Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
ta har
lokacin ba ta daina kukan ba.
Tsaye ya yi a kanta hannuwansa zube cikin aljihu ya yi gyaran murya sannan ya ce,
"Ki tashi ki zauna za mu yi magana."
Ga link;
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ICmrsyihZBzLrpXfmM7DyQ
Masarauta group ne ga masu tambayar a saka su group da masu buƙata su ma su yi joining.
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA GOMA.*
Tsawon minti biyu yana tsaye a kanta ba tare da ta motsa ba kuma bata daina kukan ba. Furzar da iska
ya yi daga bakinsa ya gyara tsayuwarsa ya sake cewa,
"Nace ki tashi zamuyi magana, saboda wannan kukan ba shi ne mafita ba, kuma nemo mafitar da kanmu
shi ne abin da ya fi dacewa a wannan lokacin."
Minal ta rage sautin kukanta, saboda sautin da ya yi amfani da shi wurin maganar ya yi nasarar shiga
jikinta. Hakan ya sa ta tashi daga kifen da take ta zauna tana shassheka tare da ƙoƙarin goge hawayen da
suka ɓata mata fuska. Ga idanuwanta sun yi jajir alamun duk wurin ranar da kuka ta yi shi.
"Please! Ki daina kukan nan kuma Ki nutsu magana ce za mu yi mai muhimmanci."
Sai sai da ya ba ta minti daya zuwa biyu ta saita kanta nutsuwarta ta dawo jikinta ta koma zuƙar majinar
kuka. Sannan shi ma ya zauna a kan kujerar da ke fuskantar ta bayan ya rage muryar Tv ya yi gyaran murya
ya ce,
"Ina so ki faɗa mini gaskiya tsakaninki da Allah. A kan ba za ki ɓoye mini gaskiyar duk abin da zan tambaye
ki ba, don ina son mu tattauna da kyau kuma mu shawo kan matsalar ni da ke."
Ba ta ce masa komai ba, amma shirun da ta yi tana kallon yatsun hannunta hakan ya nuna tana jin sa,
kuma a ranta ta saƙa za ta faɗa masa iya abin da ta sani. Amma saboda bai ji furucin bakinta ba hakan ya
sa bai gamsu da shirun da tayi masa ba. Kai-tsaye ya sake jefa mata tambayar kamar yadda ya yi tun a
farko.
"Kin yi alƙawari za ki faɗa mini gaskiya?"
Kai kawai ta ɗaga masa ba tare da ta yi magana ko ta ɗago kai ta kalle shi ba. Hakan ya ƙara masa ƙarfin
amayar da abin da ke cikin bakinsa cikin ƙumaji da takaicin da ke cizon ransa.
"Ke ce babbar ƙawar Nur idan aka cire Amna, kuma 'yar uwarta wadda na sani mafi kusanci da ita. Don
haka kin fi kowa sanin wace ce Nur da yadda matsayina yake a wurin ta. Shin me ya sa ta gudu ta bar ni a
daidai lokacin da na fi buƙatar ta? Kuma mene ne dalilin da ya sa ta haɗa aurena da ke bayan ta san ita
kaɗai ce macen da na yi wa rayuwata tanadi?"
Dam-dam ƙirjin Minal ya buga, ta yadda ba ta san mafarin zuwan wani sabon firgicin da ya farmaki
zuciyarta ba. Saboda tambayoyinsa ba ƙaramin taɓa mata zuciya suka yi ba, kuma sun dagula mata duk
wani lissafin da ke cikin kanta. Don ta sani komai za ta faɗa ba zai taɓa yarda a kan babu sa hannunta cikin
abin da ya faru ba. Amma hakan bai hana ta yin magana cikin ƙarfin hali da jarumta ba.
"Allah shi ne shaidata ko da kowa bai yarda da ni ba. Saboda ban san komai a kan abin da ya faru ba, yadda
ka ji zancen a sama haka ni ma na ji. Kuma ban san me ta tsara ba sai bayan afkuwar abin da ya faru."
Daga haka ta ja bakinta ta tsuke, saboda zuciyarta ta karye wani sabon hawaye mai zafi ya fara bin
fuskarta. Hawayen da ya ƙara lalata wa Jamal sauran kuzarin da ke ransa. Saboda har zucinsa ba ya son
ganin kukan da take yi.
"Yanzu dai a taƙaice kina nufin ba ki san komai a kai ba?"
Shiru ta yi masa don maganarsa ba ta buƙatar maimaicin amsa, a kan abin da ta riga ta yi wa rantsuwa.
Kallo ya ƙura mata tsawon lokaci yana nazarin ta, don zuciyarsa ta yarda da ita a kan babu hannunta a cikin
haɗin auren da guduwar da Nur ta yi. Kuma ya gano hakan tun a kalolin saƙonnnin da ya gani a cikin
wayarta. Waɗanda take tura wa Nur ba tare da ta yi shawara da kowa ba, kuma ba ta san zai iya taɓa
wayar ba ballantana ya gani ya goge tsatsar da zuciyarsa ta yi a kanta. Tana tura mata saƙonnin ne kawai a
duk lokacin da ƙuncin zuciya ya hana ta sukuni.
"Hmmm!" Ajiyar zuciyar da ya sauke kenan yana jingina bayansa jikin kujera, tare zamewa ya kwanta
tsawon mintuna kansa a sama yana nazari.
"Yanzu wane hukunci kika yanke wa zamanmu?"
Ya jefo mata tambayar, wadda ta zo mata a ba zata ba tare da ta shirya wa zuwanta ba. Amma hakan bai
hana ta dakiya cikin nuna ko in kula ba ta ce,
"Komai a hannunka yake."
"Kina nufin duk abin da na zartar hakan ya yi miki?"
Ya yi maganar ƙirjinsa yana bugawa, saboda ko kaɗan ba ya son fushin Hajiya. Sannan kuma ba zai iya
zaman aure da ita ba a bisa ra'ayin kansa. Ita ma ƙirjinta ya buga dam-dam, duk da auren ba ta tabbatar da
ingancinsa ba, amma ko kaɗan furucinsa bai yi mata daɗi ba.
"Ba zan so na ci gaba da cutar da ke a banza ba. Ki faɗa mini kawai ni duk abin da kike so zan bi shi ko da ba
na ra'ayi."
A nan ma shiru ta yi masa ƙirjinta yana bugawa, saboda tuno kalaman Innarmu. Waɗanda take yawan yi
mata a duk lokacin da ta kira ta a waya.
'Duk kika kuskura kika kashe aurenki ba za ki taɓa samun mijin da ya kai Jamal ba. In don Aminu kike borin
yanzu haka an yi masa baiko da wata. Kuma daga ranar da ki bari Jamal ya sake ki ki sauya uwa don ni ban
haɗa komai da ke ba.'
Furutan Innarmu kenan, waɗanda ke raba mata hankali gida biyu. Tana son yi mata biyayya kuma tana jin
takaicin raba ta da Aminu da aka yi ta ƙarfin tsiya.
"Ko kina da ra'ayin zama da ni mu ci gaba da zamanmu a yadda muke kai yanzu?"
Ya dawo da ita daga duniyar nazarin da ya fahimci ta lula. Amma ban da dukan da ƙirjinta yake yi ba ta iya
motsa ko ɗan yatsanta ballantana ta ba shi amsa. Hakan ya sa ta yi masa gum kamar ba ta ji me ya faɗa ba.
Har sai da ya sake yin maganar da ta kasa haƙurin shanyewa ɗacin furutan, sai da ta furzar da abin da ke
cikin bakinta.
"Ga shi ke ba kya so na ballantana ki koya mini son ki na jaraba na gani, ko da zan iya ba ki kaso biyar a
cikin goman son da nake yi wa Nur."
"Ba na so!"
Ta yi maganar a fusace fuskarta a cure, sannan ta miƙe a ƙufule da niyyar barin falon, don ta fahimci
lamarinsa akwai kalolin rainin hankali a ciki.
Caraf ta ji ya damƙo hannunta ta baya, ta yi hanzarin sandarewa wuri ɗaya ba tare da ta motsa ba. Saboda
riƙon da ya yi mata ba ƙaramin jan ranta ya yi ba. Duk da ta so ƙwace hannunta amma ta bi umarnin
zuciyarta ta kasa motsawa, sai bugun numfashinta da ya ƙara wa kansa gudu. Ɓil-ɓil zuciyarta ta shiga
bugawa jikinta ya hau tsuma, yanayin da take ji ya saka ta ɗora hannu ɗayan a ka ta fashe da kuka iya
ƙarfinta tana faɗin,
"Wayyo ni kaina!"
Zumbur ya tashi zaune bayan ya sake ta idonsa a kanta ya ce, "Me kuma na yi miki kike ƙoƙarin tara mini
jama'a? Ko yau ɗin ma za ki jawo maigadi ya bubbuga mana ƙofa ne? To bari ki ji ni babu abin da zan sake
nema daga gare ki. Jiyan ma tsustsayi ne da ban san dalilin da ya sa na yi abin da na yi ba. Amma in dai ni
ne ki kwantar da hankalinki ko wane irin kallo ba zan sake yi miki ba a cikin gidan nan. Idan kika cire kallon
Musulunci shi ma irin wanda shari'a ta tanadar. Ai hakan ya yi miki ko?"
Ya ƙare maganar da wata kalar murya kamar wani sakarai. A ƙoƙarinsa na son kwantar mata da hankali
take-yanke. Saboda tsoron ta cutar da kanta a banza ko kuma ta yi wa kanta wata illar da za ta jawo masa
shiga komar tuhuma. Minal kam ita kaɗai ta san abin da take ji a ranta, hakan ya sa ta kasa daina kukan da
take yi kuma ta ƙi barin wurin kamar yadda ta yi niyya a farko.
Tsam ya miƙe yana sake roƙon ta yi haƙuri ta daina kukan, tun da ba ta son maganar da safe za su ƙarasa
kafin ya fita wurin aiki tun da ta ƙi bari su kai matsayar zancen. Tana kuka ƙasa-ƙasa har ya gama kashe
komai na wuta ya shiga ɗakinsa ya ɗauko wayarta ya ajiye gefenta, sannan ya koma ɗakinsa ya datse ƙofa
zuciyarsa cike da damuwa.
Jikinta yana tsuma ta buɗe wayar ta danna wa Gwaggo Salame kira. Ta yi ƙoƙarin saita kanta wurin magana
amma hakan bai hana Gwaggon gano kukan da ta sha ba tun daga sallamarta. Ranta a ɓace ta yi magana
tun kafin ta ji dalilin kiran da ta yi mata ta rufe ta da faɗa. Sai da ta tsagaita faɗan Minal ta yi magana cikin
sanyin murya ta ce,
"Gwaggo ya ba ni zaɓi a kan zamanm..."
"Damuwar me za ki dinga yi Amina? Bayan Allah ya ba ki dama ki yi rawar gaban hantsi yadda kike so."
"Idan na yi haka na ci amana Gwaggo."
"Tun da har A'isha da kanta ta bar miki shi ya dace ki riƙe da kyau ta yadda ke ma zai so ki kamar yadda
ya so t..."
"Ta ya ya zai so ni Gwaggo? Bayan soyayyarta ta daskare masa zuciya."
"Kina mace amma ki zauna namiji yana gasa miki aya a hannu Amina? To ki sauya takunki, kuma ki iya
hannunki ta yadda zai yaba wa aya zaƙinta ke ma ya san darajarki."
"A'a ba zan iya ba."
Daga haka ta katse wayar, cike da zargin ko dai Gwaggon ta gano abin da ke damun zuciyarta. Ta jima a
wurin zaune tana saƙawa da kwancewa, tare da zance daga ita sai kanta, inda zuciya ke nuna mata hanya
amma tana ƙoƙarin kaucewa. Ta goge busassun hawayenta sannan ta miƙe ta yi nata ɗakin jiri yana ɗibar
ta. Kuma cike da tunanin yadda za ta yi ta sanar da shi ba ta son ya sake ta za ta jira har ranar da Nur za ta
dawo gare shi. Zuwa lokacin za ta goge duk wani laifinta a gun sa har ta dasa masa tausayin ta a ransa.
Sannan kuma Innarmu za ta ji daɗi idan ta ga ta daina bore da ƙoƙarin guje wa zaman auren saboda son
koma wa Aminu.
Amma fahimtar wane ne Jamal da kalolin rainin hankalinsa ya sa ta ga gara yi masa shiru a kan ta sanar
da shi ƙudurinta. Yayin da wata zuciyar ta ba ta shawarar kawai ta sanar da shi don ya san irin zaman da
yake yi da ita. Ko don ya sassauta mata zaren wulaƙancin da yake ja ba tare da ya tausaya wa halin da take
ciki ba.
'Idan abu ya dame ki, ki hana idonki bacci ki kai kukanki ga Allah. Saboda shi kaɗai ne wanda zai warware
damuwarki cikin sauƙi.'
Wata nasihar Gwaggo salame ta faɗo a ranta, hakan ya sa ta nufi toilet ta ɗoro arwala cike da kuzari ta
shimfiɗa sallaya. Don ta gamsu da babu mai maganin abin da ke ranta da matsalarta face shi.
Nafilar da Gwaggon ta koyar da ita ta fara yi kamar yadda ta yi mata bayani, tare da kai kukanta ga Allah a
kan shi ya fi sanin abin da ya fi dacewa ga rayuwarta. Don haka ya zaɓa mata mafi alheri zama da Jamal ko
barin gidansa.
"Idan zama da shi ne alheri Ubangiji ka cusa masa so na ko zai dinga jin tausayi na."
Addu'ar da ta dinga yi tana maimatawa kenan, har ta ci rabin dare sannan ta kwanta cike da tsammanin
ganin sauyi a tattare da shi kamar yadda ita ma za ta sauya masa kalar nata takun. Duk ta sani za ta sha
wuya kafin ta shawo kansa, saboda kafiyarsa da nacinsa a kan Nur da duk abin da ya shafe ta. Da wannan
ƙudurin ta kwana cike da ɗokin safiya ta waye.
Asubar farin ta tashi duk da ba ta gama biyan bashin barcin da take ci ba. Ta shiga gyaran ɗakinta har zuwa
wardrobe ɗin kayanta da akwatunan Nur ta sauya musu mazauni. Sannan ta fito filo ta hau gyara duk da
babu wani abin da ta ɗauke, kasancewar komai yana mazauninsa amma sai da ta ƙara wa komai saiti.
Sannan ta jawo wayarta ta shiga YouTube binciken kalolin breakfast.
Kitchen ta faɗa a gurguje ta shiga fere doya tare da farfasa tarugu tattasai da albasa, a gefe ɗaya kuma ta
ɗora tukunyar dafa doyar bayan ta koma fere Irish cikin sauri.
Cikin lokaci ƙalilan ta fara haɗa yam ball ta soya faka-faka. Sannan ta koma kan miyar ƙwan da za a ci da
zallar farar doyar, wadda ta sha kayan haɗi sai ƙamshi ke tashi. Bayan ta soya wainar ƙwan hatta ruwan
zafin tea sai da suka sha haɗin kayan ƙamshi. Sannan ta ɗebo komai ta jera a falo ta koma kitchen gyaran
inda ta ɓata da wanke kayan da ta yi aiki da su. Zuciyarta cike da ƙaguwa a kan son ganin sa da irin yanayin
da zai tarbi bajintarta. Duk da ta sani abu ne mawuyaci ya ci girkin, amma ta yi don kawai ta auna baiwarta
kamar yadda Gwaggo Salame ta zaburar da ita.
Harabar gidan ta fita, babu ɓata lokaci ta shiga wanke masa mota maigadi yana kallon ta ta gefen ido. A
ransa yana jinjina ƙarfin hali irin Jamal saboda ganin yadda yake ƙoƙarin mayar da aure bauta. Ita kam ko a
jikinta ta wanke motar tas ta goge masa, sannan ta koma sharar harabar gidan cike da ƙumaji ta tattara
sharar, sai a lokacin maigadin ya ce ta bari shi zai kwashe sharar ya zubar.
Tana ƙoƙarin komawa cikin gidan suka yi kiciɓis da juna a bakin falon yana ƙoƙarin fitowa cikin gidan.
Don yana hangen ta ta sama a lokacin da take sharar tsakar gidan. Wannan dalilin ya saka shi fitowa daga
ɗakinsa, saboda ƙamshin girkin da ya cika masa hanci ko kaɗan bai saka shi sha'awar fitowa ba. Sai dai
ganin tana sharar ya ji tausayin ta ya tsirga masa a zuciya. Ya fito da niyyar hana ta amma ganin ta gabansa
ya basar, raɓawa kawai ya yi ta gefenta ya wuce ba tare da ya ce da ita komai ba.
Ita kuma ƙirjinta da ke bugawa tun a lokacin da suka yi ido biyu da juna bai daina ba har ta isa cikin
ɗakinta, dafe da zuciyarta ta jingina bayanta jikin ƙofar ɗakin tare da rufe idanuwanta tana sauke ajiyar
zuciya wata bayan wata.
'Me ke shirin faruwa da ni?'
Tambayar da ta yi wa kanta kenan, tare da saka yatsun hannu ta yi watsi da ƙwallar da ta cika idonta tana
ƙoƙarin gangarowa fuskarta. Wanka ta faɗa cikin kasala bayan zuciyarta da ke ta harbawa tana hasko mata
fuskar Jamal da irin kallon da ya yi mata a lokacin da suka yi ido biyu.
Uhum
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA ƊAYA.*
A gurguje ta kammala wankan ta fito cikin yanayin mutuwar jiki. Tsawon minti biyar tana gaban madubi
ba tare da ta yi abin da ya zaunar da ita ba. Jin motsin rufe ɗakinsa ya sa hankalinta ya dawo jikinta. Cikin
sauri ta goga mai da turare tare da zumbula doguwar riga ta fito jikinta yana tsuma. Da sassarfa ta sauka
ƙasa, gudu-gudu sauri-sauri ta fita harabar gidan cikin bugun zuciya. Saboda hango Jamal yana ƙoƙarin
shiga motarsa alamun fita zai yi.
Dole ta ja ta tsaya rungume da hannu tana kumbura fuska a ranta tana jin takaicin kanta a kan zaman da
ta yi ɗaki ba tare da ta taya masa abin karin ba. Hango ta a tsayen a daidai lokacin yake ƙoƙarin fito da
motar a mazauninta; murmushi kawai ya yi don zuciyarsa ta hasko masa sabon sauyin da ya wanzu gare ta,
a tsakanin dare zuwa safiya.
"Zan je restaurant, daga can na biya shago."
Abin da ya faɗa kenan a lokacin da ya nufi bakin gate, ba tare da ya kai kallonsa gare ta ba. Saboda ba
don ma ya ɗaga murya ba ba za ta yi tsammanin da ita yake maganar ba. Mamaki da tulin haushi suka
dirar mata a ƙoƙon ranta, saboda ganin ta ɓata lokaci wurin haɗa masa abin kari amma ya yi kamar bai san
ta yi ba. Bayan motarsa ta bi da kallo kamar ta bi shi ta roƙe shi don Allah ya dawo ya ci nata girkin. Gudun
sammakonta ya tashi a iska, amma aikin gama ya gama don ya fice fit har maigadi ya kulle ƙofar gate.
Sharr ta ji wani hawaye mai zafi yana bin fuskarta, a fusace ta juya tana danne kukan da yake ƙoƙarin zo
mata, a haka ta isa falo ta faɗa kan kujera tana haki tamkar wadda ta sha gudu.
Ta jima a wurin da tagumi hawaye yana zarya a kan fuskarta, bayan saƙe-saƙen tunani da kwancewar da
take yi. Sannan ta miƙe cike da takaici ta zuba abin karin daidai cikinta, ta fito da sauran ta miƙa wa
maigadi, bayan ta sauya kula. Saboda sai da ta tsaya ta darje sannan ta zaɓi kular da ta fi burge ta ta zuba
wa Jamal abin karin. Da niyyar burge shi kuma don ya ji daɗi ya yaba wa gwanintarta. Sai ga shi ya lalata
mata tsari, tare da ruguza sabon shirin da take ƙoƙarin shiryawa tun a tashin farko. Don sosai ta ci burin
faranta masa ya gano amsar tambayarsa ba tare da ta furta ba.
Bayan ta gama karin ta nufi ɗakinsa kanta