Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
shauƙi, kuma karo na
farko kenan da ta ji a ranta tana sha'awar ya kasance ta.
Sai da aka yi sallar magrib sannan ta daina tunane-tunanen da ke ranta ta miƙe ta ɗoro alwala. Tana kan
sallaya har aka yi Isha ta gabatar da ita sannan ta fito falo. Daidai lokacin da Hajiya ta fito daga ɗakinta ita
ma bayan ta gama sallar da nufin cin abincin dare. Minal isa gabanta cikin sauri ta durƙusa har ƙasa ta
gaishe ta. Hajiya ta dafa kanta daga tsayen tana sa mata albarka cike da jin daɗi ita tana faɗin,
"Amin Hajiya."
kafin Hajiyar ta ɗora tambayar, "Kin ci abinci kuwa?" Minal ta girgiza tare da miƙewa tana faɗin,
"Bari na fara kawo miki naki yanzun nan."
Ta yi hanzarin juyawa zuwa kitchen, sai da ta haɗo mata komai a kan tire har da ruwa, sannan ta kawo
gabanta ta ajiye cike da jin daɗi ta dinga saka mata albarka. Ta koma ita ma ta zubo nata tuwon kaɗan a
plate, saboda nauyin Hajiyar da take ji ba zai bari ta saki ciki ta kwashi tuwon yadda take so ba, duk da ya
kasance best food ɗin ta waton tuwon shinkafa miyar taushe. Ganin tuwon kaɗan Hajiya ta yi murmushi
kawai ammaba ta ce mata komai ba. Suna ta kallon tashar Arewa24 suna cin abincin har Minal ta cinye
nata ta miƙe da nufin kai plate kitchen ta wanke. Hajiya ta kalle ta cike da kulawa tana faɗin,
"Da ma jira nake yi ki gama cinyewa na ƙara miki wani. Oya kawo plate na zuba miki wannan abincin da
kika zubo ko yaron goye ba zai ƙosar ba."
Cike da jin kunya Minal ta rufe ido tana faɗin, "Na ƙoshi fa.."
"Ba wani ƙoshi da kika yi, kin ga abincin nan sai kin cinye shi duka, loma ɗaya ban ce ki bar mini ba."
Minal ta zura hannu tana ƙoƙarin karɓar plate ɗin suka jiyo ƙarar buɗe gate da shigowar mota cikin gidan.
Ƙirjin Minal ya buga dam-dam, saboda ko ba a faɗa jikinta ya ba ta Jamal ne ya dawo gidan.
Hajiya ta kalli ƙofa bayan ta haɗe rai ta ce, "Waton ya rantse sai ya dawo gidan don ya saka bakina surutu
ko! To ai shikenan ya zo ga ni ina jiran sa...ina za ki je ke kuma? Dawo ki zauna ki ci abincinki. Ai wannan
karon bai isa ya yi miki komai ba, matuƙar ina wurin nan zaune."
Ta yi maganar idonta a kan Amina da ke ƙoƙarin barin falon ta shige ɗaki. Jiki babu kuzari ta dawo falon a
ɗarare ta zauna ƙirjinta yana bugawa. Shigowar Jamal da wani mai aikin Hajiya ya sa muka bi su da kallo,
saboda ganin suna shigowa da akwatunan lefen Nur ɗaya bayan ɗaya har ƙwara ƙwara bakwai kamar
yadda suke a saiti.
Fuska babu yabo babu fallasa bayan fitar mai aikin Hajiya ta kalli Jamal tana faɗin,
"Shigar mata da su ɗakin Amna!"
Kallon ta ya yi cikin sauri baki a sake kamar ya ce wani abu, tuno abin da ke ransa da wayon da yake son
yi wa Hajiyar; cikin hanzari ya saita kansa ya miƙe yana gyara zaman wuyan rigarsa. Kamar ya yi dariya
amma ya fuske ya fara jan akwatunan da ɗaiɗaya yana kaiwa har ya gama. Fuskarsa a washe ya kalli Hajiya
da ke fuske bayan ya kalli Minal ita ma fuskarta a haɗe ya ce,
"Ki ce ta gaishe ni Hajiya."
Banza Hajiyar ta yi masa tsawon sakonni kafin ta ce, "Dole ne sai ta gaishe ka?"
"Yanzu fisabilillahi ban cancanci ta gaishe ni ba Hajiya? Wai don Allah me na yi da kuke sauya mini fuska
Kamar na yi wani ƙatoton laifi?"
Shi ma ya jefo mata wasu tambayoyin yana 'yar dariya. Saboda ya fahimci sai biyo da siyasa ko zai samu
ciyo kan Hajiyar har ta saurare shi. Ganin ta yi masa banza tana ƙoƙarin haɗa kan kayan abincin da ke
gabanta, ya sake mayar da kallonsa a kan Minal da idonta suke a kan Tv. Alamun kallon ya tafi da ita, amma
a zahiri hankalinta gabaɗaya yana kansa da duk wani motsinsa.
Kan kujerar ya sauko ya yi durƙuso gaban Hajiyar gwiwa biyu ya haɗa hannuwansa wuri ɗaya alamun
roƙo ya ce,
"Na tuba ki yafe ni don Allah Hajiya Mummy. Fushinki gare ni tsaf zai iya jefa ni cikin gararin rayuwa. Idan
kuma so ake yi mutum ya bi duniya ai sai ya bi tun da ba a son s..."
Ya miƙe da nufin barin wurin fuska a haɗe, yayin da ta yi hanzarin cafko ƙafar wandonsa tare da kai masa
duka a ƙafar da murfin kula tana faɗin,
"Ka bi duniyar, da ma ka saba bin 'ya'yanta don ka bi ta ai ba wani abu ba ne. Sannan kuma ko na yafe
maka ka sake kyarar Amina ko yi mata wani abu mara daɗi za mu ƙara hawa sama da kai."
"Ai na tuba yanzu kuma na gane kuskurena Hajiyarmu. A ba ni abinci idan na ƙoshi sai na ƙara neman
wata yafiyar."
Kallon uku kwabo ta yi masa mai ɗauke da harara sannan ta ce, "Mayya ta dafa fa, na san kuma ba za ka
iya ci b.."
"Zan ci, a ba ni a hakan tun da kina so na ci ai dole na ci."
Babu shiri ta yi 'yar dariya tana faɗin, "Oh! Ni ce ma nake so ka ci ashe? To na fasa son ka bar shi kawai."
"Ni nake so a ba ni da kaina Hajiyarm...Ke tashi ki je ki kawo mini kin wani share mutum kamar ba san da
shi b..."
Irin kallon da Hajiyar ta wurga masa ne ya fara sassauta murya yana sosa kai saboda ko kaɗan ba ya son
shirinsa ya lalace.
Minti uku a tsakani bayan Hajiya ta gama nazarí sannan ta ce, "Amina kawo masa abincin, kuma kaɗan
za ki zuba masa abincin mayu a ci da yawa."
Murmushi Aminar ta yi sannan ta bar wurin da plate ɗin da ta ci, cikin rashin sani ta juya juya bom-bom
saboda saurin da take yi. Babu shiri ya bi ta da wani kallo har sai da Hajiya ta yi gyaran murya, sannan ya
ankara da abin da yake yi ya koma sosa ƙeya yana faɗin,
"Ni mamaki yarinyar can take ba ni Hajiya. Shikenan ta raina ni kin ga irin kallon rainin da ta yi mini har
da su gwalo?"
"Duk abin da ta yi maka kai ka ja."
Daga haka kowa ya yi shiru har Aminar ta dawo ɗauke da tuwon ta ajiye gabansa. Babu ɓata lokaci ta
shiga kwashe kayan da Hajiya ta ci abinci ta kai kitchen ta wanke, sannan ta nufi ɗakin Amna da nufin yin
kallo a wayarta. Saboda tsawon kwanaki babu data a wayarta kuma babu kati, hatta bonus da take mora
shi ma ya ƙare. Sannan account ɗin ta babu ko ficika sai kwabo 31 da ke zaman daɓaro mara amfani.
Ta shiga neman wayar a cikin ɗaki lungu da saƙo ba ta gan ta ba, tsabar nema har inda Jamal ya ajiye
akwati ta duba ba ta gani ba. Kuma iya sanin ta Jamal ne kaɗai ya shiga ɗakin kuma zuciyarta ta ba ta tsaf
zai iya ɗaukar ta kamar yadda ya taɓa yi mata.
Cikin sauri ta fito falon da nufin ta ce ya ba ta wayar, saboda da ita take rage kaɗaici a wasu lokutan. Sai
dai daga shi har Hajiyar ba sa falon, hannu ta ɗora a ka cikin rawar jiki ta fice harabar gidan saboda sautin
tashin motarsa da ta jiyo.
Bakin motar ta isa a daidai lokacin da yake ƙoƙarin gyara zaman motar da sassarfa ta da leƙa shi tana
faɗin,
"Wayata za ka ba ni."
"Ok, buɗe ki shigo ki karɓa."
Ya yi maganar cikin ko-in-kula yana haɗe fuska. Hakan ya sa ba ta kawo komai a ranta ba ta buɗe murfin ta
zauna tare da faɗin,
"Ba ni na koma sauri nake y..."
Jawo ƙofar da ta ga ya yi da sauri tare da kwanto mata a jiki ya mayar da gilasai ruf ya rufe ko'ina jikinta
ya ɗauki rawa. Cikin tashin hankali ta shiga magana idonta a zare ta sake cewa,
"Ka...ka.. ba ni wayar na ce maka.. sauri nake yi ba na son Hajiya ta neme ni ba ta gan ni ba..ban ma faɗa
mata ba da zan fito."
Banza ya yi da ita tana ta surutun yana ƙoƙarin cinna kan motar waje kamar bai san tana yi ba. "Malam
ina za ka kai ni a cikin daren nan? Ko ba ka ji ina zancen ka ba ni wayata ba?" Ta ƙare maganar a ruɗe tana
kallon gefe da gefen titi cikin firgici kamar wadda aka sato.
"Idan na ji kuma sai me?" Ya Yi maganar a fusace, ita ma ta amsa masa cikin isa ta ce,
"Sai ka ba ni tun da ba kai ka saya mini ba!"
Wani kallo ya yi mata kafin ya yi guntun tsaki ya ce, "A Kan wannan jahilar wayar kike mini surutan banza
a sama?"
"E ɗin, kuma idan ma daƙiƙiya ce mutum bai saya mini ba ballantana ya yi iko da ita."
"Ni kike ɗaga wa murya?" Ya yi tambayar yana nuna kansa tare da ƙure ta da kallo alamun ta gama kai shi
bango. Kuma sai sharara gudu yake yi a saman titi kamar wanda zai tashi sama.
To fa! 😆
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan
08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA TARA.*
Wani masifaffen tsoro ya kama Minal cikin ruɗewa ta shiga haɗu hannu wuri ɗaya hawaye yana fareti a
kan fuskarta ta ce,
"Don Allah, don girman Ubangiji ka mayar da ni inda ka ɗauko ni, tun kafin Hajiya ta yi nema na ba ta
gan ni ba."
Banza ya yi mata ba tare da ya ce da ita kanzil ba, ya ci gaba da tuƙinsa fuska a cure tamkar bai taɓa yin
dariya ba. Hakan ya sa ita ma ta haɗe rai cike da jin haushin ya ƙi kula ta ballantana ya ji roƙon da take yi
masa, ya mayar da ita kada Hajiya ta ga laifinta.
A tsure ta shiga kallon titi tana shesshekar kuka zuciyarta cike da tunanin inda zai kai ta. Har ya shiga
harabar wani wuri mai ƙaton gate. Ƙirjinta ne ya buga dam-dam, a lokacin da ta ɗaga kai ta kai kallonta gan
sunan da ke saman allon bangon ginin. Inda aka rubuta... HOTEL, da hanzari ta dawo da kallonta gare shi a
firgice ta yi magana cike da tsoro ta ce,
"Me kake nufi da ni da za ka kawo ni hotel? Ko an faɗa maka ni 'yar iska ce za ka kawo ni matattararku ta
'yan bariki?"
Wani kallo ya yi mata mai ɗauke da dariya sannan ya gyara parking yana faɗin,
"So nake ke ma ki iskance kamar yadda mu ma muke gogaggun 'yan barikin da kika san..."
"Wallahi ni kam ba Zan taɓa lalacewa ba, ku dai da kuka ɗauki duniyar wata tsiya ku ci gaba da abin da
kuka sa gaba, da ma can kowa da kabarinsa kuma babu wanda za a saka tare da wani, ballantana laifin
wani ya shafi wani."
"Ke dai kika san..."
Kafin ya dire zancensa kiran Hajiya ya shigo wayarsa, da hanzari ya dafe kansa yana faɗin,
"Ya Salaam! Ashe na manta ban kashe wayar ba Hajiya ta kira"
Wani sanyin daɗi ya ratsa mata a zuciyata, jiki babu kuzari ya ɗauki wayar kamar ba ya so yana haɗe rai,
kuma tun kafin ya ji abin da Hajiyar za ta faɗa ya yi hanzarin faɗin,
"Ga mu nan zuwa yanzun nan Hajiya, da ma ita ce ta roƙe ni don Allah na kawo ta shopping...na so ta bari
sai gobe ta matsa sai da na kawo t...to...ki yi haƙuri yanzu zan kawo t.. ."
Ƙit Hajiya ta katse kiran saboda ƙufular da ta yi a kan zancensa. Don ta sani sarai tsarinsa ne Minal ba za
ta ce ya fita da ita a cikin daren ba. Tsaki ya ja mai ƙarfi tare da kai kallonsa gare ta cikin harara ya ce,
"Idan ma addu'a kika yi mini shi ya sa na manta ban kashe wayar ba har Hajiya ta kira ni, to ba ta ci ba.
Don tun da na yi niyyar taɓa ki sai na aiwatar da ƙudurina ko ba yau b..."
"Allah ma ba zai ba ka sa'ar cutar da ni ba."
Ta ƙare maganar tana murguɗa masa baki, wani kallo ya yi mata alamun zan koya miki hankali. Kafin ya
koma motar ya rufe ko'ina ruf ya janyo ta jikinsa tana masifa yana abin da zuciya take ta kwaɗaita masa a
kanta, kafin ya yi magana cikin izza da gadara ya ce,
"Da ma kin tsaya, don ƙauyancinki ba zai hana ni yin abin da na ga dama ba."
Ta shiga kai masa duka tana ture shi saboda ƙirjinta da ya kai wa cafka hannu biyu yana murza tare da
wani kalar nishin da bai san yana yi ba. Babu zato ta ji ya cafko bakinta cikin kiɗima ta ƙara zabura tana kai
masa duka da hannuwanta amma hakan bai hana shi yi wa bakinta tsotson lollipop ba. Duk da mutsu-
mutsun da take yi, sai da ya ga dama don kansa sannan ya sake ta, ya koma dafe jijiyarsa tare da mayar da
numfashi cikin sauri tsabar fita daga hayyacin da ya yi cikin ɗan lokaci.
Kuka ta fashe tana faman goge bakinta da take jin kamar babu leɓuna a jikinsa. Kafin ta koma tofar da
yawu tana faɗin,
"Mayen banza kawai."
Motar ya tayar fuskarsa a haɗe yana faɗin, "ki gode wa Allah kuma ki gode mini kin samu har na haɗa
bakina da naki. Sannan ba na son kayan ƙazanta ki daina yi mini tofe-tofen yawu a cikin mota. Ni ma
tsautsayi ne ya aike ni ba don ina so na yi ba. In ban da ƙaddara ma me zan yi da mace irin ki baƙauyiya a
komai sai kin nuna halinki na ƙauyanci, ke kullum babu ranar da za ki waye...mtssss!"
Ya yi maganar tare da hawa kan titi aguje tamkar an koro shi. Saboda kiran wayarsa da Hajiya ta ke ta yi
wani bayan wani babu ƙaƙƙautawa. Sanin dalilin kiran nata ya sa ya ƙi ɗauka sai dai ya ƙara ƙaimin gudun
da yake yi.
Minal kam wani kallon banza ta yi masa ba tare da ta sake cewa komai ba, amma ta daina tofin yawun
kamar yadda ya ba ta umarni, saboda har cikin ranta tsoron sa take ji. Gudun ya ƙara yi mata wani rashin
mutuncin don ta fahimci babu ƙiren kunya a cikin idanuwansa.
Sai da ya tsaya wani Shopping Mall ya saya mata kayan maƙulashe, sannan suka isa gidan Hajiyar misalin
ƙarfe goma da rabi na dare. Bakin ƙofar gidan ya tsaya saboda tsoron ya shiga ta rufe sa da faɗa.
"Ga shi na kawo ki, sai ki san yadda za ki ƙarata idan kika shiga ciki don ni babu ruwana."
Minal ta buga masa wata jar harara tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ta fice ya damƙo hannunta ya sake cewa,
"Ko da wasa kika ce mata ni ne na tafi da ke sai na nuna miki ba a mini ƙarya. Don haka ga ledar abin da
kika sa na raka ki siye nan, a ci daɗi lafiya."
Cike da mamaki ta bi shi da kallo a ranta tana jinjina ƙarfin hali irin nasa da juya zance zuwa yadda yake
so, tamkar mai bishiyar aljanu a saman kansa. Idan ban da haka ta ya ya zai sace ta tana masa magiyar ya
mayar da ita, amma kuma ya dawo faɗin raka ta ya yi?
"Hummmm!"
Iya abin da ta faɗa kenan saboda ya gama ɗaure ta da jijiyoyi. Don ta san dole ne sai Hajiya ta yi mata
faɗan me ya sa ta bi shi ba tare da ta sanar da ita ba. Bai kashe hasken motar ba har ta kai bakin ƙaramar
ƙofar shiga gidan, sannan ya shiga buga mata horn ɗii! Saboda tuno wayarta da ke hannunsa. Kamar ta
juya amma sanin rainin hankalinsa ya sa ta shige gidan, ba tare da ta bi umarnin zuciyarta da ke ba ta
shawarar komawa ba.
Kiciɓis ta yi da maigadi yana ƙoƙarin buɗe gate cike da zaton gidan Jamal zai shiga da motar shi ya sa
yake zuba horn. Kai-tsaye ta shige cikin gidan ta bar su suna magana, saboda ganin zai buɗe masa gate ya
fito daga motar yana miƙa masa wayar Minal, tare da sanar shi gidansa zai koma ba zai samu damar shiga
gidan ba. Suka yi sallama tare da addu'ar Allah Ya tashe su lafiya sannan ya faɗa motarsa ya juya zuwa
gidansa. Zuciyarsa cike da tunanin yadda zai kwashe da Hajiya idan safiya ta waye ya shiga yi mata ina
kwana.
Minal kam jiki babu kuzari ta tsaya bakin falon tana muzurai, tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ta
murɗa ƙofar, zuciyarta cike da roƙon Allah Ya sa Hajiyar ba ta cikin falon don ta saɗaɗa ta shige ɗakin Amna
ba tare da ta gan ta ba.
Sai dai tana jefa ƙafarta suka yi ido biyu da juna, gabanta ya ƙire ya faɗi jikinta ya ɗauki rawa. Sum-sum
take taku kanta a ƙasa har ta isa inda take zaune ta tsugunna tana miƙa mata ledar ta ce,
"Shi ya saya mini."
Wani kallo Hajiya ta yi mata fuskarta a haɗe, wanda ya saka hanjin cikin Minal murɗawa babu shiri. Kafin ta
baje ƙasa kamar mai neman yafiya ta fara magana cikin rawar murya ta ce,
"Wayata ya ɗauka shi ne na je karɓa ya tafi da ni ina ta roƙon ya dawo da ni kada ki yi faɗa, amma sai da
ya kai ni shagon da muka je ya yi mini wannan sayayyar..."
"Da ma na san zai aikata fiye da hakan. Shi ya sa na dame shi da kira a kan ya dawo da ke. Saboda haka
gobe kada ki sake bari yana fita