Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 29

6K to 9K   out of 85.8K words

za su zarge
ni a kan na ci amanar Nur. Sannan shi kansa angon nata ba zai taɓa karɓa ta a matsayin matarsa b..."
Ohh Allah 😔




D. Auta ce🙋
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*Masu neman littafaina ga su kamar haka; ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI, JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN
FITILA, MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA, RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE. BAKAN GIZO, ZUBAR
HAWAYENA, DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA, TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su. Ga mai buƙata ya
tuntuɓe ni ta wannan lambar; 08022014771.*

*LAMBA TA UKU.*

"A hir ɗin ki amina! Wallahi ki fita idona na rufe. Yaushe arziƙi yana kiran ki tsiya tana korar ki da gudu! To
ban son shashancin banza, don ke Allah ya bai wa mijin ba A'isha ba, kuma ita da kanta ta bar miki shi ba
matsa mata aka yi dole sai ta aikata ba, yo ɓata lokacinki na me za ki dinga yi a kan abin da kina zaune allah
ya ba ki ba tare da kin roƙa ba?"

Fusatattun kalmomin Innarmu kenan waɗanda tsabar haushin da Minal ta ba ta ya sa ta miƙe tsaye tana
neman hanyar kai mata duka. Ƙur Minal ta kafe ta da ido cike da zargi ta sake cewa,

"Yanzu ya zan yi da Aminu? Wanda kowa ya san yadda yake faɗi-tashi a kaina?"

"Yi mini shiru sakarya! Shi Aminun idan kika aure shi zai ajiye ki irin gidan nan ne? Ki faɗa mini a kaf cikin
danginmu waye ya samu arziƙin zama irin wannan gidan? To ba ki isa ki yi mana baƙinciki ba, dole ne ki
zauna ko kina so ko ba kya so! An riga an ɗaura aurenki da shi, kuma babu uban da ya isa ya kunce auren
nan! Ke ko mutuwa za ki yi sai dai a fitar da gawarki ehe!"

Innarmu ta ƙare maganar tana kumfar baki da zaro wa Minal ido, alamun ƙiris ya rage ta jibge ta don ta
gama kaiwa bango a kan lamuranta. Minal ma tsaye take kanta a duƙe tana kallon yatsunta fuskarta a
kumbure bayan bakin da ta turo tana gunguni. Tafasar da zuciyarta ke yi ya sa ta yi maganar da take jin
dole sai ta amayar da ita ko za a kashe ta. Domin idanuwan da Innarmu ta kafe ta da su ba su hana ta
furzar da abin da ke cikin bakinta ba.

"Ni fa wallahi ko kaɗan kuɗinsa ba sa gabanta..."

"Mu su ne a gabanmu! Na ce miki mu su ne a gabanmu ki je ki faɗa wa duk uban da za ki faɗawa. Kuma
za mu ci sai inda karfimu ya ƙare, matuƙar muka samu damar cin sai mun ci...ke Amina wallahi na kusa
nakasa ki! Ni za ki gwada wa ƙarfin imani da taƙawa? To idan kin so ki ce da mu kwaɗayayyiya ai ba a
kanmu aka fara son abin duniya ba. Wawuyar banza ana nuna miki hanyar arziƙi kina runtse ido. Kuma
Aminu da kike zancensa a yanzu babu ke babu shi har abada! Saura kuma na ji labarin kin neme shi ko shi
ya neme ki ki ga irin matakin da zan ɗauka a kanku. Sakaryar banza sai na shayar da ke gubar mamaki
matuƙar ba ki shiga taitayinki a kan auren nan ba....Salame ni na tafi idan kin gama ki same ni waje ina jiran
ki..."
Martanin Innarmu ya ƙara lalata nutsuwar Minal, ta kasa shanye zafin maganganun a ranta tun kafin ta
dire zantukan, waɗanda ta ji mugun ɗacinsu a zuciya har cikin bakinta. Bayan ta gama kumbura ta fashe
da wani kalar kuka cikin ɗaga murya tamkar wadda ake tsula wa bulala. Innarmu tana gama faɗar
batutuwanta ta fice daga ɗakin a fusace tana ci gaba da faɗar duk abin da ya zo bakinta cikin faɗan da
sautinta yake tashi.
Ajiyar zuciya Gwaggo Salame ta saki mai ƙarfi kafin ta riƙo Minal ta zaunar da ita a kan gado. Jarumtar
rarrashin ta ta shiga yi har ta samu ta rage sautin kukan da take yi. Sannan ta yi jim na tsawon mintuna
kafin ta yi ƙarfin halin faɗin,

"Kowace rayuwa da kalar tata jarabawa, ke taki jarabawar ita ce wannan. Don haka ki bar wa Allah
lamuranki kada ki yi jayayya da ƙaddararki, saboda ba a sani ba ko ita ce alherinki kina ƙoƙarin turewa."

Shiru Minal ta yi ba tare da ta ce uffan ba, saboda maganganun Gwaggo Salame sun shiga jikinta, ta
share hawayenta ta koma ajiyar zuciya wata bayan wata. Duk da a ranta ba ta jin ta karɓi cushen da aka yi
mata a matsayin ingantaccen auren da ake yi wa kowace mace. Amma kuma ta fi jin daɗin maganganunta
a kan na Innarmu masu kama da ana yaƙi.

"Abu biyu zuwa uku nake so ki riƙe gam kafin mu ga kamun ludayin tafiyar." Maganar Gwaggo Salame ta
farauto hankalinta wuri ɗaya, ta nutsu tana sauraron ta ba tare da ta yi motsin kirki ba

"Na farko ki yi haƙuri a kan ba a nemi amincewarki ba, amma ki kalli hakan a matsayin gata ne da wasu
iyaye suke yi wa 'ya'yansu. Na biyu ki riƙe Ya Wadadu ɗari huɗu bayan kowace sallar asuba, tana ƙara
danƙon soyayya da kwarjini bayan farinjini na yankan shakku. Na uku kuma ki lizimci raya dare da nafilolin
biyan buƙatu a wurin Ubangiji. Na san kin sani akwai su kala-kala, amma kafin mu je ɓangaren abin da za ki
yi ki jawo hankalin mijinki; zan sanar da ke nafilar da nake yawan yi, wadda ni ma na gwada kuma nake
ganin amfaninta, saboda ina so ke ma ki amfana."

Shiru ya ziyarci ɗakin tsawon sakonni kafin Gwaggo Salame ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta ce. "Ki
tashi misalin ƙarfe ɗaya na dare zuwa biyun daren, ki yi nafila raka'a biyu kacal kuma kowace ki karanta
fatiha da Suratul Ahad, waton surar ƙulhuwallahu Ahad. idan kika sallame sai ki yi wata sujuda kada ki
ɗago kanki sai kin karanta La'ilaha Illa antassubhanaka inni kuntu minazzalumina sau arba'in. Kada ki bar
sujudar har sai kin faɗa wa Allah buƙatunki. Ina mai tabbatar miki za ki ga aikin addu'ar tamkar yankan
wuƙa da yardar Allah...."

Kiran wayar da aka yi wa Gwaggon ya sa ta yi hanzarin fito da ita daga aljihunta, ganin Innarmu ce mai
kiran; hakan ya sa ta tuno ashe ita take jira a waje. Ta miƙe tana gyara zaman lulluɓinta ta ce,

"Mu za mu tafi, zuwa anjima za a aiko miki wasu daga cikin kayanki, sauran kuma za a raba wa ƙannenki
da wanda Allah ya ciyar. Amma don Allah ki tsayar da hankalinki wuri ɗaya ki nemi zaɓin Allah. Ubangiji Ya
ba ku zaman lafiya, kuma ki riƙe sirrin mijink..."

Kiran da Innarmu ta sake bugo mata ya sa ta fice da sassarfa ta bar Minal a daskare bakin gadon, don ta
kasa motsa laɓɓanta ta yi mata sai anjima ballantana ta raka ta. Bayan idon da ta bi ƙofa da kallo tsawon
mintuna da fitarta ba tare da ta ɗauke kanta ba.

***
Jamal kuwa, tun da ya fice daga ɗakin bayan ya gama jaddada wa Hajiya ba ya son Minal. Cikin ƙunar rai ya
buga motarsa jikinsa yana rawa ya nufi gidansu. Sai dai kuma Allah ne ya kai shi gida lafiya, saboda
mahaukacin gudun da yake yi tamkar an koro shi ko kaɗan ba ya cikin nutsuwarsa. Uban horn ɗin da ya
dinga bugawa babu ƙaƙƙautawa; ya sa Baba maigadin gidansu ruɗewa jikinsa yana rawa ya buɗe gidan
bayan ya tabbatar shi ne ba gizo ya yi masa ba. Amma zuciyarsa cike da mamakin dawowarsa cikin gidan a
daidai lokacin, wanda ya dace a ce yana tare da amaryarsa a matsayinsa na sabon ango mai zumuɗi da
daren farkonsa.
Da ido Baban ya bi shi baki buɗe har Jamal ya shige sashen da ɗaƙinsa yake ba tare da ya bi ta kan
motar da ya bari a kunne ba, ballantana ya rufe murfi bayan fitarsa. Saboda idanuwansa ko gani ba sa yi
daidai ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa, a sukwane ya isa bayi ya dinga zuba wa kansa ruwan shawa ba tare da
ya cire komai na jikinsa ba. Ya ɗauki tsawon minti talatin idanuwansa rufe ba tare da ya yi dogon motsi ba.
Zuciyarsa danƙare da ƙuncin da yake haddasa mata bugawa da ƙarfi tamkar ta ɓalle daga mazauninta ta
fito ƙirjinsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, kafin ya fara atishawa wata bayan wata kuma har
lokacin ruwan yana sauka kansa zuwa jikinsa. Da lalube ya rufe shawar amma ya kasa ɗagawa daga wurin
tsawon mintuna. Saboda zuciyarsa ta ci gaba da hasko masa fuskar Nur tana feshin tsadadden
murmushinta har dimple ɗin ta biyu suna lotsawa. Hoton zuciyarsa ya hasko masa ita ne a wani lokacin da
suka je yawon shaƙatawa, inda ya ba ta cake a baki tana tauna tana yi masa wani kalar kallon da ya saukar
masa da kasala.

"Ya Allah!"

Furucinsa kenan a lokacin da kansa ya ƙara sarawa tamkar an kwaɗa masa guduma. Dafe da kan ya fito
yana layi saboda jirin da ke kwasar sa har ya zube kan gado riƙe da kansa yana faɗar kalmar Innalillahi fili
da zuciyarsa. Nan take ya fara rawar sanyi jikinsa ya hau fisga babu ƙaƙƙautawa, cikin mintuna kaɗan
numfashinsa ya fara sarƙewa, kafin ya yi luf bayan ya gama tari sama-sama yana dafe da zuciyarsa, saboda
idauwansa sun gama kafewa numfashinsa ya tsaya cak.

Ya kwashe tsawon lokaci a halin da yake ciki kafin dawowar Hajiya, bayan ta gama neman sa a waya ba
ta samu ba. Kuma maigadin gidansa ya tabbatar mata da lalle ya fita. Cikin tashin hankali ta kira
maigadinsu sannan ta samu nutsuwar faɗawa mota direban da ya kawo ta ya juya da su zuwa gida. Saboda
jin Jamal yana gidan ya rage mata kaso bakwai a cikin goman tashin hankalin da ta afka. Don zuciyarta ta
gama tsinkewa cike da tsoron faruwar abubuwa biyu, na farko kada ɓacin rai ya saka shi barin garin ba tare
da ta sani ba. Na biyu tsoron kada ya yi tsautsayi ya ja shi ya yi haɗari, don a halin da yake ciki bai dace ya
yi tuƙi ba.
Makullin motarsa da maigadinsu ya ba ta tare da yi mata bayanin yanayin da ya shigo gidan; jikinta ya yi
sanyi ƙalau, amma hakan bai hana ta isa ƙofar ɗakinsa da sassarfa ba. Amna biye da ita a cikin firgicin suka
shiga bugun ƙofarsa tare da kiran sunansa a lokaci ɗaya. Ganin babu motsinsa ballantana alamun zai buɗe
ƙofar, ga tagoginsa duka a rufe. Hakan ya sa Hajiya ta sa Baba maigadi ya ɓalle ƙofar iya ƙarfinsa.

Hajiya Mummy da Amna ihu mai ƙarfi suka fasa yayin da suka yi ido biyu da Jamal a kan gado. Baba
maigadi ya hau salati saboda alamunsa ya nuna babu numfashi a tattare da shi. Hajiya Mummy ta faɗi ƙasa
tana kuka bakinta ɗauke da kalolin salati saboda idanuwanta sun gama tabbatar mata da Jamal ya jima da
barin duniya. Amna kuma jikinsa ta haye tana ihu tare da faman jijjigarsa a kan ya tashi cikin ƙaraji da
zaucewa, bayan kururuwar da take yi a kan don Allah a kawo musu agaji.




Hmmm!😪




D. AUTA CE✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*
*Masu neman littafaina akwai free akwai na kuɗi sai wanda kuke so.*
*ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI.*
*JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA.* *MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA.*
*RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE.* *BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA.*
*DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA.* *TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su.'Yan kasuwa masu neman a
tallata musu hajarsu ƙofa a buɗe take. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar; 08022014771.*


*LAMBA TA HUƊU.*

"Ba..ba..bai mutu ba!"

Zancen direban Hajiya kenan a lokacin da ya taɓa gefen idon Jamal, waton tsakanin ƙwayar idonsa da
kunnensa, inda ya danne wurin ya ji jijiyarsa tana harbawa ɓal-ɓal. Hakan ya sa gumin tashin hankali karyo
masa ya yi maganar a rikice bakinsa yana rawa. Shi ma Baba maigadin yana taɓa wurin ya yi gaggawar
nanata zancen cike da jaddadawa ya ce,

"Da sauran numfashinsa Hajiya! A gaggauta kai shi asibit..."

Kallon da Hajiyar ke yi wa Jamal ya ƙara tabbatar mata da gaske ne. Saboda kallon da take yi musu ya nuna
zuciyarta ta gama sarewa a kan sun yi rashin Jamal, rashi na har abada. Amma maganar Baban bayan
direban ya gano da sauran ransa sa; sun ƙarfafa mata gwiwa matuƙa, duk a ranta ba ta gasgata abin da
suka faɗa ba gaskiya ne ba, duba da abin da idanuwanta suka ganar mata zahiri.

Zumbur ta zabura saboda ganin Baban da direban kowa yana bakin ƙoƙarinsa a kan farfaɗo da shi. Cikin
sa'a numfashinsa ya dawo, ya yi wani irin ƙugi sannan ya fara tari ɗaya bayan ɗaya a hankali.
Jikinsu yana rawa suka yi gaggawar saka shi mota, direba ya fice aguje Baba da sauran baƙin 'yan bikin
da suka hankalta da abin da ya faru; suka bi su da addu'ar nasara har suka isa wata asibiti mafi kusa da
gidan. Daga Hajiya mummy har direbanta a tsaye suka kwana tamkar haƙori. Sai faman zarya suke yi a
baranda, tsakanin ɗakin bayar da agajin gaggawar da aka kwantar da Jamal ɗin, zuwa kujerun da suka
zauna suna dakon fitowar likitan da ke ƙoƙarin ceto rayuwarsa. Bacci ko kaɗan bai zo idanuwansu ba tun
daga daren har aka yi sallar asuba. Tsabar tashin hankalin da suka shiga baccin da kansa ya kori kansa a
cikin idanuwansu. Har gara Amna ta ɗan runtsa a lokacin da hajiya ta matsa mata ta yi baccinta saboda
ganin tana zuba hamma wata bayan wata da tangaɗi tamkar 'yar maye. Safayar gadon maralafiya aka kai ta
daga gyangyaɗi ta ɗan kishingiɗa sai nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.

Bayan an kammala sallar asuba a cikin masallacin da ke asibitin; Likitan da ya tsayu a kan Jamal ya kira
Hajiya zuwa ofishinsa. A gurguje ta shafa addu'ar neman lafiya ga Jamal hawaye yana fareti a kan fuskarta
ta bi shi cikin sassarfa tamkar ta kifa. Amma idanuwanta a kan ɗakin ceton gaggawar zuciyarta cike da
ƙosawa a kan tsaikon zuwa ganin Jamal da likitan ya yi musu. Saboda tun fitowarsa daga ɗakin ta isa
gabansa tana jera masa tambayoyi a kan ya faɗa mata a wane hali Jamal ɗin yake ciki, har da magiya tana
hawayen ya bar ta shiga ɗakin ta yi masa ganin bankwana. Amma fafur ya ƙi barin ta gan sa, ya ce ta je ta
yi sallah idan aka kammala komai za su yi magana. A haka ya bar ta tsaye fuskarsa babu yabo babu fallasa
ya wuce ya bar ta da fargaba, saboda ta kasa tantance halin da Jamal yake ciki daga yanayin fuskar likitan.

Shiru ya ratsa a cikin ofishin, bayan Hajiya ta samu wuri ta zauna ƙirjinta yana bugawa. Sai da likitan ya
gama 'yan rubuce-rubucensa biro a hannunsa yana jujjuya shi sannan ya yi magana.

"Hajiya mene ne damuwar yaronki?" Bai tsaya jiran amsarta ba ya ɗora da cewa,

"A binciken da na yi masa, na gano yana ɗauke da ciwon kai na damuwa, wanda a likitance muna kiran sa
da Tention Headed."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"

Hajiya ta yi hanzarin yin salati tare da ɗora hannuwanta a ka bayan ta miƙe daga kan kujerar jikinta yana
kyarma. Cikin fuskar tausayi likitan ya yi magana cikin sauri ya ce,

"Ba wani ciwo ba ne ki kwantar da hankalinki. Saboda a yanzu bai zama matsalar da za ta iya jawo masa
manyan cutukan da suka danganci ciwon ba. Sannan abu mai sauƙi ne a shawo kan ciwon matuƙar aka bi
shawarar likitoc..."

"A ba mu maganin ciwon kawai likita, wanda idan ya sha zai warke nan take."

Furucin Hajiyar kenan bayan ta koma zaune kamar yadda ya yi mata nuni da hannunsa, tana haɗa gumi
tare da haɗiye wani dunƙulallen yawun da ya tsaya a maƙogwaronta. Murmushin ƙarfafa gwiwa likitan ya
yi kafin ya sake cewa,

"Magana ta gaskiya babu maganin ciwonsa a hannunmu Hajiya..."

"To ai ka faɗa mana inda za mu samo masa maganin..."

"Ki nutsu Hajiya a hankali zan warware miki komai. Saboda maganin ciwonsa yana hannunsa idan ya so
zai wartsake a cikin kwanaki kaɗan har ma ya rabu da ciwon gabaɗaya."

Hajiya ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da sake jefa masa wata tambayar, "Ta ya ya zai warkar da kansa
a irin mawuyacin halin da yake ciki, bayan ko inda kansa yake a bai sani ba? Kai-tsaye ya ba ta amsa da
cewa,

"Ta hanyar sanya haƙuri a kan abin da yake damun sa, sannan ya mayar da lamuransa ga Allah. Da cusa
wa ransa komai zai wuce idan aka mayar da shi ba komai ba."

"Alhamdulillah!"

Hajiya ta furta hamdalar tare da ɗaga hannu ta shafa saman fuskarta. Likitan ya yi 'yar dariya sannan ya
sake gyara zamansa yana cewa,

"Inda matsalar take idan ya ƙi bin abubuwan nan da na lissafo..."

"Ba ma za a samu matsala ba."

Ta yi hanzarin faɗar maganar tana wara hijabinta tare da ƙara naɗe shi cikin jikinta. Likitan ya ci gaba da
bayaninsa, wanda kusan shi ne gundarin abin da yake son faɗa tana shan gabansa da zance.

"Ciwon zai iya tashi har ma ya faɗaɗa idan ya kasa saka wa zuciyarsa haƙuri da dangana a kan ko ma
mene ne yake damun sa. Kuma idan ya dawo zai iya haddasa masa cutar bugun zuciya, wanda nan take
zuciyarsa za ta iya bugawa ya yi mutuwar fuji'a."

Hannuwan da ta ɗora a ka tana salati bai hana shi ci gaba da bayaninsa ba tiryan-tiryan ba.
"Ko kuma jijiyar ƙwaƙwalwarsa ta tsinke ya samu cutar shanyewar ɓarin jiki da sauran cututtukan da ba
a fata. Don haka tun kafin a je fagen da ba a so ya taimaki kansa ya rabu da ciwon tun yana ƙarami kafin ya
kai babban mataki."

Shiru Hajiya ta yi saboda luguden uku-ukun da ƙirjinta yake yi, idanuwanta a kan likitan ta kasa daina
kallon sa kuma ta kasa furta ko kalma ɗaya daga bakinta.
"Na san zancen ba zai yi miki daɗi ba, amma ki yi haƙuri, sanar da ku dole ne saboda ku taro kan matsalar
tun tana farko kafin ta yi nisan da abin zai damu kowa. Sannan na sanar da ke ne a matsayinki na uwa ko
akwai wata gudunmawar da za ki iya bayarwa wurin ceton lafiyarsa da ransa gabaɗaya. Shi ma idan muka
samu ya warware za mu

3 / 29