Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
a tsaye, zuciyarta cike da tunani kala-kala. Cikin zafin nama ta
gyara masa ɗakin tsaf ta feshe ko'ina da turaren wuta.
Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe ta koma kitchen ta shiga haɗa masa girki, waton shinkafa da wake. Ɗaya
daga cikin kalolin abincin da Hajiya ta sanar da ita yana so. Bayan man ƙuli da yaji har da miyar tarugu a
gefe ɗaya ko da zai yi ra'ayin haɗawa. Wayarta ta lalubo ta shiga neman lambarsa, wadda Nur ta yi mata
saving lambar da hannunta. A watarana da ta ari wayar Minal ta kira sa saboda tata wayar babu caji.
'Jaan.'
Ta maimaita sunan a cikin zuciyarta kafin ta danna masa kira ƙirjinta yana bugawa fat-fat. Sai dai har ta
gama ruri ba ta ji an ɗaga ba, babu ɓata lokaci ta sake danna wani sabon kira. Caraf ta ji an ɗaga kiran tare
da yin magana a lokaci ɗaya. Nan take hawaya ya shiga bin fuskarta tsabar takaicin da ta ji.
"Sorry, idan na dawo za mu ƙarasa maganar."
Daga haka ya katse kiran, saboda tsammaninsa a kan maganar da suka fara ne ta neme shi. Ta jima
sandare da wayar a hannu kafin tunanin tura masa saƙo ya faɗo ranta. Cikin ɗan lokaci ta rubuta masa ya
turo yaro ya karɓi abincin da ta dafa masa.
'Ki jira zan dawo.'
Tsaki ta ja tare da wurgar da wayar a gefenta tana faɗin, "Kayan haushi." Ganin amsar da ya mayar mata
mai kama da an kwaɗa mata mari. Ɗaki ta nufa ta yi sallar Zuhur saboda a lokacin har biyu ta gota. Ta jima
a wurin tana lazumi kafin ta naɗe sallayar ta koma falo zaman jiran sa. Zuciyarta cike da haushi da fargaban
hukuncin da zai zartar a kan zamansu idan ya dawo.
Jamal kam bai dawo gidan ba har aka yi sallar Isha, kuma da gangan ya ƙi dawowar ya yi zamansa a
shagonsu. Hada-hadar saye da sayarwa ya saka shi rage jin kewar Nur da ke cikin zuciyarsa. A gefe ɗaya
kuma ba ya son zamansa cikin gidan gudun su sake samun matsala da Minal ta nemi kashe kanta a banza.
Sai da ya biya Restaurant ɗin da ya saba zuwa cin abinci, sannan ya je gidan Hajiya suka yi sai da safe ya
nufo gidansa. Zuciyarsa a sake saboda tun bayan aurensa bai leƙa shagon ba. Aikinsa kuma yana cikin
hutun da ya ɗauka da niyyar cin amarcinsa a kan kari.
Minal kam zuwa lokacin ta gama cika tana batsewa, don duk ta wurga ido ta hango abincin da ta yi masa
sai ta buga dogon tsaki. Wanka ma bayan na safe sai da ta sake wani saboda, ta kashe ɗaurin ɗankwali da
baza turare a jiki amma har ta gaji da jira bai dawo ba. Hakan ya sa lokaci da ta ji shigowar motarsa gidan
ba ta motsa daga inda take kwance tana kallo ba.
Har ta ji takun hawansa saman ba ta yi niyyar tarbon sa ballantana ta nuna farincikin ganin sa. Illa dukan
luguden uku-ukun da ƙirjinta ke yi tun lokacin da ta ji buɗe gate da shigowar motarsa. Da guntuwar
sallama ya shigo falon waya a kunnensa yana magana har ya shige ɗakinsa. Jim kaɗan ya fito falon bayan
ya gama wayar ya tsaya gabanta fuskarsa babu yabo babu fallasa ya shiga ƙare mata kallo.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce,
"Lafiyarki ƙalau kuwa?"
Banza ta yi masa kamar ba ta ji ba, hakan ya sa ya leƙa fuskarta yana faɗin,
"Ko barci ne kike y...?"
Ganin idonta wuƙi-wuƙi tana muzurai ya yi hanzarin fashewa da dariya sannan ya zauna yana faɗin,
"Ke kam wa ya taɓo ki bayan ke kaɗai ce a cikin gidan? Ko maigadi ya bar wani ya shigo gidan nan ban
sani ba?"
Tashi zaune ta yi, tare da wurga masa wani kallo sannan ta ce,
"Babu komai"
Ta miƙe da nufin barin falon ya dakatar da ita, ta hanyar faɗin, "Ina abincin da kika ce kin dafa mini?
Saboda sai a lokacin ya tuno da saƙon da ta tura masa. Har a ranta ta ji daɗin maganarsa ganin ya fara
damuwa da sabgoginta, saboda haka ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta nufi kitchen ta jawo kwandon abincin da
ta haɗa masa tun ƙarfe ɗaya na rana.
Cikin ƙumaji ta shiga baje kayan abincin a gabansa, zuciyarta cike da jin daɗi ta fara buɗe kular shinkafa
da waƙen. Bumm warin waken ya daki hancinta, bayan sandarewar da ya yi a cikin kular ya sauya
ƙamshinsa daga wake zuwa warin tusa. Babu shiri ya toshe hancinsa bayan ya miƙe yana nuna kular da
hannu ya ce,
"Wannan shi ne abincin da kike so na ci? Cabɗijam! Allah Ya taimake ni ban da rabon wahala..ahhhh..."
Ya fara yunƙurin amai da gudu ya nufi ɗakinsa ya banko ƙofar. Ya jima yana sauke ajiyar zuciya bayan
feshe jikinsa da turaruka yana shinshina jikinsa don jin warin ya wuce ko ya maƙale ya biyo shi har cikin
ɗakin. oda tana buɗe kular warin waken ya daki hancinta ta yi hanzarin kawar da kai gefe.
Wata irin kafurar kunya ce ta dabaibaye Minal, saboda ita kanta ba za ta iya cin abincin ba. Tsabar takaici ta
kinkimi kular ta fice harabar gidan jikinta yana rawa ta nufi maigadi tana faɗin,
"Baba don Allah almajiri nake nema."
Kallon mamaki ya yi mata, saboda sanin wace unguwa suke da irin mutanen da ke cikin ta. Maimakon ya
ba ta amsa zura hannu kawai ya yi alamun ta ba shi kular. Girgiza kanta ta yi tana cewa,
"Abincin ya lalace ba za ka iya ci b..."
"Ke dai ba ni Hajiya, mu kashi ne kawai ya rage mana ci a tsawon zamanmu cikin duniya."
Jiki babu kuzari ta miƙa masa kular cike da karsashi ta juya tana faɗin, "Bari na kawo maka miya ka saka."
Jikinta yana rawa ta kai masa ta dawo feshe falon da turare ranta a jagule tana Allah wadai da waken da ya
tozarta ta gaban Jamal. Bayan ta saita falon ta shiga bubbbga masa ƙofa zuciyarta a tsinke kuma cike tsoron
wulaƙancin da zai tarbe ta da shi.
Tsawon minti biyar tana buga ƙofar kafin ya buɗe fuskarsa a cure yana ƙoƙarin toshe hanci cike da
tsammanin zai sake cin karo da warin waken. Ƙamshin da ya ji yana tashi a falon ya saka shi sakin fuskarsa
riƙe da ƙofar ya zuba mata kallon tuhuma ba tare da ya ce komai ba.
"Ka yi haƙuri, tun ƙarfe ɗaya na rana na gama abincin shi ya sa waken ya buga."
Abin da ta faɗa ya sa ya bar jikin ƙofar ya raɓa ta gefenta ya nufi ɗaya daga cikin kujerun ya zauna yana
faɗin,
"Zo ki zauna mu kammala maganar da muka fara, saboda ba ba so kina wahalar da kanki a kaina daga
yau."
Jiki babu kuzari Minal ta nufi kujerar kusa da wadda yake kai ta zauna a ɗarare. Ƙirjinta yana bugawa ta
shiga sauraron maganganunsa masu kama da ɗigar dalma a jiki.
"Duba da yadda aka yi aurenmu da yadda zaman ya zo mana. Yana da kyau kowa ya san matsayinsa
saboda gudun shiga haƙƙin juna. Don haka daga yau kada ki sake saka abinci da ni. Ki dafa iya cikinki ba sai
kin ajiye mini ba...ke ko da ina gida ban ce ki dafa da ni ba. Saboda ina da inda nake cin abinci ba na son
ɗora miki nauyin cikina."
Shiru ya ratsa tsakani a lokacin da ya tsahirta da maganar sannan ya ɗora da cewa, "Kin amince za ki
zauna da ni a matsayin abokin zama ba miji ba?"
Minal ta wurga masa wani kallo cikin ƙunar zuciya sannan ta yi magana da sanyin murya ta ce, "Zan
zauna da kai a bisa umarnin mahaifiyata. Sannan zan ci gaba da riƙon ka kamar yadda Nur ta ba ni ajiyar ka,
har zuwa ranar da ta dawo gare ka."
Sai da ya yi shiru yana nazarin ta kafin ya sake cewa, "Batu na gaba, tun da kin ji kin gani kina buƙatar mu
ci gaba zaman da muke kai; to duk abin da ya biyo baya kada ki tuhume ni. Saboda ni ban shirya zaman
aure da kowace mace ba. Kuma ina kan bakana kamar yadda na sha faɗa zan maimaita, da Nur kawai na
tsara rayuwa da ita zan yi zaman aure. Amma tun da ƙaddara ta haɗa mu zama ni da ke ba zan bari mu cuci
juna ba. Don haka daga yau ba zan sake shiga duk abin da ya shafe ki ba, ki yi rayuwarki ni ma zan yi tawa.
Kada ki ga na ɗaga miki ƙafa tausayin ki kawai nake ji, amma idan ke kin zaɓi ci gaba da zaman a haka babu
damuwa. Sai dai kafin nan zan ba ki dama ta ƙarshe don kafa shaidu, gobe idan Allah Ya kai mu zan kai ki
gidanku a yi komai a gaban iyayenki."
Zumbur ta miƙe zuciyarta tana harbawa ta shiga juyi a gabansa cike da jarumta ta ce, "Dube ni da kyau
Jamal, daga halittar jikina har halayena babu abin ƙyama. Don haka ban ji haushi don ka nuna ban kai
matsayin ka yi zaman aure da ni ba. Saboda haka na zaɓi bin umarnin mahaifiyata da riƙe amanar da Nur
ta bar mini duk da zuciyata ba ta farinciki."
Sheƙeƙe ya dinga ƙare mata kallo har ta gama tumbuɗin maganganun bakinta. Murmushin takaici ya yi
kafin ya ce "Ki daina yaudarar kanki, ko da mazan duniya ke son ki ni ba kya cikin tsarin matan da nake so.
Kuma zan dawo da sabgogina da nake yi tun kafin haɗuwa ta da Nur, alƙawarin da na yi mata kuma zan
riƙe amma ba zan fasa yin abin da zai rage mini sha'awa ba tun da ta iya tafiyarta ta bar ni. Saboda haka
duk abin da kika ga na yi a cikin gidan nan ido ne naki. idan kin gaji da irin zaman kawai ki sanar da
Hajiyata, ita ce za ta sa na sauwaƙe miki a duk lokacin da kika buƙaci hakan."
Akwai littafina DAKAN ƊAKA...na fara ɗora shi ArewaBooks. Kuma akwai complete book 1-2 1k ga mai
buƙatar ya taɓo ni ta nan; 08022014771.
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA BIYU.*
Wani ƙololon baƙinciki ya tokare mata a maƙoshi. Saboda maganganunsa ba ƙaramin ƙuna suke yi a
zuciyarta ba. Amma da ta tuna ita da nata shirin, hakan ya sa ta yi murmushin takaici ta ce,
"Har kullum ina yi wa Allah godiya da babu saka hannuna a cikin ɓatan Nur. Saboda haka idan ma ka
ɗauki haƙƙina Ubangiji Yana kallo kuma ba zai bar ka ba."
"Duk abin da za ki faɗa kina da damar hakan a yau kuma a yanzu. Amma ki sani daga gobe damarki ta
wuce matuƙar kin amince da sharuɗɗaina."
"Uhumm!"
Iya abin da ta faɗa kenan tare da miƙewa zuwa ɗakinta. Kallo ya bi ta da shi cike da mamakin yadda ta zaɓi
zama da shi duk da tarin ƙalubalen da za ta fuskanta. Jiki babu kuzari ya yi ɗakinsa zuciyarsa cike da kewar
Nur da irin alƙawurran da ta ɗaukar masa idan sun yi aure.
'Me ya sa kika bar ni bayan kin san saboda ke na shiryu? Me ya sa za ki bar wa wata ni bayan kin sani ba
zan so ta ba?'
Zancen zucinsa kenan saboda gabaɗaya kewarta ta addabi ransa. Kwana ya yi yana juyi saboda sha'awar da
ta yi masa mugun kamu. Duk da maganin da ya lalubo da ƙyar ya gan shi ya kora da ruwa yana rawar
sanyi. Amma hakan Bai nutsar da shi ba har daren ya yi nisa, zuciyarsa sai hango masa Minal take yi amma
yana ƙoƙarin kawar da kansa a matsayin haramtacciya gare shi. Don ya gama keɓe ta a cikin matan duniya
waɗanda zai iya yin mu'amalar aure da su.
Ɓangaren Minal kuma kwana ta yi a kan sallaya tana kai wa Allah kukanta. Ita ma ba ta yi wani barcin
kirki ba sai Bayan sallar asuba nannauyan barci ya yi awon gaba da ita.
Washegarin safiyar dukan su babu wanda ya tashi da wuri. Misalin karfe goma na safiya ta jiyo motsin
buɗe ƙofarsa, a lokacin tana tsaka da shiri bayan ta tashi da ƙyar ta yi wanka. Don ranar ba ta yi tunanin yi
masa gwaninta ba ballantana ta yi asubancin shiga kitchen. Saboda ita ma ba ta tashi da son cin komai ba,
kasanacewar ta dafa indomie bayan Jamal ya shige barci, sai da ta ci ta yi ƙat a lokacin da yunwar dare ta
hana ta sukuni, sannan ta runtsa.
Motsinsa a falo da sautin Tv da ta ji hakan ya sa ta gano ba zai fita da wuri ba. Cikin sauri ta gama shirinta
kamar yadda ta saba kowace safiya, tana tashin ƙamshi ta fito da niyyar yi masa ina kwana. Saboda ta ƙi
bin umarnin wani sashen zuciyarta da ke gargaɗinta a kan kada ta je.
Kanta tsaye ta nufi inda yake zaune yana kallo, ƙamshin girkin da yake yi yana dukan hancinta. Nan take
wata sabuwar yunwa ta taso mata, tsayawa ta yi ɗan nesa da shi tana cewa,
"Ina kwana?"
Kamar ba zai ce komai ba tsawon sakonni, sannan ya cira kansa yana ƙare mata kallo sama da ƙasa ya
watsar yana cewa,
"Ke kam har zuwa yaushe za ki waye ne? Mace haka a tsaye babu wata lanƙwasa. Ko ke a naku gidan
kalar gaisuwar taku kenan?"
"Gaisuwar da ta dace da kai dai!"
Ta amsa masa kai-tsaye tana ƙoƙarin barin wurin ba tare da wani jinkiri ba. Kansa ya shiga ɗagawa yana
jinjinawa sannan ya sake cewa,
"Ehhhh...kuma fa kin yi gaskiya. Da irin wannan gaisuwar na dace a wurin mata irin ki, waɗanda har
duniya ta tashi ba za su taɓa wayewa b...kaico!"
Sharrr hawaye ya fara bin fuskarta cikin hanzari ta shiga gogewa da bayan hannunta cikin muryar kuka ta
ce, "Ban waye ba, kuma ba zan taɓa wayewa ba. A bar ni a yadda nake ai ba jinda na yi aka ba ka sadakata
ba. Da rashin wayewar aka gano ni ce wadda na fi dacewa da zama da kai. Kuma a haka za ka zauna da
bagidajiya kuna jera kafaɗa a wuri ɗaya."
Wata mahaukaciyar dariya ce ta suɓuce masa babu shiri, kafin ya shiga nuna ta da hannu yana ƙumshe
bakinsa alamun yi wa dariyar tasa waigi. Haushi ya sa ta bar wurin da gudu tana kuka, tsabar takaicin ganin
ya gama raina ta, kuma ba ta san me za ta yi masa ya yaba ba.
Jamal kam tsaf ya gama girkin ya cinye kayansa a cikin falon, da remote a hannunsa yana canza channel
zuciyarsa wasai kamar ba ya jin tashin kukanta. Saboda ƙoƙarin ƙarfafa kansa da yake yi gudun faɗawa
tarkon da aka yi masa a kanta.
'Mu je zuwa, don har yanzu ban gama yarda da ke ba, ba a banza kike son zama da ni ba. Ke ko ma mene
ne zan gano abin da kike ɓoyewa kafin wanzuwar ƙudurinki a kaina.'
Da wannan nazarín ya datse ƙofar tausayin ta a ransa. A gurguje ya yi wanka cikin shiga ta manyan kaya,
har ya nufi hanyar fita ya dawo ya shiga ƙwanƙwasa mata ƙofa. Banza ta yi masa kamar ba ta san yana yi
ba, sai da ya gaji don kansa ya murɗa hannun ƙofar ya shiga kansa tsaye yana ce wa,
"Hajiya ki fito mu je ke nake jira."
Ba ta motsa ba, hakan kuma bai sa ya sake maimaita maganar ba ya fice tare da ja mata ƙofar. Da sassarfa
ya sauka ƙasa yana waya, fuskarsa a sake yake cewa,
"Ki zama cikin shiri da na sauke wata zan zo na ɗauke ki..ok ..bye."
Daga haka ya mayar da wayar aljihunsa cike da farinciki. Fuskarsa a sake suka gaisa da maigadi sannan ya
nufi motarsa a ransa yana faɗin,
'Yau kam mota ba ta samu gatan jiya ba.'
Ya yi wani kalar murmushi ya faɗa motar cikin karsashi ya shiga ba ta wuta yana horn wani bayan wani.
Saboda ya matsu Minal ta yi saurin fitowa ya yi abin da yake hangen shi ne babbar makamarsa. Ita kam
jikinta yana rawa ta danna wa Innarmu kira bayan fitarsa. Saboda tsoro da fargaban da take ciki a Kan
tafiyar da yake so ta yi, kada Innarmu ta ce don ba ta son zaman ne ta yi abin da zai kawo ƙarshen aurensu
da gayya. Bayan har zucinta ta ci burin zama da shi a bisa wasu ƙwararan dalilanta da take ganin su ne
makaman da za ta yi yaƙin ƙwato 'yancinta.
Aka yi sa'a kira ɗaya tana kusa ta ɗaga, saɓanin wasu lokutan da Innarmu take jefar da wayar ta yi ta
sabgoginta, ko idan tana hannun ƙannenta suna buga game su saka ta flight mood don kada ma wani ya
kira a kan uzurinsa ya katse musu game.
"Innarmu kada ki ga laifina ya ce zai kawo ni gida a yi komai a gabank..."
"Me za a yi gabanm...? Ke ki fita idona na rufe Amina! Shin Salame ba ta ce miki ki san dabarun da za ki
jawo hankalinsa ba ne?"
"Mun yi maganar."
Amina ta amsa fuskarta a cure, saboda horn ɗin Jamal da maganganunta sun ƙara dagula mata zuciya.
Musamman da Innarmu ta ce,
"To ki ce masa kin amince za ki zauna ba sai kun zo gidan b.. "
"Na faɗa masa fa wallahi...kin ma ji shi can yana ta horn Innarmu ni kawai yake jira na fito mu z..."
"To ku zo ga ni ina jiran ku daga ke har shi ɗin...wallahi muddin auren nan ya mutu kada ki yi tsammanin
Zan sake zama da ke a gabana! Mutuncinki ɗaya shi ne ki san yadda za ki yi da shi ki lallaɓa a bar batun nan
kawai. Idan ba don ya gaji da halinki ba wane zaɓin zama ko rashinsa zai ba ki...to ki bari auren ya mutu ki
dawo gidan ki ga yadda zan yi da ke."
Ƙit ta kashe wayar, jiki babu kuzari Minal ta miƙe ranta yana ƙuna ta jawo jaka ta fara loda kayanta cikin
fushi. Bayan jarumtar da ta ara ta yafa wa jikinta ta shiga jan jakar iya ƙarfinta har zuwa harabar gidan. A
jigace ta isa bakin motarsa ta tsaya tana nishi fuskarta a cure. Ganin ta da jakar kayan ƙirjinsa ya buga dam-
dam, saboda tuno kalaman Hajiya kai-tsaye suna shiga cikin kunnuwansa