Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
MARUBUCIYAR;
ABOKIN AIKINA
BAƘON YANAYI
A'ISHA
DIJE ƘARANGIYA
AMFANIN FITILA
*Na san wasu za su tuno da ɗayan cikin littafanta. To ku karkaɗe kunnuwanku ku sha labari, yanzu ma ta zo
muku da sabon salon labari mai cike da abubuwan al'ajabi, ruɗani da tarin rikita-rikita a cikin wannan littafi
na fansar ƙauna. Bayan zallar soyayya mai tsuma zuciyar makaranci. Ku biyo mu sannu a hankali kada ku
bari a yi wannan sarƙaƙiyar tafiya ba tare da ku ba.*
ƊANƊANO!
Kano ƙarfe 8:30pm.
Motocin ɗaukar amarya jere da juna suna ta gudun tsere a saman babban titin Ahmadu Bello Way. Sun bi
layi suna ƙyalli tsabar sabunta, saboda duhun dare ya ƙara ƙawata su a idon masu kallon wucewarsu ɗaya
bayan ɗaya.
Waɗanda ke cikin motocin kuma, sun yi jugum kowa da abin da yake saƙa wa zuciyarsa, yayin da
fuskokin wasun su ke ƙumshe da zallar farinciki da hira a tsakaninsu jefi-jefi. A cikin raha da annushuwa
abokan amarya suke ta tsokanar ta ganin yadda ta yi ƙuri da ido tana kallon tsakiyar titi ko ƙiftawa babu.
Bayan tagumin da ta rafka da murmushin yaƙe tamkar an yi mata dole yin sa a daidai lokacin, tsabar
fargaba da tashin hankali sun yi mata lulluɓi gumi ya hau feso mata a goshi, ta shiga fifita da gefen
mayafinta tamkar babu iskan A.c a cikin motar.
Shigar jerin motocin a cikin unguwar Nasarawa, da saukar zugar 'yan kawo amarya; ya yi daidai da
isowar motar ango da wasu abokansa a ƙofar tamfatsetsen gidan. Wanda ya sha sabon fenti da hasken
ƙwayayen lantarkin da ke maƙale a jikin katangar gidan lungu da saƙo, inda hasken ya gauraye ko'ina har
cikin gidan da wajensa gabaɗaya.
Guɗa ta kaure a lokacin da ango ya isa bakin motar da aka saka amarya, ya fito da ita da kansa, bakinsa
har kunne abokansa da wasu danginta suna ta ihun farinciki. Don tarin dandanzon mutanen da ke wurin
bai hana shi rungume ta a jikinsa ba, yana maƙale da ita suka fara tattaki a hankali har zuwa cikin gidan
cikin takun isa da taƙama.
Aka bi su ɗii a baya cike da burgewa ga wasu, yayin da hakan ya bai wa wasu 'yan adawa haushi matuƙa
suna guntun tsaki. Duba da yadda ya hana gwaggonnin amarya riƙe ta zuwa cikin gidan da kai ta har
ɗakinta, kamar yadda al'ada ta tanadar.
Guɗa ta ko'ina sai tashi take yi, hakan ya ƙara raunata zuciyar Nur da ke jefa ƙafafuwanta ido rufe cikin
sanyin gwiwa har zuwa ɗakin. Bayan an wuce babban falo aka haye saman bene inda wasu ɗakuna uku
suke, sannan da wani ƙaramin falo mai ɗauke da dinning table a gefensa.
Da kansa ya zaunar da ita a saman makeken gadonta wanda ya kusa cinye rabin ɗakin, sanan ya shiga
leƙa fuskarta da ke cikin mayafi yana wani irin tsadadden murmushi har dimple ɗin sa ɗaya yana lotsawa.
Cike da kunya ta shiga sunne kai a lokacin da ta kai bayan hannunta tana goge guntuwar ƙwallar da ta fito
idonta tana ƙoƙarin bin fuskarta. Sosai lallen hannunta ya ɗauki hankalin angont,, saboda ya sha jan lalle
da baƙi kuma ya fito fes tamkar don ita aka halicci kalar ƙunshin.
Dole ta saka shi yin kawaicin sakin hannunta da ke cikin nasa gam-gam, sannan ya dinga kutsawa cikin
dandazon matan da suka cika ɗakin ya fice cike da shauƙin ƙaunarta a ransa, yayin da wasu abokan
wasansa da nata suka raka shi da guɗa bayan zantukan tsokana iri-iri. Amma iya murmushin kan fuskarsa
kawai ke nuna sarai ya ji su, saboda bai iya tankawa kowa ba a dalilin sauyin da jikinsa ya yi a cikin ɗan
lokaci.
Ficewarsa daga ɗakin, ya bai wa wasu damar tofa albarkacin bakinsu, ta hanyar yi musu addu'ar zaman
lafiya da yabon tsarin da aka yi wa gidan da kayan adon zamani masu ban sha'awa.
Mintuna a tsakani aka shiga shelar 'yan kawo amarya su zo a mayar da su gida. A hankali mutane suka
dinga ficewa zuwa ƙofar gidan bayan sun yi mata sallama da addu'ar zama lafiya. Har aka bar ta da
amintattun ƙawayenta guda biyu. Waɗanda suka sha ado tamkar su ma amaren ne. Musamman Minal
wadda kusan komai nata iri ɗaya da amarya, kama daga kan lallensu, shigar kayansu da kalar ƙamshin
turarensu duka. Saboda Nur da kanta ta feshe Minal da turaren bayan ta gama saka wa jikinta tana cewa,
"Ya dace ita ma ƙawar amarya ta yi ƙamshi."
Bayan fitar 'yan kawo amaryar; Nur ta miƙe cikin sauri ta nufi ƙofar fita daga ɗakin cikin sassarfa, babu
shiri ta waigo saboda hannunta da Minal ta cafko da zummar yin magana. Nur ta riga ta yin maganar
jikinta yana rawa muryarta tana sarƙewa ta ce,
"Ku..ku ɗan jira ni Amna..., ku..ku..bari zan karɓo saƙona a hannun Aunty Jamila kada ta manta da shi ta
wuce gid..."
Cikin zafin nama ta fice, ta bar Minal da Amna suna kallon ƙofar kamar masu nazartar samfurinta. Cike da
tsumayen dawowarta kusa kafin su sauke ajiyar zuciya a lokaci ɗaya tamkar sun yi shawara da juna. Amna
ta miƙe tana ƙara gyara shimfiɗar gadon sannan ta ƙara feshe ɗakin da turarukan ƙamshi tana faɗin,
"Yau dai hankalin kowa zai kwanta, mun kawo wa Auncle J matarsa an huta."
Minal ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Ni ma yau zan yi bacci har da minshari,
babu tunanin za a yi kaza gobe ko wuri kaza za a je tun da sassafe."
Suka yi murmushi dukansu kafin kowanensu ya shiga danna waya shiru ya ratsa ɗakin. Tsawon minti
goma da fitar Nur amma har lokacin ba ta dawo ba. Minal ta miƙe cike da fara'a saboda tuno halin Jamal
da aika-aikarsa a kan Nur ba ya shayin idon kowa.
"Kada fa ta shanya mu a nan, dare ya yi mana ango ya raka mu da doguwar sanda. Bari na je na nemo su
a kammala komai mu ma mu yi gida mu yada haƙarƙari."
Amna ta yi hanzarin faɗin, "Jira! Jira ni na je da kaina, kin san halin Auncl J ba ya jin bari a kan matarsa,
wataƙila yana can ya riƙe mana ita su shanya mu a iska."
Amna ta fice tana gyara zaman mayafinta a kafaɗa, ta bar Minal a tsaye kafin ta ja ƙafafuwanta zuwa
jikin window, laluben tagar ta janye tana kallon farfajiyar gidan da tsirarun abokan angon da ke ta
shewarsu kamar sun manta duhun dare ya lula, saboda komai tarwai kasancewar haske ya wadaci ko'ina
tamkar rana. Ƙarar shigowar saƙon da ta ji a wayarta ya sa ta bar jikin tagar ta nufi jakarta ta fiddo wayar
tana furzar da iska mai zafi a bakinta.
Idonta a kan fuskar wayar cike da mamakin ganin Nur ce mai turo saƙon, ta shiga karantawa cikin fargaba
tare da zaro ido waje. Kafin tashin hankalin da ya game jikinta ya sa ta ɗora hannu a ka ta shiga kurma ihu
iya ƙarfinta babu ƙaƙƙautawa.
Sautin ihun nata ya sa ango da abokansa tare da Amna rige-rigen isa cikin ɗakin. Ido tsakar ka suka shiga
kallon ta baje ƙasa tana wani irin kalar kuka tamkar wadda aka yi wa saƙon mutuwa. A ruɗe suka shiga
tambayar mafari, zancen ya yi mata nauyi faɗi dole da hannu ta yi musu nuni ga wayarta, bayan ta
sassauta sautin kukanta tana rafka salati cikin wata kalar murya. Inda ta jefar da wayar ɗaga cikin abokan
angon ya ɗauko a lokacin da kira ya sake shiga wayar tana ta ɓurarin. Jikinsa yana rawa ya miƙa mata wayar
ta karɓa cikin kyarmar hannu tsabar bugun da zuciyarta ke yi, shiga buɗe lambobin sirrin wayar Amna ta yi
hanzarin fisge wayar ta ɗaga kiran ganin sunan Aminiya tarwai a jikin fuskar wayar.
"Minal, izuwa yanzu na sani kina cikin tashin hankali saboda ganin saƙona. To ki kwantar da hankalinki
Allah ne ya ba ki Jamal."
Ƙit wayar ta katse, Amna ta bi kiran cikin sauri amma tamkar almara ta ji layin a switch off. Cikin sauri
Adamu abokin Jamal ya karɓe wayar a hannunta ya shiga karanta saƙon Nur da ya gani a rubuce.
_'Minal na yafe miki Jamal duniya da lahira, saboda ke ce amaryarsa kuma da ke aka ɗaura auren ba da
ni ba. Ki yi masa biyayya sau da ƙafa kuma ki yafe mini laifin da na yi aminiyata.'_
"Ba zai yiwu ba! Sam ba zai yiwu ba!"
Furucin angon kenan a lokacin da ya ji saƙon Nur da abokinsa ya gama katantawa a fili. Wayarsa ya fitar
daga aljihu jikinsa yana rawa ya shiga kiran ta, sai dai duka layukanta uku babu wadda ta shiga duk wadda
ya kira a kashe yake jin ta.
Hularsa ya jefar ya shiga yamutsa gashin kansa a haukace kafin ya hau zarya a tsakiyar ɗakin yana cizon
haƙoransa, bayan ya cire babbar rigar da ke jikinsa ya wurgar yana tsuma. Cikin hanzarin ya dafe kansa
saboda wani mugun bugun da ya ji a tsakiyar ƙwaƙwarsa a kan harbawar da jijiyoyonsa suke yi. Idonsa ya
rufe ruf tsawon minti ɗaya sannan ya sake buɗewa babu shiri ya sauke su a kan Minal.
Saboda wani tunanin da ya ɗarsu a ransa bai san lokacin da ya isa gabanta ya shaƙo wuyanta ba. Domin
riƙon da abokansa suka yi masa da ƙoƙarin ɓanɓare hannunsa a wuyanta bai hana shi zare idonsa da suka
rine cikin ƙanƙanin lokaci ba. Magana ya yi cikin kakkausar murya tamkar wanda ba ya cikin hayyacinsa.
"Ko ki fito mini da matata ko kuma na zamo ajalinki a cikin wannan dare! Ba ki isa ki raba ni da
farincikina ba! Nur rayuwata ce ko mutuwa ba ta isa ta shiga tsakanina da ita ba.... ƙarya ne! Na ce ƙarya
ne Nur ba za ta guje ni b...."
Kukan da ya sarƙe muryarsa ya sa jikinsa raunin da abokansa suka ci galabar ƙwatar wuyan Minal daga
mummunan riƙon da ya yi mata. Tamkar ƙaramin yaro, ya shiga rera kuka wiwi yana faɗar maganganun da
babu komai a cikinsu face zallar son Nur da ƙaryata abin da ya faru. Tare da alwashin yi wa Minal
mummunan kisa idan ba ta yi gaggawar fito masa da matarsa ba. Da ƙyar abokansa suka fitar da shi daga
ɗakin yana nuna ta da hannu, saboda yadda yake ji a ransa idan ya sake furta wata kalma daga bakinsa;
zuciyarsa za ta iya fashewa tsabar nauyin baƙinciki ya danne numfashinsa.
Oh Allah! Wannan babbar badaƙala ce mai zaman kanta. Ku ci gaba da biyo ni domin jin yadda za ta kaya.
Kada ku manta sunan littafin FANSAR ƘAUNA. Ranar 15 ga watan January zan ci gaba daga inda muka
tsaya.
A taya ni sharing fisabilillahi!
D. Auta
✍🏼
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*Albishirunku! Ƙorafi ya karɓu, na janye 15 ga watan January da na faɗa zan ci gaba da yin posting. In sha
zan ƙoƙarta ta yadda za ku dinga jin motsina har zuwa lokacin da za mu kammala book 1. Masu jiran sai
sun ji ana faɗar labari ya yi daɗi su dinga faɗar daga farko ku taimake ni ku fara bibiya tun yanzu. Fatan
alheri gare ku gabaɗaya.*
*LAMBA TA ƊAYA.*
Fitarsu daga cikin ɗakin ya saka minal fashewa da wani kalar kuka mai ɗauke da majina. Amna da ke tsaye
wuri ɗaya tamkar an dasa ta tana zubar da hawaye, kukan Minal ya saka ta matsawa jikinta cike da tausayi
ta dafa kafaɗarta tana bubbugawa a hankali, ba tare da tace komai ba. Saboda ita ma kanta ya gama
ƙullewa tana buƙatar ƙarin bayani, don ba ta san me zai sa hakan ta faru ba kai-tsaye ba, sanin tana da
cikakken tabbaci a kan Minal ba za ta cutar da Nur ba, kamar yadda Jamal ya yi hasashen ita ce ta ta yi
sanadin gudunta.
Sautin kiran da ya shigo wayar Minal, Amna ta yi saurin isa wurin wayar cikin rawar jiki ta ɗauko mata,
saboda ganin an saka sunan Innarmu saɓanin tunanin da ya ɗarsu a ranta ko Nur ce ta sake kira. A cikin
dasashiyar murya Amna ta ce,
"Karɓi wayarki, Mamarku ce ta kira."
Minal ta cakumi wayar cikin hanzari ta kai kunnenta, wani kuka ya sake kubce mata. Saboda lafazin da
mahaifiyar ta fara furtawa mai kama da mummunan albishir.
"Ki yi haƙuri Amina, ke taki ƙaddarar kenan ki yi ƙoƙarin cinyewa."
Cikin hanzari Minal ta shafe hawayen fuskarta cike da mamakin lafuzan mahaifiyarta, saboda ba ta yi
tsammanin cewa ita ma ta san wainar da Nur ta toya ba. Cike da ƙarfafa zuciyarta, ta haɗiye kukan da ke
cikin bakinta sannan ta yi magana cikin raunanniyar murya ta ce,
"Me kike son sanar da ni Innarmu? Ashe ke ma har kin samu labarin abin da Nur ta aikat..."
"Ina sane Amina tun kafin yanzu, kuma sanin halin da za ki shiga ya sa na kira ki domin na yi miki kashedi.
Amma ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddararki da aurenki hannu biyu, kada ki kalli ƙalubalen da za ki fuskanta a
wurin mijinki. Don Allah za ki yi kuma sakamakonki zai fito daga hannuns..."
Cikin sautin kuka Minal ta katse ta da cewa, "Ban gane ba Innarmu! Ni fa gabaɗaya kaina ya ƙulle! Ta ya ya
zan fuskanci abin da nake ji daga bakinki? Jamal angon Nur wanda muka yi taron bikinsu a yau duniya ta
shaida; shi kike nufin zan zauna da shi a matsayin mijina na sunnah?"
Ta ƙare maganar tana kore hawayen da ke yi mata fareti a kan fuska. Bayan tsumar da jikinta yake yi
tamkar mazari tsabar firgicin da take ciki ya ƙara raunata ɗan sauran kuzarin da ya rage a jikinta.
Ajiyar zuciya mahaifiyarta ta saki kafin ta yi maganar da ta daskare numfashinta, saboda kalamanta sun
ratsa zuciyarta sun saukar mata da wani kalar firgici mai saka mutum zaucewa.
"Amina, Jamal ke ya aura ba A'isha ba. Saboda haka ban yafe miki ba matuƙar kika taka ƙafarki wajen
gidan da sunan barin sa ba tare da kin bi hanyoyin da za ki sasanta tsakaninki da mijinki ba."
Ƙit ta kashe wayar, ta bar Minal riƙe da wayar a kunne tana zarar ido kafin ta fasa ƙara ta buga wayar
ƙasa tare da kwarara wani kalar ihun da guntun fitsari ya kufce wa Amna, tsabar fargaba da tsoron Minal
sun gama kama ta.
Hakan ya sa ta kasa motsi sai idon da ta zuba wa Minal da ke ta birgima a tsakiyar ɗakin tana ƙaraji
tamkar mai bugun aljannu.
Kasancewar ta ji duk abin da suka tattauna, jikinta yana rawa ta ciro wayarta a aljihun rigarta ta ƙwala wa
mahaifiyar Jamal kira, waton Hajiya Mummy.
Cikin sa'a tana shiga ta ɗauka, a kiɗime ta yi magana tsabar ita ma ta kusa zaucewa.
"Ha..Hajiya Mumm...mummy ki zo gidan Auncle J babu lafiya!"
Daga can muryar Hajiyar ta fito raɗam tana cewa, "Ki yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali ina kan hanyar
zuwa gidan yanzu. Abokansa sun sanar da ni ya fisgi mota ya bar gidan ba mu san me zai faru da shi b..."
Ta ƙare maganar cikin muryar kuka sannan ta katse kiran. Jikin Amna ya yi sanyi ƙalau, cike da ƙarfin hali ta
isa wurin Minal da ke ta birgima har lokacin ta fara magana.
"Ki yi haƙuri, na san dole ne ki shiga irin wanann yanayin a sanadin abin da ya faru. Amma ki sani komai
na duniya fararre ne kuma ƙararre. Ki rungumi ƙaddararki kamar yadda Innarmu ta faɗa, wataƙila hakan zai
iya kawo sanadin alheri a gab...."
"Yanzu har sai na tsaya yi miki bayanin Jamal Nur yake so ba ni ba? Ta ya ya zan iya zama da wanda ba ya
so na? Yanzu a gabanki kin ji yana faɗar sai ya kashe ni, mutumin da ke dakon yi wa rayuwata kisan gilla
ake so na zauna da shi a matsayin miji da mata? Ba zai yiwu ba...ni ma ba na farincikin rabuwarsa da Nur
saboda na sani ita ma tana son sa."
Ta ƙare maganar tana zuƙe majinar kuka a cikin zafin zuciyar da take jin hayaƙinta yana ƙoƙarin rufe mata
hasken ido. Cikin sanyin murya ta sake magana bayan ta yi durƙuso a gaban Amna gwiwa bibbiyu tana
cewa,
"Ki taimake ni ki taimaki rayuwar Jamal a matsayinki na 'yar'uwarsa. Don Allah idan Hajiya ta zo ki ce ta
roƙi Innarmu ta jaye Allah Ya isarta a kaina. Saboda ko zan bi duniya na yi alwashin sai na bar gidan Jamal,
kuma ko da ina fita ƙofar gidansa bakinta zai kama ni na fara ɗaiɗaicew..."
"Dakata Minal! Kada ɓacin rai ya sa ki jefa kanka cikin fushin Ubangiji. Ki yi haƙuri ki bari mu ga yadda
abin zai kasance, ba tare da kin yanke hukuncin da zai taɓa rayuwarki b.."
Minal ta yi hanzarin miƙewa tsaye ta fara taku a tsakiyar ɗakin tana faɗin,
"Rayuwa ta ba ta da wani amfani tun da har aka aiwatar da wannan ɗanyen aikin ba tare da sanina ba.
Don haka ba zan yi wa kowa Allah Ya isa ba, amma tabbas ba zan taɓa yafewa b..."
"Minal!"
Amna ta kira sunanta da ƙarfi cikin wani sabon tsoro da ɓacin rai. Saboda jin furutanta kamar tana so ta
wuce iyakar hankalinta duk da haƙurin da take ba ta.
"Ki bar ni ina da ikon faɗar komai tun da aka yi mini abin da aka ga dama. Saboda ko za a mutu ba zan iya
rayuwar aure da Jamal ba, kuma idan aka matsa kafin shi ya kashe ni ni da kaina zan fara aika kaina zuwa
lahira."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wannan masifa da me ta yi kama?"
Furucin Hajiya Mummy kenan a lokacin da ta faɗo cikin ɗakin har tana cin tuntuɓe saboda kalaman
Minal ne suka tarbe ta.
"Na sani ba a kyauta miki ba saboda ba a yi shawara da ke ba kafin a aiwatar. Amma ki kwantar da
hankalinki babu abin da zai faru sai alheri. Ni ce mahaifiyar Jamal, kuma na faɗa na nanata ban yafe masa
ba matuƙar ya sake ki."
Wani sabon kuka ya suɓuce wa Minal, hannunta a ka ta shiga kwarara ihu saboda tana ji a ranta
gabaɗaya an gama raunata rayuwarta. Daidai lokacin da aka kira wayar Hajiyar, ta dakata daga yunƙurin
rarrashin ta da take yi ta ɗauki wayar. Bayan jin abin da aka sanar da ita a wayar ta yi magana cikin haɗe
fuska ta ce,
"Adamu miƙa masa wayar!"
Ɗaya daga cikin abokan angon ne suka kira ta, kuma babu ɓata lokaci suka ba shi wayar