Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
ka nemo waɗanda ba mayu ba su ba k..."
"Hajiy..."
Cikin hanzari ta katse shi da cewa, "Ba fa za a sake dafa komai a cikin gidan nan ba, sai girkin rana idan za
ka jira. Idan kuma ka matsu kai da ba mayen ba ka shiga kitchen ɗin da kanka ka nemo abin da za ka ci."
Ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi yana faɗin, "Allah sarki ni Jamal marayan Allah!"
Ya bar wurin yana sosa kansa ya nufi kitchen ɗin, zuciyarsa cike da son sake ganin Minal. Amma tsabar
bauɗaɗɗen hali irin nasa ko ƙofar ɗakin bai kalla ba ya wuce abin sa. Dam, ƙirjinsa ya buga a lokacin da ya
hango Minal cikin kitchen tana aiki. Turus ya yi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya gaisa da Umma Ade,
sannan ransa a haɗe ya kalle ta ya sake cewa,
"Wai ke ko'ina kina nan?"
Minal ta yi banza da shi kamar ba ta ji abin da ya faɗa ba. Amma ta gama gano maganarsa sarai da ita
yake yi, sai dai ta ci alwashin sassauta wa kanta damuwa a kan halayensa. Hakan ya sa ta ci gaba da
markaɗa kayan miyan da take yi a cikin bulanda kamar ba ta san da shi ba a wurin ba. Don duk da
maganarsa ta ƙona mata rai har ta shige ɗaki ta yi kuka, amma hakan bai hana ta sakin ranta ta koma
kitchen taya Umma Ade aiki ba. Saboda zuwansa gidan ya sa zaman falon ya fi ƙarfinta.
"Wai ke ba kya ji ina magana ne?"
Jamal ya sake yin magana yana matsawa kusa da ita cikin wata kalar murya, saboda ganin Umma Ade ta
fice daga kitchen ɗin ta bar su.
A nan ma banza ta yi masa tana ƙoƙarin zube kayan miyan, bayan ta gama markaɗawa a cikin wata
roba kamar ba ta san yana wurin ba. Saiti da bayanta ya tsaya zuciyarsa sai zillo take yi masa tsabar
sha'awar nan take da ta kawo masa farmakin gaggawa. Saboda ganin tudun bom-bom ɗin ta da shafe ɗin
doguwar rigar da ke jikinta ya tona asirin albarkatun ƙugunta.
"Wai ke ba ki iya gaisuwa ba ne? Ina ta magana kin yi wa mutane shiru!"
Ya Yi maganar a daidai lokacin da ya kasa nutsuwa har sai da ya haɗa jikinsa da nata, yayin da ya
rungumota ta baya ya shiga goga mata jijiyarsa da ke miƙe saman bom-bom yana sauke numfashi ɗaya
bayan ɗaya.
"Innalillahi!"
Abin da ta faɗa kenan cikin hanzarin tare da zabura saboda abin da ta ji tamkar almara. Ta ja gefe
fuskarta a cure tana nuna shi da hannu ta ce,
"Idan maitarka ta tashi ka dinga tsayawa ga iya matan barikin da ka saba bi, saboda ka fi kowa sanin ni
ba 'yar iska ba c..."
"Amina! Fito ki bar masa kitchen ɗin idan ya gama abin da ya kai shi sai ki ci gaba da naki aikin!"
Muryar Hajiya suka jiyo a sama, wadda ta katse mata magana babu shiri. Saboda jikin Hajiyar ya ba ta
matuƙar Minal tana cikin kitchen ɗin sai ya samu abin da ya yi mata mara daɗi. Ƙwafa kawai Minal ta yi
bayan ta amsa kiran Hajiyar da faɗin 'To' a kan umurnin barin kitchen ɗin. Sannan ta raɓa ta gefensa tana
ƙoƙarin ficewa ya damƙo hannunta ta baya fuskarsa a haɗe duk da yanayinsa gabaɗaya ya gama sauyawa.
"Ba ki isa ki mini fitsara ba! Idan kuma kika kawo mini tsageranci zan nuna miki na fi ɗanyen kai. Saboda
haka ki bi ni a hankali don ba zan juri rashin mutuncinki ba."
Kanta ta juya gefe riƙe da ƙugu tana girgizar jiki ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba. Ƙirjinta ya shiga bugawa
tsabar tsoron sa duk da tana ƙoƙarin nuna jarumtarta a fili. Don maganganunsa sosai suka kama mata
zuciya. Amma sai da Hajiyar ta sake ƙwala mata wani kiran sannan ta shiga kiciniyar ƙwatar hannunta daga
riƙon da ya yi mata, ta kasa. A ƙarshe ma fisgo ta ya yi gabaɗaya ta faɗa jikinsa ya rungume ta yana sauke
ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya. Ta shiga ture shi zuciyarta cike da fargabar kada Hajiyar ta shigo ta gan su a
yadda suke. Babu shiri ta ƙwala wa Hajiyar kira saboda jin hannunsa ɗaya ya cafko mata bom-bom tare da
zabura a lokaci ɗaya.
Sautin takun Hajiyar da faɗan da take yi tana nufo kitchen ɗin, hakan ya saka fargaba ta shige shi ya yi
saurin sakin ta tare da kai wa ƙafarta taki cike da haushin kwarantun kiran Hajiyar da ta yi don ta tona
masa asiri. Sannan ya juya bayansa yana ƙoƙarin saita kansa da nutsuwarsa ta ƙarfi gudun Hajiyar ta gano
halin da yake ciki. Cikin ruɗewa ya shiga mayar da niƙaƙƙun kayan miyan a cikin bulanda da niyyar sake
niƙawa.
Minal kuma ta durƙushe ƙasa riƙe da ƙafarta tana yarfa hannu daidai lokacin da Hajiyar ta iso kitchen ɗin a
fusace. Idonta a kan Minal tana salati yayin da ta isa wurin kwandon kwanoni ta fisgo ludayin miya ta yi
kansa da duka. Da gudu ya fice yana dariyar ƙarfin hali yana gaba tana bayansa har ta kora shi harabar
gidan ta rufe ƙofar falon, bayan ta gama yi masa kashe da babbar murya tana faɗin,
"Kada ka sake zuwa gidan nan daga yau! Kuma idan na sake ganin ka dawo sai na kakkarya maka
ƙafafuwa. Tun da kai ba za ka bar bakin mutum ya huta ba kullum sai ka yi abin magana kake jin daɗi."
Motarsa kawai ya faɗa zuciyarsa a ƙuntace ya fice gidan cikin fushi tamkar ya tashi sama. Saboda takaicin
Hajiya ta hana shi rage zafi a inda aka tsokano masa sha'awarsa. Da hakan ya shiga tunanin hanyoyin da zai
bi ya yi wa Hajiyar wayo ta bar shi ya dawo gidan da zama. Ita kuma Minal ya yi mata dabarar da zai samo
kanta cikin sirri ya kwashi ganima ba tare da Hajiyar ta sani ba. Don da ma can amfaninta gare shi kenan
tun da har zuwa lokacin bai gama gamsuwa da ingancin aurensu ba. Kuma zuciyarsa ba ta nutsu da karɓar
ta a matsayin matarsa ta dindindin ba.
A cikin gidan kuma Hajiya ta shiga rarrashin Minal, tare da nuna mata ta daina yi masa kuka, kuma ta bar
barin yana cin zalinta a banza ita ma ta dinga ramawa. Umma Ade tana murmushin ta yi magana cikin sigar
kwantar da fushin Hajiyar ta ce,
"Yaran zamani ne Hajiya. Tasu kalar soyayyar kenan ki bar shiga tsakaninsu."
"Babu wata soyayya sai baƙar mugunta Ade. Ana soyayyar zai kasa cin abincinta ya koma ƙoƙarin dafawa
da kansa?"
Hajiya ta yi maganar cikin ɗaga murya, Umma Ade ma ta sake cewa, "Abincin ne kawai ba ya ra'ayin ci,
amma ko a ido ana gano yarona ba ƙaramin so yake yi wa matarsa ba. Don haka a yi masa haƙuri Hajiya zai
daina in sha Allah. Saboda shi tasa salon soyayyar kenan sai an dinga yi ana nuna masa hanya."
"Ba hanya ba hanyo Ade! Wace irin hanya ce ban nuna wa Jamal ya kasa bi tun tana gidansa ba? Kuma
yanzun ma da na kawo ta gabana ya ce ba zai ɗaga mata ƙafa ba? To ƙaryarsa ta sha ƙarya Ade! Matuƙar ya
ce zai ɓata mata rai a cikin gidan nan ni kuma wallahi ba za mu taɓa shiryawa da shi ba. Abincin gidan nan
ma daga yau ya daina ci, sai dai ya je can inda babu mayu su dinga ba shi yana ci...ai Amina ba baiwa ba ce
ballantana ya dinga yi mata abin da duk ya ga dama."
Umma Ade ta yi shiru saboda ganin Hajiyar ta hau sama sosai. Minal ma shirun kawai ta yi amma
zuciyarta ko kaɗan ba ta jin daɗin ganin yana samun matsala da mahaifiyarsa a kanta. Sai dai dole ta ja
bakinta ta yi gum saboda 'yancinta ne take ƙoƙarin ƙwatar mata daga hannunsa.
Jiki babu kuzari ta koma kitchen ɗin, don gabaɗaya Jamal ya gama raunata mata zuciya. Musamman abin
da ya yi mata duk wani motsi abin take ta gani a cikin idanuwanta kamar almara.
Da marece sakaliya Umma Ade tana shirin komawa gida Hajiya ta kira ta har cikin ɗakinta suka zauna.
Cike da damuwa ta yi magana saboda abin da yake cizon ranta kuma tana ganin Aden za ta iya taimakon ta
tun da ta san komai da abin da ke faruwa.
"Ade, ku ne idon duniya, ina za ki samo mini sahihin maganin mata gangariya? Saboda ina so na yi
maganin matsalolin Jamal a kan yarinyar nan! Duba da yadda aka yi auren babu wani kyakykyawan shirin
da iyayenta suka yi mata. "
"Hmmmmm!" Ajiyar zuciya Umma Ade ta sauke mai ƙarfi kafin ta ce, "Tabbas wannan shawara ce mai
kyau Hajiya. Don wataƙila har da rashin gyaran ya ƙara rura rashin jituwa a tsakaninsu. Amma idan har
wannan ce matsalar, in sha Allahu daga wannan karon an zo ƙarshe. Saboda akwai wata baiwar Allah
maƙociyarmu ce, Ubangiji Ya lamunce mata nan ɓangaren. Don alamu ya nuna magungunanta suna aiki
sosai duba da yadda matan masu kuɗi suke ta zarya a gidanta koyaushe. Idan kina so zan iya kai ki har
gidanta ku tattauna ta yadda za a shawo kan matsalar cikin sauƙi."
"Yawwa Ade, na gode miki sosai Ubangiji ya saka ki cikin masu kaso a ladar ke ma. Ki karɓo mini
lambarta gobe idan kin zo, sai mu fara yin magana na ji waɗanne iri za mu fara saya mu gwada. Don ina
son ta mallake shi gabaɗaya ta yadda kallo ma ba zai ƙara yi wa kowace mace ba da sunan shashanci. Ina
so ya tsayar da hankalinsa wuri ɗaya saboda gudun ya kwaso wa kansa ciwon zamani ya bar mu da tashin
hankali."
"In sha Allahu hakan ba za ta faru ba Hajiya. Allah zai kare shi babu abin da zai faru da shi sai alheri."
"Muna fatar haka Ade don ni ma ba na masa fatar hakan, amma mace ko namiji duk wanda bai tsaya
inda Allah Ya ajiye shi ba zai haɗu da ɓacin rai watarana, matuƙar ba a kiyaye dokokin Allah aka watsar da
ƙyale-ƙyalen zuciya ba."
Ade ta muskuta tana faɗin, "Allah Ya ƙara tsarewa Hajiya."
Daga haka suka rabu, a kan Ade za ta karɓo lambar mai kayan matan da safe idan ta dawo ta kawo mata.
Bayan tafiyar Ade Hajiyar ta kira Amina da ke kallo a falo ta shigo ƙirjinta yana bugawa. Saboda kwarjini
sosai Hajiyar take yi mata, ba ta samun nutsuwa idan tana ga wuri har ta ɗaga.
Wuri ta samu a ƙasa ɗan nesa da Hajiyar ta zauna a ɗarare bayan ta yi sallama cikin muryar ladabi. Cike da
tausayin ta a ran Hajiyar ta ja numfashi ta sauke kafin ta ce,
"A cikin kayan da kika zo da su akwai sababbi?" Ta jefo mata tambayar kafin ta ƙarasa furzar da abin da
ke ranta.
"Babu." Ta amsa cikin fargaba saboda ba ta san dalilin da ya kawo tambayar ba. Hajiya ta sake jefa mata
wata tambayar da cewa,
"Me ya sa ba ki zo da su ba?"
Minal ta yi shiru kawai kanta a duƙe tana wasa da yatsunta. Fahimtar akwai abin da ke ranta wanda ba ta
son faɗa Hajiyar ta sake cewa,
"Dole ne ki yakice duk wani abu da ke nisanta ki da mijinki. Sannan ki iya ɗaukar wankan da zai dinga jan
hankalinsa gare ki. Don ba zai yiwu ki zauna a haka babu wani gyara ko kissa irin ta mata ba. Ki koyi
abubuwan da za ki shawo kan mijinki da su a cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya sani ba. Saboda na san
wane ne Jamal yana, yana son mace wayayyiya. Wataƙila har da hakan ya taka muhimmiyar rawa wurin
nisanta ki da shi. Don haka ki bi matakan gyara kanki ta hanyar da za ki farauto zuciyar mijinki daga matan
banzan da ke ƙoƙarin janye miki shi. Saboda ni uwa ce, kuma yadda ba na son abin da zai samu 'ya'yana
haka ba na son abin da duk zai same ki mara daɗi."
"Na gode Hajiya." Zancen Minal kenan cikin wata murya bayan Hajiya ta tsahirta da bayani. Minal ta
shiga share ƙwallar da ta wanke mata fuska cike da tausayin kanta ta ɗan muskuta ta gyara zamanta
sannan ta ce,
"Jikina yana ba ni koyaushe Nur za ta iya dawowa ga mijinta. Shi ya sa ba na son amfani da komai a cikin
kayan lefenta."
Kallon mamaki Hajiya ta dinga yi mata tsawon mintuna kafin ta ce, "Daga yau zancen A'isha za ta dawo ga
Jamal ya fita daga cikin zuciyarki. Saboda matuƙar ina numfashi ba zan taɓa bari ya yi zaman aure da ita ba.
Kaya kuma naki ne halak malak tun daga ranar da aka ɗaura aurenki da Jamal. Don haka komai na lefen
naki ne ki yi amfani da duk abin da kike so."
"To Hajiya."
Minal ta yi maganar tana ƙoƙarin share hawayenta, zuciyarta cike da farincikin jin tabbaci daga bakin
Hajiyar, bayan ƙwarin gwiwar da ta cusa wa zuciyarta ya faranta mata rai sosai.
A gabanta Hajiyar ta kira Jamal tare da sanar da shi ya haɗa kan lefen duka direbanta zai zo ya karɓa.
Sannan tana sauke wayar ta kalli Minal ta ce,
"In sha Allah gobe zan sa a kai ki wurin lalle da kitso. idan lokaci ya bayar har wurin masu gyaran jiki
duka za ki je a yi miki duk abin da ya dace. Saboda ina so ki yi amfani da wannan damar ta zamanki cikin
gidan nan ki ƙwato darajarki wurin mijinki."
"Na gode Hajiya. Allah Ya ƙara lafiya da nisan kwana."
Daga haka ta ce, "Ta shi ki je, kuma ki tabbatar kin saki jiki kin cire tunanin A'isha a cikin ranki."
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan
08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA TAKWAS.*
Minal ta fito daga ɗakin zuciyarta wasai tamkar an sauke mata wani ƙaton dutsen da ke saman kanta. Ta
kasa zama falon ta yi ɗakin Amna jikinta yana rawa ta danna wa Innarmu fulashin. Saboda ta gwada kiran
ta ji ashe babu ko ficika a cikin wayar.
Minti biyu tsakanin fulashin ɗin ta sai ga kiran Innarmu ya biyo baya. Da zumuɗi ta ɗauki wayar tun kafin su
gaisa ta ce,
"Innarmu Hajiya ta ce ko Nur ta dawo ba za ta bari Jamal ya aure ta ba. Kuma..."
"Ke wai ba ki da wani zance a duniya a yanzu sai na Aisha ne? Tsoron me kike ji bayan ke ce da komai
yanzu sai yadda kika ga dama za ki yi? To karkaɗe kunnuwanki ki ji; Aisha ko ni na haife da cikina kika samu
irin wannan damar ban ce ki yi wasa da ita ba. Ballantana wadda daga ni har ke ba mu san haƙiƙanin
danginta ba....ko kin taɓa ganin uwarta ko dangin Babanta sun zo gidanmu?"
Minal ta yi hanzarin girgiza kanta tamkar tana gabanta suna kallon juna. Shirun da Innarmu ta ji ta yi ya sa
ta sake cewa, "To ki kiyaye ni Amina! Zancen Aisha ya fita daga bakinki, don ba uwar mijinki ba ko ni nan ba
zan taɓa bari ki yi kishi da Aisha a gidan aurenki ba. Saboda ita ce ta bar ki shi da kanta babu wanda ya yi
mata dole, kuma yanzu ba ta isa ta dawo ta ce za ta hargitsa mana farinciki b..."
"Innarmu ina gidan su Jamal tun jiya Hajiya ta ce na dawo gabanta na zauna."
"Ki zauna kamar ya ya? Me kika je yi a gidan nasu har da kwana?"
Innarmu ta yi hanzarin yi mata tambayar cikin wata kalar murya alamun ranta ya ɓace kuma ƙiris take
jira ta dira kanta da masifa. Fahimtar hakan ya sa Minal ta sauya zancen da cewa,
"Tafiya ya yi shi ne ta ce na zauna kafin ya dawo."
"To..tooo..da sauƙi har na ji sanyi. Amma farko har hankalina ya tashi na ɗauka ko wani laifi kika yi wa
mijin ya ce ki bar masa gida kika koma can. Amma don dai tafiya Allah Ya tsare hanya ya dawo lafiya ki
koma gidanki ki ci gaba da bautar aure. Kuma wallahi kin ji na rantse ko da wasa kada ki bari ki masa laifin
da zai kawo ƙarar ki gidan nan! Kina gani ni ma haƙuri nake yi da Babanku sama da shekaru na kafe sai
mutuwa. Don haka ke ma babu fushi babu yaji ballantana kawo ƙarar miji a gida. Duk tsanani ki zauna sai
mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi har zuwa lokacin da ki ci moriyar haƙurinki. Amma a ce kina cikin
wannan kafcecen gida tsawon wata da kwanaki ko katin kira na ba ki mallaka ba, a ce ba ki da sai yi wa
mutane fulashi...?"
"Innarmu yau kaɗai ne fa!"
Ta yi maganar cikin wata murya tare da turo baki alamun ta ji haushin maganar. "Kin dai yi ko? Kuma ko
ba ki taɓa ba yau kin fara...ki dai kwantar da hankalinki daga mu har ke a gaba Za mu ji daɗin auren nan.
Burina ɗaya ne a yanzu ki samu ciki ki fara ajiye 'ya'ya a cikin gidan."
Minal ta yi hanzarin rufe bakinta cike da jin nauyin maganar tana 'yar dariya ta ce, "Cikin lafiya Innarmu?"
"A'a cikin ciwo!"
Ta amsa mata a fusace sannan ta katse kiran. Minal ta sauke wayar daga kunnenta tare da sauke wata
ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce,
"Innarmu-Innarmu! Ke komai sai kin mayar da shi faɗa...wai Allah wai ni ce zan yi ciki...ko ya zan yi idan
na samu cikin?"
Ta ƙare maganar tana shafa cikinta tana dariya saboda hango ta da ƙatoton ciki a gaba taku da ƙyar tana
tafiya. Ta jima a ɗakin kwance saman gadon Amna tana juya zancen Innarmu, kuma zuciyarta cike da
kewar Jamal da tunanin abin da ya yi mata kitchen. Nan take ta tsinci kanta cikin