Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
magana cikin fitar hayyaci
numfashinta yana fisga ta ce,
"Da na ba ki lambarsa gara na hango gawarki a kwance ana jana'izark..."
Wata mahaukaciyar dariya ce ta suɓuce wa Jamal babu shiri, saboda duk abin da suka tattauna yana ji,
kuma tun farkon kiran ya kai kallonsa gare ta cike da son sanin wace ce mai kiran. Fahimtar ƙawance ya
koma rigima ya shiga ɓaɓɓaka mata dariya babu ƙaƙƙautawa. Don tun kallon farko da ya yi wa ƙawayen
nata ya ɗauke kai, cike da mamakin ina ta san su. Amma da yake bai san komai a kanta ba kafin lokacin,
hakan ya sa ya yi tunanin wataƙila da ma can sun san juna. Sai dai fahimtar inda gizon ya yi saƙar ya saka ta
gaba da dariya har sai da ta fashe da kuka babu shiri, tsabar haushin Zulaiha da takaicin dariyar da yake yi
mata.
"Aaa'a fa! Ba za ki cika mini mota da kuka ba, idan kika matsa sai na sauke ki ki nemi abin hawa, don ba
na ciki da kayan ihu."
Minal ta ƙara sautin kukanta tare da yage baki iya ƙarfinta tamkar wadda aka yi wa mugun duka. Rage
gudun motar ya yi, kafin a hankali ya gangara zuwa gefen titi ya tsaya. Tsawon minti biyar yana danna
wayarsa tare da sauraron kukan da take yi ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba. Fahimtar za ta ɓata masa lokaci
Hajiya ta tuhume shi ya kai kallonsa gare ta yana faɗin,
"Wai duk zafin kitso da lallen ne kike yi wa kuka haka?"
Banza ta yi da shi yayin da ta rage kukanta tana kallon gefe zuciyarta a cunkushe ta dinga jan majinar
kuka tana goge hawayen fuskarta da bayan hannunta.
"Ko na mayar da ke gidan lallen idan kin kammala da ƙawayen naki na koma na ɗauko ki?"
Wani kallo ta yi masa hawaye yana bi fuskarta shaa sannan ta kawar da kanta gefe tana faɗin, "Wallahi
duk na sake yin ido biyu da ita sai na nuna mata kuskurent..."
"Me za ki yi mata?"
Ya yi maganar tare da fashewa da wata sabuwar dariya, a ƙufule ta mayar masa da amsa kai-tsaye da
cewa, "Ka rabu da ni Malam! Babu ruwanka da ni."
"Haka ne kuma."
Ya yi maganar cikin ko-in-kula yana mayar da wayarsa caji fuskarsa a haɗe ya tayar da motar sannan ya
sake hawa kan titin. Kallon sa ta yi ta gefen ido kafin ta sake goge ƙwalla tana kallon lallen 'yan yatsunta,
zuciyarta cike da jin haushin kanta. Ganin kishi ya sa ta bayar da kanta a gabansa, sai dai dole ta yi wa
kanta uzuri don ita kaɗai ta san kalar zafin kishinsa da ke kartar zuciyarta.
Har suka isa gidan Hajiya babu wanda ya sake magana, yana parking a harabar gidan ta ɓalle murfin
motar ta fice cikin sauri. Kallo ya bi bayanta da shi kafin ya yi hanzarin dafe jijiyarsa da ke harbawa tsabar
ta fara tayar masa da jaraba.
"Ohh Allah! Wannan yarinya kamar ibilishiya komai ta yi sai ta tsokano ni."
Ya jima a cikin motar yana nazarin kishin da ta nuna tare da zaucewar da ta yi a lokaci ɗaya saboda wata
ta ce tana son shi. 'Kenan so na take yi ko me?'
Ya yi zancen riƙe da haɓa don sosai abin ya ba shi mamaki. Saboda ganin babu wata shaƙuwa ko
fahimtar juna ballantana ita kanta soyayyar a tsakaninsu. "Amma me zai sa ta shiga halin da ta shiga don
kawai wata ta ce tana so na?"
Ya yi wa kansa tambayar a fili kafin ya ɗaga kafaɗa alamun ko a jikinsa ya fice zuciyarsa cike da tunanin
Nur da kewar ta a ransa. Saboda babu wani motsin da zai yi ba tare da ya tuno da ita ba, sai dai kawai ya
dinga basarwa don shi ma ya gama tsayar da zuciyarsa wuri ɗaya. A kan cewa Nur yaudarar sa kawai ta yi
amma babu wani son da ta yi masa shi ne ya ɓata lokacinsa a banza.
Bai shiga cikin gidan ba sai da aka yi sallar magrib, sannan ya isa ciki. Faɗan Hajiya ya tarbe shi tun kafin
ya ƙarasa, da guntuwar sallamarsa a baki ya samu doguwar kujera ya kwanta tare da dunƙulewa wuri ɗaya
tamkar mai jin sanyi. Sosai ya karya wa Hajiya zuciya ta sassauta faɗan da take yi ganin yanayin da ya shigo
falon. Saboda fuskar kukan da ta gani ga Minal zuciyarta ta tabbatar mata shi ne ya yi abin da ya saba. Duk
da ta tambaye ta dalilin kukan amma ta ce mata babu komai, kuma shi ma bai yi mata komai ba.
"Lafiya kake kuwa?"
Hajiya ta yi maganar zuciyarta a tsinke tare da isa inda yake tana taɓa wuyansa. "Jikinka dai babu zafi, ko
dai ni ce kake yi wa dabara don kana son na daina yi maka faɗa a kan abin da ba za ka daina ba ko na ce ka
bari? To ba zan fasa nuna maka ka yi kuskure ba. Amina ko baiwa ce ya kamata a ce ka daina yin abin da zai
ɓata mata rai, idan har ka sa girman haƙƙin da ke rataye a wuyank..."
"Ni fa Hajiya ban yi mata komai ba! Ita ma idan za ta faɗi tsakaninta da Allah ta san babu abin da na yi
mata. Kuma ina zaune kika ce na je na ɗauko ta, sai da na nuna miki a nemi Isah ya ɗauko ta saboda ba na
son ki ga laifina. Amma kika ce dole sai na je. Shikenan ni kullum sai kin ga laifina a kanta, salon ta raina ni
a banza. Komai na yi laifi ne bayan ita ma har yanzu ba ta san darajar auren ba ballantana ta san darajat..."
"Dake ni ubana!"
Hajiya ta yi maganar cikin sanyin murya saboda sosai kalamansa sun shiga zuciyarta. Sanin halinsa ya sa ba
ta son ya fahimci ta yi laushin da zai ƙara kawo mata wani sabon rashin ji.
"Kaina ciwo yake yi Hajiya."
Ba ta ce da shi komai ba ta nufi ɗaki ta ɗauko masa paracetamol da ruwa ta zauna bakin kujerar da yake
kai ta ɓallo maganin tana faɗin,
"Tashi ka sha, kuma idan akwai sauran magungunanka idan ka koma gida ka sha kafin ka yi barci."
Ya tashi babu musu ya karɓi kofin ruwan ya sha maganin sannan ya koma ya kwanta idonsa a rufe.
Zuciyarsa cike da tunanin abin da Nur ta yi masa, a gefe ɗaya kuma a matse yake da son kusantar Minal.
Wannan dalilin ya sa ya yi barcin ƙarya saboda ba ya son Hajiya ta kora shi gidansa.
Minal kuma a ɗakin ma kuka ta sha sosai, saboda takaicin Zulaiha da dariyar da Jamal ya yi mata. Ƙarin
abin haushi kuma tana buɗe data saƙonni suka fara shigowa ta hango sunan Zulaiha yana yawo a saman
notification. Ƙirjinta ya buga dam-dam, saboda ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin buɗe saƙon ta danna mata
ashar. Duba da kalar saƙon da ta turo mata mai cike da rainin hankali da barazana.
_"Ko ki so, ko kada ki so, sai na yi soyayya da shi tun da na gan shi na ji ina son sa. Saboda ni babu ɗa
namijin da zan yi ido biyu da shi na ji ya kwanta mini ba tare da na farauto shi ta ƙarfin tsiya ba. Ban san ki
ba sai a yau, amma zan nemo wace ce ke a cikin kwana uku, sannan ko mijinki ne tun da kika zage ni a
kansa sai na nuna miki na fi ki zama kalar 'yan hau. Don haka ki shirya zuwan ranar da za ki gan ni da shi a
matsayin mata ko budurwarsa."_
Wata sabuwa 🤔
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. A turo shaidar biya ta nan; 08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA ƊAYA.*
Wurgar da wayar Minal ta yi a kan gado cikin ƙunar zuciya. Kafin ta shiga zarya a tsakiyar ɗakin tana
cizon yatsa.
"Ba ki isa ba! Wallahi ba ki isa ki mayar mini da hannun agogo baya ba! Ƙarya kike yi, ba Zulaiha kike ba
ko ke kika koya wa shaiɗan shaiɗanci sai na nuna miki na fi ki tashanci. Don babu macen da ita ta raɓu jikin
Jamal idan ba ni b..."
Boyis ɗin da ta yi kenan bayan ta rarumo wayar ta tura mata saƙon, ƙirjinta yana bugawa babu
ƙaƙƙautawa. Kafin zuciyarta ta shiga aika mata tambayar da ta saka jikinta yin sanyi laƙwas.
'Ta ya ya za ki yi masa iyaka da mata bayan ke ma har yanzu ba ki gama samun mazaunin dindindin ba?'
Hannu ta ɗora a ka tamkar ta fasa ihu, tsabar firgicin da ta shiga ya saka ta ɗimuwa. Da hanzari ta bi
umurnin wata zuciyarta mai nuna mata ta sake fesar da abin da ke cikin ranta da gaggawa. Ta sake mayar
wa da Zulaiha wanu raddi jikinta yana rawa ta ce.
"Idan ke 'yar halas ce ba shegiya ba, ki yi mini kwatancen inda kike a yanzun nan na zo mu yi gaba da
gaba da ke, don ina so ki maimaita abin da kika faɗa a gaban idona."
Ta saki typing ɗin jikinta yana tsuma idonta a kan rubutun tsabar masifar kishin da ke cin zuciyarta.
Ganin shiru minti uku a tsakani Zulaiha ba ta yi mata reply ba ta danna mata kira ta WhatsApp call. A nan
ma ta yi banza ba ta ɗaga ba, duk da alamu ya nuna tana online ɗin. Hakan ya sa Minal ba ta haƙura ba ta
sake danna mata wani kiran, ringing ɗaya a na biyu Zulaiha ta ɗauka. Kafin ta yi magana Minal ta riga ta da
cewa,
"Ashe matsoraciya ce ke ban sani ba? Amma kuma kike taƙama da rashin mutunci!"
Wata kalar dariya Zulaiha ta yi kafin ta ce, "Allah Sarki, shirun da kika ga na yi miki ba tsoro ba ne matar
Jamal. Saboda ja baya ga kowa ya sani shirin faɗa ne. Don haka ki rubuta ki ajiye, in dai da gaske ni Zulaiha
ɗiyar sunnah ce cikin uwa da uba, sai na farauto zuciyar Jamal ya bi ni tamkar bawa da uwagijiyars..."
"Ƙarya kike yi baƙar 'yar iska! Jamal ya fi ƙarfinki don kakan ubank..."
Zulaiha ta sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ta sake cewa, "Allah Sarki Minal, ni fa tausayi kike ba
ni. Yanzun nan na gama jin labarin ashe ke ma ɗin ba wani sonki yake yi ba...amma me ya sa za ki dinga
hauka a kan wanda bai wani damu da ke ba? Shi fa namiji ba a cin alwashi da shi ko da kina da madafun
ikonsa a hannunki. Don haka matuƙar ba ki iya allonki ba, to ki daina kishi a kan wanda ba ki da ikon saka
shi ko ki hana shi. Na ba ki shawara ne saboda ƙawancenmu na farko, abin da zai haɗa mu na biyu kuma
mu zuba ni da ke mu ga wa zai yi nasara Saboda ina kan bakana, ni da ke wanda ya fi iyawa ya ja igiyar
faɗan daidai da ƙarfinsa."
Ƙitt! Zulaiha ta katse kiran ta bar Minal riƙe da wayar a kunne tamkar wadda aka zare wa lakar jiki.
Saboda gwiwowinta sun yi sanyi tun a lokacin da Zulaiha ta ce ta san Jamal ba wani son ta yake yi
ba. Wani hawaye mai zafi ya shiga bin fuskarta, saboda takaici da baƙincikin kalaman Zulaiha.
'Ban san me ya sa na biye ta ta faɗa mini abin da ya ɓata raina a banza ba. Amma kuma to wa ya sanar
da ita ba ya so na? Ko dai gidan lallen ta ji ana labari bayan tafiyata? Tabbas biri ya yi kama da mutum,
daga gidan lallen ne ta ji zancen, idan kuwa haka ne ba zan taɓa yafe wa wadda ta bayar da labarin b...'
Ta yi maganar tana goge ƙwallar da ke fareti a saman kumatunta. "Me ya sa tawa ƙaddarar ta zo a haka?"
Ta sake jefa wa kanta tambayar da ta ji amsar a bakin Hajiya da ke bakin ƙofar ɗaki tana kallon ta. Wadda
ta shigo daidai lokacin da take jefa wa kanta tambayar, cike da tausayin Minal a ranta ta ƙaraso cikin ɗakin
ta zauna bakin gado, tare da dafa kafaɗarta tana cewa,
"Ita rayuwar duniyar nan da kika gan ta kowa da kalar jarabawarsa. Ki ɗauka taki ita ce wannan, kuma in
sha Allah za ta juya duk wani ƙunci da damuwarki zuwa alheri. Yanzu ki yi haƙuri ki goge hawayenki, ki tashi
mu je ki ci abinci akwai magungunan da za ki fara sha daga yau ɗin nan zuwa kwana bakwai. Kuma ki sha
da kyakkyawar niyya don in sha Allahu su ne warakar duk wata damuwar da kike ciki. In dai Jamal ne ki
saka wa ranki tamkar kin mallake shi kin gama. Don Allah ma da ya saukar da cuta sai da ya fara saukar da
magani kafin zuwanta. Sannan in dai ina numfashi babu Jamal babu macen da duk za ta gurɓata mana
farinciki da kwanciyar hankali. Don haka a kodayaushe ki saka wa ranki ke kaɗai ce a wurin Jamal, kuma ke
kaɗai ya mallaka a matsayin babbar kadara rayuwarsa da zuri'arsa gabaɗaya."
Kukan daɗi Minal ta fashe da shi babu shiri, saboda Hajiya ta gama wanke duk wata tsatsar fargaban da
ke cikin zuciyarta. Sannan kuma ta wanke damuwar da Zulaiha ta cusa mata gabaɗaya. Ranta fes ta sauko
daga kan gadon ta duƙa har ƙasa kanta a sunkuye tare da haɗa hannu wuri alamun roƙo tana cewa,
"Na gode, na gode miki sosai Hajiyarmu. Ubangiji Ya jiƙan magabata kuma ya ƙara miki lafiya da nisan
kwana."
Hajiya ta dafa kanta tana murmushi ta ce, "Amin-amin Amina. Ubangiji Ya albarkaci aurenku da zaman
lafiya tare da zuri'a ɗayyiba."
Cike da jin nauyi ta amsa a ciki kafin Hajiya ta miƙar da ita tsaye tana faɗin, "Mu je ki ci abincin sannan ki
sha maganin. Ga shi rigimar Jamal ma ta hana ni sukunin yaba lalle da kitson tun lokacin da kika dawo."
Minal ta yi 'yar dariya ba tare da ta ce komai ba suka fice daga ɗakin.
Hango shi kwance a saman doguwar kujera ya sa ta yi turus bayan ƙirjinta ya buga dam-dam. Ɗan ja baya
ta yi kamar ba za ta shiga falon ba. Nan take Hajiya ta fahimci ba ta son zama falon ne saboda ganin Jamal.
"Tsayuwar me kike yi a nan? Ƙaraso mana."
Hajiya ta yi maganar cikin haɗe rai tare da nuna mata inda za ta zauna a kusa da ita. Tamkar wadda ƙwai
ya fashe wa a ciki ta isa wurin ta zauna idonta a kan Tv ƙirjinta yana bugawa. Plate ɗin tuwon shinkafa
miyar yauɗi ta ja zuwa gabanta tana faɗin,
"Oya cinye mini shi kafin na fito miki da maganin ki sha."
Ta yi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi ɗakinta, Minal ta ƙura abincin kallo tsawon sakonni kafin ta
wanke hannunta a cikin ruwan wata tasa, sannan ta kai hannun cikin abincin ta shiga juya lomar a cikin
miya amma ta kasa kai tuwon a bakinta. Tsabar jin nauyi da kunyar Jamal wanda ya tashi daga kwance
bayan shigewar Hajiya yana aika mata kallon ƙasan ido.
Wani kalar murmushi ya yi a lokacin da ya miƙe tsaye ya nufo ta. Kanta a sunkuye ta ji takunsa kamar zai
fice falon, babu zato ta ji ya cafko ƙirjinta da hannu biyu. Ta zabura babu shiri tana faɗin,
"Innalillahi!"
Bai bi ta kan buge masa hannuwan da take yi ba ya ranƙwafa daidai fuskarta ya kai sajensa gefen fuskar
yana goga mata gashin sajen har zuwa gemunsa. Sannan hannuwansa a ƙirjin yana murza tare da yin wani
kalar nishin da ya hautsina ta cikin ɗan lokaci.
Motsin Hajiya da buɗe ƙofar ɗakinta ya sa ya yi hanzarin sakin ta ya nufi hanyar fita cikin sassarfa. Da
mamaki ta ƙaraso cikin falon tana cewa,
"Kai da ba ka da lafiya ina kuma za ka je?"
"Masallaci zan tafi na yi Isha na dawo."
Iya abin da ya faɗa kenan cikin wata kalar murya, ba tare da ya juyo ba saboda jijiyarsa da ke miƙe, sannan
kuma ba ya son ta fahimci halin da yake ciki. Ficewarsa ya sa ta dawo da kallonta a kan Minal tana faɗin,
"Ba dai ko loma ɗaya ba ki ci ba tun da na bar ki?"
Minal ta yi ƙoƙarin saita nutsuwarta tana sosa kanta da hannu ɗaya ta fara kai lomar abincin a bakinta.
Zuciyarta sai zillo take yi tsabar tsantsar jarabar da Jamal ya jefa a ciki ba tare da ta shirya ba. Yamm!
Jikinta ya hau tsuma tana haɗiyar loma da ƙyar tamkar mau cin magani.
"Ikon Allah! Yanzu cin abincin ne har da gumi Amina?"
Cikin sauri Minal ta girgiza kai tana zarar ido tsabar kunya da yanayin da ke son tona mata asiri.
"Ni na ga duk kin firgice a lokaci ɗaya, ko ya yi miki wani abin ne bayan tafiyata?"
Ta sake girgiza kai tana ƙoƙarin yin magana ta sarƙe, babu shiri ta fara tari babu ƙaƙƙautawa. Hajiya ta
ruɗe ta shiga bubbuga mata baya tana faɗin 'Sannu' tare da taimaka mata ta sha ruwa har aka samu tarin
ya lafa mata.
"Ki ci a hankali kada ki sake sarƙewa."
Ta yi maganar cikin kulawa tare da barin wurin ta ɗauko kofi ta dawo ta zauna. Tsawon minti goma babu
wanda ya yi magana a tsakaninsu, har Minal ta gama cin tuwon ta kwashe kayan ta kai kitchen, sannan ta
dawo bayan ta wanke hannunta.
Kofin maganin infection ta miƙa mata, wanda ta cika taf da ruwan maganin sai ƙamshinsa ke tashi. Babu
musu ta karɓa ta shanye a lokacin ɗaya, zuciyarta cike da niyyar samun warakar matsalolin da ke
tsakaninta da Jamal. Don har ranta ta nutsu da cewa kyakkyawan albishirin Hajiya zai yi tasiri ga rayuwarta
cikin ɗan lokaci. Ganin yadda ya