Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 29

78K to 81K   out of 85.8K words

ɗin kuma har ya gama abin da ya kai shi suka fito bai saki hannun nata ba.
Bakin ƙofar ya nufa kai-tsaye bayan ya sake ta, buɗewa ya yi cike da jarumta ya gayyato murmushin dole a
kan fuskarsa, sannan ya shiga yi wa securitys bayani a cikin harshen Turanci yana cewa,

"Wannan shi ne darenmu na farko, tsoro ya sa amaryata yin raki."

Wannan bayanin ya sa suka kalli juna suna murmushi tare da yi masa kalaman ƙarfafa gwiwa cikin raha,
suka bar wurin ya rufe ƙofar yana sauke ajiyar zuciya. Bakin gadon ya koma ya zauna, idonsa a kanta ganin
tana goge aman jinin da ya yi cikin zafin nama. Sai da ta kammala ya kira sunanta ta kalle shi fuska a
kumbure ta ce,
"Me ya sa ka hana ni neman mutanen da za su taimaka mana a kai ka asibiti?"

"Saboda ba na fatar alhakin ciwon ko mutuwata ya rataya a wuyanki. Domin duk abin da ya faru za ki
shiga zargi da tuhumar ke ce sanadi. Mutane za su zargi ke kika aika mini komai duk da babu ruwanki."

Wani kallo ta yi masa cike da mamaki a kan fuskarta ta ce, "Yanzu saboda gudun a zarge ni ya sa ka ƙi bari
a kula da lafiyarka? Hummm!" Ta ƙare maganar tare da sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya sannan ta ɗora
da cewa,

"Ban san me ya sa kake ƙoƙarin yin wasa da lafiyarka ba. Ka taimake ni ka taimaki waɗanda nauyinka ya
rataya a wuyanka ka daina bari lafiyarka tana zama abokiyar wasark...."

"Please! Zo ki kwanta dare ya fara yi, gobe da ƙarfe biyar da rabi jirgin da za mu bi zai tashi."

Kallon sa ta yi ido tsakar ka ganin ko kaɗan ba ya son zancen ciwon ko zuwa ganin likita. Haushi ya sa ba
ta sake cewa komai ba ta nufi kujera ta zauna, kai ta ɗaga sama rungume da hannu bayan ta jingina
bayanta ta rufe ido. Numfashi ta shiga saukewa a hankali saboda wani kalar yanayin da take jin kanta a ciki.

"Ki dawo kan gadon sai kin fi jin daɗin kwanciyar." Banza ta yi da shi ba ta motsa ba kamar yadda ba ta
ce da shi ƙanzil ba. Shi ma ganin ba ta son magana ya sa bai sake cewa komai ba ya koma bakin gadon ya
kwanta tare da rufe nasa idon kamar mai bacci.
Minti biyar a tsakani nannauyan bacci ya yi awon gaba da Nur a kan kujerar. Ya fahimci hakan ne a
lokacin da ya buɗe ido d niyyar satar kallonta kamar yadda yake yi duk bayan minti da sakonni. Saboda
wata nannauyar ajiyar zuciyar da ta sauke alamu ya nuna ta yi nisan bacci. Tsam ya miƙe bayan wasu
mintunan da ya bayar gudun ya taɓa ta ta firgita.
Cancakak ya ɗauke ta sama ta langaɓe masa, a haka ya isa da ita kan gadon ya shimfiɗe ta a hankali
kamar wata jaririya. Abin rufa ya lulluɓa mata tare da rage sanyin Ac kafin ya koma kan kujerar ya zauna.
Kamar yadda ya ga ta yi haka shi ma ya yi zuciyarsa cike da burin baccin ya sace shi ko zai rage nauyin da
yake ji a cikin zuciyarsa. Amma fafur bacci ya ƙi zuwa, har sai da ya saka wayoyinsu a caji sannan ya koma
kan kujerar ya ɗora kansa saman wardrobe ɗin kujerar, ya shiga sauke ajiyar zuciya wata bayan wata
tamkar wanda ya sha gudu. Ya rufe idonsa cike da ƙoƙarin kawar da kansa daga kan abin da yake hasashen
faruwarsa a ransa. Cike da burin ƙarfafa kansa don ya samu damar cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa da
Baban Amina. Kasancewar akwai gajiya tare da shi sannan da jikin ciwo, bayan maganin da ya sha mai saka
bacci a cikin magungunansa, cikin ɗan lokaci ya fara sauke numfashin baccin yana nishi a hankali. Bai farka
ba sai karfe huɗu da rabi na asuba, inda ya fahimci Nur ba ta farka ba har lokacin; ganin ko kwanciya ba ta
juya daga yadda ya ajiye ta tana nan babu dogon motsi.

Toilet ya faɗa ya yi wanka, cike da ƙarfin zuciya da jin daɗin sauƙin da ya samu, sannan ya hau kan sallaya
yana kai kukansa wurin Allah, bayan ya jera nafilolin da ya ji sun ƙara masa kuzari. Ƙarfe biyar saura Nur ta
tashi da salati ɗauke a bakinta, ido ta shiga warawa cike da son tabbatar da abin da ta ga yana ƙoƙarin
faruwa a mafarki. Ganin Jamal a zaune idonsa ƙur a kanta ya sa ta runtse ido cikin sauri ta buɗe saboda
tuno abin da ke gabansu.

Jiki babu kuzari ta miƙe ta yi toilet zuciyarta cike da tunanin Minal da abin ta hango a mafarki. Wanka ta
fara yi sannan ta mayar da kayan da ke jikinta ta fito, sai da ya ga tana ƙoƙarin shimfiɗa ɗankwalinta da
niyyar yin sallah sannan ya tashi daga kan sallayar yana faɗin ta hau kai ta yi sallar. Babu musu ta ƙarasa
sallar tare da guntuwar addu'a ta shafa, ganin yadda yake shiri cikin gaggawa tare da duba agogonsa da ya
mayar a tsintsiyar hannunsa. Ina kwana ta yi masa tare da ya jiki amma ko ɗaya bai amsa ba, a gabanta ya
shiga sauya kayan jikinsa babu shiri ta kawar da kai cike da jin nauyin sa. Shi kam ko a jikinsa, bayan ya
gama ya fara harhaɗa komai da za su buƙata a cikin ledar da ya zo da su, sannan ya bar wanda ba sa so a
wurin yana faɗin,

"Ga rigar da za ki saka nan... ki yi sauri mu tafi lokaci yana tafiya."

Idonta ta kai a kan rigar da ke ajiye bakin gadon. Wadda sai a lokacin ta tuna jakar kayanta da ke wurin
Adamu. Amma ko tana son karɓa babu dama gudun ta ƙara saka wa Jamal mugun zargin da yake yi a
kansa.
Rigar ta ja ta faɗa toilet, cikin sauri, mintuna a tsakani ta fito, ya bi ta da kallo bakinsa a sake tamkar
wani wawa. Saboda shigar a jikinta ta ƙara yi wa rigar kyau matuƙa, fiye da yadda ta burge shi kafin ya siyo.
Amma dole ya basar ganin ta cure fuska alamun ko kallon sa ba ta son yi. Murmushi kawai ya yi mata ya
riga ta fita ɗakin jakarsa saɓe a kafaɗa. Ta biyo shi wayarta a hannu zuciyarta cike da tsoro bayan fargabar
komawa gida da ke danƙare a ranta. Kasancewar yana sauri har ya sallama da ma'aikatan wurin ya ba su
katin ba ta sauko ƙasan ba.
Ko da ta fito cikin girmamawa ta gaisa da ma'aitan sannan ta iske shi bakin mota. Inda ta tarar yana ba ta
wuta babu ɓata lokaci ta buɗe baya ta shige. Bai ce da ita komai ba ya ja motar suka fice hotel ɗin, duk da
duhun safiya amma hakan bai hana shi saita madubi a kan fuskarta ba. Motsi kaɗan sai ya ɗaga kai ya kalle
ta, ita kam dannar wayarta kawai take yi ba ta ma san yana yi ba. Fahimtar hakan ya kasa haƙuri sai da ya
furta.

"Kin yi kyau fa."

Kai ta ɗago ta kalle shi tare da aika masa harara ta ce, "Na gode." Murmushi ya yi saboda garin godiyar har
da kallon sama da ƙasa ya samu. Aljihun motarsa ya buɗe, ya ɗauko kwalin turare ya miƙa mata ba tare da
ya kalle ta ba ya ce,

"Ki shafa."
Ido ta ƙura wa turaren nan take wani farinciki ya mamaye zuciyarta, kafin wani hawaye ya biyo cika mata
ido bayan ta karɓi turaren ta shiga juya shi kafin ta hau fesawa a jikinta ƙwalla tana sauka a kan fuskarta.
Saboda tuno matsayin turaren a wurin ta da girman ƙaunar da take yi masa a ranta.
Har suka kai airport babu wanda ya sake cewa uffan. Sun isa saura minti biyar jirgin ya tashi, babu ɓata
lokaci aka fara cuku-cukun shiga jirgin kafin tashinsa.


*****
Ɓangaren Minal kuma, bacci don yana ɓarawo ya ɗauke ta a ranar. Saboda ƙuncin da take ciki juyi kawai
yake yi kan gado idan ta gaji da gefen da take kwanciya ta sauya wani. Zuciyarta cike da kewar Jamal da
kalolin soyayyarsa mai tsayawa a maƙoshi, bayan tunanin daren da suka raya a kan gadon tamkar babu
mutuwa a cikin duniyarsu ballantana saki a kutso wa rayuwar aurensu.

Asubar farin Innarmu ta yi wa gidan tsinke, don rashin baccin dare ya sa wani nannauyan baccin sace ta
bayan ta gama sallar asuba. Sallamar da Innarmu ta shiga doka mata wata bayan wata ya sa ta farka firgigit
babu shiri. Kamar almara ta hango Innarmu a kanta riƙe da ƙugu tana cewa,

"Yanzu duk wannan masifar da muke ciki ashe ke ba ki hango ta babu abin da ya dame ki!"

"Na damu Innarm..." Minal ta amsa mata cikin jiri da baccin da ke cikin idonta. Innarmu ta kwaɗa mata
wata ƙatuwar harara tana faɗin, "Da ba ki saki baki kina irin wannan baccin mutuwar ba, don alamu ya
nuna ba kya cikin wata damuwa ni kika bari da kwanan takaici. To ba ni saƙon da na ba ki jiya na yi abin da
ya kawo ni na ƙara gaba."
Ta yi maganar a ƙufule tana barin wurin tare da ficewa daga ɗakin ta zauna falo. Ranta a ɓace ta dinga
ƙare wa falon kallo tana wassafa wa ranta gidan ya kusa zama nasu, waton daga Minal sai jikokinta.

Tsam Minal ta yi a ranta, saboda ta gama tattara hankalinta a kan haƙuri da duk yanayin da za ta tsinci
kanta. Ta dogara ga Allah a kan ya yi mata mafita. Amma dole ta bi umarnin Innarmu matuƙar tana so su
rabu lafiya. Jiki babu kuzari ta sauko daga kan gadon jiri yana kwasar ta ta ɗauko ƙullin ledar a inda ta yi
mata mugun ɓoyo, da niyyar sai ta samu dama ta jefar, sai ga shi Innarmu ta wargaza mata tsari.

Ɗaki ta buɗe fuskarta babu yabo babu fallasa ta isa inda Innarmu take zaune tana gaishe ta. Amma ko
kaɗan Innarmu ba ta bi ta kan gaisuwar ba ta wafce ledar tana faɗin,

"Na fahimci ba ki san wahalar da na sha kafin na samu wannan damar ba. Bayan kuɗina da kika sa na yi
asara jiya har dubu goma sha ɗaya da ɗari biyar."

"Asara kuma?" Minal ta yi tambaya cike da mamaki, Innarmu tana buɗe ledar ta ba ta amsa da cewa,
"Zancen kike so!" Sai da ta miƙe ta fara tafiya sannan ta dakata tana cewa,

"Mai adaidaitasahun da ya kawo jiya, shi na tura wa kuɗin gabaɗaya ba tare da na sani ba. Kuma hakan
ya faru ne duk a sanadin tashin hankalin ganin ki gidan a wannan lokacin. Don haka ki sani sai kin biya ni,
don ba zan lalace a kan hidimarki ke kaɗai ba, waɗannan kayan aikin ma ba ki san nawa na kashe kafin a a
ni ba. Saboda haka ficikata ba za ta yi ciwon kai ba, duk lokacin da kika samu kan mijinki ki karɓo mini su a
jimillarsu dubu ashirin da huɗu cas har da ɗari biyar."

Dariya ta so kufce wa Minal babu shiri ta ƙumshe ta tare da bin bayanta tana cewa, "To yanzu ke
Innarmu ina za ki kai kayan a cikin gidan nan?"

"Ke dai biyo ni, duk da ban san kan gidan ba zan yi abin da ya dace. Fatana kawai Allah Ya sa haƙarmu ta
cimma ruwa buƙata ta biya."
Minal ta bi bayanta zungui-zungui har suka sauka ƙasa zuwa farfajiyar gidan. Innarmu ta yi bayan gidan
kai-tsaye cike da burin aiwatar da abin da ya kawo ta, yayin da Minal ta kai kallonta a kan Baba maigadi
cike da tsoro tana faɗin,

"Innarmu kada fa asirinmu ya tonu, saboda Baba mai yana gidan kuma zai iya fahimtar abin da muke
ƙoƙarin aikatawa." Minal ta yi maganar a hankali tamkar raɗa, Innarmu kam ko waige ba ta yi ba ta ci gaba
da nausa kanta tana faɗin,

"Shi ma idan ya samu irin wannan damar a cikin iyalansa so yake yi. Don haka ganin sa ba zai hana ni yin
abin da zai kawo mana mafita ba."

Cike da jarumta Innarmu ta ɗage interlock ɗaya a can ƙuryar bayan gidan ta saka laya biyu a wuri daban-
daban ta danne. Sannan ta ciro ƙullin simintin a jakarta, wanda ta yo guzuri tun daga gida saboda sanin
gidan babu ƙasa. Da kanta ta kwaɓa simintin da ruwan fanfon da ke bayan ɗakunan gidan ta liƙe interlock
ɗin tsaf ta shafe shi. Sannan ta kalli Minal da ke nesa da ita rungume da hannu ta kasa ta tsare gudun
Baban ya yi musu ba zata su ji kunya.
Innarmu ta yafito ta da hannu alamun ta je, jiki babu kuzari ta isa wurin ƙirjinta yana bugawa.

"Kin ga wannan layar? Ki tabbatar kin saka masa ita a cikin filon da yake bacci da shi. Saboda wannan
wata dama ce da zai dinga kwana da ke yana tashi a cikin ransa ko yana so ko ba ya so. Wannan maganin
kuma ki saka masa a cikin abinci kuma ki tabbatar da ya ci a gaban idonki. Daga kin yi haka shi kenan kin
gama komai sai dai mu jira sakamakon abin da zai biyo baya. Amma da yardar Allah babu shi babu kauce
wa umarninki matuƙar kika ƙarasa aiwatar da abin da na ce miki. Don ko uwarsa kika ce ba kya so ya gaishe
ta zai daina, ballantana wata koɗaɗɗiyar banza mara asali."

Minal ta yi shiru kawai tana nazarin maganganun kafin ta ce, "Ban da damuwa da Hajiyarsa Innarmu,
amma tabbas ba na fatar Nur ta sake shiga gabansa kamar yadda ta yi mini a can baya. Don na yi alƙawarin
ko da wuta take yawo sai na raba ta da Jamal tun da tun farko ba ni na ce ta bar mini shi ba."

Cike da jin daɗi Innarmu ta dafa kafaɗarta tana faɗin, "Ma sha Allah, tun da har kika fara gano abin da
nake nusar da ke koyaushe. Ni zan tafi Babanku bai san na fito ba, Allah Ya ba mu sa'arsa a hannu."

Suka fito daga bayan suna ci gaba da tattauna zancen har zuwa bakin gate. Minal ta raka ta tana yi mata
Allah Ya tsare suka yi sallama, bayan ta fice gidan Minal dawo zuciyarta cike da tunanin anya irin agajin da
Innarmu ta kawo wa rayuwar auren nata zai yi alfanu kuwa?
Sanin babu wanda zai ba ta amsa ya sa tana shiga ta kira Hajiya, cikin marairaice murya suka gaisa, daga
nan ta yi shiru saboda nauyin faɗar abin da ya sa ta yi kiran. Fahimtar hakan ya sa Hajiyar ta ce,

"Na faɗa miki idan akwai abin da kike buƙata ki faɗa mini zan sa a kawo miki." Minal ta ji wani daɗi ya
rufe ta cikin fara'a ta ce,

"Da ma babu kuɗi ne a hannuna, shi ne nake so na riƙe wani abu har zuwa lokacin da zai dawo."

"Idan wannan ne kada ki damu, ki turo mini account ɗin ki zan sa a turo miki abin da za ki ɗan lallaɓa
kafin wasu su sake zuw..."

"Babu damuwa Hajiya na gode ƙwarai Allah Ya ƙara girma. Sannan idan da hali don Allah a haɗa ni da
wadda za ta taya ni zama gidan babu daɗi babu motsin kowa."

Hajiya ta yi mata alƙawarin kawo mata wata 'yar aikin da za ta taya ta kwana kafin a ga abin da Allah zai
yi. Sai bayan sun yi sallama ta kashe wayar sannan ta kira Innarmu cike da jin daɗi. Kira ɗaya ta ɗauka tana
faɗin,
"Me kuma ya faru yanzu?"

Murmushi Minal ta yi kafin ta ce, "Innarmu ki tafi wurin Abba mai p.o.s zan tura masa kuɗi yanzu ki karɓa.
Kuma Hajiya ta ce za ta kawo mini 'yark...."

"Ki faɗa mata kina da ƙanne su za ki ɗauko su dinga taya ki aikin gidan."

Innarmu ta yi maganar cikin rawar jiki da zumuɗi, ganin Allah Ya kashe ya ba su, kuma sabuwar dama ta
samu. Minal ta yi 'yar dariya tana faɗin, "A dai bari ta turo 'yar aikin Innarmu ba na son ta gano shirin da
muke yi..."

"Yi mini shiru sakarya! To don ubanki ko ni aka ce na dinga yi miki aikin zan zo na yi ballantana ƙannenki,
to mene a ciki Allah na tuba?"



Caiii😅

Next page

34.

"Innarm..."

Minal ta yi maganar cikin muryar dariya tana rufe baki tare da zaro ido tsabar dariyar da zancen nata ya ba
ta. Amma kafin ta faɗi abin da ta yi niyya Innarmu ta katse ta da cewa,

"Faɗa mini haramun ne ko zunubi ne zan aikata don na zo gidanki na yi miki aiki? Ai da samu a gidan
wasu gara namu gidan, don ke ma kin san aikin da kike sha a gida rabinsa ma ba za ki yi a gidan mijin naki
ba. Amma saboda kin samu gidan arziƙi gidan hutu har ana hangen dacewar nema miki 'yar aikin amma ki
kasa cewa ga ƙanwaki ta isa. Don haka ki sani ni, a wurina ba abin kunya ba ne don na zo gidanki na hunce
tufa ina yi miki aikatau. Sai dai yanzu tun da ba ki yi wannan Hausar ba; ko da 'yar aikin ta zo idan aka
kwana biyu sai kin ƙara da Maryama. Saboda ita ma tana son zama gidan naki ta zauna, ko Allah zai ba ta
wanda zai ɗauke ta a cikin dangin mijinki ko a cikin unguwar taku ta masu kuɗi, idan ita ma ta samu gidan
hutun ai sai mu ƙara hutawa."

Sai da ta dire maganarta tsaf sannan Minal ta yi magana cikin dariya ta ce, "Innarmu kin gama yarda da
kuɗi wallah..."

"To me ake yi da talauci Amina? Ai ko Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama Ya nemi tsari da shi
ballantana mu 'yan baya, waɗanda ko sunanmu babu a cikin ahalari ballantana hadisi. Ko so kike yi yadda
muka ginu cikin talaucin mu yi sakacin da ginin tsiyar zai rushe da mu a cikin sa?"

Dariyar da Minal ta shiga yi babu ƙaƙƙautawa ya sa Innarmu ta sake cewa, "Wallahi laƙada kawas
tsakaninmu da talauci izaja'a

27 / 29