Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
Ta ƙare zancenta na zuci tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana runtse ido. Saboda ta kasa
manta rawar ɗuwawun da Jamal ya yi a kanta tsabar ya same ta cikakkiyar mace bayan gyaran Hajiya.
"Idan ka ba ni zuciyarka ma ta wadatar da ni. Hakan ya sa ba na buƙatar komai sai kai kawai....Nur kum.."
Ta yi saurin toshe bakinta tamkar wani zai ji ta, cikin sauri ta yi niyyar gyara kwanciyarta babu shiri ta ce,
"Ashh!" Saboda zogin da ta ji a ƙasanta dole ta lallaɓa a hankali har ta daidaita kwanciyar sannan ta rufe
idonta da niyyar yin barci.
Sai dai kafin barcin ya yi awon gaba da ita ta jiyo tashin murya a falo ana ta rafka sallama. Ta ƙara lafewa
a cikin gadon tare da kasa kunne tana son tantance muryar mai sallamar. Cikin sauri ta zaro ido, saboda jin
muryar Inna Ade tana faɗin,
"Matar gidan tana kusa kuwa?"
"Inna ga ni a ɗaki, ki shigo kawai."
Ta yi maganar cikin wata kalar muryar mara lafiya, tare da tsabar jin nauyi da kunyar Inna Aden, gudun ta
gano halin da take ciki har ta fahimci abin da ya wakana. Muryar Inna Ade ta so ɗakin tana faɗin,
"Ai na ɗauka ke ma ba kya nan ganin yaron nawa ma ba ya gidan. Don na yi mamaki da maigadinku ya ce
kina ciki don na yi sallama ta fi goma ban ji motsin kowa ba."
Tana maganar har ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ɗauke da wani ƙaramin kwando a hannunta.
"Ban ji ba ne Inna ai da na amsa miki, saboda barcin da ya fara ɗiba ta sai daga baya na ji sallamar." Ta yi
maganar tana runtse ido tare da cije leɓenta saboda yunƙurin tashin da ta yi kafin ta shigo ɗakin amma ta
kasa.
Bakin bed side Inna Ade ta zauna idonta a kan Minal cike da son tabbatar da abin da take zargi ta ce,
"Allah Ya sa dai lafiya lau kike, don na ji muryar taki kamar ta marasa lafiya."
Murmushin dole Minal ta janwo a kan fuskarta sannan ta ce, "Ƙalu nake Inna, kawai dai ɗan zazzaɓi ne ya
kafce ni cikin dare har sai da aka yi mini allurai."
"Allah Sarki matar yarona, ashe Hajiya ta canka daidai. Don takanas ta tayar da ni na zo saboda kawai na
kawo miki abin da ta dafa miki. A cewarta ma, jikinta ya ba ta kina can kina kewar ta, ko iya wannan zai sa
ki Yi zazzaɓin. Sannu kin ji, Allah Ya ba ki lafiya, amma za ki iya tashi ko na taimaka miki don ki ci abincin.
Saboda ta ce na saka ki gaba har sai kin cinye komai na dawo mata da kulolinta."
Murmushi Minal ta yi mai sauti, cike da Jin daɗi a ranta ta ce, "Ɗan kama ni dai Inna, jikin ne nawa ko'ina
ciwo yake yi. Ga bakina babu daɗi kamar na yi sati ina jinya."
Ta ƙare maganar tana cije leɓe Inna ta ɗago ta a hankali cikin dabara ta kai ta jikin gadon ta ɗora mata a
bayanta ta jingina. Cike da tausaya wa ga halin da take ciki ta sake ce mata,
"Wannan ciwo ya buge da yawa matar yarona, na ji jikin naki da zafi rau har yanzu kamar zazzaɓin bai
gama sauka ba."
Shiru kawai Minal ta yi cike da jin nauyin ta a ranta, saboda jikinta ya ba ta kamar ta gano abin da ya
faru, tana biye ta ne kawai a yadda take so.
"Me kike son ki fara ci? Akwai farfesun kaji, akwai na kayan ciki da kuma taliyar Hausa."
Minal ta yi murmushi sannan ta ce, "Haɗa mini ruwan tea kawai Inna, saboda bakina babu daɗi ba zan iya
cin komai ba."
Kitchen Inna Ade ta tafi cikin sauri ta haɗa mata tea mai kauri don ta zabga mata madara. Sannan ta
nemo plate guda uku mai faɗi da masu zurfi biyu, tare da cokali ta dawo ɗakin. Cikin kulawa ta miƙa mata
kofin shayin tana fara sha ta koma zuba mata taliyar da Hajiya ta dafo mata da hannunta, a gefe ɗaya kuma
tana ta jera mata sannu. Sai da shanye shayin tas sannan Inna ta karɓi kofin ta miƙa mata plate ɗin taliyar
ta karɓa tana faɗin,
"Kaɗan zan ci Inna saboda Hajiya ta ji daɗi, amma ko kaɗan ba na jin son cin abinci bakina babu
ɗanɗano."
"To ki ci ko ya yake ya fi rashin cin." Kaɗan ta tsakuri taliyar Inna Ade tana matsawa har ta ci rabin plate
sannan ta karɓi plate ɗin ta ɗauko wanda ta zuba mata farfesun kajin da suka sha dafuwar ruwa sai ƙamshi
ke tashi. Minal ta karɓa yawunta yana tsinkewa ta fara ci tana faɗin,
"Wannan daɗin duk ni kaɗai Inna?"
Inna Ade tana 'yar dariya ta ce, ni ma umarnin kawowa kawai aka ba ni matar yarona, yadda kika gan shi a
haka na gani don Hajiyar ce ta yi komai da kanta. "Ubangiji Ya saka mata da mafificin alherinsa." Ta yi
maganar cikin muryar kuka tana goge ƙwalla da bayan hannunta, saboda har zuciyarta mutuncin Hajiya a
idonta ya yi girman da dole sai ta zubar da hawaye.
"Kuka kuma?" Inna ta yi maganar tana 'yar dariya bayan ta gama faɗin amin. Minal ma ta yi dariyar bakinta
a washe ta ce,
"Abin da Hajiya take yi mini ko mahaifiyata ban samu wannan darajar a wurin ta ba. Don haka ban san
da wane baki zan ce mata na gode b..."
"Abu ɗaya za ki yi mata ki faranta ranta, idan kin riƙe mata yaro tsakani da Allah. Da kin yi hakan
shikenan kin gama biyan ta, don iya abin da take so kenan a wurin ki kada ki sake barin wasu mata su
ɗauke masa hankali. Babban burin Hajiyar kenan, wanda ya sa take sadaukar da komai nata a kan samun
wannan biyan buƙatar."
Shiru Minal ta yi tsawon mintuna tana nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Da yardar Allah zan riƙe
shi irin riƙon da wata mace ba ta isa ta sha gabana a wurin sa ba. Kuma na yi wa kaina alƙawarin zan yi
haƙuri da halinsa ta yadda komai zai yi mini zan jur...."
'Nur fa?' Tsam ta yi da ranta a lokacin da Inna Ade take zuba mata ruwan albarka, ita kuma zuciyarta ta
tafi tunanin ba za ta iya jurar ganin sa da Nur ba. Za ta iya haƙuri da shi a kan komai amma babu shirgin da
ya kwaso Nur a ciki. Don ko sunanta ta tuna ƙirjinta faɗuwa yake yi, ballantana ta tsunduma tunanin
rayuwarsu kafin lokacin aure har zuwa shagalgulan bikin da ranar da aka kawo ta cikin gidan. Ajiyar zuciya
ta sauke mai ƙarfi tare da kai kallonta ga Inna Ade tana murmushin yaƙe, tare da faɗin,
"In sha Allahu Inna." Saboda duk abin da take faɗa ba ta ji komai ba sai ki riƙe mijinki da take ta nanatawa
a bakinta. Bayan ta gama jera mata kalolin nasihohi a kan haƙuri da zaman aure da zama jajirtacciya a kan
kowace irin matsala. Cikin dabara Inna ta ja hankalinta suna ta hira har ta kusan cinye duka ferfesun da ta
zuba mata sannan ta sha romon duka. Cike da jin daɗi Inna Ade ta laƙume sauran taliyar da ta rage, kuma
lashe sauran abin da ta rage na ferfesun ta je ta wanke komai da aka ɓata, tare da juye mata da sauran
taliyar da ke kula da ferfesun a nata kalolin sannan ta yi sallama da ita da niyyar tafiya.
Minal ta roƙi alfarmar ta haɗa mata ruwan ɗumi a bahon wanka, sannan ta taimaka mata ta yunƙura da
ƙyar ta kai ta toilet, cikin ƙarfin hali Minal take takawa tare da ƙarfafa zuciyarta a kan jin sauƙin dole kafin
Jamal ya dawo, don ta ci burin yi masa sabuwar kwalliyar da idan ya gani zai yaba ita ma ta ji daɗi.
Hakan ya sa ta ɗauki tsawon mintuna a toilet ɗin tana gasa kanta har zuwa lokacin da ji ƙarfin jikinta ya
dawo. Sannan ta yi wanka tare da ɗoro arwala ta dawo ɗaki, inda ta ga Inna Aden tana share ɗakin bayan
ta gyare gadon tas kamar ba a taɓa kwanciya kansa ba.
A zaune ta yi sallar Zuhur da Asr ganin Inna ta fice daga ɗakin, kafin ta shafa addu'a ta koma bakin
madubi ta shiga tsara kwalliyar tarbon Jamal. Duk da wani gefen zuciyarta yana hango mata rashin
kyautawarsa a kan barin ta daga siyo abinci ya dawo har zuwa lokacin bai dawo ba. Amma ta yi masa uzuri
saboda yadda ya nuna mata kulawa kafin ya fita tana a ji a ranta bai yi hakan da gangan ba, ta ɗora laifin a
kan wataƙila wani babbab uzuri ne ya danne shi wanda ya hana shi dawowa cikin lokaci.
Bayan ta gama shirin ta fito fes cikin wata sabuwar shadda golden colour mai ɗinkin doguwar riga ɗauke
da aikin baƙin zare da golden ɗin. Sannan ta feshe jikinta da turaruka tana baza ƙamshi ta fito falon ganin
Inna a falon kwance.
Fitowarta ya sa Inna kai kallonta a kanta tana faɗin, "Ma sha Allahu tubarakallah! Yarona ya yi sa'ar mace
mai tsada a gidansa."
Murmushi kawai Minal ta yi ta isa inda wayarta take caji tun daren jiya har lokacin. Sai dai ganin ta a zare
zuciyarta ta tabbatar mata Jamal ne ya cire bayan cajin ya cika.
Zama ta yi da wayar a hannunta bayan ta kunna musu Tv tana 'yar dariya tare da faɗin, "Alamu ya nuna
Inna kin fi son yaronki a kaina."
"Kamar yadda Hajiya ta fi son ki a kansa Kenan!"
Gabaɗaya suka saka dariya, daidai lokacin da ta hau WhatsApp ƙarar saƙonni suka dinga shigowa cikin
wayarta. Kacokan hankalinta ya koma a kan wayar, musamman saƙon wata ƙawar Nur da ya ja hankalinta
kai-tsaye inda take tambayar ta,
"Yaushe Nur ta dawo?"
Ƙirjinta ya buga dam-dam, cike da jin haushi ta fita daga saƙonta ta koma bin groups amma hakan bai hana
ƙirjinta ci gaba da bugawa ba. Ranta a ɓace ta koma Tiktok tsabar haushin tambayar da Summy ƙawar Nur
ta yi mata. Ta shiga Tiktok da niyyar ganin abubuwan da za su rage mata takaicin Summyn, sai dai kamar
haɗin baki tana shiga da bidiyon Jamal da Nur ta ci karo inda suke rungume da juna suna kuka.
Babu shiri ta zaro ido har da goge su da niyyar gani daidai kada a ce gizo ne suke yi mata. Hannunta a
ƙirji ta bi comments inda take jin kalaman yabawa da jinjinawa a kan irin zazzafar soyayya. Cikin sauri ta
fita bidiyon ta ja shi sama wanda ya biyo bayansa ma su ne a lokacin da Nur ta kwaɗa masa mari tana kuka
tana faɗin,
"Da za ka zamo ajalina a yanzu nan zan iya yafe maka Jaaan kuma har gaban Allah. Amma wallahi!
Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka kashe kanka a kain...ina son ka Jaaan kai ma ka sani wallahi
ina son k..."
Faɗawar da ta yi a jikinsa ya yi daidai da zaburar Minal tsaye, dafe da ƙirjinta da ke dakan kuguden tara-
tara idonta a kafe kan wayar cikin fitar hayyaci tana faɗin,
"Tabbas ba zan iya haƙurin zama da shi ba! Saboda kishin ta zai iya kai ni ƙiyama babu shiri matuƙar abin
da na gani ya tabbata!"
"Innalillahi mene ne kuma ya faru?"
Inna da ke kallo kalaman Minal suka farauto hankalinta da ke kan Tv. Zuwa gare ta. Da sauri ta isa
gabanta da niyyar riƙe ta daidai lokacin da Minal ta wurgar da wayar ta daki bango ta tarwatse ɗaiɗaya.
Tashin hankali wanda ba a saka masa rana, Minal ta shiga ihu da kururuwar faɗin,
"Sai na kashe ta! Wallahi sai na kashe ta!"
Ta yi maganar cikin ƙaraji tamkar wadda aljanu suka taka kanta. Ta shiga fisge-fisge da niyyar ficewa falon
zuwa barin gidan Inna Ade tana rirriƙar ta cikin tashin hankalin ita ma. Don tsabar hana Minal fita har
zaninta ya kwance ta koma daga ita sai buje amma ko kaɗan hakan bai dame ta ba.
Da ƙyar da gumin goshi Inna Ade ta samo kan Minal da kalaman Innalillahi wa inna ilaihirraji'un da
Hasbunallahu wa ni'imal Wakil. Tana yi tana maimaita a bakinta tare da taro Minal har ta zube ƙasa ta fasa
yunƙurin fitar tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar wanda ya saurara.
"Ba zai yiwu ba! Inna ba zai yiwu na zuba ido Minal ta kassara mini rayuwa ba! Wallahi Wallahi sai na kashe
ta! Enough is enough! Abin da ta yi mini ya isa ya isa haka nan Inna! Ba zan lamuci wasa da zuciyar da take
son yi mini ba! Na rantse da Allah ni ce nan zan kashe ta da hannuna!"
"Subhanallah! Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Waɗannan lafuzan ba su yi daɗi ba, ko kaɗan ba furucin
mumini mai imani ba ne."
Maganar Inna Ade kenan a lokacin da ta samu ta rufe ƙofar falon da makullin da ke jiki ta zare makullin a
cikin kwagirinta ta mayar da zanenta ta ɗaura. Tsabar firgici da tashin hankalin da Minal ta saka ta. Hakan
ya sa cikin sauri ta ɗaga waya ta kira Hajiya, babu ɓata lokaci ta sanar da ita ta zo gidan babu lafiya.
Sannan ta katse kiran ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun ta yi tagumi. Don har lokacin ba ta san a kan
wace ce Minal ta haukace ba. Amma jikinta ya ba ta budurwar Jamal ce wadda ta yi wa dukan kawo wuƙa
har Hajiya ta kore ta gidan ita kuma ta dawo da ita hannunta. Tunanin da take yi kenan a ranta saboda
Hajiya ta sanar da ita komai kasanacewar ta ɗauke ta 'yar'uwa kuma abokiyar shawara.
Tabbas yanzu aka fara🧐
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.
D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA TAKWAS.*
Tsawon awa ɗaya Hajiya ta ɗauka kafin ta isa gidan Jamal , amma tsawon lokacin Minal ba ta daina
kukan da take yi ba. Saboda kaiwa maƙura har jakar kayanta ta haɗa Inna Ade tana rarrashin ta a kan ta jira
sai Hajiyar ta zo a san abin yi, amma hakan bai hana ta harhaɗa duk abin da take so a jakar ba. Duk da ba
ta yi wata maganar da ke tona asirin zuciyarta a kan makomar aurenta da Jamal ba. Amma haɗa kayan da
ta yi ya bayyana wa Inna Ade manufarta da shirin barin gidan da take yi. Ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi
ya sa Inna Ade fita daga ɗakin cikin sauri ta buɗe ƙofar. Kallon juna suka yi da Hajiya dukan su fuskokinsu
ɗauke da damuwa. Don kai-tsaye Hajiyar ta nufi ɗakin Minal zuciyarta a tsinke, saboda tunanin da ta zauna
kansa ɗaya ne, a kan cewa Jamal ya ɓarke 'yar mutane saboda ya ji daɗin wuri. Cike da tsoron abin da zai je
ya dawo, gudun hakan ya jawo musu surutun jama'a a gari, idan har zancen ya fita.
Sai dai abin mamaki, tana tura ƙofar ɗakin ta hango Minal tsaye a tsakiyar ɗakin rungume da hannu
tana jijjigar jiki. Wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyar Hajiya, duk da hankalinta bai gama kwanciya ba
musamman da ta hango jakar kayanta a gabanta. Sannan yanayinta ya nuna babu lafiya duba da kiran
gaggawar da Inna Aden ta yi mata.
"Amina, me ke faruwa ne?"
Nan take ta fashe da wani sabon kuka tare da durƙushews ƙasa ta ƙanƙame jakar kayanta tare da ɗora
kanta saman jakar tana ta rero kukan. Shiru Hajiya ta yi na ɗan lokaci kafin ta yi tattaki zuwa wurin ta cikin
sanyin jiki da bugawar ƙurji falfal.
"Ki faɗa mini abin da ya faru, saboda ni uwa ce gare ki ba suruka ba. Kada ki ji kunyar komai ki sanar da
ni ko ma mene ne zan yi maganin abin idan ina da ikon yin hakan."
Ta yi maganar tare da tayar da ita zuwa bakin gado suka zauna. Kallon yatsunta Minal ta dinga yi kafin ta
gama zuƙe-zuƙen majinar kuka ta ce,
"Nur ta dawo, kuma Jamal yana tare da ita yanzu hak..."
"Anya dai Amina gaskiya ce kika faɗa?" Hajiya ta yi maganar fuskarta a cure kuma idonta a kanta cike da
son tabbatarwa.
"Wallahi-wallahi ba ƙarya na yi musu ba! Suna can suna yawo a cikin garin nan har da yin bidiyo kala-kala
suna watsawa a social media."
"To ke wa ya zo miki da wannan labarin?"
"Da idona na gani suna kuka tare da faɗa wa juna kalaman soyayy...."
Ta ƙare maganar cikin wani sabon sautin kukan da ya so bai wa Hajiya dariya, amma dole ta fuske tare
da ƙarfafa kanta tana faɗin, "Ki kwantar da hankalinki, in dai ni ce na haifi Jamal da cikina ba zai taɓa auren
A'isha ba. Ya dai je ya gama bidiyon da kalaman soyayyar ya dawo ya iske ni, don babu inda zan je ina nan
har sai ya dawo gidan nan ya same ni."
Minal ta yi tsam da ranta tana wasa da yatsunta tare da share hawayen idonta da gefen hannunta jefi-
jefi tana ajiyar zuciyar kuka.
"Hmmm! Ni dai Hajiya ina da wata shawara, idan da hali ki hana ta yin wani furuci a bakinta. Saboda ni
dai kam gaskiya na ji tsoron abin da ta faɗa kafin ki zo, don ta tabbatar mini da lalle sai ta kashe ita A'ishar
da ake magana a kanta, kuma ta ce lalle ita ce ajalin ta."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Lalle ire-iren waɗannan maganganun suna da hatsarin gaske Amina!
Don Allah ki daina yin su ba maganganu ba ne masu daɗi, saboda ko ba ki yi abin da kika faɗa ba, idan
wani ya ji zai iya yi miki mummunar fassara, a je garin ɓarin baki ƙaddara ta sa wani abu ya same ta a ce ke
ce. Don haka ki kiyaye faɗar kowace irin maganar da ta fito daga bakinki idan