli a idon ta ..yayunta na mata magana aman ta
kyallesu ga babu su Mudeeda sun tafi bare su rakata..dole ta fito ta shiga palon da
sallama ..kanta a kasa tunda ta shigo dan bata ma son ganin shi..ta gaishe su
Mark kam tunda tayi sallama ya zuba mata ido ..miyan bakinshi sun kafe..
kuma daga shi har Mahmud babu wanda mamaki be kusan kashe shi ba..yama kasa magana
dan duk gani yake gizo ne take mishi ...shi kuwa Mahmud mamakinshi dan yana labari
soyayyar su ta can england
Mahmud daya lura da haka se shi ya amsa ta tare da fadin tripleM ykk ya shirye2.
Da.sauri ta dago idonta dan ta gane muryar Mahumd ..aman abunda ta gani ya kara
bata tsoro ...sororo take kallonshi shima haka ..
Mahmud yayi dan murmushi tare da tafa hannushi. Firgit suka dawo da tunanin hucin
gadin da sukayi. ..kowa yana jiran bayani daga bakin dan uwan shi..
Shikam daya ga abun bana karewa bane se yace to Mariam ga abokina Ma'aruf Elh
Ma'azu kuma dan abokin abbanki kamar yanda kika sani kuma shine wanda ze aureki ...
A tare suka sauke ajiyar zuciya ..aman kuma sun kasa magana ..se sakin murmushi
suke akai2 ..
Mahmud yace to ni ina mota idan kun gama kurmaci se ka zo muta fi..
Yana fita Mark ya matsa kusa da ita ..yace lovely ta kinga wani okon Allah ko?
Alhamdulillah ashe addu'ar mi bata fadin ba ..shiru tayi ..yace baza ki mun magana
ba ..se lokacin ta dan saki..nan fa hira ta barke har sun manta da wani Mahmud
bare su tuna da ba a daura auren su ba ..hirar masoya kawai suke sharba..
Har goma da wani abu shima seda Mahmud yayi mishi magana ne kamar kar su rabu haka
suke ji ..
Ai tana shiga ta dannawa su Maysam kira dan murna tama manta da Maysam matar
aurece....
Ai kuwa hada musu call su ukku tayi ta shiga basu labarin abunda ya faru...sun
tayata murna badan dare yayi ba sun zo gidan kam..
Ai tunda ga nan kullum a gidan yake kusan wuni a cewar shi yana zuwa gaida su Umma
ne ....
Biki ya kan kama ..duk wani event da akeyi Murad be hana Maysam dan yasan irin
shakuwar dake tsakanin su ..sede yana cewa ta rage aiki dayawa ...
To Alhamdullilah ranar daurin auren dunbun nan jama'a ne suka sheda aure Ma'arud
elh Ma'azu. Da Mariam elh Moctar ...murna wajen ma'auranta ba'a ma magana ..da dare
akayi paty na gani na fada wanda Murad shi ya dau nauyin komi ..an ci
ansha ....tun a daren aka sada amariya da gidan mijinta..
Abun mamaki ita irin kukan nan batayi ba ..su Maysam se shakiyanci suke mata ..
Mahmud ,Murad da wasu couz dinshi biyu ne suka tako shi ..ya yinda su ukku kade a
dakin wato tripleM se wasu yan uwanta biyu ...
Barkwanci sukayi tare da yi musu addu'oi samun zaman lfy ..sanan shi Murad yaja
matarshi ..shima Mahmud ze sauke Mufeeda agida...se sauran kuwa couz dinshi zasu
sauke su..
Bayan tafyar su ne su ka nan tattaba hira har take tambayar shi taya sunan shi ya
koma Mark ne ..yar dariya yayi yace yaude ba ranar wanna tambayar bace ...yanzu ki
tashi ki doro alwala wata rana insha Allah zan baki labari...
Raka'a biyu sukayi kamar yanda sunna tazo dashi .tare dayi musu addu'oi.ya ciyar da
ita kaji da fresh milk din da ya shigo da su....
Daga nan kuma suka fara kokarin fara pratical ...sum2 na fice a dakin tare da
ragowar kajin😋😋...
Washe gari kam Maysam da rigima ta tashi dan dama a al'adar garin amariya bata
girki wani daga dangin mijita koma daga dagin amariyar ko kuma kawar ka zatyi maka
girki har na tsayon sati dan haka Maysam tace ita tayi alkawarin yi musu su duka
in aurensu ya tashi...
Shide lallabata yake ita da ko tuwon gidanta wuya take sha bare tayi na wani ..dan
bata cin abinci kuyangi in ba doleba acewarta ta fiso ta girkawa mijinta da kanta..
Suna haka ya daga waya ya kira Mark yace ya bawa Mariam zeyi magana da ita ..nan ya
sanar mata rigimar Maysam ..kawai setace bata wayar ..
Tana tura baki ta amsa ...sama2 suka gaisa dan bata son tace mata a'a..
Cike da lallashi da lallaba tace haba triple M so kike ki wahalar da babyn
mune ..ke bakiga kin yi nauyi bane ..pls and pls kiyi hakuri ni na yafe kada
kidamu..da kyar ta shawo kanta...nan suka dan tattaba hira suka kayi sallama
Ba jimawa sega kiran Mufeeda ma ya shigo bayan sun gaisa itama tayi mata rigakafin
ta yafe in nata yazo base tayi mataba..
Hka de rayuwa tayi ta juya musu inda har yau akayi auren su Mufeeda da Mahmud
suma ..gajiya de Maysam ta tara ta .. Dan yar bidi'ar nan ta event seda akayi dan
kala kusan hudu akayi wanda duka Murad ya dau nauyin su....
A ranar da aka kaita shima kuwa Mahumd be dagawa Mufeeda kafa ba ..masha duk sun
kai budurcin su gidan mijin su sede mu musu fatan kazantar daki....
Bayan sati Murad suka fara shirye2 sun na dawowa...ana gobe zasu tafi suka shirya
wa kansu nan karamin paty su ukku kowa da matarshi ..
Anan ne ma su Maysam suka nemi sanin taya wai daga sunan Ma'aruf ya dawo Mark..
Ai kuwa su Murad suka shiga kwasar dariya tun kafin su basu labari yayin da Mark ya
cika yayi fam ..yana fadin wly kada su sake su sanar musu ..aman sukayi kunnen
shegu da shi..Mahmud yace *SANADIN ACCIDENT* ne ya samu sanan nan..
Murad ya fara basu labarin cewa lokacin suna england ne ..ranar da aka rantsar
dasu cewa sun zama cikakkun doctorori ..bayan munyi patyn murnar mune .dare yayi
sosai ..kowa ya kama haramar zuwa gida to daman shi lokacin be wani kware da motaba
kawai ya yanka kan titi se ga wani guy yayi shaye2n shi ya bugu se langi yake a
titi ..abunka ga dan koyo ..yayi ta mishi horn aman ko motsi ..ai kuwa Ma'aruf ya
kade saurayi..dayake gaba da baya ne muke tafiyar kasancewar unguwa guda muke ...da
sauri muka fito muka shigar da yaron motarmu lokacin bayama numpashi..muna zuwa aka
shiga dashi emergency room ..aka bashi temakon gaggawa aman har lokacin be farka ba
kuma gashi komi is normal ..lokacin da muka diba card din saurayi se mukaga sunan
shi MARK
tofa seda muka shafe two days aman be farka ba. .nan Muka shiga damuwa
matuka ..bare ma shi Ma'aruf duk gani yake baze farka ba..se ya zamanto bashida
aiki se kiran sunan Mark ko kuma ya tisa shi gaba yana fadin pls Mark kada ka mutu
ka farfardo ..kai abun har cikin baccishi zakaji yana sambatun pls Mark kada ka
mutu ,..wayoo Allah na kaji k'aina ka tashi kafadar Mark ..
Ina zan saka rayuwa na in ka mutu Mark ..ace ni na kashe mutum....
Tun abun yana damun mu har ya dawo bamu dariya dan yanda yake yi ne se wanda ya
gani...
Ranar da ya farfado kuwa har da rawa yayi wai Mark be mutu ba ...
Kamar da wasa se Mahmud yace wanna ai kaine ma Mark din ...
To fa tunshi ne muke kiransa da sunan Mark din..
Gaba daya suka sa dariya har shi Ma'aruf din ..nan suka shiga tonawa kansu asiri
bama kamar Murad ba daya kusan Mutuwa akan sweetbaby ba...da sabbatun da yayi
tayi...
Haka suka wuni ranar cike da farin ciki...da raha
Washe gari su Maysam suka dawo Zinder cike da kewar junan su...
Naso yafi haka aman am buzy ne ..littafin yama zo karshe ..ku kara hakuri akan na
da..
Ina yinku irin totaly din nan😍
Fassouma ce🖊(yar mutan zinder)
[9/14, 9:12 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[9/14, 9:13 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )
🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
S.W.A✍
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
*Don't forget azumin Arfa na gobe Monday. In sha Allah...yanada falala me yawa
dan* ```Manzon Allah (SAW) yana cewa;
Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda
biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)
@6335 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ.
```
*Allah .. ya sa muyi a dede ya kuma karbi ibadun mu Ameen(yar karmar tunatarwa
ce)* *Allah ne masani.*
Dedicated to all my fans😍❤
🅿105__106
```Manzon Allah (SAW) yace ''d'abi'u biyu basu taruwa ga mumuni:rowa da mummunar
d'abi'a.
Bukhari ya rawaito shi.```
[20/08/18 à 00:00]
Tunda suka dawo suke sharba soyyayar su ..kuma har yau neman zoben take aman tama
kasa tunano inda ta ajeshi .....cikinta kuwa har ya shiga wata na shida ..yayi
girma sosai kowa yana mugun tausaya mata musamma ma Murad....
Bayan sati da dawowar su suna palon ta wani yi lamo a cinyarshi tace ''My only one
..nayi maka wata tambaya mana...
Yana wani lumshe ido yace umm..dan hannayenta ba wuri daya suke ba
A ranta tace mulki ya motsa kenan ...a fili kuma se tace miyasa baka son ayi
celebreted din birtday dinka ne.
Da kamar bazece komi ba se kuma yace saboda a ranar wani birtday dina dana
sweetbabyna dan ranar birtday din mu daya ne kuma a ranar ne na rasa
sweetbabyna ..SANADIN ACCIDENT din da mukayi.yana fadin haka yayi shiru dan tuni ya
tuno da abubuwan da suka faru ranar .
Maysam tace am so sorry aman pls wannan karon ka bari muyi celebreted..ka gafa
saura two month ..se mufara shirye2 tun yanzo ko...
Yace um baza ayi ba . fa.
Tace why ..
Saboda sweetbabyna ..
Zata sake wata maganar
Ya kuwa dankara mata wata
zunkudediyar tsawa yace to baza ayi ba ....yana yi kamar ze doke ta ne..
Ai kuwa Maysam ta saki wani kuka me cin rai ...dan ta tsorata dashi
Rumtse idon shi yayi dan har cikin zuciyarshi yake jin zafin kukan ..yana kokarin
lallashin ta dan baze iya jurewa ba ..
Ai kuwa kan ya ankare har bar mishi wurin ....room ta shige ta fada gado tare da
sakin wani sabon kukan. ...
Yana ganin ta harta shige .ya SALAM ya furta se kuma ya .rufe ido tare da dafe
setin zuciyar shi yana fadin na fasayi saboda rabin zuciya na ..ga kuma dayan
rabin yana so nayi ..nikam ya zanyi da rayuwata ne..se kuma yace am sorry my
sweetbaby badan nayi fifiko ba sedan cikin dake jikinta ne kawai zan
amince.....shikade yake ta hirar shi se kace tana gabanshi
Can de ya tashi ya shiga daki ganin har lokacin bata yi shiru ba yasa da sauri ya
isa ya dagota ..se yaji wani tausayinta ya kamashi. .ga cikinta . a memakon ya
kwantar mata da hankali aman ace shi da kanshi ne yake tada mata shi kuma amatsayi
sa na docto..
Rumgumeta yayi tsam a jikin shi yana fadin am sorry wify i don't mean to hurt
you.......
Maysam tace dama ni nasan ba wani sona kakeyi ba k....
Da sauri ya hade bakinsu yana girgiza mata kai yace kidena zancen nan pls ..ke
kanki shedace akan irin sanda nake miki ..ko ban fada miki ba gangar jikina kadai
ya isa ki gane da haka ...ke ta musaman ce a rayuwata .....shikenan yace bade
birtday bane..yana share mata hawaye ?
Ta daga kai..
To ki kwantar da hankalinki za'ayi shi .....kuma yanda kike son haka za'ayi
shi .....
Ai bata san lokacin data rugumeshi ba tana zuba mishi godiya ..harda tamishi kiss a
kumatu tace ''tu es le meilleur mari dans ce monde (you are the best husband in
this world)...je t'aime à la folie...
Lakuce mata hanci yayi yace rigima ta kare kenan.....in sonki my beauty ,so na
hakika ..kin kasance lantarki farin wata dake haskaka rawuya wata ...dan soyayyarki
a hankali take shiga cikin zuciyata ..kin dasa gadargar kujerar mulkin ki a zuciya
ta .....ki tausaya mun kada ki gujeni ..kamar yanda sweetbaby ta g.....
Da sauri ta rufe mishi baki tace kada kayi sabo .ba ita ta guje ka ba.Allah da ya
halliceta yafimu santa.......kayi hakuri da kaddara
Nan de sukayi ta kwantarwa da juna hankali .....
🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Bari mu leko Inna Murza..
Ita kam tun lokacin da taga Maysam da cikin nan hankalin ta ya dada tashi ..tana
ganin Maysam zata kara samun wurin zama fa..dan haka ta kwallafa ran son ta zubar
mata da cikin ko ta halin qaqa...shiyasa ma ta tare abangaren Fulani dan ta samu
tasan irin shige da ficen Maysam din kuma .kusan kullum tana harin cikin sede bata
samun nasara ..har yau Da Allah yayi Maysam ta fito daga bangaren M.Musa zata na
fulani ..har ta fito hararabar gidan sega Murza da dan