Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
ƙafa dubu Amina. Don haka komai zan iya yi matuƙar na san za a yi yunƙurin
raba ki da wannan gida. Maryama ma irin sa nake yi mata fatar samu tun ranar da na fara zuwa gidan,
addu'ata kullum ba ta wuce wannan ba. Don haka ki shirya ko kin samu 'yar aikin Maryama tana nan tafe
matuƙar buƙatarmu ta biya dole mu dama."
Shigowar alert a wayarta ya sa Minal ta yi hanzarin faɗin, "Allah Ya taimake mu gabaɗaya, sai kin ga kuɗin
Innarmu." Minal ta ƙare maganar cikin fara'a.
Innarmu ta amsa da Amin suka yi sallama. Baki har kunne ta dinga kallon alert ɗin cike da jin daɗi, ganin
30k lakadan suna kallon juna. Jikinta yana rawa ta tura wa Innarmu rabi ga mai p.o.s ɗin unguwarsu
sannan ta biya bashin katin da MTN suke bin ta cikin zumuɗi. Zuciyarta wasai ta raya wa ranta cewa,
'Haka zan yi ta yi ina cin kuɗi har sai na tara kuɗi masu yawa a account ɗi na kafin ya dawo. Ko babu
komai na fanshe takaicin zaman da zan yi a cikin gidan ni kaɗai. Nur kuma ko ba ya so dole ya bar ta tun da
har suka yi sakacin da na riga ta aurensa.'
Ƙwafa ta yi a ƙarshen zancen zucin saboda ƙudurin abubuwa da yawa a cikin ranta.
****
Jamal da Minal kam jirginsu ya tashi kamar yadda aka tsara, inda ya bar motarsa ga wani abokinsa a
cikin filin jirgin. Mazauni ɗaya suka zauna duk da Minal ta so yin nesa da shi, don ba ta son a gano tafiyarsu
guda ballantana wata hira ta haɗa su. Amma dole ta haƙura saboda hannunta da ya riƙe gam ya ƙi saki, ta
zauna kusa da shi tana cin magani. Lokacin da jirgin zai tashi ma fuskewa ta yi har ya gama daidaita a sama
ba ta bari umarnin zuciyarta ya yi tasiri ba. Don zuciyarta sai wassafa mata ruƙunƙume shi take yi, saboda
yadda take jin jirgin yana wani abu kamar zai faɗo da su ƙasa.
Murmushi kawai ya yi mata, ganin da gaske ƙoƙarin raba kanta da shi take yi, hannunsa da ke cikin nata
ya matse sai da ta yi 'yar ƙara tare da ɗora idanuwanta cikin nasa tsawon mintuna suna kallon juna. Hakan
ya jawo musu shiga cikin wani sabon yanayin da dukan su suka dinga aika wa juna saƙon idon ba tare da
sun sani ba.
"Me ya sa ba kya tausayi na?"
Wani kallo ta yi masa kafin ta amsa masa a kan leɓenta tamkar ba ta son maganar ta ce,
"Tausayi ko?"
Kai ya ɗaga mata yana lumshe ido saboda ƙamshin turarenta sosai ya shiga jikinsa ya saukar masa da
kasala.
"Akwai yiyuwar ki saki komai da ke ranki, saboda na gama tsara komai kuma ina so mu yi rabuwar da za
ki dinga tunawa koyaushe."
Ƙirjinta ya buga dam-dam saboda kalmar rabuwar ba ƙaramin dukan zuciyarta ya yi ba. Amma cikin ko-in-
kula ta ba shi amsa da cewa,
"Da ma can ba ma tare ai."
"Ko?"
Ya tambaya idonsa a kanta yana haɗe fuska, nan take ta diririce saboda tuno ciwonsa da alƙawarin da ta
ɗaukar masa. "Ni..ni..fa ba haka nake nufi b..." Ta yi maganar cikin rawar baki, yayin da ya jefo mata wata
tambayar bayan ya sauke ajiyar zuciya.
"To, me kike nufi?"
"Kawai dai ba na son mutane su zargi akwai wani abu tsakanina da kai a yanzu bayan zumuncin matarka."
"Matata ko?"
"I, kai ma ka sani don haka ana barin halas don kunya. Yanzun ma idan da hali ina son idan muka sauka ka
bar ni na ƙarasa gida, kai ka je sabgoginka."
Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba, amma dole ya furzar da iska mai zafi a bakinsa yana cewa,
"Alƙawarin da na ɗaukar wa Baban kuma fa?"
Harara ta aika masa kafin ta kafe shi da ido ta ce, "Tun da ka kawo ni gida ai shikenan ka sauke."
"Ba shikenan ba gaskiya." Ya yi maganar cikin sauri yana murmushi. Ita ma ta kafe shi da ido tana cewa,
"To me ya rage?"
Ta cillo masa tambayar tana jin wani ɗaci a maƙoshinta. Bai ba ta amsa ba, ganin yanayinta da zuwan
ma'aikatan jirgin wurin. Hannu ta zura ta karɓi kofin ruwan bunun da ake miƙo mata cikin fuskewa. Shi ma
ya karɓi nasa idonsa a kanta ya shiga juya ruwan da cokali kafin ya fara sha yana kallon gefe. Sai da ya zuƙe
ya ajiye kofin ba tare da ta yi wa nata ko kurɓa ɗaya ba. Hakan ya sa ya yi magana cike da basarwa ya ce,
"Malama da kin sha tun kafin ki zubar a jikinki."
Babu musu ta kai bakinta tana kurɓa kamar ba ta so, wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana dubawa, hakan
ya ba ta damar shan rabi ta ajiye saura a saman tiren tangaran ɗin da aka ɗora kofin a kai, hankacif ya yi
hanzarin miƙa mata a lokacin da take ƙoƙarin goge bakinta da hannu. Kallon sa kawai ta yi sannan ta karɓa
tana haɗe rai ta goge bakin tare da gyara zamanta ta lumshe ido.
Fuskarta ya ƙura wa kallo yana jin wani yanayin yana tsirga wa cikin ransa da zuciyarsa, gazar-gazar na
gashin girarta ya ƙura wa kallo kafin ya dawo kan leɓunanta masu matuƙar burge shi.
Ajiyar zuciya kawai ya shiga saukewa wata bayan wata, tare da haɗa cinyoyinsa wuri ɗaya ya matse
saboda jijiyarsa da ke harbawa. Nan take jikinsa ya hau rawa, hannunsa da ke cikin nata ya ɗauki gumi da
karkarwa. Cikin sauri ta buɗe idanuwanta da ke lumshe ta sauke su a kansa, kafin ta dawo da kallonta a
hannun nasa da ke riƙe da nata hannun. A cikin maganar ido ta yi masa tambayar lafiya, amma ya waske
kamar bai fahimci komai ba ya shiga goge gumin da ke tsattsafo masa a goshi da wani hankacif yana ƙara
matse jiki.
Ganin yadda ya takure waje ɗaya hankalinta ya tashi, cikin maraita ta ɗora kanta saman kafaɗarsa tana
faɗin, "Idan har ni ce na jawo ciwon don Allah ka yi haƙuri Jaann."
Ta ƙare maganar cikin muryar kuka saboda fargaban kada ya sake shiga wani halin da ya fi wanda yake
ciki, gudun aman jinin ya biyo baya. Ai kuwa nan take ya fara rawar sanyi, don kalar muryar da ta yi amfani
da ita a cikin taushi; hakan ya jawo wa jarabarsa ƙarfi jikinsa ya hau ciccira tamkar mazari yana gumi.
"Please! Wai mene ne haka don Allah?"
Ta yi maganar a ruɗe cikin sanyin jiki saboda tuno wani lokaci a baya da irin hakan ya faru suna tare. Jikinsa
da ya cure wuri ɗaya ya sa ta yi hanzarin riƙe shi tana faɗin,
"Ni dai ka sha maganinka don Allah dai..."
"Lafiyata ƙalau fa!"
Harara ta aika masa tare da rungume shi a jikinta tana faɗin, "Ni dai don Allah ka sha, wallahi ciwon nan
naka yana ɗaga mini hankali da yawa. Ba na son ka sake yin amai kamar na jiya zan iya kamuwa da wani
ciwon ni ma."
Dole ya ƙarfafa kansa tare da gyara zamansa. Kanta ta ɗora a saman hannunsa tana faɗin, "Ba zan sake ba
Jaaan, ka yafe mini don Allah."
Ta ƙare maganar da hawaye shaa yana sauka a kan hannunsa, zuciyarta cike da tsarguwa a kan cewa
ciwon ne ya taso, kuma ita ce sanadin tashinsa. Dole ya shiga saita kansa da nutsuwarsa wuri ɗaya, tare da
tabbatar mata babu komai ta kwantar da hankalinta. Don kawai ta gano ba asalin ciwon ba ne ya taso
kuma babu wata matsala.
Ta bar jikinsa ta zauna daidai tare da makurewa jikin kujerar tana sharar ƙwalla jefi-jefi. Daga haka barci
ɓarawo ya yi awon gaba da ita, a ƙarshe da daɗin kwanan ya ɗebe ta jikinsa ta langaɓe har jirginsu ya kai
babban Birnin Niamey ba ta san an kai ba.
Sai da jirgin ya zo sauka a filin jirgin ne ta farka, daidai lokacin da ƙirjinta ya shiga bugawa fal-fal.
Idanuwanta ta kai saitin tagar jirgin a nan ta fahimci sun iso ƙasar.
Bayan jirgin ya yi landing aka fara fita ɗaya bayan ɗaya, yayin da Nur take gaba yana bayanta suka sauko
daga jirgin jakarsa saɓe a kafaɗarsa. Mutane suka shiga murna da tarbon 'yan'uwansu, Nur da Jamal kuma
suka shiga kallon-kallo. Motocin taxi suka dinga shawagi a wurin suna ɗaukar mutane, Jamal ya jefa jakarsa
cikin wata taxi da ta iso gabansu yana cewa,
"Mu je malama kada ki ɓata mana lokaci."
Gaban Nur yana faɗuwa ta isa bakin motar tana magana cikin maraicewa ta ce, "Ina tsoron zuwa gida
tare da kai, saboda akwai damuwa idan har aka gano inda na je."
Wani kallo ya yi mata kafin ya rungume hannu ya furzar da iskan bakinsa ya ce, "Babu wata hanyar da za
ta kare ki idan ba wannan ba, saboda haka mu je kawai ni na san abin da zan faɗa musu wanda ba za a ga
laifinki ba."
Ba don ta gamsu ba, ta bi umarninsa ne kawai ta shiga motar ƙirjinta yana bugawa. Har motar ta fice
daga filin jirgin ba ta yi motsin kirki ba, illa hirar Jamal da direban kawai da take sauraro amma ko kaɗan
hankalinta ba ya wurin. Zuciyarta ta tafi hangen taron 'yan biki da jimamin inda ta je. Don ta tabbatar zuwa
lokacin an gama gano ba ta garin idan har an duba ko'ina ba a gan ta ba. Ɗoɗar motar ta nufi Zandar,
saboda shi ne asalin garin mahaifin Nur, kuma inda ta koma a lokacin ta da gudo daga Nigeria.
Next page
35.
Tafiya suke yi ɗoɗar a kan hanyarsu ta zuwa Damagaran, hankalin Nur gabaɗaya ba ya jikinta ta shiga zarar
ido, musamman da ta ga an kama hanyar zuwa family house ɗin Babanta gadan-gadan. Tsumaniyar da ta
shiga yi a bayan da take zaune; hakan ya sa Jamal ya waigo ta bayan, idonsa a kanta ya ce,
"Wai ke lafiyarki kuwa?"
Ba ta ce da shi komai ba amma ta kasa zama daram da ɗuwawunta, sai leƙen hanya ta gaban motar take yi.
Bayan gumin da ta dinga haɗawa ta ko'ina ya shiga karyo mata tana fifita da mayafin rigarta.
"Don Allah ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai faru sai alheri."
Komawa ta yi ta zauna tare da jingina bayanta tana addu'a da fatar leɓunanta bakinta yana muimui,
idonta a rufe tamkar wadda ba ta cikin hayyacin ta. Dariya ta bai wa Jamal, amma ganin yanayin firgicin da
take ciki ya mazge tare da sake cewa,
"Idan kin san akwai damuwa a tsayar ki zauna cikin motar, na ƙarasa gidan ni kaɗai.."
Ido ta yi hanzarin buɗewa tana faɗin, "Mu je kawai, amma duk abin da ya faru ka yi haƙuri kuma don
Allah kada ka bari ciwonka ya tashi."
Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce, "Na shirya ɗaukar komai matuƙar zan wanke ki daga zargi kuma na
cika alƙawarin da na ɗauka."
Daga haka babu wanda ya sake cewa komai, har suka dinga kutsawa a cikin unguwanni bayan sun shiga
tsakiyar garin Damagaran. Da kwatance motar taxi ɗin ta isa bakin wani babban gida mai dogayen katangu,
inda tun kafin su isa suka hango dandazon mutane cike a ƙofar gidan. Daga ita har Jamal ƙirjinsu ya hau
bugawa, saboda ganin mutanen ya tuna musu tarnaƙin da ke gabansu, wanda ko tantama babu a kan cewa
hidimar bikin Nur ne ake yi, duk da ba ta garin kuma ba a san inda ta je ba. Mai taxi da ƙyar ya kutsa cikin
mutanen ya samu wurin tsayawa, amma har bayan minti biyar babu wanda ya fito daga cikin su, saboda
tsoro da fargaba ya raunata zukatansu. Don takaicin ganin mutanen ya tuna masa da ɗacin auren da Nur za
ta yi da wani ta bar shi. Amma sanin ba a bori da sanyin jiki, ya ɓalle murfin motar ya fito cike da jarumta,
sannan ya ce ita ma ta fito ta yi masa iso a wurin iyayenta maza. Sai da ta haɗa hannu ta yi addu'ar kariya
daga abin da zai taɓa ciwon Jamal ta shafa; sannan ta fito ƙirjinta yana bugawa fal-fal ta nufi cikin gidan ko
waige babu.
Jikin motar Jamal ya koma ya jingina bayansa tare da rungume hannu ɗaya a ƙirji, yana ta bubbuga
goshinsa da ɗayan hannun idonsa a rufe. Saboda shawagin mutanen wurin yana ƙara masa tashin hankali
idan ya tuna wai taron auren Nur ne ake yi.
Ita kam kutsawa ta dinga yi kanta a ƙasa ta shige cikin gidan, ba tare da ta nemo wani a cikin iyayenta
maza ba kamar yadda Jamal ya nema. Sai dai shigarta gidan ta ji gwiwowinta sun yi sanyi ƙalau, sannan
jikinta ya yi wa ƙafafuwanta mugun nauyi. Saboda ganin mata cike da gidan ana ta aikin abinci kowa da
abin da yake yi, sannan da kallon mamakin da suke bin ta da shi tamkar a ranar suka fara ganin ta.
Don kamar yadda yake a al'ada irin tasu, a ranar ɗaurin aure mata suna haɗuwa a yi ta yankan albasa da
kayan miyan da za yi girke-girke da su. Sum-sum Nur ta dinga tafiya tamkar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki
tana ƙoƙarin shigewa wani ɗaki. Sai dai tsawar da wata guntuwar tsohuwa ta buga mata daga gefenta; ya
sa ta yi hanzarin tsayawa cak tare da kai kallonta a kan fuskar tsohuwar, bayan ta sha jinin jikinta kafin ta
iso inda take. Babu zato ta ji saukar mari ta ɗayan gefenta. Fuska ta dafe tare da ɗaga kai cike da son ganin
wane ne mai marin. Caraf idonta ya sauka a kan fuskar Salissou yana huci tare da nuna ta da hannu yana
cewa,
"Ni za ki tozarta? Ana shagalin bikin aurenmu ki gudu don kina 'yar iska! To wallahi ko za ki mutu sai an yi
aurena da gawarki babu fashi kamar yadda aka tsar..."
"Dakata Salissou! Ba kai za ka ɗauki mataki ba ka bar ni da ita ni zan yi maganin tsinanniya! Sai ta faɗa
mini gidan uban da ta je ana tsaka da hidimar auren nan! Don yadda na tsane ta daga ita har uwar da ta
haife ta; ba don kai da nake yi wa kallon jikana na gaske ba, babu abin da zai sa na sake shiga shirgin
matsiyaciya. Saboda gaba da ni da ita har abada, matuƙar ba kai ta aura ba; babu ranar da zan ƙaunaci
yarinyar nan! Na tsane ta na tsani uwarta da ta kawo mana ita a cikin zuri'armu, Sulaimaney ma da na
haifa a kansu nake jin tsanar sa a raina. Har ya mutu yana fushi da ni a sanadin wannan muguwar
yariny....yiiiii!"
Ta ƙare maganar cikin kuka saboda tuno rabuwarta da ɗanta Suley, waton mahaifin Nur. Don a kullum
idan ta tashi kukan rashinsa tana jingina hakan da cewa Nur ce sanadin rabuwarsu ta har abada. Shi ya sa
koyaushe tsanar ta ƙaruwa take yi a cikin ranta, don babu ranar da ba ta furta mata kalaman tsinuwa da
muzanci matuƙar za su yi ido biyu. A wannan karon ma laifin da ta aikata ya jawo mata tsanar Nenne ta
dawo sabuwa fil, bayan jihadin rage ta da shalelen jikinta Salissou yake ƙoƙarin yi kodayaushe, wanda
hakan ya jawo buƙatar haɗin aurensa da ita, ko don ta samu sassauci a kan ƙyamar da ake nuna mata, a
cikin gidan da ma zuri'arsu ta Zabarmawa gabaɗaya.
Nanne ta dinga rusa kuka wiwi tana tsine wa Nur, jama'a suka taru a kanta ana ba ta haƙuri tana ƙara
wutar bala'i da faɗanta bakinta yana kumfa. Yayin da wasu ma-ga-isan 'ya'yanta mata suka rufe Nur da
duka ido rufe, tare da faɗin idan ta kashe musu uwa da ɓakinciki sai sun ga bayanta ita ma.
Nan take gida ya hautsine da hargowa, wadda ta jawo hankalin mutanen waje masu hada-hadar shirin
ɗaurin aure. Da ƙyar wani yayan Sulaimanou ya shiga tsakanin Nur da masu dukan ta. Hannunta ya ja suka
shiga wani babban falon gidan, yana mai bayar da umarnin a kira duk wani mai matsayin da ya dace a
tattauna matsalar da shi. 'Ya'yan Nanne suka rirriƙe ta tana yunƙurin zubewa ƙasa tsabar kuka suna kwaso
ta, a haka aka nufi babban falon da ita.
Kiran gaggawar da aka yi wa yayu da ƙannen Sulaimanou ya sa aka tsahirta ɗaurin auren da ake ta shirin
ɗaurawa, gabaɗaya aka ɗunguma zuwa tattaunawar gaggawa da babban yaya ya haɗa.
Yayin da falon ya ɗauki mutane da yawa tsakanin matansu da mazan duka. Tsakiya aka saka Nur kowa da
kalar kallon da yake aika mata, ita ko ta dunƙule ƙasa tana shesshekar kukan da babu sauti sai ajiyar zuciya.
Don tunaninta gabaɗaya yana kan Jamal da irin tarbon wulaƙancin da za a yi masa idan aka gano tare suka
zo. Hakan ya sa ta yi hanzarin zuge jakar da ke maƙale a hamatanta, wadda ta kasa sakin ta duk da kalar
dukan da aka yi mata. Saƙo ta shiga tura masa a gaggauce ta yi typing ɗin, gudun a raba ta da wayar tun
kafin ta gama. Ai kuwa tana tura masa saƙon wani ƙanen Sulaimanou ya fisge wayar tare da kai mata harbi
da ƙafa cikin fushi yana cewa,
"Don ubanki har kin samu damar danna waya a gabanmu! Bayan kin gama tozarta mu a idon duniya?"
Wuƙi-wuƙi ta yi da ido tana haɗe fuska ba tare da ta ce komai ba. A ranta tana faɗin,
'Idan saƙon ya tafi ai kuma shikenan.'
Amma a fili ƙasa ta yi da kanta tana Allah-wadai da baƙar aƙida da al'adar da ta haddasa mata ƙiyayyar
ahalinta. Majinar kuka ta ja a lokacin da Babban yaya ya fara magana tare da jefo mata tambaya.
"Kamar yadda na ce kowa ya zo, ina son a tattauna abin da ya haɗa mu kafin mu yi abin da ke gabanmu.
Amma kafin nan ya dace mu ji wani abu daga bakin ita A'ishar, shin me ya sa ta bar gida ba tare da kowa ya
sani ba? Kuma me ya sa ta dawo gidan bayan mun cire rai da faruwar hakan a nan kusa?"
Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba, sai da wata ƙanwar Sulaimanou ta yi mata tsawa da hargowa a
cikin faɗa sannan ta yi magana tana zuƙe majinar kuka ta ce,
"Ina mai ba ku haƙuri