Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   29 / 29

84K to 85.8K   out of 85.8K words

a kan tafiyar da na yi ba ku sani ba. Na bar gida ne saboda ba na jin daɗin zama a
cikin ku. Kuma na zaɓi komawa Nigeria a wurin saurayina saboda ba zan iya auren Salissou kuna nuna mini
ƙiyayya b..."

Salatin da ɗakin ya ɗauka ya sa ta fashe da wani sabon kuka cikin sauti. Ganin wasu masu zuciya kusa har
sun fara kawo mata hari da duka, sai da babban yaya ya hana kowa ya taɓa ta. Sannan ɗakin ya nutsu aka
daina surutan da ake yi tsawon minti biyar, kafin ya sake jefa mata wata tambaya da cewa,

"To mun jin kin bar gida kin tafi Nigeria wurin saurayinki. Ya aka yi kika dawo mana bayan kin san ba ma
son ki kuma muna ƙiyayyar ki?"

Hawayen idonta ta share, tare da gyara zamanta tana cewa, "Ban dawo don ina so ba, na dawo ne a
sanadin saurayin nawa da ya yi tattakin dawo da ni tun daga Nigeria har nan Damagara..."
"Ahhhhh! Lalle yarinya ta girma da yawa! Sulaimanou dole ka mutu tun da ka bar mana abin faɗi a cikin
dangi."

Zancen Nenne kenan tana buga ƙafa ƙasa tare da kai wa cinyoyinta duka tana girgiza kai, tamkar wata
zautacciya. Babban yaya ya sake tambayar Nur ina saurayin nata yake. Kai-tsaye ta sanar da shi ya tafi tun a
lokacin da taxi ta kawo ta ƙofar gidan suka juya.

"Ƙarya take yi! Yanzu haka yana ƙofar gidan nan, na gan shi tsaye jikin motar yana yi wa mutane kallon
banza."

Salisso ya karɓe zancen a ƙufule saboda ya ga Jamal a lokacin da zai shigo gidan, cike da mamakin abin
da ya kawo shi ganin bai san shi ba kuma kalarsa ba ta yi kama da ahalinsu ba, ballantana ahalin mahaifiyar
Nur da suke fararen fata kuma buzaye. Wannan zancen nasa ya sa babban yaya bayar da umanin a shigo da
shi. Jikin Salisso har rawa yake wajen miƙewa tsaye, har yana cin tuntuɓe yayin ficewa daga falon.
Zuciyarsa a wuya ya isa ƙofar gidan, bai tsaya yin komai ba ya ɗaga hannu da nufin kifa wa Jamal mari.
Caraf ya riƙe masa hannu cikin zafin nama ya shiga aika masa kashedi da ido. Saboda tun kafin ya iso wurin
Jamal ya ga fitowarsa da fahimtar yanayinsa gabaɗaya, kuma saƙon da Nur ta tura masa ya fahimtar da shi
babu lafiya, don haka ganin ya nufo shi ya saka wa ransa ba arziƙi ya kawo shi ba. Hakan ya sa ya yi shirin
tarɓonsa a kan duk abin da ya zo da shi.
Jiki babu kuzari Salissou ya fara yunƙurin ƙwacewa daga mugun riƙon da Jamal ya yi wa hannunsa amma
ya kasa, ya shiga muzurai da ido yana kallon mutane cikin basarwa ya ce,

"To ka je ciki neman ka ake yi. Don ba ka isa ka yi mana wulaƙanci ka ci bulus ba. A'isha kuma ko za ta
mutu sai na aure t...."

Wata kalar dariya ta suɓuce wa Jamal babu shiri, saboda zancen Salissou ya bayyana masa shi ne wanda
zai aure ta. Dariyar da Jamal ya dinga yi yana nuna shi da hannu har da riƙe ciki ya sa Salissou kallon sa
ƙurin cike da alamar tambaya a kan fuskarsa. Don ya kasa gano me yake yi wa dariya, ganin yana nuna shi
ya shiga kallon kayan jikinsa cike da son gano abin da yake yi wa dariyar. Shi kuma Jamal yanayinsa kaɗai ya
saka shi jin dariyar, ganin wai ashe ma shi ne mijin da ake son aura wa Nur, sai ka ce ta rasa masoya a
duniya. Don a kallo ɗaya da ya yi masa ya gama tantance halittarsa duka, baƙi ne wulik kuma siriri kamar
sullen kara, sai ƙwala-ƙwalan ido da kunnuwa fiki-fiki tamkar na zomo.

Haushin dariyar da Jamal yake yi masa ya saka shi komawa cikin gidan yana faɗin, "Idan ka gama haukar
ka shiga daga ciki za mu ji abin da ya kawo ka gidanmu."

Daga haka ya shige ya bar Jamal dariya a kan fuskarsa yana magana da mai taxi, don sun gama kaiwa
ƙarshe a kan zaman kuɗi yake yi kuma zai kai shi masauki idan ya gama abin da ya kawo shi gidan. Cike da
sabon kuzari Jamal ya bi bayan Salissou da ya tsaya jiran sa don su je ƙafa-ƙafa a gano gaskiyarsa ta cewa
yana nan ba ƙarya ya yi ba. Kasancewar gidan babban gida ne mai ɗauke da sashe-sashe, haka Jamal ya
dinga wucewa yana gaishe da waɗanda ya hango har suka isa bakin falon. Da addu'a a ransa ya shiga
bakinsa ɗauke da sallama, kansa a ƙasa ya isa inda babban yaya ya nuna masa ganin mutanen falon shi
suke kallo. Cikin ladabi ya rusuna yana gaishe da su amma bayan babban yaya babu wanda ya amsa masa,
sai kallon banzan da suke bin shi da shi yayin da wasu ke aika masa harara.

"Bawan Allah! Mene ne haɗin ka da A'isha?"

Jamal ya faɗaɗa fuskarsa da murmushi kafin ya yi magana kansa tsaye yana cewa, "Soyayya mai ƙarfi ce
ta haɗa ni da Nur."

Shiru ɗakin ya yi cike da mamakin maganarsa, don baki sake Salissou ya ƙura masa kallo ganin da gaske
fassarar da ya yi masa ta mara mutunci haka yake. Nur kam kanta ƙasa kuma ƙirjinta bai daina bugawa ba
tun a lokacin da ta yi arba da shi yana ƙoƙarin shigowa falon, don ta yi zaton zai tafiyarsa kamar yadda ta
tura masa saƙon ya tafi, duk da ta san shi sarai babu abin da zai hana shi tsayawa matuƙar ya yi ra'ayin
hakan. Gabanta ya sake bugawa dam-dam a lokacin da ta ji furucin bakin babban yaya a kan amsar da ya
ba shi.

"Tabbas na gasgata ƙarfin soyayya taku, ganin yadda ka yi tattaki tun daga ƙasar Nigeria har ƙasar Niger
don kawai ka kawo ta gida. Saboda haka na amince kuma na yarda a matsayina na yayan mahaifinta zan
aura maka ita tun da ita ma tana son ka."

Nan take surutu ya fara tashi a cikin falon, Nenne ta hau rurin kuka da kururuwar matuƙar tana raye ba
za ta bari Nur ta auri Bahaushen Nigeria ba. Yayin da wasu ke goyon bayan Salissou da ke ta aika wa Jamal
zagi, yana faɗin bai isa ya auri Nur ba sai dai ta tabbata a haka babu mijin aure.
Babban yaya ya yi gyaran murya bayan an rarrashi Nenne ta yi shiru ya sake cewa, "Ban amince da
wannan auren nasu kai-tsaye don ra'ayina ba, na yi hakan ne saboda gudun A'isha ta sake guduwa ta bi shi
ba mu sani ba. Saboda a yadda ta san hanyar barin ƙasar Niger ta tafi Nigeria a kansa; ba a san me zai sake
faruwa ba a nan gaba. Don haka masalaha ce ake nema, tun da an musanya wa Salissou zai auri Hadizatou;
ita ma a ba ta dama ta auri wanda take s...."

"Ranka ya daɗe ina da magana!"

Jamal ya katse shi saboda abin da ya kawo shi kenan, kuma dalilin da ya sa ya zaɓi dawo da ita gida da
kansa kenan, sannan kuma yake son furta zancen a gaban kowa. Babban yaya ya ba shi umarnin magana
duk da kallon wulaƙancin da sauran danginsa suke yi masa. Jamal ya gayyato nutsuwar dole ya yafa wa
kansa, saboda abin da zai faɗa yana jin ɗacinsa har cikin tsakiyar zuciyarsa.

"Tabbas ina son A'isha, irin son da ban taɓa yi wa kowace mace a duniya ba. Amma a wannan lokacin da
nake sanar da ku wannan maganar; ba na jin zan iya aurenta don na gama cire wa raina buƙatar aurenta
gabaɗay...."

"Da ma ta ya ya za ka aure ta bayan ka gama lalata mata rayuwa! Wa ya san irin tanbaɗewar da kuke yi a
can Nigeria ɗin?"

"Ai hakan ya yi daidai! Gobe ta sake cira ƙafa ta bi ka Nigeria!"

"Tirr da halinki A'isha kin ji haushin duniya Sulaimanou ya bar mana jarfa a cikin dangi. To Salissou ma ba
ya son ki yanzu an ba shi Hadizatou a madadinki. Sai ki jiƙa kanki ki sha, da ma a duniya kaf babu mai
ƙaunar ki sai Sulaimanou, kuma shi ma ya mutu, munafukar uwarki kuma tun kina ƙarama ta bar wa
duniya ke. Daga ita har danginta babu mai son ki ballantana su neme ki, mu ma ƙaddara ta ba mu ke da
tuni mun jefar da ke mun huta. Da kin sani ma ɓoyon da Sulaimanou ya yi miki ba ki fito ba, har zuwa
lokacin da za ki bi shi zuwa lahira kowa ya huta."

Maganar Nenne kenan, ɗaya daga cikin ukun maganganun da suka taɓa mata zuciya, duk a cikin jerin
kalolin miyagun maganganun da ake ta jifar ta da su, a sanadin furucin Jamal mai nuna rashin buƙatar
auren ta zahiri ƙarara. Tsam ta miƙe ta dinga bin kowa da kallo ɗaya bayan ɗaya hawaye yana bin fuskarta
tana nuna kanta ta ce,

"Ni...ni...kaina...na yi danasanin zuwana duniya a cikin ku, na tsani kaina kuma na tsine wa mutuwar da
ta ƙi kashe ni tare da Baban...."

Kukan da ya sarƙe ta ya sa maganar ta tsaya babu shiri, sai da ta haɗiye dunƙulallen yawu ya wuce muƙut a
maƙoshinta, sannan ta sake nuna Jamal tana cewa,

"Kai kuma...ban san ba ka so na ba sai ka ɗauki wuƙa ka soka a tsakiyar zuciyata zan gan...kamar yadda
kalamanka suka bar mini mugun dafin da har na mutu ba zai daina yi mini zafi a cikin zuciya ba."
Tana ƙare maganar ta bar wurin idonta a rufe, gudu-gudu sauri-sauri take taku da wani irin mahaukacin
kukan da ya turnuƙe mata zuciya. Kamar almara Jamal ya isa inda take ya cafko hannunta. Tana tirjiya tare
da kai masa duka cikin jarumta ya kawo ta gaban babban yaya, da hanzari ya rusuna riƙe da hannunta ya
sunkuyar da kansa ƙasa yana cewa,

"Babu wani aibi ko nakasar da za ta sa na ƙi auren Nur a duniya. Ina son Nur ko da duniya za ta tsane ta,
ina son Nur ko da ba ta fito a cikin sunnah ba, ina son Nur ko da ni ba ta so na. Don haka ina neman gafarar
ku a kan ƙin karɓar tayin auren ta, na yi hakan ne saboda wani babban dalilin da ba zan iya tsallake shi na
yi gaban kaina ba. Don haka tabbas ba zan iya aurenta ba a wannan lokaci..."

Ihu da kururuwar da Nur ta fasa ya dawo da hankalin kowa a kan Jamal. Ganin tari ya turnuƙe shi yana
aman jini babu ƙaƙƙautawa.



Wayyo Jamal😭



Next page😥



Ga mai buƙata ya biya 1k domin ci gaba da jin wannan badaƙala. 1230094555 Access Bank Hadiza D. Aura
Ibrahim. Shaidar biya ta wannan layin 08022014771.

29 / 29