Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 29

30K to 33K   out of 85.8K words

Nan take murmushi ya bayyana a kan fuskar Innarmu tana cewa, "Da kin taimaki kanki. Amma muddin
kika tsaya kallon ruwa kwaɗo zai yi miki ƙafa. Sannan ko ma wane alƙawarin ne sai na gano shi, don ba zan
zuba ido hannun agogo ya dawo mana baya ba..a kan me..ba zai yiwu ba...da sake."

Haka Innarmu ta ci gaba da mitar maganar har ƙannen Minal suka dawo makaranta. A nan suka baje ana
ta hirar yaushe gamo da bai wa juna labarin abubuwan da suka faru. A nan Minal ta ji labarin an hana
kowa zuwa gidanta har ƙannenta. Saboda surutu da gulmar auren da ake ta yi a cikin unguwa da danginsu.
Inda aka ɗauki laifin kacokam aka ɗora wa Innarmu, sannan ita ma aka ce ta ci amanar Nur tun da ta
ƙwace mata saurayi. Ɓatan Nur ma cewa aka yi Innarmu ce ta yi mata kurciya saboda ta yi nisa da inda aka
san ta. Surutai kala-kala kuma duk sun dawo wa Innarmu har shi Babban. Amma kasancewar sun san
yadda aka yi auren ko kaɗan hakan bai tayar musu da hankali ba.

Hakan ya sa Innarmu ta sha ɗamarar babu wata mace a gidan Jamal sai Amina. Shi ya sa har dare ya yi
tana ta maimaita mata zance ɗaya, "Kada ki kuskura ki yi abin da kika ga ina yi a cikin gidan nan. Ni ma
wani lokaci ba don ina so ba nake yi. Don haka ki bi Allah ki bi aurenki. Sirrin mijinki ki rufe kuma babu ke
babu kai ƙarar sa. Idan ma ya cuce ki ki bar shi da Allah shi ne zai saka miki."

Da ire-iren waɗannan nasihohin ta cinye wunin. Don Innarmu ta hana ta zuwa gidan kowa a cikin
unguwar har maƙota. Saboda saɓanin da ya faru a kan gutsiri-tsomar da ke shiga suna fita a tsakanin
mutanen unguwar tasu. Hakan ya sa ta bushe fitilarta a kan duk uban da ya haɗa auren ya raba idan ya isa.

Amma har ƙarfe takwas na dare Jamal bai zo ɗaukar ta ba. Innarmu ta matsa ta kira shi a waya ta ce
masa shi take jira. Ba don ta so ba, haka ta ɗaga wayar ta kira shi, amma har ta tsinke bai ɗaga ba.
Mintuna a tsakani sai ga saƙonsa ya shigo a kan ta nemi adaidaita sahu ta koma bai gama abin da yake yi
ba. Har ta fara surutan ɓacin rai a kan ba za ta koma ba a nan za ta kwana, Innarmu ta tusa ƙeyarta gaba
har zuwa bakin titi. Da kanta ta taro mata abin hawa ta shiga, bayan ta biya ta sake yi mata gargaɗi da jan
kunne a kan ta riƙe aurenta hannu biyu.

Haka suka rabu ƙannenta suna ɗaga mata hannu har suka miƙa titi. Tafiya ɗoɗar suka yi kafin su isa
unguwar misalin ƙarfe tara saura minti shida na dare. Da kwatance har adaidatan ya kai ta ƙofar gidan,
bayan ta fito jiki babu kuzari ta nufi bakin gate ɗin tana ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar. Maigadi ya buɗe mata
bayan ya gama yade fuskarta tas da fitilarsa mai mugun haske. Cike da mamaki ya yi hanzarin faɗin,

"Hajiya da ma ba ki dawo gidan ba ashe?"

Dariyar yaƙe kawai ta yi masa, a lokacin da ya saki ƙofar ta shiga ta hango motar Jamal a mazauninta.
Alamun yana cikin gidan, kuma ya dawo amma ya kasa biyawa ya ɗauko ta. Zuciyarta a cunkushe ta nufi
hanyar shiga cikin gidan tana ƙara danne ɓacin ranta saboda tuno nasihohin da ta sha, wuni zungur ana yi
mata bitar haƙuri da biyayyar aure. A kan haka ta saki ranta har ta haye sama ta tura ƙofar shiga falon cike
da karsashi.

Dam-dam! Sautin bugun ƙirjinta kenan a lokacin da ta yi ido biyu da Jamal kwance saman kujera, ya yi
matashin kai da cinyar wata mace suna kallo tamkar miji da mata. Hankalinsu a kwance sai dariya suke yi
alamun suna jin daɗin yanayin.
SANARWAR!
INA NEMAN MUTUM MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2 PRIZE 1K GA MAI
BUƘATA YA TAƁA NI TA NAN; 08022014771 ZAN SAKE SHI A RANAR 3 GA WATAN FEBRUARY. LABARI NE
MAI ƊAUKE DA RIKICI, HARGITSI, TASHIN HANKALIN DA RIKITA-RIKITA BAYAN ZALLAR TSAGWARON
SOYAYYA.




D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Dsn5IB2qqtYAG3EDJ04sce

*Assalamu alaikum*
*Na ce kuna neman inda za ku saya wa yaranku da kuma kanku kaya cikin sauƙi?*
*Shin kina neman kayan kitchen da bedsheet masu quality da sauƙi?*
*Tom ki shigo ki gane wa idonki idan price ɗin bai yi miki ba ki fece. Shaharariyar 'yar kasuwa; Rukayya
Musa Mahmud. Business name; Maman Suhaila. Dealers of all kind of kids clothes. Kitchen Ware's.
Necklace. Bedsheet. Shoes and bags.*
*Muna Kano Muna tura kaya ko'ina a cikin aminci da kula da amanar kayanku.*


*LAMBA SHA HUƊU.*

Tsaye ta yi tsawon sakonni tana ƙare musu kallo, zuciyarsa ɗauke da kalmar Innalillahi wa inna
ilaihirraji'un. Kafin ta cira ƙafafuwa babu kuzari ta fara taku gumi yana tartsatso mata a jiki. A haka ta isa
tsakiyar falon daidai ta gabansu ta ja ta tsaya idonta a kansu, zuciya ta shiga nuna mata ta cakumo macen
ta rufe ta da duka kawai. Yayin da wata zuciyar ke yi mata kashedin babu ruwanki gidansa ne kuma shi ya
kawo ta.
Zumbur macen ta yi ganin Minal tsaye a gabansu cikin tsoro ta kalli Jamal a firgice ta ce,
"Babe, da ma kana da mata amma ka ce na zo gidanka na taya ka kwana?"

"No, wannan ba matata ba ce. Kada ki wani damu ki tayar da hankalinki a banza. Idan za ki zauna kawai ki
zauna gidana ne ina da ikon kawo duk wanda nake so."

Daga haka ta faɗa jikinsa ya shiga shafa ta yana shinshinar ta tana faɗin,
"Ohhhh... baby ina son...ka."

Nan take Minal ta fara ganin dishi-dishi jiri yana kwasar ta ta yi hanzarin barin wurin da sassarfa
kafafuwanta suna harɗewa. A haka ta nufi bakin ɗaki jikinta Yana rawa ta murɗa ƙofar cike da jarumta,
sannan ta tura a hankali ta shige tare da mayar da ƙofar ta rufe ruf har da makulli.
Tsaye ta yi jikin ƙofar bayanta jingine kanta a sama yayin da wani zafafan hawaye ya shiga bin fuskarta
wani bayan wani. Saboda jin sautin dariyar da suka bi bayanta da ita babu ƙaƙƙautawa. Tsawon lokaci tana
haka kafin ta samu kuzarin furta La haula wala ƙuwwata illah Billah. Hasbunallahu wa ni'imal Wakil. Haka
ta yi ta faɗa a fili da cikin zuciyarta, faɗa take yi tana maimaita kalmomin cikin saurin murya. Kamar
almara jarumta ta yi mata lulluɓi, don cikin ɗan lokaci ta samu wani ƙarfin zuciya da nutsuwa suka sauka
jikinta.
Ta bar jikin ƙofar ƙirjinta yana harbawa ɓil-ɓil ta shiga zare kayan jikinta. Ta ɗaura towel kenan da nufin
shiga wanka, ta fara jin ana ƙwanƙwasa mata ƙofa. Kamar kada ta kula, don jikinta ya ba ta Jamal ne kuma
babu abin da zai faɗa ta saurare shi. Amma a haka wata zuciyar ta ba ta umarnin je ki buɗe ki ji me ya
kawo shi. Cikin ƙunar zuciya ta isa bakin ƙofar ta buɗe, abin mamaki babu Jamal sai matar da ta gani tsaye
ƙiƙam. Suna haɗa ido ta yi hanzarin juya bayanta tana kallon Jamal ta ce,

"Babe ka faɗa mata da kanka."

Da ido Minal ta bi Jamal ɗin da kallo tana jiran ta ji me za a faɗa mata. Daga can inda yake zaune ya yi
Magana cikin isa ya ce,

"Indomie take so ki dafa mata. Kuma kada ta yi yaji kada ki bar ta ta ƙame ruwanta ya tsotse."

Mamaki ya so kashe Minal a tsaye, bakinta a sake ta shiga ƙare wa Zee kallon sama da ƙasa riƙe da ƙofa a
hannunta. Kafin wani tunani ya faɗo ranta ta yi wani murmushin ba zata a kan fuskarta ta ce,

"Ok, yanzu ake so ko za a jira na yi wank...?"

"Je ki yi wankan. Ita ma za ta fi jin nutsuwar cin abincinki?"

Kafin ma ta kai ƙarshe ya ba ta amsa, tana ƙoƙarin mayar da ƙofar ta rufe Zee ta yi hanzarin daka tsalle tana
buga ƙafa cikin shagwaɓa ta ce,
"Babe, ni ba zan bari ta yi wankan ba ka ce ta je ta dafa mini a hakan yunwa nake j...."

"Ahhhh sorry sorry...je ki dafa mata ɗin kawai."

Ya yi maganar da murya biyu, ɗaya ta Zee cikin tattausa harshe. Yayin da ɗayar ta Minal ya sauya ta zuwa
kakkausa cikin tsare gida. Minal ta saki ƙofar ta fito tana taku a hankali daga ita sai towel ɗin da ke jikinta
iya cinya. Fuskarta babu babu fallasa ta nufi kitchen bom-bom suna juyawa, kasanacewar Allah Ya
albarkace ta da lafiyayyen ƙugu da cikar ƙirji daidai jikinta. Hakan ya sa Jamal ya bi bayanta da kallo cike da
mamakin ganin halittarta. Abin da ya saka shi kasa ɗauke ido a kanta don bai taɓa hangen surarta a fili ba
sai a ranar.
Zee ta fasa ihu saboda ita ma ganin halittar Minal ta raina tata halitta. Da rera waƙar kuka ta isa gare shi ta
faɗa jikinsa tana faɗin,

"Babe ni ba son indomin idan ba ta je ta saka kayanta ba."

"Ki bar ta a haka mene ne damuwarki?"

Ya Yi maganar cikin sanyin murya, saboda jikinsa ya mutu murus kuma ya shiga yanayin da komai ya
Zmzo masa a gaɓa.

"Warin hamata Babe, don Allah ka ce ta saka kayanta ni dai...uhum-uhumm Babe zan yi kuk.."

Jamal ya miƙe ya nufi kitchen ɗin cikin wani yanayi, don shi ma yana buƙatar sake ido biyu da Minal a
yadda take. Zee ta bi shi da kallo tana kumbura fuska cike da mugun jin haushinsa. Don kishin da take yi
masa ya sa ba ta so kowa ya raɓe sa sai ita, hakan ya sa ta dunƙule tana faɗin,

"Babe kada ka je ka dawo don Allah."
Ya juyo idonsa a lumshe ya yi mata wani kallo yana faɗin, "Ba kya so ta saka kayan ne?"

Zee ta sake magana cikin shagwaɓa ta ce, "Kawai ba na so ka gan ta ne Babe..plss ka zo ni zan yi mata
magana da kaina."

"Ok!"

Jamal ya yi maganar cikin murya ya dawo ya zauna yana shafa kansa ya rungumo ta jikinsa cikin sabon
yanayin da ya fara shiga jikinsa. Zee ta miƙe cikin sauri ta riƙo hannuwansa duka biyu ta jawo shi ya miƙe.
Sannan ta kwanta a ƙirjinsa tana faɗin,

"Ina son ka."

Kanta ya fara shafawa yana leƙen fuskarta ya ce, "Kin faye kishi, na faɗa miki ba matata ba ce, kuma babu
komai a tsakanina da ita. Yanzun ma don kin ce na je da ba zan so sake ganin fuskarta b..."

"Ba fuskarta ne ba na so ka gani b..."

Ta yi maganar cikin sauri tana turo baki, shi ma ya katse ta da cewa, "To mene ne?" Ya yi tambayar yana
hango bombom ɗin Minal a cikin idonsa.

"Bar Shi kawai tun da ba ka ga komai ba. Zo mu je ɗakinka na ma fasa Cmcin komai."

Ta ƙare maganar tana jan shi yana 'yar dariya ya bi ta suka shige ɗakin. Minal kam tsam ta yi da ranta
tana kallon indomin da ke tafasa siraci yana fita a cikin tuunyar ƙamshi yana tashi. Rungume da hannuwa a
ƙirji take tana cizon leɓenta, saboda duk abin da suka faɗa a kunnenta tana ji. Hakan ya saka ta ƙara samun
wani sabon darasin da ba a koya mata a gida ko makaranta ba.
Da murmushi a fuskarta ta nemo plate ta juye indomin ta rufe da wani plate tare da cokali mai yatsu a
sama, bayan ta soya mata faifai ɗaya na wainar ƙwai ƙwara biyu. Zuciyarta wasai ta fito daga kitchen ɗin ta
ajiye musu indomin saman dinning table. Sautinsu da ke tashi daga cikin ɗakinsa ya saka ta jin bugun
zuciya, cikin sauri ta koma ɗakinta hawaye yana zarya a kan fuskarta.
Ta ci kuka daren ranar kamar hawayenta ba za su kai safiya ba. Sannan ta kwana tana faɗa wa Allah
damuwarta da abin da take buƙata a wurin sa. Ruwan addu'o'in da ta zuba ta samu ƙarfin gwiwar ƙarfafa
kanta da zuciyarta a kan cewa Allah ya karɓa mata su duka. Baccin da ya ƙi zuwa idanuwanta ma tana tuno
ɗaya daga cikin ilmukan da Gwaggo Salame take ba ta tana yi ta samu nannayan barci mai daɗi.

'A duk lokacin da bacci ya ƙaurace wa idonki; ki karanta suratul Falaƙ uku, Nas uku da ƙulhuwallahu Ahad
ita ma sau uku. Da yardar Allah ba za ki kammala su ba ki fara jin barci ba. Wannan wani sirri ne da na riƙe
ina aiwatarwa a duk lokacin da damuwa ta aure ni. Ke ma ki riƙe duk tsananin damuwa matuƙar kika yi a
yadda na sanar da ke za ki yi barci har da minshari.'

"Tabbas na ga amfanin hakan gwaggo. Don ba don na yi ba da ba na jin takaicin abin da na gani da wanda
nake ji da kunnena yana faruwa su bar ni na runtsa."

Furucin Minal kenan a lokacin da ta farka sallar asuba. Domin kamar da gayya tana farkawa zuciyarta ta
hango mata Jamal da Zee rungume da juna. Ta jima bakin gadon zaune ɗauke da tagumi tana nazari kafin
ta miƙe ta yi sallah. A nan ma ta kai kukanta ga Allah kuma ta yi laziminta tsaf tare Ya wadudu ƙafa arba'in.
Sannan ta tashi cikin kuzari ta shiga gyaran ɗakinta har zuwa falo, bayan ta gama ta koma ta kwanta da
carbi a hannunta tana ja wani sabon barcin ya kwashe ta.
Misalin ƙarfe tara na safiya ƙwanƙwasar ƙofa ya tayar da ita. Cikin sauri ta sauko gadon tana ƙarfafa
zuciyarta a kan haƙuri har ta buɗe ɗakin. Ido cikin ido suka kalli juna kafin ya shiga shafa kansa cikin haɗe
rai ya ce,
"Baƙuwata tana jiran breakfast. Ta ce indomin jiya ta yi mata daɗi yanzu ma abincinki take son ci."

Cike da jarumta Minal ta gayyato murmushin ƙarfin hali ta ce, "Ayya! Ka ce ta jira ni kaɗan zan yi wanka
na fito."

Ta ƙare maganar har da 'yar dariya tamkar babu komai a cikin ranta. Jamal ya yi tsayar da kallonsa a
tsakiyar idanuwanta cike da mamaki, yana so ya yi wata magana amma ya kasa. Saboda girar da Minal ta
ɗaga masa tare faɗin,
"Ummm!" Alamun tabbatarwa ga zancenta. Ya juya yana waigen ta ba tare da ta sake cewa komai ba ta
juya ko rufe ɗakin ta kasa yi. Sai da ta sha kukanta a toilet sannan ta yi wankan a gurguje ta fito.

'Za ku ga tsiya.'

Abin da ta furta kenan a lokacin da ta shiga buɗe kayan lefen Nur tana zaɓen wasu ƙananun kaya cikin
sauri. Can ta hango wani mini siket baƙi iya gwiwa da wata jar riga half vest, wadda ake ɗaure ta gaba a
saki jelar a saman ciki. Cikin sauri ta shirya a cikin kayan babu shiri dariya ta ƙwace mata. Musamman a
lokacin da ta ga kanta jikin madubi tamkar wata Ingozi, duk da kayan sun hau jikinta ta yi mugun kyau.
Saboda tun da take a duniya ba ta taɓa shiga irin wannan ba. Asali ma ƙananun kaya ba su taɓa burge ta
ba. Ko kayan lefen da aka kawo wa Nur duk ta ɗaga kayan sai dariya ta zo mata a ranar da aka kawo lefen.
Saboda tunanin ta ya ya ita za ta iya saka su a jikinta, don har kullum tana jinjina wa Nur a kan yadda ba ta
jin nauyin shiga duk yadda ta ga dama, kuma ko a gaban waye ita babu ruwanta da ɓoye jikinta. Saɓanin ita
Minal da ba ta saba da hakan ba, kuma ba ta tashi ta ga ana yi a cikin unguwarsu ma ballantana a gidansu.
Har ganin take yi babu ranar da za ta iya shigar 'yan bariki a cewarta koyaushe.

"Ashe akwai ranar."

Zancen da ta yi kenan tana juya jikinta gaban madubin bayan ta saka wata hula mai kama da pesin cap
mahaɗin siket ɗin. Ƙwanƙwasa mata ƙofar da aka sake yi ta yi hanzarin fesa turaren Nur a jikinta har saman
hula, sannan ta maƙala passion ɗin ɗan kunne ja da baƙin agogo a tsintsiyar hannunta. Ta nufi ƙofar da
sassarfa ta buɗe fuskarta a sake tamkar wadda ke cikin matsanancin farinciki.

"Babe!"

Zee ta ƙwala wa Jamal kira saboda ganin Minal a yadda take ba ƙaramin firgita ta yi ba. A ruɗe ya iso wurin
yana ƙoƙarin tambayar lafiya ta faɗa jikinsa tana dukan ƙirjinsa a haukace tana faɗin,

"Zan mutu Babe idan ina ganin matar nan."

Haka ta dinga ɓarin sambatun da Jamal bai ma san tana yi ba, saboda hankalinsa da tunaninsa gabaɗaya
suna kan Minal. Tsabar mamaki da tashin hankalin da ya Yi masa dirar mikiya a saman ka. Saboda ƙamshin
turaren Nur da Minal ta saka zuciyarsa ta shiga birbration. Nan take ya tsinci kansa a cikin wani yanayi
mara misali, don Minal ba ta bar shi da iya turaren da shigar ba, sai da ta haɗa masa da kanne ido ɗaya
tare da fari da ido tana cizon leɓenta kafin ta koma yi masa wani kallon ƙasan ido tana jingine jikin ƙofar
rungume da hannuwanta a ƙirji. Da ma ta ga halin da yake ciki ta ƙara masa da juyi a gabansa tamkar
tarwaɗa, tana shafa jikinta da lasar baki cike da ƙwarewa a kan zama gogaggiyar 'yar duniya.

Ƙaƙƙarfan dukan da Zee ta kai masa a ƙirji hannuwa biyu ta tura shi, hakan ya saka shi yin baya ya faɗi ƙasa
daɓas babu shiri. Amma hakan bai saka shi ɗauke kallon sa a kan Minal ba, tamkar wani sakarai ya saka
hannu ya janye Zee da ke gabansa tana masifa, tsabar kishi ya saka ta ƙaramar hauka.

Miƙewa ya Yi jikinsa yana rawa ya isa gaban Minal yana muzurai tare da saita kansa cikin ƙarfin hali ya
ce,
"Je ki sauya kayan jikinki ba na buƙatar sake ganin ki da su."

Sai a lokacin Zee ta daina surutai da kukan da ta ja gefe tana yi. Saboda jin daɗin zai rama mata
wulaƙanci da cin zarafin da Minal take son yi mata a fakaice. Don surar jikinta ko ita da take mace ta ƙyasa
ballantana shi a matsayinsa na namiji

11 / 29