Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
muryarsa ta fito a
ɗashe cikin wayar yana cewa.
"Hajiya Mummy ba zan dawo gida ba sai da tare da matata. Ki ce kowa ya yi tafiyarsa a bar ni zan nemo
Nur da kain..."
"Ni na ce ka dawo, ga ni a cikin gidan naka kai kawai nake jira."
Ta kashe wayar idonta a kan Minal da ta yi tsaye kamar an dasa ice ta kasa motsin kirki. "Ku kwantar da
hankalinku in sha Allahu babu abin da zai faru sai alheri. Aure ne an riga an ɗaura, kuma babu yaji
ballantana saki sai dai mutuwa ta raba da yardar Allah."
Wani kallo Minal ta yi wa Hajiya Mummy kafin ta koma cizon yatsanta tana wassafa yadda za ta bar
gidan a cikin daren. Saboda ta ci alwashin haramta wa kanta Jamal har zuwa lokacin da Nur za ta dawo
gare shi.
Da rarrashi da ban-baki Hajiya ta samu Minal ta yi shiru. Amna tana gefe da tagumi saboda tuno wasu
abubuwan da Nur ta yi yayin hidimar bikin, waɗanda sai a lokacin ta gano ma'anarsu da abin da take nufi.
Shiru ɗakin ya yi ban da ƙarar Ac babu abin da ke motsi idan aka cire kukan tsuntsayen da ke saman
bishiyoyin gidan. Kowa da abin da zuciyarsa take saƙa, duba da yadda suka shiga nutsuwarsu tamkar an
saka musu dokar yin shirun.
Hajiya Mummy ce ta kawar da shirun, ta hanyar duba agogon wayarta sannan ta sake doka wa Jamal kira.
Ranta a mutuƙar ɓace ta sake ba shi umarnin dawowa gida a cikin biyar kacal, saboda ta fahimci idan ba ta
yi masa jan idon gaske ba; rashin tawakkalinsa zai iya karya mata zuciya. Kuma faruwar hakan tamkar
gayyatar wani sabon tashin hankali ne a cikin ahalinta.
Gama wayarsu babu jinawa suka jiyo ƙarar sautin shigowar mota a cikin gidan. Ƙirjin Minal ya shiga
bugawa dam-dam saboda sanin arba da Jamal a lokacin tamkar arangama da mutuwarta ne. Musamman
da ta tuna irin muguwar shaƙar da ya yi mata yana ƙoƙarin aikata lahira.
Zumbur ta miƙe tsaye tana rabon ido a lokacin da takun tafiyar ke ƙarato ɗakin. Buɗe ɗakin da aka yi ya yi
daidai da faɗawarta cikin toilet a sukwane, cike da matsanancin tsoron da ya mamaye mata zuciya.
Ƙasa ta sulale bayan ta rufe toilet ɗin da makulli, jikinta yana rawa ta shiga wani irin marayan kuka mara
sauti. Wanda babu hawaye sai gunjin da yake ƙara yunƙuro mata takaicin ɗaurin talalar da aka yi wa
rayuwarta.
'Me ya sa kika yi mini haka aminiyata?'
Tambayar da ta jefi kanta da ita kenan a zuciya, saboda ta kasa fahimtar dalilin da ya sa Nur ta zaɓi guduwa
ta bar Jamal duk da zazzafar soyayyar da take yi masa.
'Shin Nur ko ta ga wani abu a tattare da ni wanda ke nuna son Jamal nake yi ba tare da na sani ba?'
Zargin da ta yi wa kanta kenan wanda babu tabbacin faruwar hakan, idan saɓanin fahimta ne ya jawo Nur
ta yi mata irin wannan yankan baya.
"Ki dawo ga masoyinki ƙawata, ni ban taɓa ji ina son sa ba."
Zancenta kenan a fili tamakr an faɗa mata idan ta yi maganar Nur za ta ji ta, wanda ta yi a cikin sanyin
murya da raunin zuciya.
Daidai lokacin da ta fara jin sautin Hajiya Mummy a sama tana faɗa. Jikinta ya hau tsuma wata ƙwalla mai
zafi ta fara bin fuskarta. Saboda duk abin da take faɗa da amsar da ya ba ta a cikin kunnuwanta.
"An ɗaura aurenka da Minal ne a bisa wani uzuri mai girma. Don haka ba zan taɓa yafe nonona da ka sha
ba matuƙar ka saki igiyar aurenka da ke kanta. Kuma ka sani A'isha ba matarka ba ce don ba a ɗaura
aurenka da ita ba. Idan ka yi biyayya ga zaɓin da Allah Ya yi maka za ka ga amfanin hakan a gaba. Idan
kuma ka tayar wa da 'yar mutane hankali za ta bar ka saboda ita ma cushen ka aka yi mata ba tare da ta
sani b..."
"Hajiya ba zan taɓa son ta ba. Na faɗa miki ne don ki sani saboda ba zan iya yi mata kallon mace ba. Don
babu abin da zan so a jikinta duk tsawon zaman da za ta yi cikin gidan nan. Bambancinta da namiji a
wurina shigar mata ce kawai..."
Kallon da Hajiyar ta wurga masa ya saka shi miƙewa jiri yana ɗibar sa ya sake cewa, "Gaskiya na faɗa miki,
saboda Nur na tsara rayuwata kuma zan nemo ta a duk inda ta je a faɗin duniyar nan."
D. Auta ce
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*Na ji daɗin yadda kuka karɓi littafin nan tun a farkonsa. Kuma in sha Allahu za ku same shi fiye da yadda
hasashenku ya bayar. Masu neman littafaina ga su kamar haka; ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI, JIKI DA
JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA, MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA, RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE.
BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA, DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA, TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran
su. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar; 08022014771.*
*LAMBA TA BIYU.*
Minal ta jima a bayin ba tare da ta motsa ko ɗan yatsanta ba, saboda duniyar ta gama juya kanta. Ta
yadda bakiɗaya ta kasa fahimtar mene ne mafita, kuma me za ta yi, sannan me za ta aikata?
Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi ya saka ta dawo cikin duniyar hayyacina, tare da sauke nannauyar ajiyar
zuciya. Zumbur ta miƙe tsaye tamkar an tsira mata allura, ta shiga kokawar buɗe ɗakin tare da ƙoƙarin saita
nutsuwarta.
"Kada ki sake ɗaga hankalinki a kan wannan matsala, saboda in sha Allahu haɗinki da shi alheri ne, kuma
matuƙar ina raye ba zan bari Jamal ya yi miki abin da ya ga dama ba."
Zancen Hajiya kenan, a lokacin da na buɗe bayin ta riƙo hannuna ta zaunar da ni a kan gado. "Ki yi haƙuri,
saboda babu wata kalmar da ta wuce haƙurin nan dai duk da ba daɗi ne da shi ba. Mu za mu je gida, sai da
safe idan allah ya kai mu."
Ta miƙe tana dafa kanta tare da jera mata wasu albarkatu cike da tausayin ta a ranta. Ta ƙara yi wa auren
kyakkyawar addu'ar da ko a cikin zuciyar Minal ba ta ji za ta iya amsa ko ɗaya ba.
Tana ƙoƙarin barin wurin Minal ta yi hanzarin riƙo hannunta, sannan ta durƙushe ƙasa gwiwa biyu tana
ƙoƙarin danne kukan da ke son kufce mata. A haka ta yi ƙarfin halin yin magana a cikin sanyin murya ta ce,
"Don Allah idan kin san dalilin da ya sa Nur ta bar mini aurenta ki sanar da n... saboda ba zan taɓa yafe
wa kaina ba matuƙar na shiga tsakiyarta da angonta. Idan kuma har da gaske ta gudu ta bar mini
masoyinta a irin wannan rana da ta jima tana dakon zuwanta; zan ci gaba da tuhumar kaina daga yau har
ranar da na bar duniya. Ki sanar da ni gaskiya don Allah Hajiya, saboda zuciyata ba za ta taɓa nutsuwa ba
matuƙar ban san dalilin da ya sa Nur ta bar mini Jamal ba."
"Hmmmmm!"
Ajiyar zuciyar da Hajiyar ta sauke kenan tare da miƙar da ita tsaye, sannan ta shiga bubbuga bayanta cikin
sigar rarrashi. Saboda a lokacin hawaye sun ba ta haɗin kai ta hanyar zubowa ziii suna layi a kumatunta.
"Ko ma me ya sa ta bar miki shi; ki bar shi a matsayin ya wuce daga yau. Don haka ki karɓi mijinki kuma ki
kwantar masa da hankali ta hanyar da za ku daidaita kanku ba tare da kowa ya sani ba. Saboda Jamal yana
da zafi amma yana da sauƙin kai idan aka biyar da shi ta hanyoyin da yake so."
Jim Hajiyar ta yi tana kallon gefe, yayin da kan Minal yake ƙasa tana shesshekar kuka. Cike da son kawar
da zancen Hajiyar ta sake cewa,
"Dare yana ƙara yi Amina, ki yi haƙuri na manta da abinci a mota Amna za ta kawo miki kafin mu wuce.
Kuma ki saki jiki ki ci kada ki yi wa kanki horon yunwa. In sha Allahu komai zai wuce kuma za ki ji daɗin
zama da shi idan kuka daidaita."
Waɗannan maganganun nata suka sa ta gama sarewa a kan za ta samu amsar tambayar da ta yi mata.
Idonta a kan bayansu suka fice daga ɗakin tare da takun saukarsu a ƙasan benen har zuwa lokacin da ta
daina jin motsinsu. Ta jima a tsaye inda n'take ba ta motsa ba, kafin ta ja ƙafafuwanta n'ta ɗosana
ɗuwawunta a bakin gado. Amna ta dawo da foodflaks a hannunta ta ajiye gabanta cikin sauri ta fice, ba
tare da ta ce da ita komai ba.
Shiru ya ratsa falon sai sautin agogon bango da ke ta aikinsa yana harbawa ƙit-ƙit. Hakan ya sa ta cira kai
tana ƙare masa kallo cike da mamakin ganin adadin lokacin da agogon ya nuna mata. Karfe ɗaya da minti
goma na dare 1:10am, amma ba ta gasgata ba har sai da ta duba ƙaramar wayarta da ke cikin jakar
hannunta, a nan n'ta ga zahirin abin da agogon ya sanar da ita babu ƙarya.
Nan take wani sabon tsoro ya shige ta, saboda ba ta da masaniyar ita kaɗai ce a cikin gidan ko akwai
wasu mutanen. Saboda ko kaɗan ba ta yi zaton ƙiyayyar da Jamal ya nuna mata ta bar shi kwana a cikin
gidan ba. Sai dai tuno akwai maigadin da ke kula da shiga da ficen gidan ta ɗan rage jin tsoron. Amma
tabbas ba ta tunanin zuciyarta za ta samu nutsuwa matuƙar ba ta yi ido biyu da Nur ta amsa mini
tambayoyin da ke zuciyarta ba.
Hakan ya sa ta shiga ƙwala wa lambobinta kira ɗaya bayan ɗaya amma babu wadda n'ta samu. Ajiyar
zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da furzar da wani iska mai zafi daga bakina.
Gadon ta sauko ta rafka tagumi hannu biyu, don ta gaji da zaman har ƙafafuwanta sun fara kumbura.
Saboda ba ta san ta yi zurfi a tunanin da ta lula ba sai da ta sake duba agogon wayarta ta ga 2:30am ƙarfe
biyun dare daidai. Kenan ta kwashe awa ɗaya har da wasu ɗorin mintuna a zaunen ba tare da ta sani ba.
Guntun tsaki ta ja tare da Allah wadai a kan abin da ya faru, musamman da ta tuno maganganun Nur a
lokacin da aka ce ga motocin ɗaurkar amarya sun zo. Da irin diriricewar da ta yi ta faɗa bayin da ke cikin
ɗakinsu har ƙawayensu suna tsokanarta.
Jimawar da ta yi a bayin ya sa Minal bin ta tana faɗin, "Malama ki fito ke fa ake jira!"
Nur ta buɗe bayin tana dariyar yaƙe, domin alamunta duka ya nuna kuka ta yi a cikin bayin, cikin wata
kalar murya sassanya ta ce,
"Ba sai kin kore ni ba, na sani yau za ki yi kwanan farinciki."
"Ke fa wata irin mutum ce wallahi, yanzu rabuwa da ke shi zai sa na yi kwanan farincikin?"
Minal ta jefa mata tambayar tana hararar ta cike da jin haushin abin da ta faɗa. "Kwantas Hajiyata, in sha
Allah daga yau sai kin jima ba ki saka ni cikin idanuwanki ba."
"Ke dai kika sani, kuma komai za ki faɗa ki faɗa, daga yau dai mun sauke nauyinki a kanmu."
Zancen Minal kenan wanda ya saka Nur juyawa tana yi mata wani kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa.
Kamar ta ce wani abu amma ta yi hanzarin tsuke bakinta gum, fuskarta a cure ta bar wurin tana ƙoƙarin
saita kanta a lokacin da mata suka cika ɗakin da guɗa.
Wannan nazarin ya ƙara ɗaukar lokaci kafin Minal ta gano kwanan zaune ta yi. Saboda bacci bai ɗauke ta
ba sai da asuba ta kawo jiki. Kasancewar ana yanayin zafi hakan ya sa ta ƙara bajewa ƙasan tayis tana
nannauyan baccin mai ɗauke da mafarkai kala-kala.
Ba ta tashi farkawa ba sai da ƙarfe 9:11am na safiya. ko shi kiran waya ne ya tayar da ita, a firgice ta
farka tana dube-duben da ya tabbatar mata ba gidansu ba ne, kuma da gaske abin da ya faru ba almara ne.
Cike da ƙuncin zuciya ta nufi bayi, saboda kiran ya katse kuma lokaci ya ƙure mata ba tare da ta yi sallar
asuba ba. A gurguje ta nemo hijabi a cikin wardrobe ɗin kayan Nur, ta miƙa raka'a biyu ta tofa addu'ar da
ba ta san me ta roƙa ba. Allah Ya taimake ta tun kafin a fito da amarya ta yi sallar Isha. Da ba ta yi sallar ba
wataƙila tashin hankalin da ya kunno mata kai ba zai bar ta nutsuwar yin sallar a cikin daren ba.
Ta jima saman sallayar da tagumi kafin wani kiran ya sake shigowa cikin ƙaramar wayarta. Muryar Hajiya
ta jiyo ta yi hanzarin gaishe ta ba tare da ta amsa ina kwanan da take yi mata ba. Saboda ganin ita ce ya
dace ta gaishe ta a matsayinta na babba.
"Ki ƙara haƙuri kin ji! Na aiko miki da abinci ki sauka ƙasa ki karɓa. Kuma ki ƙara haƙuri da yardar Allah
komai zai daidaita."
"Babu komai."
Iya abin da Minal ta faɗa kenan saboda bakinta ya yi nauyin da ba za ta iya cewa komai ba. Sannan ta
sauke wayar idonta a kan abincin da Amna ta kawo mata cikin dare wanda ko buɗewa ba ta yi ba
ballantana ta san mene ne a ciki. Jiki babu kuzari ta miƙe ta ɗauki foodflaks ɗin ta fice, zuciyarta tana jin
babu wani abinci da zai burge ta a daidai lokacin. Saboda ko yunwar ma ba ta ji kuma ba ta jin sha'awar cin
komai. Amma dole ta isa harabar gidan tana wara ido kafin ta hango maigadin gidan yana nufo ta da wani
madaidaicin kwando.
Cikin ladabi ya gaishe ta ita ma ta amsa babu yabo babu fallasa kafin ta karɓi kwandon ta miƙa masa
foodflaks ɗin ta juya ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba. Tana ƙoƙarin shigewa cikin gidan ta ji sautin maigadin
yana cewa,
"Me za a yi da wannan Hajiya?"
"Abinci ne, ka je ka ci."
Amsar da ta bayar kenan ba tare da ta juya ba. Ranta yana tafarfasa ta koma saman ta zauna a kan bedside
tare da rungume hannuwanta a ƙirji tana cizon leɓenta. Hawaye ta shiga gogewa a kan fuskarta saboda
kanta ya yi ƙullewar da ba ta san ta ina za ta fara ba. Saboda tunanin a wane hali saurayinta yake wanda
bai zo a ranta ba sai da safiya ta waye ta tabbatar abin da ya faru babu wasa a ciki. Saɓanin kallon da take
yi wa abin kamar shirin da zai ƙare Nur ta dawo ɗakinta ita ta koma gida.
Zumbur ta miƙe, ta shiga watso kayan Nur da ke cikin wardrobe ɗin ɗakin ta shiga birgima a cikin su.
Saboda tuno lokacin da take jera mata kayan da hannunta cike da farincikin burin aminiyarta ya cika ta auri
wanda take so. Kayan ta shiga runguma tana shinshina ƙamshin turaren Nur da ta feshe mata kayan da shi
yayin jera su.
Wani sabon kuka ya zo mata, wanda ta kwashe lokaci tana juya zantuka a ranta babu mai rarrashin ta.
Kafin ta ji takun tafiyar mutane yana nufo ɗakin da sautin maganganu sama-sama. Amma ko kaɗan hakan
bai saka ta motsawa ba, har aka fara ƙwanƙwasa mata ɗaki ba ta yi magana ba ballantana ta tashi ta buɗe.
Muryar Innarmu ce a gaba kafin ta jiyo muryar gwaggonta Salame, waton ƙanwar Babanta. Da ido kawai
ta bi su, ganin salatin da suke yi a kan hango halin da suka iske ta cikin sa.
"Ahir ɗin ki Amina! Wallahi ki kiyaye ni tun muna shaida jun..."
"Dakata Binta, abin fa sai da rarrashi. Kuma abin da kike so ta bi ba zai biyu ta daɗin rai ba. Don haka ki
bar mini komai ni zan shawo kan matsalar."
Zancen gwaggonta Salame kenan cikin tausasa murya. Sannan ta nufi inda Minal take kwance cikin kayan
Nur, ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye tana faɗin,
"Kwantar da hankalinki Amina, ai ita rayuwar duniya mai sauƙi ce idan aka bi ta a hankali. Yaushe za ki
hana kanki zama lafiya a kan abin da ke ma kina da ikon taimakon kanki da kanki? Don Allah yi shiru share
hawayenki lamarin duniya ba a yi masa gaggawa. A sannu ake bin komai har cim ma nasara cikin iyawar
Allah."
Da waɗannan kalaman Gwaggo Salame ta yi nasarar hana Minal wani kuka, sannan cikin dabara ta zuba
mata abinci ta shiga tsakura duk da shesshekan kukan da take yi jefi-jefi. Amma ko kaɗan ba ta son haɗa
ido da Innarmu, saboda hararar da take wurga mata kamar ta rufe ta da mugun duka. Bayan ta ɗan ci
abincin ta kai ta bayi da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta baro ta, tare da ba ta lokacin da za ta
kammala ta fito tana jiran ta.
Minal ba ta ɓata lokaci a bayin ba, ta yi wankan a gaggauce ta fito. Gwaggo Salame ta miƙa mata ɗaya
daga cikin kayan Nur da ta gama gyara ta mayar wardrobe kamar yadda suke tun farko. Minal kayan ta
kalla sannan ta kawar da kai ƙirjinta yana bugawa ta ce,
"Ba kayana ba ne."
Gwaggon ta matsa kusa da ita cikin ƙarafafa gwiwa ta ce, "Duk abin da kika gani a cikin gidan nan naki
kuma haƙƙinki ne. Don A'isha da ta bar miki mijin har da komai nata ta bar miki, tun daga kan kayan
ɗakinta har zuwa suturarta."
"Gwaggo kayan Nur..."
"Kada ki ce komai saka kayan kawai."
Ta yi hanzarin katse ta saboda ganin tana so ta kawo mata wasa. Minal ta buɗe doguwar rigar lesin ta saka,
wadda ta sha adon aiki mai ɗauke da ɗinki stone work. Sannan gwaggo Salame ta ɗaura mata ɗankwali
tana faɗin,
"Ko ke fa! Kin ga yadda kika yi kyawu kuwa? Ma sha Allah ki tsaya a haka kada na sake ganin kuka a
idonki."
Nur ta yi marau-marau da ido ƙwalla ta cika idonta ta saka gefen hannunta ta share. Sannan ta zuƙe
majinar kukan tana cewa,
"Don Allah Gwaggo ku tausaya mini, wallahi ba zan iya zama a gidan nan ba. Saboda mutane